An ciro daga littafin:
BIƊA DA TANADI A DUNIYAR INTANET
(Sana’o’i, Kasuwanci, Ƙwadago)
Na
Abu-Ubaida SANI
Abdulrahman ALIYU
3.4 Tasirin Intanet Ga Hausawa
A
yau, intanet ya yi matuƙar tasiri ga rayuwar
Hausawa. Wannan tasiri ya shafi ɓangarori daban-daban, tun daga harshen kansa,
har zuwa adabi da al’adun al’ummar. Al’ada da harshe da adabin Hausawa duk sun
samu sauye-sauye a sakamakon tasirin zamani, musamman intanet. Dansabe (2019
sh. 138) yana da fahimtar cewa, kafafen sada zumunta suna taimakawa wajen
haɓaka al’adun da suka haɗa da “abinci da sutura da sana’o’i da bukukuwa da
tarbiyya da kuma zamantakewa.”
Tahir
(2016) yana
da fahimtar cewa, ta hanyar adana adabin baka a duniyar intanet ne kaɗai adabin
harshe zai ci gaba da dauwama. Koma-bayan haka, sannu a hankali za a neme shi a
rasa. Ya nuna cewa, matakin da za a iya ɗauka shi ne na adanawa da yaɗa adabin
baka ta hanyar fasahar intanet. Ta haka ne za a samar da wani kandamin kundin
adabin bakan (Tahir, 2016 sh. 133).[1]
Wamba
(2019 sh. 97) ya bayyana cewa: “Bayan sauyin zamani mai ƙarfi na samuwar intanet, waƙoƙin baka sun samu haɓaka
sosai.” Haɓakar waƙoƙin baka da aikin Wamba (2019) yake
magana a kansa zai iya shafar:
a. Kafafen
intanet da na sada zumunta da ake yaɗa bidiyoyi da odiyo-odiyo na waƙoƙin
b. Yadda
ake iya tura odiyo da bidiyoyin waƙoƙin cikin sauƙi a wayoyi da sauran na’urori dangin kwamfuta ko memori
c. Yadda
ake iya samar da manhajojin waƙoƙin sannan a ɗora su cikin rumbunan manhajoji kamar
PlayStore da makamantansu
d. Yadda
ake ɗaukar hannu daga salon waƙoƙi da kayan aikin haɗa waƙoƙi na waɗansu al’umma
sakamakon kallo a kan intanet
Wani
abin lura shi ne, binciken matakan adanawa da bunƙasa harshe da al’ada da
adabi na da matuƙar alaƙa da juna. Lura da tasirin da zamananci yake da shi a kan
intanet, Yakasai (2010 sh. 126) yana da fahimtar cewa: “... a fili yake cewa
matsalolin harshe a Nijeriya na buƙatar a yi wani abu na gaggawa domin adana harsunan gida,
cikin ƙalubalen
shirin zamanantar da duniya.” Ya nuna cewa, ta wannan hanya ce kawai za a iya
tabbatar da cigaban harshe da kuma al’adunsa. Ya jaddada cewa: “... duk ƙasar da ba ta ga fa’idar
adana harsunanta ba, to kuwa ba za ta iya adana al’adunta ba, musamman ma da
yake ta hanyar harshe kawai za a iya tabbatar da ɗorewar al’ada.” Yakasai (2010
sh. 123).
A
ɓangare guda kuwa, yana da kyau a fahimci yadda intanet yake
da gurbi na musamman a harkar tsaro a yau. Hasali ma, ƙoƙarin da ya fara samar da
intanet an yi shi ne ƙarƙashin hukumar tsaro a Amurka kamar yadda binciken Bincike
Gerf (2004 sh. 1360) da Mukoshy, (2015 sh. 21) suka tabbatar. Tasirinsa a yau a
bayyane yake. Muhimmin bagire ne na yaɗa farfagandar siyasa da yaƙin sunƙuru.
