Ticker

6/recent/ticker-posts

Kadagi Kanin Mutuwa: Nazarin Talauci a Mahangar Adabi Da Al’adun Hausawa

NA

MU’AZU SA’ADU MUHAMMAD

 Tsakure

Maƙasudin wannan bincike shi ne ƙoƙarin gano wasu abubuwa game da talauci da yadda yakan shafi ko yin tasiri a rayuwa da ɗabi’un mutane. Duk da yake talauci ba ciwo ba ne, amma yakan yi illa ga harkokin yau da kullum, a wani lokaci har halayen masu fama da matsanancin talauci kan saɓa da na lafiyayyen mutum. Binciken kuma ya nazarci irin yadda Bahaushe yake kallon talauci, da sanadojin dake jawoshi tare da duba illolinsa, da kuma matsayinsa a al’ada. Haka kuma za a harari wasu hanyoyi ko dabarun na kawar da talauci a tsakanin mutane a Bahaushiyar al’ada. Za a kawo fashin baƙin wasu muhimman kalmomi kuma a dubi ma’anar talauci da sanadojin dake jawoshi, da ire-iren sunaye da Bahaushe ya kirashi da su, Hanyoyin da aka bi don gudanar da wannan bincike, sun haɗa da nazarin wasu bugaggun littattafai, da mujallu, da muƙalu, da yanar gizo, Dangane da muhallin bincike, shi ne, Ƙasar Hausa. Don cim ma nasarar wannan nazari, an tsara shi kamar haka: goshin aikin yana ɗauke da gabatarwa, sai kuma ƙirjin aikin yana ƙunshe da; ma’anar talauci a idon masana al’ada. Gangar jikin kuma tana ƙunshe; muhimman bayanai, da fito da matsayin talauci da kuma mutanen da talauci ya shafa wato a mahangar al’ada, da jirwayen talauci a adabin bakan Bahaushe, wanda ya zama kamar wani sinadarin harhaɗa wannan bincike. An kawo sakamakon bincike, da shawarwari sai kammalawa da manazarta.

 Keɓaɓɓun kalmomi: ƘADAGI, ƘANI, MUTUWA

ƘADAGI ƘANIN MUTUWA: NAZARIN TALAUCI A MAHANGAR ADABI DA AL’ADUN HAUSAWA

1. 0 Gabatarwa:

Babu shakka motsi yafi laɓewa, wannan yasa za a ɗan harari al’amarin tsananin talauci da raɗaɗinsa a Arewacin Nijeriya, tare da fito da halayen wasu mutane da suke rayuwa a cikin ƙunci. Bayan haka kuma, za a gudanar da wannnan bincike ne ta hanyar ɗora shi a mizanin al’ada don gano inda suka yi canjaras da wasu adabin Bahaushe. Da farko dai Bahaushe na cewa, komai ba ya rasa dalili, haƙiƙa Bahaushe na da wani tunani da ya danganta wasu dalilai da suke jawo talauci, tun a farkon al’amari. Misali: lalaci ko ragwanci, da jahilci, da ƙauyanci. Mu’azu Haɗeja a waƙar Ilmin Zamani yana cewa:

Da tsiya da talauci duk suna,

Gun da jahilci yai sansani.

Bayan waɗannan dalilai kuma, sai wani dalili shi ne, wanda zamani ya zo da shi wato tsarin shugabanci na siyasa a inda babakere da wasu mutane ƙalilan suka yi a harkokin rayuwa, musamman shugabanci inda suka zama bakan gizo, a ƙarshe kuma sai aka samu wasu mutanen masu kala kusa da tari, wato masu ƙuruciyar ɓera (sata).

1.1 MA’ANAR TALAUCI:

 Abubakar A. Y. (2015: 475) Tsananin rashin wadata,2. Tsananin tsiya. (2015: 135) Fatara: rashin kuɗi na ɗan lokaci. BUK (2006: 423) Rashin Wadata,Tsiyata,Fatara, ƙarancin Ko Rashin Kuɗi na Wani Lokaci. Newman (2020: 246) tsiya, ko tsananin rashi.

