Ticker

6/recent/ticker-posts

Shafukan Farko - Zogale a Kasar Hausa: Magani, Abinci, Tattalin Arziki

An Ciro Daga: Bakura, A.R., & Sani, A-U. (2026). Zogale a ƙasar Hausa: Magani, abinci, tattalin arziki. SAS Publishers. ISBN: 978-978-63958-1-4. https://doi.org/10.5281/zenodo.22682300

 Na

Adamu Rabi’u Bakura

Da

Abu-Ubaida Sani

Zogale a Kasar Hausa: Magani, Abinci, Tattalin Arziki

SADAUKARWA

Mun sadaukar da wannan littafin ga iyaye da malamanmu da duk waɗanda suka taka rawar gani wajen karatu da gwagwarmayar rayuwarmu har zuwa yau.

Jinjina ta musamman ga mutanen ƙwarai da suke aikata aiki nagari; tare da kira zuwa ga jama’a a kan gudanar da nagartattun ayyuka.

GODIYA

Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin Ƙai. Allah ya yo daɗin salati ga Manzon Tsira, Muhammadu (SAW), ya ƙara masa rahama tare da iyalansa da sahabbansa da mabiya tafarki nagari har ya zuwa ranar ƙiyama.

A har kullum, muna jaddada godiyarmu ga iyaye da malamanmu da suka sha ɗawainiyoyin rayuwa da mu, saboda mu zama nagartattun mutane. Sun yi ƙoƙari a rayuwarmu tun daga kan tarbiyantarwa har zuwa jagoranci a tafarkin neman ilimi da aiki da shi, da kuma shawarwari nagartattu. Allah ya jiƙan marigaya a cikinsu. Waɗanda muke kan hanya tare da su, Allah ya ƙara mana imani da albarkar rayuwa da za su kai mu ga kyakkyawan ƙarshe.

Muna miƙa godiya ta musamman ga malaman da suka sadaukar da lokutansu domin dubawa da ba da shawarwari don daidaita alƙiblar wannan littafi, wato:

Ø Prof. Salisu Ahmad Yakasai (UDUSOK)

Ø Prof. Yakubu Aliyu Gobir (UDUSOK)

Ø Dr. Jibril Yusuf (KASU)

Ø Malam Ibrahim Dalha (SLU)

Muna ɗimbin godiya ga dukkannin malamai da ma’aikata da suke Jami’ar Gwamnatin Tarayyara Gusau, musamman waɗanda suke Sashen Koyar da Harsuna da Al’adu .

Muna miƙa ɗimbin godiya da yabo ga waɗanda suke ƙarfafa mana guiwa a wannan fanni na bincike da rubuce-rubucen ilimi, wato:

Ø Prof. S. M. Gusau (BUK)

Ø Prof. AB. Yahya (UDUS)

Ø Prof. Haruna A. Birniwa (UDUS)

Ø Prof. I. Malumfashi (KASU)

Ø Prof. Tukur Adamu (FUGUSAU)

Ø Prof. Aliyu Moyi (FUGUSAU)

Ø Prof. Lawal Sa’ad (FUGUSAU)

Ø Prof. I.S.S. Abdullahi (UDUS)

Ø Prof. Ahmad Galadima (FUGUSAU)

Ø Dr. Mas’ud Bello (FUGUSAU)

Ø Dr. Musa Fadama Gummi (FUGUSAU)

Ø Dr. Aliyu G. Tsafe (UDUS)

Ø Dr. Bello M. Janbako (FUGUSAU)

Allah ya saka wa kowa da mafificin alkhairi. Amin.

Jinjina ta musamman ga dukkannin mutanen ƙwarai da suke da wankakkiyar zuciya a duk inda suke.

Mun gode.

Dr. Adamu Rabi’u Bakura
Dr. Abu-Ubaida Sani

MUƘADDIMA

Da sunan Allah (SWT) mai jinƙai da rahama.

