WANDA A KA GABATAR A TARON TALLAFAWA MARAYU A GARIN KUDAN A ZAUREN TARO (TOWN HALL) DAKE LIKORO ROAD SABON GARIN KUDAN. RANAR LAHADI12GA YUNI 2016, 7 GA RAMADAN 1437 DA ƘARFE 10: 00 NA SAFE.
ƊA NA KOWA NE: TSOKACI A KAN AL’ADAR RIƘO/GOYOA
RAYUWAR BAHAUSHE JIYA DA YAU
DAGA:
MU’AZU SA’ADU
MUHAMMAD
DEPARTMENT OF
LANGUAGES
SULE LAMIƊO UNIƁERSITY KAFIN HAUSA, JIGAWA STATE
1. 0. 0 GABATARWA
Da sunan Allah Mai rahama, Mai jinƙai, Mai kowa, Mai komai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga shugaban ma’aika, Annabi Muhammadu (S. A. W). Wannan muƙala, na da ƙudurin yin tsokaci a kan al’adar riƙo ko goyo da matsayinsa a rayuwar Bahaushe jiya da kuma yau. Haka kuma tare da fito da irin sauye-sauye da rayuwar Bahaushe ta samu dangane da al’adar. Bayan haka, za ta dubi dalilan da suka kawo waɗannan sauye-sauye. Ba zan yi ƙasa a gwiwa ba wajen nuna fa’idojinriƙo da kuma sakamakon da yakan haifar ga mai yin sa da kuma al’umma gaba ɗaya. A wannan nazari, zan dubi riƙo ta ƙusurwowi uku kamar haka: A Mahangar Addinin Musulunci, damahangar Al’adar Bahaushe, sannan ta Mahangar Zamani. Bisa wannan dalili ne yasa na yi wa wannan maƙalar take da “Ɗa Na kowa Ne”. Na kawo taken a matsayin matashiya ne, don ya ba mu damar lalubo mafita. Tare da fatan mai karatu ko saurare zai gano saƙonda akeson isarwa a ƙarshen maƙalar, don samun mafita ko a fid da jaki a duma.
1.
1 FASHIN BAƘI
1.
2. Ma’anar Ɗa: na nufin abin da
aka haifa mutum ko dabba ko wata halitta, ii. Wanda ba bawa ba. iii. ɗan gida watau farin
maciji wanda ba ya cutar wa[1]
1. 3. Ma’anar
Riƙo: Riƙo/goyo
shi ne wani mutum ya riƙe ɗan wani tun
daga (yaye) yarinta har zuwa girma. Idan yaro namiji ne a wasu wuraren akan
mayar da shi gidan ubansa, in kuwa mace ce da zarar ta isa aure, to daga nan
goyo ya ƙare kenan. Riƙo/goyo a kan
yi shi ne a tsakanin ɗan uwa da ɗan uwa, ko
kuma aboki da aboki.
2. 0. IRE-IREN RIƘO:
Ɗan yaye, ko
‘Yar yaye: A ɗauko yaro daga yaye a riƙe shi har ya girma
Ɗan karo, ko
‘Yar karo: A ɗauko yaro daga zaman ɗaki na amarci a riƙe shi har ya girma
Ɗan aro, ko
‘Yar aro: A ɗauko yaro daga rakiya zuwa unguwa a riƙe shi har ya girma
Agola: A auro uwar yaro ta zo da shi gidan sabon mijinta a riƙe shi har ya girma.
Bara ko Yaro. : A ɗauko yaro ya rinƙa yin aiki ko
hidima a riƙe shi har ya girma
Na wucin gadi: A ɗauko yaro a riƙe shi na wani
gajeren lokaci a mayar da shi.
Na dogon lokaci: A ɗauko yaro a riƙe shi har ya girma
da ya isa aure a mai da shi
Na dindindin: A ɗauko yaro a riƙe shi har ya girma
a yi masa aure ya zauna a gidan.
3. 0. 0 RIƘO
A MAHANGAR AL’ADAR BAHAUSHE
Riƙo
a mahangar al’ada, ana iya cewa wata ɗabi’a ce muhimmiya.
Wannan yasa gaba ɗaya al’adar
Bahaushe take ƙaunar riƙo a da,shi
kuma mai yi riƙo ana kiransa Uban goyo, ko uban gida, ko
uban riƙo. Idan kuma mace ce akan ce mata uwar ɗaki, ko uwar
goyo, ko mariƙiya. Tabbas mutum mai ɗaukar nauyin
jama’a na da farin jini da kwarjini da mutunci a cikin al’ummar Hausawa. Matuƙar
aka san mutum gidansa cike da jama’a mai rungumar kowane. To a wani lokaci har ƙoƙarin
kusantarsa ake yi kamar auren zuriyarsa ko kuma shi a ba shi auren.
3. 1. ZAMANTAKEWAR
BAHAUSHE A DA:
Zaman Gandu: Wani zama ne
da ake yi, a inda za a iske gida na ƙunshe da
kaka, da uba da uwa (mata ko matansa) , da ɗa da matarsa,
da jikoki duk a gida ɗaya ga ɗakin wannan ga na
wannan. A wani lokaci ban da ‘ya’yan tsatso, ga ‘ya’yan riƙo, ga agola,
ga ya kamata har barori. A irin wannan zama yana kasancewa komai tare ake yi.