1. 2 SUNAYEN TALAUCI:

1. Talauci.

2. Tasku.

3. Tsiya.

4. Tsomomuwa.

5. Fatara.

6. Matsi.

7. Ƙunci.

8. Ƙaƙa-ni-kayi.

2. 0 TALAUCI A MAHANGAR ADABI

An samu jirwayen talauci a adabin Bahaushe, ma’ana ya yi naso a dukkan rassan adabi na baka da rubutacce. Domin an samu karin magana, almara, tatsuniya, barkwanci, waƙar baka. Haka kuma a rubutacce akwai littattafai da aka yi kamar zube, da wasan kwaikwayo, da rubutacciyar waƙa, kamar matsalon attajiri, uwar gulma, ka ƙara karatu da sauransu.

2. 1 Zube:

 Annoba: Jabiru (1970: 22) ciwon annoba a Zango, ciwon agana (‘yan rani) ya faɗa wa al’umma a inda Ɗanduna da Wakkale suka makance wanda dole yasa suka yi hijira zuwa wani gari.

Idan muka waiwayi wannan littafi na Nagari Nakowa

2. 2 Waƙa: Waƙar Kassu zurmi waƙar Nomau Na magarya inda yake cewa:

Torankawan tsiya Uban mairogo,

Idan fatara tai yawa ta zan iko,

Nomau ko baka jin batun masu gari?

2. 3 Azancin Magana : TALAUCI A KARIN MAGANA.

1. Talauci kamar ɓeran Masallaci,

2. Talauci kamar jinjiri,

3. Talauci kamar zai rege zawo.

4. Talauci mai sa a ci iri ranar shuka.

5. Idan fatara ta yai yawa takan zan iko.

2. 4 Talauci A Kirari:

1. Talau-Talau Mugun Tsoho, Da Kasa Mutum Gaba Gara Ya Sa Ka.

2. Lalata Mutum Da Sauran Ransa

3. Talauci Ka Fi Ciwo Duka.

4. Fatara Mai Kai Maza Kwance

5. Wahala Mai Sa A Lalace

6. Mutuwar Tuji

7. Talauci Kamar Jinjiri

3. 0 TALAUCI A MAHANGAR AL’ADA

Bisa hasashe a tunanin Bahaushe yana ganin cewa lallai akwai abubuwa da sukan yi sanadin faɗawa cikin talauci. Da farko akwai waɗanda mtum kan jawowa kansa, sakamakon wasu ayyuka waɗanda yakan aikata da kansa. misalilalaci ko ragwanci, da jahilci da ƙauyanci, da girman kai, Camfi, ko raina sana’a.

Bahaushe ya yi wannan tunanin ne bisa la’akari da yadda harkoki na rayuwar yau da kullum da kuma mu’amullar zamantakewa dake wakana tsakanin sauran jama’a, kaɗan daga cikin waɗannan abubuwa sun haɗa da: lalaci ko ragwanci, da ƙyuya.

3. 1 Ragwanci:

na nufin gazawa, ko kasawa, ko lalaci. Ragwanci kishiyar jarumta ne. Ana kiran mai wannan hali da cewa rago, ko malalaci, shi kuma kishiyar jarumi ne, domin rashin jarumta ke haifar da ragwanci. Da zarar aka ce da mutum ba ya ƙulla abin ƙwarai, ko kuma malalaci, ba zai iya ƙullawa kansa komai ba, dukkan malalaci baya cin nasara a rayuwarsa don haka dole ya faɗa cikin talauci.

Hajiya Uwaliya mai amada tana cewa:

Wane rago da rigar saƙi,

In bai yo aro ba zai yo sata.

Haka shi ma wanda ya sanya ragwanci, da ƙyuya a zuciyarsa bai yin komai na bajinta domin ya zama rago, a game da su Bahaushe na cewa: malalaci ba shi da rana.

