Ticker

6/recent/ticker-posts

Tushiya Masomin Dawa: Tsokaci A Kan Asalin Bahaushe Tare Da Gano Wane Ne Bahaushe A Yau

NA

FARFESA MU’AZU SA’ADU MUHAMMAD PhD.

SASHIN NAZARIN HARSUNA NIJERIYA DA KIMIYYAR HARSUNA

JAMI’AR SULE LAMIƊO, KAFIN HAUSA, JIHAR JIGAWA

07030803404

Email: muazusaadukudan299@gmail. com

Wanda aka gabatar a taron bikin ranar marubuta harshen Hausa ta duniya, wanda Kungiyar Marubuta ta shirya Manpower Development Institute Dutse a garin Dutse, Jihar Jigawa, a ranar Laraba 31/12/2025 da ƙarfe 9: 00 na hantsi, daidai ban ruwan dawaki.

Tsakure

 Manufar wannan bincike shi ne, nazari a kan asalin Bahaushe kuma wane ne Bahaushe. Farfajiyar Bahaushe ya gudanar da kusan mafi yawan harkoki na al’adun gargajiya wanda ya gada tun iyaye da kakanni. Hanyoyin da aka bi don gudanar da wannan bincike, sun haɗa da nazarin wasu bugaggun littattafai, da mujallu, da muƙalu, da yanar gizo, Dangane da iyaka ko farfajiyar wannan bincike, shi ne, Ƙasar Hausa. Maƙalar zata kawo bayanai tare da fito da rawar da Masana suke takawa a fagen gano salsalar Bahaushe. Da farko za a kawo ma’anar Bahaushe da Harshen Hausa, sauye-sauye da Bahaushe ya gani a rayuwarsa bias wasu dalilai, da tsawon lokaci ko zamani da ya ɗauka yana mu’amulla wasu baƙin al’ummomi. Na ɗora nazarin bisa Ra’in bincike a kan ra’in Alfanun Sassan Al’ummma (Al’adun) wanda da Harshen Turanci ake kira Functionalism Theory of Culture, saboda bincike ya kawo irin yadda al’adar Bahaushe ta bai wa sanin asalin abu muhimmanci kusan kamar na abinci, kamar a wajen bikin aure, da haihuwa, da sana’a, da magani, da sauransu. Haka kuma za a kalli irin yadda Hausawa kan yi kasuwancin dare a tsakaninsu a wasu wuraren. Maƙalar zata kawo jirwayen dare a adabin Bahaushe na baka da rubutacce wato na zamani, daga ƙarshe sai sakamakon bincike, da shawarwari sai kammalawa, da manazarta.

1. 0 Gabatarwa:

Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, Allah yai daɗin tsira ga Shugabanmu Annabi Muhammad (S. A. W) da alayensa da Sahabbansa. Maƙasudin wannan takarda shi ne, yin tsokaci ko taƙaitancan bayani a kan asalin Bahaushe, sannan kuma wane ne Bahaushe a yau?. Haka kuma wannan takardar zata yi tsokaci a kan matsayin harshen Hausa a idon Duniya jiya da yau, da kuma fatan matsayin da zai kai nan gaba, wato ya ƙara ɗaukaka. A zahiri Harshen Hausa wani babban ginshiƙi ne a rayuwar Duniya, sai dai kuma kash! ana cin moriyarsa ana kushe shi. Bisa wannan dalili ya sa na yi wa takardata taken Tushiya masomin dawa. Manufa ita ce, a lalubo tushen Bahaushe wato inda Kakanni da iyaye suka fito zuwa wannan farfajiyar da ‘ya’ya da jikoki suka samu kansu a yau. Masana magabata daban daban sun yi rubuce- rubuce masu yawa. A inda suka bayyana inda Bahaushe ya fito da kuma irin rawar da Bahaushe ya taka, sannan kuma suka nuna babu ƙusurwar da ba a cin moriyar Harshen Hausa a harkar zamantakewa gaba ɗaya ba. A irin tunanina kuma Bazazzagin tunani, nake ganin ba a yiwa harshen Hausa adalci ba, tun daga kanmu mu Hausawa da sauran Al’umma masu cin moriyar Harshen.