Da damuna za a tafi gonar mai gida da ake kira gonar gandu a wurin aiki. Bayan
an dawo, maigida ne zai ciyar da kowa, ko da kuwa ɗansa yana da
mata da ‘ya’ya, dole shi ne zai ciyar da su. Irin wannan rayuwa tana da daɗi matuƙa,
domin ana taimaka wa juna a harkokin rayuwa ta fuskoki da yawa. Ba a farga ba,
zamani ya zo ya yi tafiyar ya ji da wannan ɗabi’a. Musamman
samuwar aikin gwamnati, a inda za a ɗauki mutum ya koma wani garin da ba
nasa ba, ko kuma ko yana gari, sai ka iske ya ware gidansa shi kaɗai wai kar a
dame shi. A nan ne ake rayuwa irin ta daga ƙwauri sai
gwiwa, ko kuma mu ce ba ruwan wani da wani wai mahaukaci ya yi baƙo.
3.
2. DALILAN DA KAN SANYA A YI RIƘO:
Ana yin riƙo ne saboda
wasu dalilai da suka haɗa da: -Ƙarfafa
Zumunci. Kwaɗayin Haihuwa.
Ƙauna. Tausayi. Moriya. Aure Agolanci/Kolo.
Tabanni. Mutuwar aure,saki, ko fita, ko rabuwa, jinginar aure. Maraici, mutuwar
uwa ko uba (talle da audi)
1. ƘarfafaZumunci: - Riƙo/goyo
yana da muhimmanci mai yawa ta wajen ƙarfafa danƙon
zumunci, saboda za ka samu wa ya kama ɗan ƙanin
shi ko ɗan ƙanwar
sa ya riƙe tun daga yarinta har zuwa aure. Sau da yawa
wani riƙon kan fara ne tun daga yaye, watau lokacin
da aka cire yaro daga mama, nan ma ya fi faruwa ne a tsakanin 'yan uwa kamar
kaka, koyar uwa, ko uba. Wannan al'ada ta kan ƙara ƙarfafa
zumunci, don kuwa ta kan faru in ka samu wani gida inda ake riƙon
wani yaro ba za ka iya bambance ɗan gidan da ɗan riƙo
ba, zaka gan su babu wata wariya, komai nasu ɗaya ake yi
musu. Su ci abinci tare, kai har ma suturar su bai ɗaya ta ke,
wannan kan ƙara ƙulla zumunci.
2. Kwaɗayin Haihuwa:
-
A wata fuska kuma, a kan ɗauki riƙo/goyo ne don
kwaɗayin samun
haihuwa. Kamar yadda waɗansu Hausawa musamman ma mata kan canfa cewar
in mutum baya haihuwa, to kuwa in ya ɗauki goyo, Allah Zai
bashi nashi. Hakanan kuma wasu don rashin haihuwa, sai su ɗauki goyon
don su rinƙa samun na aike. A ƙarshe akwai
masu ɗaukar yara
don sabo, misali in sun aurar da yaran su, to don ɗauke kewa sai
su ɗauko wani.
3. Ƙauna:
-
Baya ga waɗannan, akwai
kuma masu ɗaukar goyo
don ƙauna, kamar inda za ka ga cewa wasu mutane na
ɗaukar goyo ne
kawai don ƙauna, wayau soyayya. A wani halin babu dangin
iya babu na baba, ma'ana babu dangantakar komai sai dai aminci irin na abotaka.
Misali aboki da aboki, ko maƙwabci da maƙwabci,
in da zaka tarar ɗaya ya kama
yaron ɗaya ya riƙe,
babu bambanci da nashi, wani lokacin ma har ya kan fififta shi a kan waɗanda ya
haifa.
4. Tausayi: - Riƙo/goyo
a kan yi shi a wani lokacin don tausayi, misali in wani mutum ya ga wani yaro a
wani matsayi na wahala, to don tausayawa yana ɗaukar shi ya
riƙe, ko da ace yana tare da iyayen sa ne kuwa.
Akwai ma in da za ka tarar ana riƙon yaro ko
yarinya, sannan kuma ana taimakawa su kan su iyayen a lokaci guda. A wata fuska
kuma, zaka samu an riƙe almajiri don
tausayawa, misali in almajirin ƙarami ne zaka
samu ya yi uwar ɗaki wadda zai
riƙa samun taimako na abinci ko sutura a wajen
ta. Haka kuma akwai waɗanda uwarsu ta mutu ta bar su a tsumma, watau
'talle' kenan, su ma don tausayi a kan ɗauke su a riƙe.
5. Moriya: - Akan yi riƙo/goyo
don moriya a inda za ka samu an ajiye bara ko yaron gida yana yi wa mutanen
gidan hidima, watau kamar dai mai aiki kenan. A kan samu mai yin hidima wani
tun yana yaro har girmansa, koda mace ce ko namiji. Sannan kuma akwai wasu mau
yin sana'a da sukan mallaki barori masu kula da harkokin kasuwanci, su ma wasu
tun daga yarinta har zuwa tsufa; har ma wani lokacin su ma Su samu su kafu su
yi ƙarfi su samu abin hannun su.
6. Aure (Agola/Kolo) :
- Riƙo/goyo
Agola ya kan faru ne in aka auro mace mai ɗa ko 'ya, su
ne a kan kira su da sunan Agola ko Kolo. A bisa al'ada irin ta Bahaushe, riƙon
agola ya kan zama dole ne, misali in uban yaron ko yarinyar ya mutu, ko kuma
dangin uban yaron ba su a garin, ko kuma yaron bai yi girma ba, su kansu dangin
uba basa son a tafi da yaron su wani gida ya zama agola, don gudun wulaƙanci
ko kuma raba shi da 'yan'uwa. Shi ne yasa waɗansu duk
juyin da za a yi ba za su yarda a kai yaronsu wani gida ba, har ma in mace ta
fita, to sai a yaye yaron, a nemi wani a cikin dangin ya ɗauka don
kawai ana ƙyamar Agolanci.