3. 2 Camfe-Camfe:

Wasu Hausawa sun yi imani da camfi, kamar sharaɗi mai kama da addini. Don da zarar an gitta doka, sai a ce wanda ya ƙaryata zai mutu, ko wani abu mummuna zai same shi. Wannan imani da abin da camfi ya tsara, wajen harkokin yau da kullum ne ya sanya masana da yawa suka ɗauki camfi wani addini ne mai zaman kansa. Ko da yake wasu masanan suna da ra’ayin cewar, camfi wani sashe ne ko ɓangare na al’ada, don haka basa ware shi daga al’adun garggajiya. Akwai wasu kamar haka:

1. Cin naman gafiya,

2. Ladanci (kiran sallah)

3. Ɗaura ƙonannan zani ko yagaggen zani,

4. Auren mace mai farar ƙafa,

5. Gamuwa da makaho da sassafe.

3. 2. 1 Gafiya (Burgu) : Bahaushe ya camfa gafiya, don haka ko namanta bashi da farin jini. Ko da yake wannan camfi bai rasa nasaba da wani zargi da ake yiwa gafiya. Wannan zargi kuwa akan wasu ɗabi’unta ne, da suka haɗa da abincinta, da wurin zamanta. Wajen abinci gafiya kan ci komai ta samu. Domin kuwa gafiya kan shiga kabari ta ci gawa rmutum. Ana ƙyamar kuma, saboda yanayin wurin zamanta, sau da yawa gafiya kan zauna a wurare kamar juji, da kabari, da suri da sauransu. Kamar wata waƙa wadda Alhaji Mamman Shata Katsina ya yi wa Gwamma inda yake cewa:

 Gindin : Gafiyar suri mai wuyar gina,

 : Amma nama da daɗi.

 : Gafiyar juji ba wuyar gina,

 : Ku zubar namanta ɗaci garai.

 Jagora: Haka nan ne Mamman ƙanin Idi Wan Yalwa.

Muhammad (2015: 152) Camfin Bahaushe yayi tasiri a kan gafiya, don kuwa an camfa ƙashinta ko da an kama gafiya an dafa. Idan za’a ci ba ‘a tauna ƙashinta saboda ana zargin cewa gafiya na da ƙashi iri biyu. Akwai ƙashin arziki da ƙashin tsiya duk wanda ya tauna ƙashin to lallai zai yi tsiya (talauci). Don haka ne Bahaushe ya ƙyamaci tauna ƙashin, dalili kuwa shi ne ba za’a iya bambance ƙashin arziki da na tsiyar ba.

3. 3. 2 Girman kai : Tabbas dukkan mai fama da wannan to lallai yana tattare da ciwon da zai iya jawo masa talauci. Kamar yadda Bahaushe ke cewa: girman kai rawanin tsiya, don yakan hanyar arziki. Shi kuwa Alhaji Adamu Ɗanmaraya Jos a waƙarsa ta girman kai rawanin tsiya sai yace:

Girman kai rawanin tsiya,

 Don yakan hana hanyar arziki,

Tun da Allah Yayi hani a yi,

Kuma Annabi ya yi hani a yi,

Don yakan hana hanyar arziki

4. 0 SANADIN TALAUCI A MAHANGAR AL’ADA

Bisa hasashe a tunanin Bahaushe yana ganin cewa lallai akwai abubuwa da sukan yi sanadin faɗawa cikin talauci. Da farko akwai waɗanda mtum kan jawowa kansa, sakamakon wasu ayyuka waɗanda yakan aikata da kansa. misalilalaci ko ragwanci, da jahilci da ƙauyanci, da girman kai, Camfi, ko raina sana’a.

Bahaushe ya yi wannan tunanin ne bisa la’akari da yadda harkoki na rayuwar yau da kullum da kuma mu’amullar zamantakewa dake wakana tsakanin sauran jama’a, kaɗan daga cikin waɗannan abubuwa sun haɗa da: lalaci ko ragwanci, da ƙyuya.