Yankan hanzari ko in ce sarbu, bisa al’amarin da ya shafi Bahaushe da Harshen Hausa da Kasar Hausa wasu abubuwa ne masu shiga cikin juna wato sun zama tamkar hanta da jini ko tsumma da kwarkwata. Ba a iya rarrabesu wannan yasa suke yiwa juna shigar gizagizai, to wannan shi ya faru ga wannan takarda. Don haka a yi hakuri a karɓa haka, saboda idan tuwon amarya ya yi gudaji ba a Magana.

2. 0 Ma’anar Kalmar Hausa

Ma’anar kalmar Hausa ba ta tsaya ga sunan harshe kaɗai ba, akwai wasu ma’anoni da Hausawa suke danganta kalmar da su. Akwai wasu masana dake ganin ita kanta kalmar Hausa tana nufin harshe ko yare kowane iri. Misali, Ba na jin Hausarsa. Wato ba na jin harshensa ko yarensa.

Adamu (2021) babban abin da za a tambaya a nan shi ne, wai shin wane ne Bahaushe ? wannan tambayar tana da ban mamaki, domin ganin cewa babu wata ƙabila da ake tantanmar salsalarta a Nijeriya irin Bahaushe. Misali idan aka ce Yarbawa an san waɗanda ake nufi. Amma da zarar kace Hausawa sai a fara musu domin ana ganin yawan gaurayar al’ummomi, da kuma iya yaren Hausa na mutane da yawa ya sa ba ma za a iya cewa ga Bahaushe wannan tunani ya ƙarfafa bisa nazarin wani mai nazarin Harshe da ake kira Joseph Greenberg. A turbar nazarin da ya gina, Ya gina babu wata ƙabila Hausawa domin su kansu Hausawa a wajensu tana nufin yare.

Bayan wannan kuma kalmar Hausa a wani lokaci tana nufin harshen da Hausawa suke magana da shi.

A wurin Sakkwatawa kuwa kalmar Hausa tana nufin Ƙasar Sakkwato.

 Ibrahim Narambaɗa Tubali a waƙar Sarkin Gobir yana cewa:

Jagora: Tun daga Kaduna har Gusau ƙarewa Hausa,

 Amshi: Baban Shamaki Namalam Toron Giwa,

 Baban dodo ba tamma da batun banza.

Haka kuma, Bahaushe da kansa yakan ambaci kalmar Hausa a matsayin nufin azancin magana.

Wannan ya sa ake danganta azancin Magana wurin mutane biyar, kowanne daga cikin waɗannan mutane suna da baiwar azancin Magana a harkoki na yau da kullum ta fuskoki mabambanta:

1. Bafade. (Iya juya Magana nan take)

2. Gardi. (Ƙirƙirar Magana cikin hanzari)

3. Mahauci. (Mayar da martani ga abokin Magana cikin sauri)

4. Maroƙi. (Iya ajiye Magana da zaɓar kalmomi)

5. Wanzami. (Iya haddace labarai da yin tilawarsu)

3. 0 Sanin asali yasa Karen cin alli:

 Bunza (2019) Binciken gano diddigin tarihin mutane wata matsala ce mai cin rayuwar masu bincike da waɗanda ake yiwa binciken a lokacin da ilmi ya bunƙasa kowace al’umma ƙoƙari take ta taskance tarihin asalinta. Wurin da gizo ke saƙar, shi ne, babu mai nunin gidansu da hannu hagu, maimakon a yi canjaras da abu guda, sai a ga kowane bakin wuta da irin nasa hayaƙin a ƙarshe aka kasa rarrabe tatsuniya da tarihi da tarihihi, da ƙari faɗi, da kintaci faɗi, da jita-jita hadisin Bamaguje.

 Dangane da asali kuwa, har yanzu ba a tabbatar da asalin kalmar Hausa ba, saboda saɓanin ra’ayoyi da ake samu dangane da asalin inda Bahaushe ya fito.