Tabanni: Wannan riƙo/goyo
akan yi shi ne a wani lokacin don tausayi, ma'ana shi ne in wani mutum ya ga
wani yaro a wani matsayi na ƙaƙa
–ni- ka –yi, komaraici. To don tausayawa, ko da a ce yana tare da iyayensa ne,
ko kuma maraya. Akwai ma inda za ka tarar ana riƙon yaro ko
yarinya, sannan kuma ana taimakawa iyayensu a lokaci guda. Bayan wannan, sai
kuma a wata fuska, inda za ka samu an riƙe almajiri
don tausayawa, misali in almajirin ƙarami ne, za
ka samu ya yi uwar ɗaki wadda zai riƙa samun
taimako na abinci, ko sutura. Haka kuma akwai waɗanda uwarsu
ta mutu bayan haihuwa, watau talle, su ma don tausayi akan ɗauke su, ko
da babu dangantaka, ko kuma yaron da aka tsinta. To amma kuma, daga ƙarshe
sai a mayar da su kamar ‘ya’yan tsatso, watau za su iya gadon mai riƙonsu.
A wani lokaci akan kira irin wannan goyo da goyon hankaka mai da ɗan wani naka.
Ko da yakemusulunciyahanairinwannanriƙon,
tundagakanZaidu.
3. 3. SAUYIN RAYUWAR
YARO:
Sauyin yanayin rayuwa kan yi tasiri ga
rayuwar yaro ta hanyoyi da yawa, kamar tun daga jikinsa watau girmansa,
lafiyarsa, ko hankalinsa kai har da tarbiyyarsa. Bahaushe ya yi imani cewa
sauyin rayuwa wanda ya faru ta sanadin maraici ko talauci ko kuma kaɗaici kan yi
tasiri ba kaɗan b a ga
yaro, ko da yake wani tasirin na gajeren lokaci ne, in yaro ya girma sai ya
yanke, amma kuma wani tasirin na har abada watau din-din-din. Ko da yaro ya
girma ya riga ya yi masa illa.
3. 4. TASARIN YANAYI (MATSAYI)
GA RAYUWAR YARO.
Yanayi ko matsayin da yaro ya samu
kansa a ciki, kuma ya rayu sukan yi tasiri ga rayuwarsa, tun daga kuruciyarsa
har girmansa. Tun daga iyayensa da suka raineshi, ko kuma makamantansu watau
iyayen goyo ko mariƙa, ko kuma maraici na
rashin iyaye, ko talauci ko wadata, ko kaɗaici. Domin a san
yaro da kwaikwayo.
IYAYE (MAHAIFA). Matsayin
rayuwa da iyaye ke ciki, kamar idan masu wadata ne, watau suna da arziki, yaro
kan samu sauyin rayuwa, wadda kan yi tasiri har girmansa. Haka kuma idan iyaye
matalauta ne, wato waɗanda basu da abin hannu (kuɗi) nan ma
yaro kan samu sauyin rayuwa. Game da iyaye masu ilmi ko sarauta nan ma yaro kan
samu tasiri a rayuwarsa, su kuma iyaye jahilai ko matalauta nan ma yaro kan
samu tasiri ga rayuwarsa.
IYAYEN GOYO. Iyayen goyo
na nufin waɗanda suka
goyi, ko riƙe yaro waɗanda basu
suka haifeshi ba sai dai a dalilin auratayya, kamar agola wanda aka auro
uwarsa, ta zo da shi gidan. Wasu kuma a dalilin zumunta watau 'yan riƙo.
Su ma matsayinsu na rayuwa kan yi tasiri ga yaro har girmansa.
MARAICI. Maraici wata
rayuwa ce dake samun yaro, wanda ya rasa wani daga cikin iyayensa, uwa ko uba,
ko kuma dukansu akan kiran yaro da maraya yarinya da marainiya, jam'i marayu. Wannan
rayuwa kan yi tasiri ga yaro ta fuskoki da yawa kamar haka: wasu yaran sukan
tsumbure watau su ƙi girma, wasu kuma su
fanɗare su gagara
su watse.
TALAUCI. Matsanancin
talauci kan takura rayuwa wanda kan hana gudanar da rayuwa yadda ya dace.
Wannan kan shafi rayuwar yaro, kamar ƙarancin ko
samun cikakkiyar tarbiyya. Rashin girma da wuri watau tsauri ko tsumburewa. Ko
da yake in aka yi sa'a wasu yaran matalauta sukan shiryu, fiye da 'ya'yan
mawadata.
WADATA. Wadata na
samar da walwala a rayuwa wanda kan sanya mutum ya samu abubuwan buƙata
na rayuwar yau da kullum, wannan kan yi tasiri ƙwarai ga
rayuwar yaro ta fuskar samun tarbiyya da saurin girma, saboda ƙoshi.
Ko da yake in kuma aka yi rashin sa'a wasu yaran mawadata tarbiyyar su bata yin
kyau, maimakon su gyaru sai su lalace, saboda gata yayi yawa. Amma kuma wasu
sukan shiryu ka gansu natsattsu.
KAƊAICI.
Kaɗaici na nufin
zama a ware, ba a cikin jama'a ba. Akwai rayuwar kaɗaici iri uku
kamar haka: 1. Goyon gwauro. 2. Goyon mace. 3. Goyon kaka.