4. 1 Ragwanci: na nufin gazawa, ko kasawa, ko lalaci. Ragwanci kishiyar jarumta ne. Ana kiran mai wannan hali da cewa rago, ko malalaci, shi kuma kishiyar jarumi ne, domin rashin jarumta ke haifar da ragwanci. Da zarar aka ce da mutum ba ya ƙulla abin ƙwarai, ko kuma malalaci, ba zai iya ƙullawa kansa komai ba, dukkan malalaci baya cin nasara a rayuwarsa don haka dole ya faɗa cikin talauci.

Hajiya Uwaliya mai amada tana cewa:

Wane rago da rigar saƙi,

In bai yo aro ba zai yo sata.

Haka shi ma wanda ya sanya ragwanci, da ƙyuya a zuciyarsa bai yin komai na bajinta domin ya zama rago, a game da su Bahaushe na cewa: malalaci ba shi da rana. Alhaji Adamu Ɗanmaraya Jos a waƙarsa ta mu kori malalaci, sai yace:

Mu kori malalaci,

Mu zagi malalaci,

Wofi mutumin banza,

Wanda bai sana’ar komai

4. 2 Jahilci: Idan muka koma ta fuskar jahilci shi ma yana jefa mutum cikin talauci saboda matuƙar aka ce mutum bai san komai ba to lallai yana cikin duhu, to kuwa dole ne ya rayu cikin ƙunci kamar yadda Mu’azu Haɗeja a waƙar Ilmin Zamani yana cewa:

Da tsiya da talauci duk suna,

Gun da jahilci yai sansani.

Duk wanda yake ba ya shiga jama’a don yin ma’amalla to babu mamaki ya faɗa cikin talauci da ƙuncin rayuwa.

4. 3 Aikin Gwamnati: Bayan waɗannan kuma an samu baƙin dalilai da suka yi sanadin faɗawa talauci shi ne, karatu ko ilmin zamani, wani bahagon tunani da wasu ke da shi, shi ne, duk wanda yayi ilmin boko to dole sai ya samu aikin Gwamnati.

Ɗangambo (1984: 3) Wannan tunani ya kashe zukatan matasanmu da yawa, sun ƙi sana’a, saboda sun raina ta kuma aikin bai samu ba, dole sai zaman kashe wando, wanda yake ɗakinsu ɗaya da talauci.

Abdullahi (1993) cewa ya yi: Ma’aikaci ɗan albashi ko na Gwamnati, ko kamfani ko masana’anta, da shi da bashi ɗan wa ne da ɗan ƙani. Domin duk yadda zaka yi baka raba su da bashi. Ga wani kirarin Ɗan albashi:

Ɗan albashi mai taƙama da bashi,

 Ka yi aiki a bashi,

 A baka albashi ka biya bashi,

Ka ƙara cin bashi kafin wani albashin. [1]

4. 4 Siyasa: Shigowar siyasa shi ma ya ƙara ingiza mutanenmu a talauci, dalili kuwa shi ne ya kashe wa wasu zuciya da son a ci bulus ko cin banza, da yawon maula ko garam. Da yawa wasu sun watsar da sana’o’i, sun kama gaibu wai su kan su ya waye.

4. 5 Babba da jaka: Usman (2023) wato babakere da wasu ƙalilan suka yi a harkokin rayuwa,idan Gwamnati ta ƙirƙiro wani shiri na tallafawa talakawa masu ƙaramin ƙarfi, ko don a rage masu raɗaɗin talauci sai su handame, anan sai suka zama kamar bakan gizo, a ƙarshe kuma sai aka samu wasu masu yin kala kusa da tari, wato masu wawure dukiyar Hukuma. [2]