Amma wasu masana sun yi ƙoƙarin bayyana ra’ayinsu game da asalin kalmar Hausa kamar haka:

i. Akwai Masana masu ra’ayin cewa Bahaushe ya fito daga arewacin Afrika suka yiwo yamma, waɗannan mutane ana zaton su ne kakannin Goburawa. Bunza (2023) ko da Goburawa suka zo sun iske Zamfarawa.

ii. Akwai masana masu ra’ayin Misira, daga cikinsu akwai Muhammad Hambali Junju cewa: Mutane ne da suka taso daga Misira wanda ya kafa hujja da cewa Hausawa sun kama da ƙibɗawa ta fuskar launin fatar jiki da ginin jumla. Wannan ra’ayi ya yi kusa da ra’ayin Muhammad U. Adamu (2011) ya ce an samo kalmar ne daga sunan Fir’auna Hausal, wanda yake ganin daga zuriyarsa ne aka samu Hausawa.

iii. Ban da wannan akwai Masana masu ra’ayin Habasha daga cikinsu akwai Malam Aminu Kano da Yusufu Maitama Sule Ɗanmasanin Kano, waɗanda suka ce asalin Bahaushe ya samo ne daga Ƙasar HABASHA, domin Hausawa daga Habasha (Ethiopia) suke.

iɓ. Ra’ayi na ƙarshe shi ne wanda ake kallonsa kamar tarihihi wato tarihin zuwan Bayajida. Sarkin Tarihin Daura da Sarkin Ningi Haruna, wanda yace an samo kalmar ne sakamakon zuwan Bayajidda Daura.

4. 0 WANE NE BAHAUSHE?

 4. 1Allah shi kaɗai yasan uwar kwaɗo in ji masu maganar azanci.

Wannan dalilin yasa har yanzu ba a tabbatar da tahaƙiƙin asalin Bahaushe ko harshensa ba, amma akwai hasashe da dama da ake yi game da asalin Bahaushe ko harshen Hausa. Mafi yawan manazarta suna ganin harshen Hausa ya malalo ne daga Arewa maso gabas daga gurbin da yake a yanzu, wato Ƙasar Hausa. To da yake ance rashin jini rashin tsagawa, bisa wannan hujjar ta sa na lalubo wasu bayanai daga nazarin Manazarta magabata kamar haka :

4. 2 To da yake idan dambu yai yawa ba ya jin mai:

Duk da haka zamu dubi ƙoƙarrin da wasu masana magabata suka yi ta fuskar lalubo mana asalin Bahaushe. Ga kaɗan daga cikinsu.

Malumfashi (2024) yace babu wata al’ummar da ta faɗo daga sama, babu al’ummar da zaka ce ba halastacciyar al umma bace tun daga zamanin annabi Adam saboda haka ana bincikar tarihi ne a duba yadda alumma na duniya suka samu da yadda suka wanzu suka barbazu a doron ƙasa dukkaninmu muna da yaƙini asalin mu daga Annabi Adamu ne da Hauwa.

Kamar yadda Bunza (2024) yace: Abu ne mawuyaci a samu cikakken Bahaushe wanda yake uwa da uba kakanninsa duka Hausawa ne. Dalili kuwa shi ne Farfesa Mahadi Adamu yace: idan ana son cikakken Bahaushe dole a samu Ubansa, kakansa uban kakansa kakankasa Bahaushe. Ana iya haƙuri ta ɓangaren uwa. Bisa lura da samun haka zai yi wahala, sai Bunza yace: in aka samu uwa da uba da kakanni Hausawane sai a haƙura. A yanzu sanin ko wane ne Bahaushe na sali sai an yi ƙoƙarin tantancewa, saboda irin cuɗanyar da Hausawa suka yi da wasu ƙabilu wadda ta yi sanadiyar sauyawarsu. Don haka siffa ko harshe ba ya tabbatar da Bahaushe. Bahaushe ya ɗauki dogo lokaci mai tsawo yana yin mu’amulla da baƙin al’mmu masu yawa daga wasu ɓangarori na Duniya ta fuskar zamantakewa da kasuwanci, da ƙwadugo/bauta, da addini, kamar:

Fulani, zamantakewa Daular Usmaniya Sakkwato, da Barebari kasuwancin kanwa da Buzaye kasuwancin dabbobi, da dabino, da Nufawa Kasuwanci abinci da Yarabawa cinikin gwanja (cinikin goro) da Jukunawa da wasu ƙabilu na Afirka masu yawa da wasu daga Asiya da Nahiyar Turai ciki har da Ƙwarori da Larabawa a lokacin har da Turawa da Hindiyawa da sauransu.

5. 0 Hausa Mesa uwar haɗiya:

 Harshen Hausa na haɗiye wasu ƙabilu waɗanda ke maƙwabtaka da shi, a inda harsunansu na asali sukan sumɓule su ɓace su koma Hausawa ciki ruwan sanyi sai su koma Hausawa. Ta fuskar Harshe da al’ada irin su Magana, da abinci, da tufafi a wani lokaci har da muhalli. Gulma J. (2024 wakilin Blueprint Birnin Kebbi) Yaren Hausa shi ne ya haɗiye kowane harshe musamman ƙananan harsuna dake cakuɗe da Hausawa.

 Aujara da Bunza (2021) sakamakon wannan mu’amulla ta haifar da auratayya da cakuɗuwar al’adu a tsakaninsu da Hausawa, wanda hakan ya yi sanadiyyar mayar da wasu Hausawa ta fuskar harshe da al’ada duk da cewar hakan bai hana su iƙirarin asalinsu ba. Za a iya fahimtar Hausawa ta waɗannan fuskoki:

i. Hausawa ta fuskar muhallin zama. (gari ko yankin da suke zaune)

ii. Hausawa ta fuskar addini. Yawancinsu musulmi ne ko maguzawa.

iii. Hausawa ta fuskar halayya da al’ada.

iɓ. Hausawa ta fuskar asali. Waɗanda suke iƙirarin su Hausawa iyaye da kakanni.

Adamu, da Bunza da Aujara Don haka a yanzu Bahaushe shi ne mutumin da yake ba shi da wani harshe sai harshen Hausa, kuma al’adunsa na Hausawa ne, ko da kuwa yana iƙirarin wani asali daban, yana zaune ne a Ƙasar Hausa ko a wajen Ƙasar Hausa. A yanzu kalmar Hausa ta zama ta harshe ba ta ƙabila ba. Domin kalmar ƙabila, kamar yadda Zarruk da wasunsa (2009) suka bayyana na nufin:

“... al’umma mai asali ɗaya, da yare ɗaya, da ƙirar jiki kusan iri ɗaya, da al’adu iri ɗaya, da falsafa ko ra’ayin zaman duniya iri ɗaya. Bayan haka cikin al’ummar kowa zai riƙa alfaharin shi ɗan ƙabilar ne. ”

6. 0 Farfajiyar Ƙasar Hausa a jiya:

Adamu (1970) Ta yi iyaka da Daular Bono daga gabas ta kaɗa tayi arewa har zuwa Filige, ta kaɗa ta yi yamma zuwa yawuri ta dunguri kogin kwara, ta yi kudu har ƙasar Gwari zuwa Zazzau, ta yi gabas har ƙasar Bauchi sai da koma ta duguri Borno. Wannan farfajiya it ace Ƙasar Hausa a da. Aujara () Ƙasar Hausa ta asali tana yankin Afirka ta Yamma a farfajiyar da ke a Arewacin Nijeriya da kuma Kudancin Jamhuriyar Nijer. Daga Gabas ta yi iyaka da yankin Mangawa da Badawa a gabas kaɗan da garin Haɗejiya ta Jihar Jigawa, daga Yamma ta yi iyaka da ƙasar Zabarmawa daidai doron Kogin Kwara, daga Arewa ta yi iyaka da ƙasar Agadas wato yankin Buzaye (Auzinawa) a Kudancin ƙasar Nijer, sannan daga Kudu ta yi iyaka da ƙasar Gwari da wasu ƙananan ƙabilu da ke Kudancin ƙasar Zazzau (Zariya) a jihar Kaduna.