1- GOYON GWAURO: Gwauro na
nufin mutumin da ba shi da mata a dalilin mutuwar aure bisa sanadiyyar saki, ko
mutuwar matar. Da zarar aka ce namiji na riƙo ko goyon
yaro, akan samu mtsaloli game da tarbiyyarsa, saboda shi zai fita neman abinci,
tun safe ƙila ba zai dawo gida ba, sai dare to don haka
uwa ko wata matar da zata tarbiyyartar da shi ko tsawata masa. Wannan kan yi
tasiri, sosai ga rayuwar yaro. Shi ya sa Bahaushe kan ce wane kamar goyon
gwauro, kana yin abu ba kwaɓa kamar goyon gwauro
2- GOYON MACE: Duk matar da
ba ta da miji, a al'adar Bahaushe na ganin ba cikakkiyar mata ba ce, kuma ba ta
da ƙima. Goyon mace na nufin mace ta riƙe
yaro ko yarinya ba tare da ita matar tana da miji ba. Rayuwa tana da wani
matsayi mai kama da wuƙa balatti mi kaifi
biyu, duk inda ya dakushe, to dole ne a samu cikas. Ya zama wajibi, kamar yadda
gwauro ya samu matsala wajen tarbiyyar yaro a dalilin rashin mata, to haka ita
ma mace a dalilin rashin namiji ko miji da zai tsawatar dole ne a samu matsala.
Wannan tunani ko kallo da Bahaushe ke yiwa riƙon
mace da cewa mai rauni ne, kamar wata Karin Magana mai cewa “ wance ai 'yar
mace ce” “me za'ayi da gayon mace”
3- GOYON KAKA. Kaka na nufin
mahaifan iyaye mace ko namiji. Akwai kaka na wajen uwa waɗanda suka
haifi uwa namiji ko mace. Akwai kaka na wajen uba waɗanda suka
haifi uba, mace ko namiji. Gayon kaka na nufin kakanni su ɗauko yaro a
dalilin yaye ko haka kawai su riƙe shi ya
girma.
Wannan yanayi kan yi tasiri ga rayuwar yaro
gaba ɗaya a dalilai
kamar haka:
I. Da farko dai kakanni na son jika,
kuma bas a son abin da zai ɓata masa rai, wannan zai sanya a ƙi
yi masa faɗa wanda a ƙarshe
sai yaro ya sangarce.
I. I Dalili na biyu, shi ne gata zai
yi masa yawa don kuwa dukkan abin da ya so zai samu sai ya zama shagwaɓaɓɓe.
III. Dalili na uku shi ne jika dama
shi ba ya tsoron kakanni, saboda suna yin wasa da, to ko da sun yi masa faɗa ba zai ɗauka da gaske
ba ne sai ya zaton wasa ne don haka tarbiyya zata samu cikas, a ƙarshe
sai yaro ya lalace. Wannan yasa Bahaushe ke cewa:
“wane goyon kaka ne”, “kaka ke ɓata jika,
jika wahal da kaka”“sangartacce goyon kaka”.
4.
0. 0 MA-BA-DA HALI YA RIGA MAHORI:
A wasu lokuta Bahaushe kan ɗorawa mariƙi
ko uwar goyo laifi idan yaro ya lalace, alhali kuwa abin ba haka yake ba. A
wani lokacin akan samu saɓanin haka, a inda mariƙi
ko uwar goyo zasu yi iyakar ƙoƙarinsu,
amma abin ya gagaresu. An fi zargin mace uwar goyo, ko kakanni da irin haka,
bayan kuwa akwai wasu dalilai da kan haifar da haka. Misali:
4.
1. YARO DA ƘWAZO/JARUMTA: Ƙwazo /jarumta
na nufin dagewa da jurewa duk wata kwaramniya ta rayuwa da ta tasowa mutum tare
da rashin tsoro ko razana, mai wannan hali ana kiransa da jarumi ko gwarzo.
Kowacce irin rigima ce ta fuskanto shi ba zata razana shi ko kaɗa masa zuciya
ba. A kan wannan akwai wasu karin maganganu irinsu “Jure kwaram sai goga” “Faɗuwar gaba
asarar namiji” “Namiji matsotsin ƙarin kunama”.
Bahaushe na ganin cewa jarunta a wurin yaro kashi-kashi ce, ko matsayi-matsayi
ne, ya danganta da wasu dalilai kamar haka: -Dalilingado, ko baiwa,ko
muhalli,ko yanayi/hali,ko Bambancin jinsi,ko mu'amulla,ko yanayin shekaru.
GADO: Bahaushe ya
yi imanin cewar yaro na iya zama jarumi ta dalilin gado, ma'ana dai yaro na iya
gadon jarumta daga wurin iyayensa uwa ko uba, a wani lokaci kuma har daga
kakanni har zuwa zuriyyarsu. Bisa wannan yasa in wani mutum gwarzon maza ne,
sai aka samu wani ɗansa ko jika mai jarumta, sai ace ai ba
mamaki, kamar wasu karin maganganu masu cewa: “Harbi ga ɗan jaki gado”
“Haifi ka ga kamarka” “Barewa ba ta gudu ɗanta ya yi rarrafe”,
da sauransu.
BAIWA: Bahaushe na
ganin cewa yaro na iya zama jarumi a dalilin baiwa daga Allah, watau don kyauta
daga Allah, saboda a wani lokaci za ka ga ana iya samun yaron da zai zama
jarumi ba tare da ya gada daga iyayensa ba, sai don kawai kyautar Allah. A irin
wannan ne Bahaushe kan ce: “ƙuda ya haifi
zuma” “Maba da hali ya riga mahori” ko “Tun ran gini ran zane”.
MUHALLI:
Bahaushe
na da tunanin cewa yaro na iya zama jarumi bisa dalilin muhallin da ya samu
kansa a ciki, kamar gida, unguwa, ko gari. Yaro idan ya tashi a gida, ko
unguwa, ko garin da ake da jarumai, shi ma da sannu zai ɗauki halin,
ya zama jarumi. Yaron da ya saba tarewa kansa faɗa ko. alama
ce ta jarumta, wanda ba a koro shi gida, sai dai a kawo ƙararsa cewa
ya doki wancan da sauransu.