5. 0 ILLOLIN TALAUCI

Bahaushe kan yiwa talauci kirari da cewa: “Talau-talau mugun tsoho, ƙadagi ƙanin mutuwa, lalata mutum da sauran ransa”. Wannan kirari na talauci gaskiya ne, saboda talauci kan yi tasiri ga rayuwar Ɗan adam, ta kowacce fuska. Rayuwar ma gaba ɗaya takan samu dabaibayi ko tarnaƙi a kasa sukuni da walwala a cikin al’umma. Talauci kan yi tasiri matuƙar aka ce ya shafi mutum, to sai kuwa an ga alama. A kan wannan hujja ce ya sanya duk mutumin da ya tsinci kansa a cikin talauci ko kuma ya faɗa masa, yake shiga wani hali na gaba damusa baya siyaki. Mafi yawa mutane matalauta ke galabaita fiye da tsararrakinsu da suke da wadata. Wannan kuwa na bayyana ne tun daga ɗabi’unsu, da tunaninsu, da kamannunsu, kai hatta yanayin fatar jikinsu kan bambanta da sauran jama’a.

Shi kuwa Baba mai gyaɗa Agege marubucin waƙoƙin Hausa a waƙar ‘Yan Duniya cewa yayi: -

“Idan baka da dukiya, a yau an raina ka,

 Sa’o’in ‘ya’yanka, Su sukan riƙa taka ka.

 Idan kai Magana, Su ce wane fa yana hauka.

 Da ka yi shiru sai suce fa Wane bai cika fara’a ba. ”

Tabbas talauci kan haifar da illoli masu yawa waɗanda suka shafi mutum wato shi kansa matalaucin da kuma al’umma kai hatta da muhallinsa. Bisa lura da bayanai da suka gabata, ana iya cewa talauci na cutar da ko jawo illa ga rayuwar matalauci ko ya sani ko bai sani ba. Da farko talauci na haifar masa da wasu abubuwa takwas.

1. Baƙin jini ko rashin kwarjini,

2. Ƙyama,

3. Kyara,

4. Tsangwama.

5. Tauye tunani da hazaƙa na harkokin duniya da na mu’alla da jama’a.

6. Talauci na yanke zumunta,

7. Yana hana samun walwala, don yana tauye matalauci ya tsangwami kansa a inda zai riƙa ɗari-ɗari da jama’a.

8. Sanya zargi.

Bayan ga illolin da suka shafi matalauci shi kaɗai, to haka kuma akwai illolin da suka shafi al’ummar da yake cikinsu. Da farko dai talauci na haifar da ƙiyayya ko gaba a tsakanin mawadata musamman marowata da talakawa mabuƙata. Wannan na haifar da mummunar alaƙar zamantakewa,

6. 0 HANYOYIN MAGANCE TALAUCI A BAHAUSHIYAR AL’ADA

Akwai wasu hanyoyi ko dabaru waɗanda Bahaushe ya ƙirƙirar wa kansa waɗanda suke magance talauci. Dabara ta farko ita ce sana’a, haƙiƙa Bahaushe ya gaji sana’o’i masu yawa tun iyaye da kakanni. Baya waɗannan sana’o’i kuma akwai wasu hanyoyin taimakekeniya, kamar su gudumowa da tafiye-tafiye.

6. 1 SANA’A

6. 2 MUHIMMANCI SANA’A A BAKIN MAWAƘA.

Muhimmancin sana’a ya bayyana a bakin mawaƙan baka na Hausa da yawa, wasu sun yi waƙoƙin kai tsaye wasu kuma sun yi a kaikaice.

Alhaji Sani Aliyu Ɗandawo a waƙarsa ta Mutane a kama sana’o’i yace:

Mutane a kama sana’o’i,

A mai da hankali wajen noma.

Abdu Minjibir a waƙarsa ta Mu kama sana’a ‘yan Najeriya,Yace:

Mu kama sana’a ‘yan Najeriya,

zaman banza ba namu ne ba.

Sai kaga kanti na yawo a titi

ba asali ba tattali ba.

Mu kama sana’a ya fi kyau

tunda ya fi zama na lido da karta.

Zamanin nan wanda muke ciki

babu banza sai mara yin sana’a.