A
fannin tasirin intanet a kan kasuwanci da sana’o’in Hausawa kuwa,
abin kullum gaba yake ƙara yi. Ko a bayyane ana iya lura da hakan ta yadda
sitatus-sitatus ɗin ‘yammata da samari da dama suke cika da tallace-tallacen
hajoji daban-daban. Ko da ma dai, biɗa da tanadin Hausawa a duniyar intanet shi
ne ƙashin
bayan wannan bincike. Almajir (2013 sh. 9) da Rambo (2014 SL. 26) sun kawo
yadda Hausawa suke ƙulla kasuwanci a kan intanet tare da amfani
da katin banki wajen tura kuɗin sayayyar kaya. Aikin Mukoshy (2016) ma ya kawo
yadda intanet yake taimakawa wajen samar da aikin yi da ba da damar gudanar da
kasuwanci da biyan kuɗi ta kan intanet.
Lura
da duk waɗannan bayanai da alƙaluma, ana iya zayyano amfanin intanet kamar haka:
1. Intanet
yana
taimakawa wajen samun tallafi daga masu aikin jinƙai a faɗin duniya, dangane
da wata annoba ko wani aikin da ake son aiwatarwa.
2. Intanet
yana
taimakawa wajen yaɗa bayanai cikin gaggawa.
3. Intanet
yana ba da damar bayyana ra’ayoyi cikin sauƙi, waɗanda suka shafi
siyasa da zamantakewa da makamantansu.
4. Intanet
yana
ba da damar kallon abubuwan da suke gudana kai tsaye a waɗansu wurare na kusa
ko na nesa ta hanyar fasahar nuna abu kai tsaye (livestreaming).
5. Intanet
yana
ba da damar kauce wa hasarar kuɗi da dukiya ta hanyar adana kuɗi a bankunan
zamani tare da amfani da tsarin taransifa.
6. Intanet
yana
ba da damar samar da makarantu da halartar su a sauƙaƙe ba tare da wahalar da
jiki ko neman wurin zama da bayyanannun kayan aikin koyarwa ba.
7. Intanet
yana
ba da damar samun bayanai masu muhimmanci game da fannonin rayuwa, kamar kiwon
lafiya da tarihi da al’adu da al’ummomi da makamantansu.
8. Intanet
yana
ba da damar samun shawarwari daga abokai ko waɗansu mutane da suke ba da haske da
ƙarfafa
guiwa a kafafen intanet daban-daban.
9. Intanet
yana
samar da ayyukan yi ga mutane da dama.
10.
Intanet yana
samar da hanyoyin adana bayanai cikin sauƙi tare da kaiwa gare su a duk lokacin da ake
buƙata.
11.
Intanet yana
samar da hanyoyin gudanar da kasuwanci a sauƙaƙe.
12.
Intanet yana
taimaka wa lafiyar ƙwaƙwalwa a matsayin wani abokin hira da ɗebe kewa.
13.
Intanet yana
taimakawa a ɓangaren tafiye-tafiye, ta hanyar taswirorin wurare kamar Google
Map da makamantansu.
14.
Intanet yana
taimakawa a ɓangaren tsaron ƙasa da na yankuna da na ma’aikatu.
15.
Intanet yana
taimakawa wajen adana muhimman bayanai da suka shafi al’adu da adabi da harshe
da tarihi da sauran nau’o’in ilimummuka daban-daban.
16.
Intanet yana
taimakawa wajen aikin haɗin guiwa cikin sauƙi tsakanin mutanen da suke
da nisa da juna.
17.
Intanet yana
taimakawa wajen duba yanayi tare da tsara gudanar da lamura ta la’akari da
yanayin da ake sa ran fuskanta, kamar ruwan sama ko iska da sauransu.
18.
Intanet yana taimakawa wajen gwagwarmayar neman ‘yanci, musamman ta hanyar
shirya zanga-zangar lumana da tattauna ra’ayoyi da mafita game da waɗansu ƙalubalen danniya ko wariya
ko rashin adalci da al’umma suke fuskanta.
19.
Intanet yana taimakawa wajen kai saƙo ko samun saƙo daga wata uwa duniya, ko
tura buƙatar
wani abu kamar kiran direban mota da makamantansu.
20.
Intanet yana
taimakawa wajen rage cunkoson ababen hawa yayin da ya kasance mutane na ayyuka
daga gida a maimakon zuwa ofisoshi.
21.
Intanet yana
taimakawa wajen sadarwa a sauƙaƙe.