A tsawon zamuna da suka gabata, Allah (SWT) ya tanadar wa da al’umma hanyoyin warkar da cututtuka, wato tun ma kafin samuwar mutane masu harhaɗa magunguna. Daga cikin mafi ɗaukaka na wannan baiwa shi ne Moringa olefera (ZOGALE) wato wani tsiro da yake da sinadarai da yawa da suke warkar da cututtuka. Samuwar wannan littafi mai suna: Zogala a Ƙasar Hausa (Magani, Abinci, Tattalin Arziƙi), ya zo a lokacin da ya dace. A ƙasashen Afirka da Asiya da kuma sauran wurare, al’umma na bukatar magunguna masu sauƙi da ƙarfin warkar da matsanantan cututtuka kamar na matsalar rashin abinci mai gina jiki. Zogale ne maganin irin waɗannan cututtuka na dauri da kuma na zamani.

Kama daga ganyensa da yake ɗauke da sinadarai, zuwa ‘ya’yansa da suke tace ruwa da kuma saiwarsa da bayansa da ake amfani da su a magungunan gargajiya, kowane ɓangare na wannan itaciya yana da magani. Wannan littafi yana da muhimmanci saboda ya haɗe tudu biyu, wato ta haujin gargajiya da aka daɗe ana warkar da cututtuka irin su kumburi da ciwon suga da hawan jini da kamari (wato kamuwa da cuta); da kuma ɗimbin sakamakon bincike-bincike da nazarce-nazarce a kimiyance da suka tabbatar da waɗannan fa’idoji. Bugu da ƙari, an yi amfani da harshe mai sauƙi dangane da yadda Zogale yake aiki a jiki da yadda za a yi amfani da shi ba tare da wata matsala ba da kuma yadda za a shuka shi domin iyali da lafiyar al’umma. Littafin zai amfani ɗalibai da masu bincike da nazari da jami’an kiwon lafiya da manoma da kuma masu tanadin kiwon lafiya. Marubutan littafin sun yi gagarumin aiki na ilmantar da al’umma matsayin Zogale na magani da abinci da kuma tattalin arziƙi. Allah (SWT) ya saka musu da mafificin alheri.

Farfesa Salisu Ahmad Yakasai, FLAN
Darakta, Cibiyar Nazarin Hausa,
Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato.

FOREWORD

It is with profound delight and a deep sense of intellectual excitement that I write this foreword for the remarkable work, "Zogale a Ƙasar Hausa (Magani, Abinci, Tattalin Arziki)" by Dr. Adamu Rabi'u Bakura and Dr. Abu-Ubaida Sani. This book represents a significant milestone in the documentation of indigenous knowledge, bridging the gap between traditional wisdom and modern scientific inquiry.

The Moringa tree (Moringa oleifera Lam.), known as Zogale in Hausa, is no stranger to those familiar with the landscapes of West Africa. For centuries, it has stood as a silent yet powerful companion to the Hausa people, offering sustenance, healing, and economic opportunity. Yet, despite its ubiquitous presence in our farms, backyards, and markets, the full extent of its value has often been underappreciated or confined to oral traditions. This book changes that narrative.

What makes this work particularly commendable is its comprehensive approach. The authors have meticulously examined Zogale from three critical dimensions of human life: medicine, nutrition, and economics. They have not only documented the traditional uses of the tree but have also validated these practices through contemporary scientific research, citing studies from botanists, pharmacologists, and nutritionists across the globe. This dual perspective (grounded in both cultural heritage and modern science) makes the book an invaluable resource for scholars, healthcare practitioners, farmers, entrepreneurs, and anyone interested in sustainable development.