7. 0 Hausawa A yau.

 Mahadi Adamu yace Bahaushe shi ne wanda a tarihinsa daga Ƙasar Hausa ya tsira ko zriarsa tafuskar iyaye maza haka kuma wadɗanda suka shaƙu da aladun Hausawa sosaisuka riƙe harshe da ɗabiunsu da ddininsu. Duk da haka tilas a ba da kafa ga Fulani da suke zaune a ƙasar Hausa, cikin yunƙurin tantance Bahaushe ya kyautu a waiwayi ƙirar zatinsa da ɗabiunsa domin fayyace Bahaushe gado da kazo-nazo da maziyarta da maƙwabtan da aka hausantar a ilmance. Bahaushen asali za a sameshi yana da baƙi sosai irin na jama’ar tsakiyar Sudaniyya. Zubin kansa na da tsawo da ƙurungun kai da ɗan jemo za asameshi. Waɗannan siffofi na zati da launi idan aka ƙura masu idon nazari za a fitar da Bahaushe kai tsaye a taron jama’a dake zaune a ƙasarsa.

 Malumfashi (2024BBC Hausa) Asali mutane ba irin siffar da ake yanzu suke da ita ba. Ya ci gaba dacewa Hausawa sun kasance daga cikin mutanen da suka tsira daga ruwan da aka tafka a lokacin Annabi Nuhu su ne mutanen da ake kira Omo-kibishi. Inda yace Daga cikin waɗannan al’umma ne Hausawa aka samo asali shekara 1000 da suka gabata.

Bisa dalilin faruwar mulkin mallaka da Bahaushe ya tsinci kansa, wannan yanayi ya haifar da karatun boko shi kuma sai samuwar aikin Gwamnati da na kamfanoni da masana’antu, da samar kasuwanci iri daban daban. Wannan ya sa Hausawa suka riƙa yiwa juna shigar gizai-gizai da wasu baƙin al’ummomi, wanda ya haifar da wani sabon zubi na Bahaushe.

Manyan garuruwan ƙasar Hausa a yanzu sun haɗa da Kano da Katsina da Daura da Sakkwato da Kebbi da Zazzau (Zariya) da Gusau da Haɗejiya da Bauci da Azare (ƙasar Guddiri) a arewacin Nijeriya, da kuma Damagaran da Maraɗi da Filinge da Dogon Dutse da Ƙonni a jamhuriyar Nijer.

A taƙaice ƙasar Hausa ta asali, daula ce da ta wanzu a tsakanin daular Barno daga gabas da kuma daular Songhai daga yamma, ko da yake tarihi ya fi ganin yankin a matsayin daular birane, inda kowane sarki yake da ikon cin gashin kansa, wato babu wani shugabanci da ya haɗe yankin a matsayin dunƙulalliyar daula.

8. 0 Sakamakon Bicike:

Babu shakka gane tsintsar Bahaushe a yanzu ba ƙaramin aiki ba ne. Haƙiƙa kowa ya yarda cewa tun daga zamanin maguzanci har zuwa lokacin da addinin Musulunci ya iso Ƙasar Hausa ya tarar Hausawa suna gudanar da wasu harkokin rayuwar yau da kullum wasu baƙin al’ummu a Ƙasar Hausa. Don haka wannan daɗewar da aka yi ana gudanar da harkokin rayuwa, sai hakan haifar da cakuɗuwar al’ada, haka kuma da Turawa suka shigo Ƙasar Hausa sai aka ƙara samun wasu sauye-sauye. Ga ɗan abin da bincike ya hararo akwai:

Bahaushe na kwarai, wajibi ne ya yi kishin Harshe da al’adarsa, amma ina a yau ba haka abin yake ba. A bisa gaskiya wasu daga cikin Hausawanmu mu muka fara wulaƙanta harshen Hausa, a inda muka ƙyamaci al’adunmu, mu ka yi jifan matacciyar mage da Bahaushen tunani. A inda muka zaɓi baƙon harshe muka fifita baƙin al’adu, muka rungumi baƙon tunani (abinci, da magani, da tufafi). Irin wannan wauta da muka yi shi ya ba da dama ga wasu jama’a ko ƙabilu har suke tsangwamar Hausawa da Harshen Hausa da Al’adunsu. Ashe ke nan, Hausawa mu ne masu awaki, muka fara zagin Kura, don haka sauran jama’a ko ƙabilu suka samu damar zagin harshen Hausa. Alhali kura bata da laifin komai. Alhaji Musa Ɗankwairo Maradun a waƙarsa ta mubi Al’adunmu na gargajiya yana cewa:

“sai ka ga ɗan Musulmi da wandon yadi guda,

Ga ‘yar shet yasa ga wuya nai,

Ba hulla ga kai nai,

Aljihu nai ba tasbaha, sai kwalin sigari.

Kar mu sake mu mance,

 mubi al’adunmu na gargajiya.

Ɗiya mata waɗanda aɗ ɗiyan musulmi,

 su ɗora sayen siket da ‘yar kanti,

suna ta yawo rariya-rariya,

 abin ga ya bamu kunya.

Shi kuma Alhaji Adamu Ɗan maraya Jos a waƙarshi ta mu so al’ada yake cewa:

“Kamar mutum da halayanshi,

 sun kama da al’adunshi,

Kamar mutum da al’adunshi,

 sun kama da halayenshi.

‘yan Uwa mu so al’ada,

 kowa ya bar gida kai Malam,

 Na tabbata gida ya barshi.

Na tuna akwai wasu ‘ya’ya,

 idan kace sannunku,

Sai ka ji sun ce,

 ai no da hiya Hausa,

Na tuna akwai wasu ‘ya’ya,

 idan kace kwale se dadani,

Sai ka ji sun ce,

 ai no da hiya Yaroba.

Na tuna akwai wasu ‘ya’ya,

 idan ka ce kedun adunma.

Sai ka ji sun ce,

 ai no da hiya Ibo.

Abin da su suka ɗauka,

 Harshen Nasara shi yafi na su.

Ba ni jin Turanci,

 Mai ingilish sam teki wan we.

Kayan aro abin banza ne,

 in mai abin ya karɓi abinsa,

to dole zaka komo naka. ”

9. 0 Shawarwari:

 Bahaushe na cewa: “ba a dafa gawa a tashi ba hawaye” a ƙarshe sai na fahimci. Tabbas wannan takarda na da fatan alheri da samun kyakkyawar rayuwa ga al’ummar Hausawa da kuma shi kanshi Harshen Hausa nan gaba. Domin idan ruwa bai koro gafiya ba, to kuwa hayaƙi zai korota.

Ban da wannan kuma, na hararo irin tasku da halin ƙaƙa-ni-ka-yi da Bahaushe da kuma Harshensa suka tsinci kansu a ciki. Haka kuma, wasu Masana sun karkasa Bahaushe zuwa gida hudu, kamar haka:

1. Bahaushe na tsatso babu sofane (uwa da uba Hausawa).

2. Bahaushe Barbaran yanyawa (uwa Bahaushiya, uba daban, ko uba Bahaushe uwa daban).

3. Bahaushe Feƙe kafi ƙaya tsini (uwa da uba ba Hausawa ba).

4. Bahaushe na ara ka yafa ( Waɗanda suke wata Nahiya amma sun rungumi harshen Hausa)

Bahaushe yace: zamani ba kan ji magani, to yanzu zamani ya zo da wani sauyi na nau’in Bahaushe, shi ne kamar haka:

Duk wanda ke jin Hausa kuma yake yin Magana da Harshen Hausa, yana yin al’adun Hausawa yana bugun kirji shi Bahaushe ne, to wannan Bahaushe ne a yau.