YANAYI/HALI: Yaro na iya
zama jarumi a dalilin yanayi ko halin rayuwar da iyayensa ke ciki, kamar
maharba, 'yantauri, fatake, mayaƙa da
sauransu. Yaro na iya zama gwarzo kuma gagararre, domin ganin yau da gobe irin
halin da iyayensa suke ciki, ko kuma iyayen su bashi wasu magunguna ko 'yan
sauyoyi don ya shiryu. Kamar irin su hankufa, kaimin ƙadangare da
sauransu.
MU'AMULLA:
A
ɗabi'a irin ta
ɗan Adam
Bahaushe na ganin cewa yawan mu'amulla watau irin cuɗanya da
jama'a iri daban-daban na iya sanya yaro ya zama jarumi, saboda irin
gwagwarmayar da yake yi yau da kullum, tun yana tsoro ko gajiya, to wataran shi
zai yi jagora, saboda ya dake. Zuciyarsa ta dake shi ma ya zama goga ba sauran
tsoro.
BAMBANCIN
JINSI:
Bahaushe na da ra'ayin cewa, a kan samu jarumta a dalilin bambancin jinsi.
Domin a al'adance an fi samun jammi a maza, don haka ne tun yaro na ƙarami
a kan nuna masa ko sanya masa wannan tunani, ko ra'ayi, a inda in yaro namiji
ya faɗi sai ace:
“Kar ka yi kuka kai namiji ne” Ko “haba wane ai jarimi ne” ko ace “Kar ka yi
kuka, kai namiji ne” ko ace “Yaya kake yin abu kamar mace”. Amma kuma a kan
samu wasu mata jarumai har su fi wasu mazan, irin wannan sai a rinƙa
cewa: “Wance ai mace ce mai kamar maza kwari ne babu”. Watau ana nufin jaruma
ce.
YANAYIN
SHEKARU:
Bahaushe na ganin cewa yaro na iya zama jarumi gwargwadon shekarunsa, wani yaro
tun yana ƙarami a cikin sa'o'insa tsararrakinsa baya taɓo, kuma babu
mai kayar da shi idan suka kokuwa, haka kuma zai yi wuya wani tsaransa ya sa
shi kuka. Wani yaron yana ƙara shekaru
yana ƙara zama jarumi, kuma sai ya zama saurayi na
yake gagara.
4.
2. YARO DA RAGWANCI
Ragwanci na nufin gazawa, ko kasawa,
ko lalaci. Ragwanci kishiyar jarumta ne. Ana kiran mai wannan hali da cewa
rago, ko malalaci, shi kuma kishiyar jarumi ne, domin rashin jarumta ke haifar
da ragwanci. Da zarar aka ce yaro ba ya ƙulla abin ƙwarai,
ko kuma malalaci ko matsoraci, ba zai iya ƙwatar kansa
ba, ko da ga tsararrakinsa.
Bahaushe na ganin cewa ragwanci a wurin yaro
kashi-kashi ne, ko matsayi-matsayi, ya danganta ne da wasu dalilai kamar haka:
-. Dalilin gado, ciwo, muhalli, yanayi/hali, mu'amulla, bambanci jinsi, yanayin
shekaru
GADO: A al'adance Bahaushe na da
tunanin cewa yaro na iya gadon ragwanci daga iyayensa uwa ko uba, a wani lokaci
ma har daga kakanni ko zuriyyarsu. Wannnan tunani ne ya haifar da wata karin
magana mai cewa: “wane bai yar a ƙasa ba” ko
“magaji mafiyi” ko “haifi ka ga kamarka”.
CIWO: Bahaushe na ganin cewa yaro kan
zama rago bisa dalilin kamuwa da wani ciwo kamar ciwon iskoki, ko kuma sanadin
wani ciwo mai zafi ko ciwon fara, ko tamowa, ko soki. Wasu yaran sai bayan sun
warke ne, sai su zama masu son jiki a sakamakon jinya, sai su ɗore da lalaci
har ya zama jikin su zama ragwaye.
MUHALLI: Bahaushe na jingina wa
muhalli nauyin yin tasiri ga rayuwar yaro gaba ɗaya, wannan
ya haɗa da
ragwanci. Yaro na iya zama rago a bisa ga irin muhallin da ya samu kansa a
ciki. Kamar yaron da ya rayu a gida, unguwa, ƙoƙarin
da yake gani da azama ko kuzari, to shi ma zai zama haka. Saboda yau da kullum.
YANAYI/HALI: Ana iya samun yaro rago,
saboda irin yanayi ko halin rayuwar iyayensa, kamar talauci, sana'a. Idan
iyayen yaro basu da abin hannunsu, amma kuma basa yin komai, amma kamar
mafarauta, ko manoma, zai yi wuya yaransu su zama ragwage, saboda irin horon da
suke samu. Amma yara masu wadata ko jinin sarauta musamman waɗanda suke
birni wasu sukan zama ragwage dan yawan hutu da ƙoshi kuma
babu motsa jiki.
MU'AMULLA: Bahaushe na ganin cewa
mu'amulla da wasu mutane na yin tasiri ga mutum, don haka ƙarancin hulɗa da jama'a
na iya mayar da yaro ya zama rago. Duk wanda ke yin kasuwanci, ko wata sana'a
yana kaiwa yana dawowa kai ko a zaune yake matuƙar zai yi hulɗa da wannan
ko wancan, dole ne ya sanya shi ya zama jarumi, don haka rashin yin haka na iya
zamar da mutum rago.
SHEKARU: Bahaushe na ganin cewa, yaro
na iya zama rago na ɗan wani lokaci watau daga yaye zuwa a yi masa
kaciya, domin in ya girma zai sanya ya zama jarumi. Ko da yake a kan samu wasu
tun suna ƙanana har girmansu, ba sa son su motsa
jikinsu don haka a kan ɗauke su a matsayin malalata ko ragwage.
