Ticker

6/recent/ticker-posts

Tabbatar Da Ingancin Fassara (Linguistic Quality Assurance (LQA))

An ciro daga littafin:

BIƊA DA TANADI A DUNIYAR INTANET
(Sana’o’i, Kasuwanci, Ƙwadago)

Na

Abu-Ubaida SANI
Abdulrahman ALIYU

Bida Da Tanadi a Duniyar Intanet (Sana’o’i, Kasuwanci, Kwadago)
Manazartar Littafi: Sani, A-U. & Aliyu, A. (2026). Biɗa Da Tanadi a Duniyar Intanet (Sana'o'i, Kasuwanci, Ƙwadago). Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-978-62480-1-1. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.21361768

Tuntuɓa Domin Samun Littafi: 
Dr. Abu-Ubaida Sani: Imel - abuubaidasani5@gmail.com | WhatsApp - 08133529736
Dr. Abdulrahman Aliyu: WhatsApp - 08036954354

Tabbatar Da Ingancin Fassara (Linguistic Quality Assurance (LQA))

Yayin da aka kammala fassara, akwai buƙatar dubawa da tabbatar da ingancinta. Mafi yawan manhajojin fassara (CAT Tools da Workbenches) suna da tsarin tabbatar da ingancin fassara a cikinsu. Waɗansu daga cikin manhajojin fassara da suke da wannan tsari waɗanda kuma ake ayyukan Hausa a kansu sun haɗa da:

i.Crowdin (https://crowdin.com/)

ii.memoQ (https://www.memoq.com/)

iii.Phrase (https://phrase.com/)

iv.TMS (http://gt.gotransparent.com/)

v.Wordfast (https://www.wordfast.net/)

Yayin da mai fassara yake aiki a kan ire-iren waɗannan manhajoji, kai tsaye zai iya duba matsalolin da suke tattare da fassarar domin gyarawa. Akwai kuma manhajojin da suka shahara a ɓangaren fitar da rahoton ingancin fassara. “Hausawa masu aikin fassara sukan yi amfani da irinsu” A.M. Umar (keɓantacciyar tattaunawa, 17 ga watan Satumba 2024). Yayin da aka gudanar da fassara, za a shiga sashen da zai duba matsalolin da suke tattare da fassarar. Daga nan za a sauke rahoton a matsayin fayil mai cin gashin kansa. Waɗannan manhajoji sun haɗa da:

i.Transform 

ii.Xbench

Yayin da aka ciro bayanan matsalolin da suke tattare da fayil, akan nemi ƙwararre da ya iya aikin domin a ba shi. Nau’o’in matsalolin da ake iya samu a tattare da aiki sun haɗa da:

a. Ba wa wani ɓangaren rubutu (iri ɗaya da ya fito a wurare biyu ko sama da haka) fassarori daban-daban[1]

b. Ba wa ɓangarrorin fassara biyu mabambanta fassara iri ɗaya[2]

c. Fassara wuraren da ba a fassarawa (DNTs)[3]

d. Saɓa wa gurbin ƙunshiyar rubutu (placeholder)[4]

e. Saɓa wa ƙa’idojin rubutu[5]

f. Sanya adadin harufan da suka haura waɗanda aka ƙayyade a fassara[6]

g. Tsallake kalmomi ba tare da an fassara ba

Ko bayan waɗannan da aka zayyano, akwai nau’o’in matsalolin da na’ura za ta iya zayyanowa a matakin Tabbatar Da Ingancin Fassara. Wani abin lura a nan shi ne, ɗan ƙwadagon kan intanet da yake wannan aikin zai iya cin karo da matsaloli nau’o’i biyu:

i.Matsalolin gaskiya (Actual/Real Issues)

ii.Matsalolin da ba na gaskiya ba (False Positive)

Yana da kyau a tuna cewa, na’urori ne suke fito da jerin wuraren da aka samu matsala ba mutane ba. Akwai wuraren da na’ura za ta ɗauki wani al’amari a matsayin matsala, alhali a zahirin gaskiya ba matsala ba ce. Ire-iren wuraren su ake kira ‘False Positive’ (FP). Misali mai sauƙi a nan shi ne, a duk lokacin da aka rubuta kalma mai ɗauke da hamza a sashen manufa (target string), to na’ura za ta bayyana sashen a matsayin mai matsala saboda ba ta ga hamza a sashen tushe (source string) ba. Misali, yayin da aka fassara freedom da ‘yanci, to na’ura za ta nuna /’/ a matsayin rashin daidaiton alamomin rubutu (inconsistency in punctuation). A irin wannan yanayi, ɗan ƙwadagon da yake aikin zai nuna cewa matsalar ba ta gaskiya ba ce (FP).


[1] Wannan nau’in matsalar ana kiran ta ‘Rashin Daidaito a Sashen Tushe’ (Inconsistency in Source).

[2] Wannan nau’in matsalar ana kiran ta ‘Rashin Daidaito a Sashen Manufa’ (Inconsistency in Target).

[3] Ana kiran su da suna ‘Kada a Fassara’ (Do Not Translate (DNTs)).

[4] Gurbin ƙunshiyar rubutu (placeholder) alamomi ne da ake sakawa a cikin fassara waɗanda bami idan ya gan su, ba zai iya gane abin da suke nufi ba. A ƙashin kansu ba su da wata ma’ana. Duk da haka, ƙwararre zai iya karanta rubutun da yake wurin daidai ta hanyar ba su wata ma’ana ta musamman. Misali, yayin da aka rubuta “%^% da wasu mutane %#$ sun duba rubutun da ka ɗora ranar %#@”, haƙiƙanin yadda yake yana iya kasancewa “Musa da wasu mutane 85 sun duba rubutun da ka ɗora a ranar 23/07/2024.”

[5] Ana kiran wannan da suna ‘Rashin Daidaiton Alamomin Rubutu’ (Inconsistency in Punctuations)

[6] Akwai fayilolin fassarar da ake ƙayyade adadin harufan da ake buƙata ga fassarar kowane sashe. Yayin da aka haura adadin ko da da harafi ɗaya ne, to akwai buƙatar sai an duba an bi wata hanyar da za a rage adadin harufan.

Post a Comment

0 Comments