Alhaji Mamman Shata Katsina a waƙarsata Kai ‘yan yara gumina nake ci,

Yace:

Kai ‘yan yara gumina nake ci,

masu zuwa tebur su yi tebur

lebura kan hanya ku yi aiki

a yau kowane guminai yake ci.

Masu tireda nata tireda

su leƙa nangun

su leƙa can gun

wannan gumunsu suke ci.

Alhaji Adamu Ɗanmaraya a waƙarsa wofi mutumin banza ya ce:

wofi mutumin banza,

Wanda bai sana’ar komai,

Ga sana’ar fawa ita ma sana’a ce ai,

Ga turin kura,

ga yankan farce ita ma sana’a ce ai.

Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun a waƙarsa ta Noma babbar sana’a

Ya ce:

Noma babbar sana’a

koway yita ya bar rasawa

taimaki bayinka Allah,

Allah kai an mai iyawa.

Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun a waƙarsa ta Sarkin Muri

Ya ce:

Mai sana’a in dai akwai riba

sai ka riƙeta ba illa ne ba,

mai sana’a in baya cin riba,

shi ma riƙeta ba ririyal ne ba.

Hajiya Barmani Choge a waƙarta ta sakarai bata da wayo. ta ce:

Mata ku kama sana’a,

sakarai bata da wayo.

Duk wanda ba ta sana’a,

ta bani ta lalace.

Hajiya Barmani Choge a waƙarta ta Mai soso ke wanka. ta ce:

Mai soso ke wanka,

Duk wadda ba ta da shi sai ta ara,

Duk matar da bata sana’a aura ce.

7. 0 Sakamakon Bincike:

Babu shakka talauci a arewa ya zama ƙarda baƙon dole ana ba wuri yana kafa ɗaki ko kuma ana murna baƙo ya tafi ashe baƙo na bayan gari. Bisa zahiri kowa ya yarda cewa an ɗauki dogon zamani ana gudanar da rayuwa cikin baƙin talauci a Ƙasar Hausa. Tarihi ya nuna cewa tun ana amfani da wuri a matsayin kuɗi gabanin bunƙasar samun tsabar kuɗi da takardun kuɗi da zamani ya kawo Ƙasar Hausa. Haka kuma, a wancan lokaci ba a Ƙasar Hausa kaɗai aka yi fama da talauci ba, har da wasu sassan Afrika. Shigowar ilmin zamani, tare da kwaɗayin samun aikin Gwamnati sun bayar da gaggarumar gudummowa ga mutuwar zuci da raina sana’a tare da zaman kashe wando a Ƙasar Hausa. Ga ɗan abin da bincike ya hararo akwai:

1. Tabbacin cewa, binciken ya fito da wasu tunane-tunanen Bahaushe, game da talauci a fagage masu yawa.

2. Haka kuma binciken ya nuna talauci a matsayin wata tsohuwar Magana ce wadda take ta yi tasiri matuƙa a al’adar Bahaushe.

3. Binciken ya bayyana cewa talauci gyare tsohon nama ne don kuwa babu wanda ya san lokaci da aka fara talauci ko kuma mutumin da ya fara faɗawa talauci.

4. Bahaushe ya ba talauci mahimmanci shi yasa yake jefa shi a maganganun hikimarsa, a inda ya yi tasiri kuma har yanzu ake samun jirwaye ko nasonsa a dukkan rassan adabin baka.

5. Bahaushe na cewa ko ba a shafa ba maruru ya ɗara kaluluwa, ma’ana irin dabaru ko hanyoyin magance talauci, da suna samun tallafi daga Hukuma lallai da sun taimaka wa Ƙasar Hausa wajen rage talauci.

