Ticker

6/recent/ticker-posts

Illolin Intanet Ga Hausawa

An ciro daga littafin:

BIƊA DA TANADI A DUNIYAR INTANET
(Sana’o’i, Kasuwanci, Ƙwadago)

Na

Abu-Ubaida SANI
Abdulrahman ALIYU

Bida Da Tanadi a Duniyar Intanet (Sana’o’i, Kasuwanci, Kwadago)
Manazartar Littafi: Sani, A-U. & Aliyu, A. (2026). Biɗa Da Tanadi a Duniyar Intanet (Sana'o'i, Kasuwanci, Ƙwadago). Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-978-62480-1-1. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.21361768

Tuntuɓa Domin Samun Littafi: 
Dr. Abu-Ubaida Sani: Imel - abuubaidasani5@gmail.com | WhatsApp - 08133529736
Dr. Abdulrahman Aliyu: WhatsApp - 08036954354

3.6 Illolin Intanet Ga Hausawa

Intanet hanjin jimina ne, akwai na ci akwai na zubarwa. Duk da ɗumbin alfanun da yake tattare da intanet, ya zo da tarin matsaloli da ƙalubale. Daga cikinsu akwai waɗanda suka kasance gama-gari. Akwai kuma waɗanda suka shafi al’ummar Hausawa kai tsaye (da sauran al’ummu da suke al’adu da falsafa irin na Hausawa).

Rambo (2014 SL. 42-56) ya kawo waɗansu illolin intanet ga Hausawa. Sun haɗa da, taɓarɓarewar tarbiyya da yaɗa ƙarya da haddasa gaba da tonon silili da makamantansu. Haka kuma, yana da fahimtar cewa intanet yana daga cikin dalilan da Hausawa suka rungumi rayuwar ƙarya a yau, musamman domin burgewa a kafafen sada zumunta. Wannan fahimta ta yi daidai da ta Umar (2012 sh. 119-127) inda har ya jaddada cewa, wayoyin zamani suna daga cikin dalilan mace-macen auren Hausawa a yau.

Masana da manazarta daban-daban sun bayyana yadda intanet take da tasiri a kan Hausa da Hausawa. Aikin Dansabe (2019) ya fi mayar da hankali a kan yadda intanet yake tasiri a kan al’ada da adabi. Dansabe (2019 sh. 143) ya zayyano illolin intanet musamman kafafen sada zumunta kamar haka: (a) gurɓata tarbiyya da (b) koyar da shigar fitsara da (c) koyar da fasiƙanci da (d) durƙusar da adabin Hausa.

Gobir & Sani (2021 sh. 117-120) sun nuna yadda intanet da kafafen sada zumunta suke haifar da dusashewar wasannin gargajiya na Hausawa, musamman wasannin kwaikwayo. Hakan yana faruwa ne yayin da hankula suke karkata a kan wasannin zamani da suke kan na’urori. Dusashewar wasannin kuwa yana haifar da gushewar danƙon zamantakewa da cuɗanya tsakanin yara. A ɓangare guda kuwa, yana haifar da dusashewar waɗannan al’adu masu matuƙar taimakon yara a fannin motsa jiki da fasaha da ilimantarwa da koyar da lissafi da sauran dabarun zaman duniya.

Ta la’akari da waɗannan ayyukan da suka gabata, ana iya fahimtar cewa illolin intanet ga Hausa da Hausawa sun haɗa da:

1. Akan yi amfani da intanet domin cin mutunci ko ɓata suna ga wani mutum ko waɗansu mutane.

2. Ana iya dogaro sama da ƙima a kan intanet wanda hakan naƙasu ne ga bunƙasar basirar mutum. Wannan ya haɗa da neman kowane nau’in bayani ko mafita a kan intanet kai tsaye ba tare da amfani da basira wajen ƙoƙarin samun mafita ba.

3. Aurar intanet yana iya haifar da naƙasu ga koyon muhimman lamuran zamantakewa, kamar jawabi ga mutane ko zurfafa tunani da yanke hukuncin da ya dace game da abubuwan da suke buƙatar nazari.

4. Intanet ƙalubale ne ga sirrin duk wani mai amfani da ita .

5. Intanet yana haifar da salwantar waɗansu adabin baka.

6. Intanet yana haifar da taɓarɓarewar zamantakewa.

7. Intanet yana iya haifar da matsalolin da suka shafi rashin bacci yayin da yake ɗauke wa mutum hankali daga bin tsarin hutun da ya dace a bisa yanayin halittar ɗan’adam.

8. Intanet yana iya kasancewa hanyar damfara da zamba.

9. Intanet yana janyo ɓata lokaci da koma-baya ga gudanar da ayyuka yadda suka kamata.

10. Intanet yana kame zuciya ta yadda har akan ƙwallafa rai da rungumar ta ba-ji-ba-gani.

11. Ƙwallafa rai a kan intanet yana iya haifar da ƙaurace wa al’umma da zaman kaɗaici sama da ƙima wanda hakan ka iya shafar lafiyar mutum.

12. Labaran ƙarya suna da saurin yaɗuwa sakamakon intanet.

13. Mutane suna hasarar kuɗaɗe a kan intanet yayin da suka ɓata datarsu ba ta hanyar wani abin da yake mai amfani a gare su ba.

14. Tarbiyya tana iya gurɓacewa ta dalilin intanet.

15. Tasirin intanet yana haifar da mutuwar al’adu.

16. Yawan amfani da intanet yana iya illata lafiya, misali yin ƙiba sama da ƙima yayin da aka auri intanet, ko kuma ciwon ido na ɗan lokaci yayin da aka tsananta kallon fuskar na’ura.

3.7 Naɗewa

La’akari da bayanan da suka gabata a wannan babi na uku, lallai intanet gagarumin al’amari ne da ya samar da sauye-sauye a ɓangarori daban-daban na rayuwar ɗan’adam. Tasirin intanet ya ratsa al’adu da harsuna da adabi a duniya. Haka kuma, a kullum mutane suna ƙara yin tasiri tare da sauya akalar lamura daban-daban da suka shafi intanet. Duk al’ummar da ba ta tashi tsaye wajen wakiltar kanta a intanet ba, akan samu wasu al’ummomi daban sun yi amfani da wannan dama domin taka rawa a madadin al’ummar.

Post a Comment

0 Comments