The structure of the book is equally thoughtful. Beginning with the origins and spread of Zogale, the narrative takes readers on a journey through time, tracing the tree's migration from South Asia to Hausaland. The chapters on medicinal applications are particularly enlightening, detailing over one hundred ailments that Zogale can address, from diabetes and hypertension to skin conditions and digestive disorders. The sections on nutrition reveal the astonishing richness of Zogale's leaves, seeds, and flowers, comparing their nutritional content to more familiar foods like milk, carrots, and oranges. Finally, the exploration of Zogale's economic potential offers practical pathways for income generation, from farming and selling fresh leaves to producing powdered supplements and oil for international markets.

I am especially impressed by the authors' commitment to preserving indigenous knowledge while embracing scientific validation. They have interviewed traditional healers, gathered oral testimonies, and studied local practices, ensuring that the voices of those who have carried this knowledge for generations are heard and respected. At the same time, they have drawn on research from institutions across the world, from Nigeria to India, Senegal to the United States, demonstrating that Zogale is not merely a local curiosity but a global treasure.

This book also serves as a call to action. In an era of climate change, food insecurity, and rising healthcare costs, Zogale offers a sustainable and affordable solution. It grows in harsh conditions, requires minimal resources, and provides exceptional nutritional and medicinal benefits. By promoting the cultivation and utilization of Zogale, we can enhance food security, improve public health, create employment opportunities, and reduce dependence on expensive imported medicines and supplements.

I am confident that this book will find a wide audience. For students and researchers, it offers a rich source of data and references. For healthcare practitioners, it provides alternative and complementary approaches to treatment. For farmers and entrepreneurs, it opens doors to new economic ventures. For the general reader, it is an accessible and enlightening introduction to the wonders of a tree that truly deserves to be called a "miracle."

Dr. Bakura and Dr. Sani have done a great service to scholarship and to humanity. Their work exemplifies the best of what academic research can achieve: The preservation of cultural heritage, the advancement of scientific knowledge, and the promotion of human welfare. I pray that this book receives the attention it deserves and that it inspires further research, innovation, and action.

May Allah bless the authors, enrich their efforts, and make this work a source of benefit for generations to come. Amin.

Prof. Yakubu Aliyu Gobir
Department of Nigerian Languages
Usmanu Danfodiyo University, Sokoto
August, 2026.

Tsokaci I

Godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki, Mahaliccin kowa da komai, wanda in ya ba ka ka samu, in kuwa ya hana ka babu mai iya ba ka. Tsira da aminci su ƙara tabbata ga Annabinsa Muhammad (S.A.W) da iyalansa da sahabbansa baki ɗaya.

Na yi matuƙar farin ciki da na samu damar karanta wannan littafi daga farko har ƙarshensa. Shi ne ya ba ni damar fahimtar abin da littafin ya ƙunsa na ilimi da kuma tsinkayar irin alfanun da al’umma za ta samu daga cikin wannan hoɓɓasa na marubutansa.

Alal haƙiƙa ilimi ya kasance wani abu wanda ba shi da na biyu, domin babu abin da ake kwatantawa da shi. Duk kuwa abin da aka nemi kwatanta shi da ilimi to akan ga kasawarsa nan take. Wannan ya tabbata a cikin faɗin Allah (S.W.T) a littafinsa mai tsarki; Alƙur’ani, a sura ta 39 aya ta 9, inda Allah ya ce: “Shin ko masu ilimi za su taɓa zama daidai da waɗanda ba su da shi....”. Idan aka duba za a ga cewa wannan ƙalubale ne gare mu da kuma zaburarwa wajen tashi haiƙan domin neman ilimi.

Tabbas wannan littafi mai suna Zogale a Ƙasar Hausa, ya tattara ilimi mai zurfi da faɗi dangane da dukkan abin da ya shafi amfanin wannan itaciya mai albarka. Marubutan littafin sun yi ƙoƙari wajen yin gamsasshen bayani dangane da zogale da amfaninsa ta fuskoki da dama. Sun kuma fayyace bayanai ta yadda ba lallai sai mai zurfin ilimi kaɗai zai iya fahimtar abin da littafin ya ƙunsa ba. Wannan ya nuna cewa, littafin zai amfani al’umma a dukkan matakai na ilimi tun daga ƙasa har sama.