Kishin Harshe wajibi ne:

Da fatan za a fahimce ni, kar a yi min bahaguwar fahimta. Ba wai nace kar Bahaushe ya ɗauki wani Harshe ya yi magana da shi ba ne, a’a, abin da nake so in ce, shi ne, ko da kana amfani da wani Harshe to kar kuskura ka mance da naka harshen, don haka ina ba ka shawara. Idan har kana da tunani, to ka tsaya ka duba ta sosai. Ka yi wa shawarar dubi irin na sayen goron tsohuwa, ka juya, ka ƙara juyawa, sannan zaka fahimce ni.

Bisa lura da bayanai da suka gabata, ana iya cewa an gani kuma an gamsu. akwai buƙatar a ɗauki matakin fito tare da bayyana asalin Bahaushe da Harshensa da kuma al’ada. shawarwari waɗanda ya kamata mu ɗauka su ne:

Ya dace masana masu koyarwa da wannan Harshe na Hausa mu bai wa juna shawarar neman mafita.

Akwai wasu abubuwa da yawa da suke buƙatar a fito da su don al’umma su ƙaru.

Akwai buƙatar yaƙar zuciya, da kuma cire ƙyuya mu zurfafa nazari a kan abubuwan da suka shafi al’adar Bahaushe.

9. 2 Rashin sani yafi dare duhu:

Turawan yamma da ‘yankoransu sun shigo da wata guba suna dasa ta a tsakaninmu na kiyayyar juna, wai da sunan kishin Hausawa. To ka sani za a yi amfani da kai ne a cimma buri, don a tartsa al’ummarka. Da zarar an cimma buri shi ke nan, saboda haka suka yiwa wasu Kasashe da wasu al’ummomi, misali, Ruwanda, da Burundi, da Afrika ta Tsakiya, sannan ga Somaliya, da Libiya, da Sudan da sauransu. Domin haka, Kungiyar Hausawa zalla guba ce mu gujeta mu kiyayeta domin ba zata haifar mana da da mai ido ba.

10. 0 Kammalawa:

Ƙarshen tika-tika tik, komai yai farko, dole ne yai ƙarshe, don haka wannan tsokaci dangane da bayanai da suka gabata bisa ga asalin Bahaushe tare da gano muhimmancin Harshen Hausa a rayuwar bil’adama. Duk wasu bayanai game da abin da ya shafi asalin Bahaushe da Harshen Hausa ya wuce wasa, haƙiƙa wannan fage ne kandami, ba zai yiwu a taɓo shi duka ba. Amma dai mun yi abin da zamu iya ta hanyar binciko da nazartar bayanan Masana manazarta da suka gabata rubutattu da nab aka. Bisa wannan dalili ne, yasa muka Ɗan tsakuro wani abu daga cikin fage, saboda ko ba a shafa ba maruru ya ɗara kaluluwa. Dukkan bayanan da muka yi, to ya zo ne a matsayin fitila abin haskawa da kuma jagora. Bahaushe dai yace; lomar hasafi tafi kaɓakin tsiya, ƙaramin goro yafi babban dutse, sai a yi haƙuri da abin da samu. Alhamdu lillahi.

Manazarta

Abubakar A. T. (2015) Ƙamusun Hausa. Northern Nigerian Publication Company,Zaria.

Adamu U. A (2021) Wai shin Wane ne Bahaushe?

BUK (2006) Ƙamusun Hausa. Bayero Uniɓersity Press Kano.

Bargery, G. F. (1993) A Hausa-English Dictionary and English-Hausa Ɓocabulary. Zaria: Ahmadu Bello Uniɓersity Press.

 Bunza, A. M. (2006) Gadon feɗe al’ada. Tiwel Nigeria Limited Surulere,

 Lagos.

Bunza A. M (2019) Jaridar Aminiya Asalin Hausawa 1

Bunza (2023) Hira da shi Haske online T. Ɓ.

Malumfashi (2024) BBC Lodon Sashin Hausa.

Malumfashi (2024) Digital Journalist Isyaku Muhammad. 

 Hausa Post

Post a Comment

0 Comments