4.
3. YARO DA SHAGWAƁA KO SANGARTAKA
Shagwaɓa ko
sangartaka na nufin lalacewar tarbiya ko rashin kwaɓa, ko yaron
da ya taso a gaban iyaye da ba sa son yiwa yaronsu faɗa, a
sakamakon haka yara kan tashi da wannan ɗabi'a. Idan yaro
namiji ne sai ace masa shagwaɓaɓɓe ko
sangartacce, in yariya mace ce sai ace mata shagwaɓaɓɓiya ko
sangartacciya.
Dangane da haka Bahaushe ya ɗora wannan
bisa wasu dalilai, ko yanayi da kan jawo yaro ya zama shagwaɓaɓɓe, ko shagwaɓaɓɓiya. Akwai
dalilai masu alaƙa da matsayi, ko halin da iyaye suka samu
kansu ko kuma muhallin da yaro ya tashi. Waɗannan dalilai
sun haɗa da: -
'Ya'yan fata, da 'Ya'yan tsofaffi, da ɗan fari, da ɗan Auta,
daGoyon kaka, da 'Ya'yan wabi, da ɗan so.
'YA'YAN
FATA: Bahaushe
na nufin 'ya'yan da iyayensu ba su samu haihuwa da wuri ba, a dalilin son ɗa, sai su yi
ta yin addu'a cewa Allah Ka bamu ɗa kowane iri ne waɗannan 'ya'ya
su ake cewa 'ya'yan fata, ko 'yan Allah bani. Wannan so da suke yiwa ɗa kan hanasu
yi masa faɗa sai su ƙyale
su, suce kar a matsa musu. Bisa wannan dalili ne ya kan sa yara su tashi ba kwaɓa har su
sangarce, kuma duk abinda suke so iyaye zasu yi musu.
'YA'YAN
TSOFAFFI: A
al'dance Bahaushe ya ɗauka cewa idan mutane suka daɗe basu samu
haihuwa ba, sai daga baya, ba kuma tare da sun yi fata ba, ko kuma sai da suka
daɗe da barin
haihuwa, sai kwaram suka haihu to sukan ɗauki so su ɗorawa yaron.
Irin wannan soyayya na sanya yaro ya zama shagwaɓaɓɓe abu kaɗan ya kama
kuka in kuma ya girma ya sangarce, bai iya ƙulla komai ga
kansa balle waninsa.
ƊAN FARI: Al'adar
Bahaushe na kallon yaron da aka fara haihuwa a wurin iyayensa da cewa ɗan fari. Haka
kuma a kan jingina wauta ga ɗan fari. Wasu iyayen sukan tsawatarwa
da yaro ga wasu abubuwan da yake yi sai ya gyaru, amma wasu iyayen saboda su ma
sabon shiga ne, da kuma son ɗa sai ya sanya su ƙi
tsawatar masa, to a dalilin haka sai yaro ya zama shagwaɓaɓɓe.
ƊAN AUTA: Bahaushe na
ganin cewa ɗan auta shi
ne yaro na ƙarshen haihuwa, wasu iyayen kan ba yaron
gata, ba sa kwaɓarsa, basa
son abin da zai sashi kuka. Bisa wannan sai kawai yaro ya tashi da shagwaɓa, saboda
yadda ya ga iyayen na son sa. Don haka, sai ya ga kamar yayi dai-dai ne.
GOYON
KAKA:
Wani tunani da Bahaushe ke da shi game da yaron da ya girma a hannun kakanninsa
na dangin uwa ko na uba, a kan kira shi da goyon kaka ko riƙon
kaka. Yaron kan tashi ba kwaɓa ba tsawatarwa don haka zai zama
shagwaɓaɓɓe. Bisa
wannan har wata karin magana ake da ita mai cewa: “Kaka ke ɓata jika” ko
“Jika wahal da kaka” ko “Goyon kaka goyon banza”.
ƊAN WABI: Akwai kuma
wani ɗan da kan
zama shagwaɓaɓɓe, bisa
dalilin kasancewarsa ɗan wabi, watau waɗanda iyayensa
yaran su ba sa zama, da uwar ta haihu sai su mutu, to idan yaro ɗaya ya rayu
sai su ɗauki so su ƙwallafa
a kansa ba sa yi masa faɗa, ba sa son a yi masa. Wannan kan
haifar da lalacewar yaro.
ƊAN SO: Bahaushe na
nufin cewar duk ɗan da ya taso
ko da a gaban iyayensa ne, sai aka nuna masa so fiye da ƙima bisa wasu
dalilai da suka haɗa da: -
1. Uban na matuƙar son ɗa namiji, Uwa
na matuƙar son 'ya mace
3. 'Ya'ya masu sunan kakanninsu (
Babangida, Abba, Momi, Ummi)
4. 'Ya'ya masu shiga rai daga Allah (
'ya'yan mowa, 'ya'yan amarya)
5. 'Ya'ya masu hazaƙa,
ko biyayya. Ɗa ɗaya ƙwal a wurin
iyayensa
A ƙarshe ana iya
fahimtar cewar shagwaɓa ko sangarta ga yaro kan yi na da dalilai
masu dama, kuma kowanne da irin nasa yanayi ko fuskar da ya kan yi tasiri ga
rayuwar yaro. Matuƙar yaro ya samu
sakaci a wajen lura da tarbiyarsa, lallai ne zai zama shagwaɓaɓɓe, ko
sangartacce, haka kuma wasu ya kan zarce har ya zuwa girma.