22.
Intanet yana
taimakawa wajen samar da dandali da gidajen nishaɗantarwa.
23.
Intanet yana
taimakawa wajen samun ƙawararrun ma’aikatan wucin-gadi (freelancers) domin
gudanar da ayyuka masu buƙatar ƙwarewa da fasaha.
24.
Intanet yana
taimakawa wajen samun sababbin abokai.
25.
Intanet yana taimakawa wajen sanya ido ga gida ko wurin aiki yayin da ake wani
wuri na daban, ta hanyar kyamarorin zamani da suke tura hotuna da sautuka da
bidiyoyi ta intanet.
26.
Intanet yana
taimakawa
wajen fahimtar al’adun al’ummomi cikin sauƙi.
Duk
waɗannan (da ma waɗansu da wataƙila tunani bai kai kansu ba) suna daga cikin nau’o’in
alfanun da intanet ya zo da su, waɗanda kuma Hausawa suna daga cikin al’ummomin
da suke cin gajiyarsu.
3.5 Tasirin Hausawa a Kan Intanet
Masu
iya magana sun ce: “Idan an bugi jaki, sai a bugi taiki.” A wannan gaɓa, yana
da kyau a fahimci cewa tasirin da ake samu bai taƙaita ga wanda intanet yake
yi a
kan Hausa da Hausawa ba. Su ma Hausawa suna da tasiri a kan intanet. Ana iya fahimtar
hakan tun daga yadda ake samar da gurabu da ba da kulawa ta musamman ga Hausa
da Hausawa a intanet.
A
fannin kasuwancin kan intanet, an sanya Hausa a matsayin ɗaya daga cikin
harsunan da ake mu’amala da su a kan kafar hadahadar kuɗin intanet ta Paxful
(https://paxful.com)
a farkon shekarar 2021. Wannan yana nuni ga muhimmancin Hausawa a kan wannan
kafa da tasirin da suke da shi na yin ciniki a cikinta . A duba hoton da yake ƙasa:
Hoto Na 3.10: Zaɓin Harshen Hausa a Kan Kafar Paxful
Madogara:
Shafin shiga akawun ɗin
Paxful (https://accounts.paxful.com/login/)
Tasirin
Hausa a duniyar intanet ya kai wani mataki inda har ta samu shiga cikin jerin
harsunan da ake amfani da su a kafar Fesbuk. “Yanzu haka masu amfani da shafin
da dama suna yi ne ta hanyar amfani da harshen Hausa a matsayin harshen umurni”
(Morison a cikin ’Yartsakuwa, 2017 sh. 26). Masu amfani da Fesbuk suna da damar
mayar da saitin akawun ɗinsu cikin harshen Hausa.
Bayan
haka, kamfanin Fesbuk yana ba da dubban ɗaruruwan rubuce-rubuce da aka yi a kan
Fesbuk domin a fassara su zuwa harshen Hausa. Duk wani rubutu da aka yi kan
Fesbuk cikin wasu harsuna daban, mutum yana da damar duba fassarorinsu cikin harshen
Hausa. Idan ya kasance ba a fassara su zuwa Hausa ba a daidai lokacin da aka
duba, injin ɗin Fesbuk zai yi ƙoƙarin fassara su ta hanyar amfani da ilimin makamantan
fassarori da suka gabata. Hoton da yake ƙasa ya kawo misalin akawun ɗin Fesbuk cikin
harshen Hausa:
Hoto
3.11: Tsarin
Fesbuk Cikin Harshen Hausa
Madogara: Akawun Ɗin Abdulrahman Muhammad Manga na Fesbuk
A
hoto na 3.11 da yake sama, za a iya lura da cewa akawun ɗin
Fesbuk ɗin cikin harshen Hausa yake. Dukkanin ɓangarorin akawun ɗin an sanya
sunayensu ne cikin harshen Hausa. Haƙiƙa wannan ci gaba ne sosai ga harshen. Hakan
kuwa ya samo asali ne sakamakon tasirin da Hausawa suke da shi a wannan kafa ta
Fesbuk, sakamakon yawansu da yanayin amfaninsu da kafar.