8. 0 Kammalawa

A ƙarshe, wannan Bincike ya nazarci tare da kawo bayani game da talauci da irin yadda Bahaushe yake kallon rayuwa da talauci, da sanadoji ko dalilai da suke jawoshi tare da fayyace illolinsa, da kuma matsayinsa a al’ada. Haka kuma an nuna wasu hanyoyi ko dabarun na kawar da talauci a tsakanin mutane. Sannan kuma an kawo fashin baƙin wasu muhimman kalmomi kuma da ma’anar talauci da sanadojin dake jawoshi, da ire-iren sunaye da Bahaushe ya kirashi da su. A ƙarshe kuma, an samar da wani abin nazari. Wanda zai kasance kamar wata taska ce, wadda za ta zama wuri da aka adana bayanai da suka shafi talauci. Sannan kuma wannan ajiya ta zama wani abu da zai amfani manazarta zuwa nan gaba.

 9. 0 Shawarwari.

Dangane da shawarwari waɗanda ya kamata mu ɗauka su ne:

Bisa lura da bayanai da suka gabata, ana iya cewa an gani kuma an gamsu. talauci wani aiki ne ko ɗabi’a mai matuƙar tasiri ga rayuwar Hausawa, saboda haka akwai buƙatar masana su ɗauki matakin fito tare da bayyana matsayinsa a al’ada.

 Ya dace masana masu koyar da wannan Harshe na Hausa mu bai wa juna shawarar neman mafita. Musamman a kan irin waɗannan abubuwa da ake da ƙarancin bayanai ko rubuce-rubuce game da su.

Akwai wasu abubuwa da yawa da suke buƙatar a fito da su don al’umma su ƙaru, kuma al’umma masu zuwa zasu yi alfari.

Akwai buƙatar yaƙar zuciya, da kuma cire ƙyuya mu zurfafa nazari a kan abubuwan da suka shafi al’adar Bahaushe. Mu daina raina ƙanƙantar abin da za a riƙa yin bincike akansa, ɗan abin da Allah Ya sa ka fito da shi, sai wani ya faɗaɗa tare da zurfafawa.

10. 0 MANAZARTA.

 Abraham, R. C. (1947) Dictionary of the Hausa Language London Hodder & Stoughton.

 Bargery, G. F. (1993) A Hausa-English Dictionary and English-Hausa Vocabulary Ahmadu Bello University Zaria.

 Bunza, A. M. (2006) “Gadon Feɗe Al’ada”, Lagos Tiwel Nigeria Limited.

 Bunza, A. M. (2009) “Narambaɗa” Lagos Ibrash Islamic Publication Centre Limited.

Bunza, A. M. (2014) “Wauta A Tunanin Bahaushe” Maƙala da aka gabatar a Jami’ar Umaru ‘Yar’adua, Katsina.

Ɗan Gambo A. (1983) Kitsen Rogo. Triumph Publication Kano.

Ɗangambo A. (1984) Rabe-Raben adabin Hausa da Muhimmancinsa garayuwar Hausawa. Triunph Publication Kano.

Daura S A (1970) Tauraruwar Hamada. Northern Nigerian Publication Company,Zaria.

Garba, M. (1998) Azancin Magana a Waƙoƙin Makaɗan Baka. M. A. Hausa.

 Bayero University Kano.

Gusau, S. M. (1996) Makaɗan da Mawaƙan Hausa Fisbas Media Service Kaduna.

Imam A. (1973) Ruwan Bagaja Northern Nigerian Publication Company, Zaria.

Imam A. (1973) Magana Jari ce Littafi Na 2, Northern Nigerian Publication Company, Zaria.

Jabiru A (1970) Nagari Na kowa Northern Nigerian Publication Company,Zaria.

Ƙamusun Hausa (2006) C. N. H. N. Jami’ar Bayaro Kano.

Katsina M. S (1960) Uwar Gulma. Northern Nigerian Publication Company, Zaria.

Wushishi, B. J. (1998) Adabin Baka sigoginsa a Hikimominsa. M. A. Hausa

 Bayero University Kano.




[1] Abdullahi Mustapha (1993) hira da shi a gidansa layin Bashama tudun wada Kaduna.

[2] Usman Babangida Haɗejia (2023) A shirin Fitilar Rayuwa Rediyon Sawaba F.M Haɗejia.

 Hausa Post

Post a Comment

0 Comments