5. 0. 0 RIƘO
A MAHANGAR ADDININ
MUSULUNCI:
Riƙo a mahangar
addinin musulunci, ana iya cewa wata ibada ce mai matuƙar
muhimmanci. Wannan yasa gaba ɗaya addinin musulunci ke kwaɗaitar da
al’ummar musulmi kan yin riƙo, saboda
taimako ne. Allah Subuhanahu Wata’ala Yace: Ta’awanu
alal birri wattaƙawa, wala ta’awanu alal ismi wal udduwan. Ku yi
taimakekeniya a kan aikin alhairi da tsoron Allah, kar ku yi taimakekeniya a
kan saɓon Allah da ɓarna da ƙetare
iyaka. Bayan haka akwai ayoyi da yawa da suka yi umarnin ko kwaɗaitar da riƙo
na yaro mai uba ne, ko maraya.
5. 1. HAƘƘIN MARAYA A KAN
WALIYYIN SA.
Waliyinmarayashi ne, ɗanuwanuba (danginuba) wako ƙani, idanbabukuma,
ɗan uwanuwa (danginuwa).
Dukiyar da marayayagadanwajibi ne a sanya ta hannunwaniwaliyyinsawandazaitsare
ta yalura da ita. Wannanwaliyyishi ne zairiƙa ɗaukarnauyinsawajenciyarwa, tufatarwa da tarbiyantarwa,
wannanya haɗa har da ilimi.
An sharɗantacewa a rinƙa juyakuɗin don gudunkarzakka ta cinye, a bisawannan ne shari'a ta
tsarawaliyyinmarayanaiyaamfani da kuɗin marayan nan
idanbamaiwadataba ne. ammakaryayi da ɓarna.
Wajibi ne waliyyinmarayaya aurar da
yarinya/marainiya in ta isaaure, kumaya bi wasiyya da mahaifiyabari,
kokumayashawarce ta, ammabazaiyimataauren dole ba. In yakasancemaraya ne,
wataunamijiidanyabalagayakawo ƙarfi, yazamamaihankali, to sai a miƙa masadukiyarsa
tare da shaidu, amma in wawa ne (sahuhu) to shiza a rinƙa kulamasa da
dukiyar.
5. 2. FALALAR RAINON MARAYA.
Akwaiwatagaraɓasawadda Allah (S. W. T) yatanadarwadukmutumin da
yarainimarayaharzuwagirmansakumayayimasaaure. Wannankuwayabayyana a wanihadisi
da Manzon Allah (S. A. W) yayibayani a kanhaka.
An karɓodaga Ɗan Abbas yace: Manzon Allah (S. A. W)
yace: "Dukwandaya ɗaukimarayanamusulminadagaabincinsakoabinshaharsai
da Allah yaazurtashi. Allah (S. W. T) YawajabtamaiAljannah, saidai in
yaaikatawanizunubi da ba a gafartawa.
Manzon Allah (S. A. W) yace: Dukwandayashafa
(dafa) kanmaraya, baishafakan don komaibasai don Allah. Yana da
ladagwargwadonyawangashinkansa (suma) da hannunsayataɓa. ni da shimunakamarhaka a Aljannah.
Ya zo cikin Bukhari:
Manzon Allah (S. A. W) yace: Ni da
mairainonmarayaaAljannahhakamuke. Saiyayinuni da yatsunsabiyu ɗan Ali da babbanatsakiya. Yagwamesu.
Yazo a Sahihu Muslim:
Manzon Allah (S. A. W) yace: Mai
rainonmarayanashi ne? wataudanginsakonawaninsanin da shihakamuke a Aljannah.
Saiyayinuni da yatsunsa ɗanali da
babbanatsakiya.
An kwaɗaitar da kula da kyautatawamaraya ta kowaccehanya a
wurare da yawa a Ayoyin Ƙur'ani:
SuratulMa'un: Shin kagawandake ƙaryatawa game da
ranarsakamako?. To, wannanshi ne ketunkuɗemarayadaga haƙƙin sa.
SuratulFajr: aha! Ba hakaba,
aibakugirmamamaraya!
SuratulInsan: Gamatalauci da maraya
da kamamme.
SuratulMa'un: To, wannanshi ne
ketunkuɗemarayadaga haƙƙin sa.
Sunaciyar da abincigamabuƙata, miskinaibayi
da marayu don nemanyardar Allah.
5. 3. KYAUTATA WA NA ƘASA DA KAI.
Manzon Allah (S. A. W) yaumarni da
akyautatawana ƙasa,
wataumutumyakyautatawawandadukke ƙarƙashinsa, tundagamata,
ya'ya, barori, kaihattadabbobi, banda ma umarni, shi da kansayaaikata an gani.
Akwaiwaniabu da yafaru a kanwaniyaroBahayudemai yin hidima a gidanManzon Allah (S.
A. W) , a lokacin da yatashibashi da lafiya, saiManzon Allah (S. A. W) yatashi
da kansayatafigidanyaron don kawaiyagasheshi. Ko da
yaisagidanyashigayadubayaron, saiyacemasakayiimani,
saiyaronyanakallonAnnabikumayanakallonbabansa, a ƙarshesaibabanyace ma
yaronkayiwababan Ƙasim ɗa a, ma'anaya bi abin da Annabiyacemasa, nan take
kuwayayiimani, sai aka zareransa. SahabbaisukagaAnnabiyafitoyanafara'a,
saisukatambayeshi, saiManzon Allah yacemadalla da Allah Yashiryar da shi.
Akwaiwanihadisi da Manzon Allah (S. A.
W) yayiumarnicewakukyautatawabayinku, kuciyar da suabin da kuke ci, kutufatar
da suabin da kuketufata, kutausasamusu don sumasuna da raikamaryaddakuke da
shi.
Saikumawanihadisin da yacebashi tare da
mu wandabaijitausayinna ƙasa da shiba, baikumagirmamanagababa.