Yayin
da aka bincika jerin harsunan da ake iya amfani da su a kan Fesbuk, za a tarar
da cewa ba su kai ɗari da hamsin (150) ba (har ya zuwa ranar 17 ga watan
Fabarairu na shekarar 2024). Kada a manta da cewa, harsunan duniya ba su gaza
dubu bakwai (7,000) ba (Bunza, 2019 sh. 7). Ko Yoruba da Igbo da suke bi ma
Hausa cikin harsunan Nijeriya ba su da gurbi a Fesbuk.
Bugu
da ƙari,
kamfanin Gogul ya daɗe da ba wa Hausa muhimmanci. Yakan fitar da dubban
ɗaruruwan jumloli da kalmomi a-kai-a-kai domin fassara. Kamfanin yana da injin
fassara wanda aka fi sani da Google Online Translator (Injin Ɗin Fassarar Gogul Na Kan
Intanet). Daga cikin harsunan da suke kan wannan tsari har da Hausa.
Kasancewar harshen Hausa a kan wannan kafa na nuni da tasirinta a duniyar
intanet. Manyan kamfanonin da suke ire-iren waɗannan muhimman ayyuka, ba sa yi
har sai idan akwai wani alfanu da za su samu daga hakan.
Wani
ƙalubale
na wannannan injin ɗin fassara shi ne, yana iya kasancewa a ci karo da fassarar
da ba ingantacciya ba. Hakan yana faruwa ne kasancewar yayin da jumlar da
aka bincika ba ta da fassara a cikin injin ɗin, to injin zai ƙirƙiri fassararta. Zai ƙirƙiri fassarar ne ta hanyar
amfani da ilimin fassarori makamantanta da suke kan injin ɗin. A kullum
kamfanin yana ƙara inganta tsarin. A ƙasa an ba da misalin
fassara mai inganci da marar inganci waɗanda aka ɗauko daga injin fassara na
Gogul ranar 28 ga watan Fabrairun shekarar 2024:
Hoto
3.12: Fassara
Mai Inganci Daga Injin Fassara na Gogul
Madogara: https://www.google.com/search?q=english+to+hausa
A
hoto na 3.12 da aka kawo a sama, za a iya lura da cewa fassarar da injin na
Gogul ya bayar tana da inganci. A ƙasa an kawo misalin fassara mai rauni (duba hoto na
3.13):
Hoto
3.13: Fassara
Marar Inganci Daga Injin Fassara na Gogul
Madogara: https://www.google.com/search?q=english+to+hausa
A
hoto na 3.13 da yake sama, za a iya lura da cewa, fassarar da
injin na Gogul ya bayar tana da rauni. Ya fassara “liar” a matsayin
“karya” a maimakon “maƙaryaciya”. Bayan haka, bai yi amfani da baƙin /ƙ/ mai ƙugiya ba. Ko bayan haka, an
yi amfani da Bagwariyar Hausa (suka ce) wanda hakan yake nuni da fassarar injin
ce kai tsaye.
Ko
bayan Gogul, akwai waɗansu injunan fassara a kafafen intanet waɗanda Hausa take
ɗaya daga cikin harsunan da suke kansu (supported languages). Wasu kuwa ƙamusoshin fassara ne daga
cikin harshen Hausa zuwa wasu harsuna daban, ko kuma daga wasu harsuna zuwa
harshen Hausa. A ƙasa an kawo misalan wasu daga ciki:
1. Bargery
Online Dictionary (Ƙamusun Bargery na Kan Intanet). Adireshinsa shi ne: http://maguzawa.dyndns.ws/.
2. Hausa
Dictionary (Ƙamusun
Hausa). Adireshinsa shi ne: http://hausadictionary.com/Main_Page.
3. Stars
21 (Taurari 21). Adireshinsa shi ne: https://www.stars21.com/translator/english_to_hausa.html.
4. Translation
2 (Fassara 2). Adireshinsa shi ne: https://translation2.paralink.com/English-Hausa-Translator/.
5. Translator
(Mai fassara). Adireshinsa shi ne: https://imtranslator.net/translation/hausa/to-english/translation/.
Bugu
da ƙari,
akwai manhajojin fassara daban-daban da ake iya amfani da su a kan wayoyin
salula. Ana iya sauƙe ire-irensu daga rumbunan manhajoji kamar PlayStore ko
F-Droid da sauransu. A ƙasa an kawo misalai cikin hoto:
Hoto Na 3.14: Misalan Manhajojin Fassara Zuwa Harshen Hausa
Madogara: Rumbun Manhajoji na PlayStore.
A ɓangare
guda kuwa, kafar Wikifidiya (Wikipedia) fitacciya ce a duniyar intanet.[2] Da
wuya a binciki wata kalma a injin nema na Gogul ba tare da an ci karo da zaɓin
Wikifidiya ya fito a shafin farko ba. Rubuce-rubucen wannan kafa ya shafi
dukkanin ɓangarorin rayuwa tun daga kan siyasa da zamantakewa da addini da
tarihi har zuwa kiwon lafiya da harsuna da al’adu da dai sauransu. A yanzu
haka, wannan kafa ta fara samar da bayanai cikin harshen Hausa.[3]
Babu makawa wannan kafa za ta taimaka wa harshen matuƙa wajen yaɗuwa da yayatuwa
a duniya.[4] A ƙasa an kawo misalin shafin
farko na wannan kafa cikin hoto.
Hoto
3.15:
Kafar Wikifidiya ta Hausa
Madogara:
Shafin farko na Wikifidiyan
Hausa (https://ha.wikipedia.org/wiki/Babban_shafi)
A
hoto na 3.15 da aka kawo a sama, za a iya lura da cewa wannan shafi na
Wikifidiya cikin harshen Hausa yake. A zuwa lokacin da aka ɗauki hoton (ranar
28 ga watan Fabrairu, shekarar 2024), an ɗora rubuce-rubuce guda dubu talatin
da takwas da ɗari biyar da sittin da bakwai (38,567) a kansa. Wannan ya nuna
yadda shafin yake ci gaba sosai. Dalili kuwa shi ne, a ranar 25 ga watan Maris
na shekarar 2020, maƙalun da suke kan shafin sun kasance dubu huɗu da ɗari
bakwai da tara (4,709) kawai.
Za
a iya fahimtar wani tasirin Hausawa a kan intanet daga al’amarin da ya faru na
dakatar da ayyukan Tuwita (Twitter) a Nijeriya (5 ga watan Yunin shekarar 2021
zuwa 13 ga watan Janairun shekarar 2022). Duk da cewa wannan ya shafi Nijeriya
ne baki ɗaya, ba Hausawa kawai ba, Hausawan suna daga cikin waɗanda ake yawan
kallon rubuce-rubucensu a kan wannan kafa. Katse harƙallolin Tuwita a Nijeriya
ya yanyo wa kamfanin hasarar kuɗaɗe masu tarin yawa.[5]
Adadin
Hausawan da suke kan manhajar TikTok ma yana nuni da tasirinsu a kan intanet. Dubban
Hausawa maza da mata ne suke amfani da wannan kafa. Suna gudanar da harƙalloli daban-daban tun daga
kan abin da ya shafi barkwanci da nishaɗantarwa da wa’azantarwa har zuwa kan
koyar da nau’o’in ilimomi daban-daban.[6]
[1] A Ingilishi ya rubuta
cewa: “The possible action that we take is to preserve and promote our oral
traditions by the use of digital technology, creating a comprehensive and
database of our oral traditions.”
[2] Domin ƙarin bayani a kan wannan
kafa ana iya duba https://wikipedia.org.
[3] Shafin farko wanda ake
kira “gida” (home page) na Hausa da yake kan kafar Wikifidiya yana da adireshi
kamar haka: https://ha.wikipedia.org/wiki/Babban_shafi.
[4] Ya rage ga masana da
manazarta Hausa da su shiga a dama da su cikin harkar bunƙasawa da inganta wannan
kafa. Koma bayan haka, kafin a farga, ɓarnar da za a yi wa Hausa a ilimance ba
za ta misaltu ba!
[5] Domin samun ƙarin bayani, ana iya duba
BBC Hausa (2022).
[6] An kawo cikakken bayanin harkokin Hausawa a kan TikTok a babi na huɗu.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.