Hakakumawanihadisincewayayi,
dukwandayaciyarda ɗanyar hanta Allah
nakallonsa.
Mu tuna da watamata a BanuIsra’ilawadda ta
shayar da kareruwa Allah yasanya ta aaljanna.
5. 4. FALALAR RAINON 'YA'YA MATA.
Akwaiwatagaraɓasawadda Allah (S. W. T) yatanadarwadukmutumin da yaraini
'ya'yamataharzuwagirmansukumasukayiaure. Wannankuwayabayyana a wanihadisi da
Manzon Allah (S. A. W) yayibayani a kanhaka.
Kamarhaka: -
"Manzon Allah
(S. A. W) yacedukkanwandaya ɗaukinauyin
'ya'yamatagudabiyukoukuko 'yan'wabiyukoukuharsukagirma (sukayiaure) ,
kokumayamutuya bar su, zankasanceni da shi a cikinAljannahkamarhaka,
saiyayinuni da hannunsamanuni da wandayakebinsa. Kumazaisamuladarmai jihadi don
ɗaukakakalmar Allah, wandayakeazumi da sallar dare a
wurinjihadin. Saiwata mace tacehar 'ya ɗaya? SaiManzon Allah (S. A. W) yacehar da mai 'ya ɗaya. "
An karɓodagaAnas (R. A) yace, dagaManzon Allah (S. A. W) yace,
dukwandayaraini (riƙe) yaramatabiyuharsukagirma, watausukabalaga, ranar ƙiyamazaizoni da shihaka…..
6.
0. 0 RIƘO A MAHANGAR ZAMANI
A wannanzamani da
mukecikiabubuwa da yawa sun taru sun hanamu ɗaukargoyonyaro.
Wannankumaya haɗa da mazanmu da matanmu, sabodawasubaƙin ɗabi’u da muka ɗauka. A
zamaninyanzumunafakewa da wasuuzurori, wandamukeganinkamarmuna yin wayau ne.
Bisa haƙaƙa kumabahakaba ne, mukan fake da talauci, ko ƙarancinwaurinzama, ammawasubahakaabinyakeba.
Manyandalilai da sukakawowannansu ne, son abinduniya, da baƙarrowa, sannanmatanmu da baƙin kishi. A ɗaya ɓangarenkuma
son ‘ya’yayayimanayawa, da zararka ɗauki ɗan wani,
sai a sanyamakaido ‘yantsegume-tsegumesufarayawo. Dukabinalhairidakeyibaza a
ganiba. Ta ɓangarenyarankumaga ɗan Karen
rashin Magana, ɗan cikin ma saika miƙe tsayezakaladabtar da shi. Idan ɗa riƙo ne, sai a ce kana gallazamasa, in ka ƙyaleshikumayalalace, nan ma a zageka. A
zahiringaskiyawaɗannanabubuwasu ne sukasanyariƙon yaro a yanzuke da wuya, dole sai an daure. Don
haka dole ne mu dage mu dawo da wannanal’ada ta riƙonyara, sabodaalhairandaketattare da ita.
7.
0. 0 KAMMALAWA
A ƙarshe
wannan muƙala, ta yi bayani ne a kan al’adar riƙo
ko goyo da matsayinsa a rayuwar Bahaushe jiya da kuma yau. Haka kuma takawo
wasu sauye-sauye da rayuwar Bahaushe ta samu dangane da wannan al’adar. Bayan
haka, an fito da dalilan da suka kawo waɗannan sauye-sauye.
Bugu daƙari an nuna fa’idojinriƙo da kuma
sakamakon da yakan haifar ga mai yin sa da kuma al’umma gaba ɗaya. An yi
wannan nazarine bisa mahanga guda uku watau tamahangar Al’adar Bahaushe, da
mahangar Addinin Musulunci, sannan ta mahangar Zamani. Haka kuma an dubi wasu
abubuwa da sukan yi tasiri a ɗabi’un yaro, wanda ba laifin mai riƙo
ba ne ko goyo. Da fatan Allah Ya ba mu ikon aikata alhairi amin summa amin.
Akwai shawarwari tare da kammalawa sai kuma manazarta.
MANAZARTA.
Alhassan H. D (1982) Zaman Hausawa.
Islamic Publication Bureau, Lagos.
Bunza A. M. (2006) Gadon feɗe al’ada. Tiwel
Nigeria Limited Surulere, Lagos.
Banbale M. B. (1994) Kukan Kurciya.
Ibramud Nigeria Limited, Zaria.
Ɗangambo A. (1983)
Kitsen Rogo. Triunph Publication Kano..
Ɗahiru B (2007)
Tafsirin Watan Ramadan. Rediyo Najeriya Kaduna.
Imam A. (1937) Magana Jar ice na 1, da
2, da 3. Northern Nigerian Publication Company, Zaria.
Madauci I. (1963) Al’adun Hausawa.
Northern Nigerian Publication Company, Zaria.
Sadiya G. Y. (2005) Talauci Hauka ne?
Super Prints Press, Kano.
Williams B. (1979) Human Design. Harɓard Uniɓersity
Printed USA.
Yaro Y. I. (1971) Tatsunniyoyi da
Wasanni. Oɗford Uniɓersity Press,
Ibadan.
Zindani A. A. (2000) Human Deɓelopment.
Muslim World League Printing Press.
Saudi Arabia.
Sarki H. A (2000) Zuwan Musulunci a
Afirka da shigowarsu Ƙasar Hausa.
G. A. Computer Centre. Ikere – Ekiti, Ekiti
State.
Ɗanfodiyo S.
U. (2002) Faɗakar da
‘Yan’uwa a kan halayyar Ƙasar Sudan.
(Fassara) Muhammad Mode Shuni. C. I. S Usman Ɗanfodiyo Uniɓersity, Sokoto.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.