Tun da farko marubutan wannan littafi sun kawo tarihin samuwar zogale da asalinsa wanda suka danganta shi daga samuwar ɗan’adam a doron ƙasa. Babban abin birgewa dangane da wannan littafin shi ne, yadda ya kawo muhimmancin zogale ta manyan fuskokin rayuwa guda uku; wato ta fuskar abinci domin maganin yunwa, da magani domin kula da lafiya warkar da cututtuka da kuma tattalin arziƙi domin samun abin gudanar da rayuwa. Wani abin sha’awa dangane da littafin shi ne, inda ya yi bayanin cututtuka sama da 100 da zogale yake iya magance su ta hanyoyin sarrafawa mabambanta. Ba kamar yadda aka saba yin bayanin magungunan Hausawa na gargajiya ba, wato a kawo su a tsintsar gargajiyarsu - a’a, wannan littafi ya ƙunshi bayanai da suka nuna cewa an gudanar da bincike na zamani a kimiyyance da kuma likitance, wajen tabbatar da ayyuka da magungunan cututtuka da dama da zogale yake iya yi.

A ƙarshe, ina kira ga dukkan al’umma a kowane mataki na ilimi, da su rungumi wannan littafi don ya zama wani abin dogaro dangane da abin da ya shafi amfanin zogale ga ɗan’adam. Riƙo da littafin hannu bibiyu zai taimaka ƙwarai da gaske wajen bunƙasa samar da abinci da kiwon lafiya da tattalin arziƙi, sannan kuma zai agaza wajen bunƙasa ilimi.

Ina addu’ar Allah ya saka wa marubutan littafin da alheri, ya sanya albarka a cikinsa , ya sa ya zamo mai amfani ga al’umma baki ɗaya.

Jibril Yusuf Dokan Lere, Ph.D.

Sashen Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harshe,

Jami’ar Jihar Kaduna.

11-08-2026

Tsokaci II

Dukkan godiya da yabo sun tabbata ga Allah Maɗaukakin Sarki; wanda shi ne ya hore wa wasu daga ciki bayinsa ilimin abubuwa da dama. Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammadu, mai gaskiya kuma abin gaskatawa. Yardar Allah ta cigaba da yalwata ga iyalan gidansa da sahabbansa da kuma masu ƙoƙarin koyi da su har ya zuwa ranar sakamako.

Samuwar wannan littafi yana ƙara gwada mana masana da manazartanmu ba a kwance suke ba. Suna bakin ƙoƙarinsu wajen sanar da mu nau’o’in ilimin da suka faku a gare mu. Wannan littafi dai yana ƙunshe da babuka guda huɗu. Babi na farko ya mayar da hankali a kan fito mana da tushen samuwar itaciyar zogale a duniya da kuma yadda ta yaɗu a ƙasashen Afirka har ta gangaro ƙasar Hausa. Babi na biyu kuwa, ya tunkari fayyace mana alfanun itaciyar zogale a fannin maganin cututtukan da suke addabar jikin ɗan’adam a ciki da wajensa. Shi kuwa babi na uku, ya tattauna ne a kan gurbin da zogale yake da shi a cimakar Bahaushe ta gargajiya da kuma ta zamani. Babi na huɗu kuwa, ya kalli amfanin itaciyar zogale ta fuskar bunƙasa tattalin arzikin al’umma.

Haƙiƙa, marubutan wannan littafi sun yi tsinkaya da hangen nesa mai kyau. Samun littafi irin wannan zai haska wa al’umma muhimmancin itatuwa da tsirran da suke kewaye da su. Haka kuma, al’umma za su ƙara gaskata abin da magabata suke cewa, maganin cututtukan al’umma yana kewaye da su. Illa iyaka, al’ummar suna cikin yanayin nan ne da Hausawa suke cewa: “Raƙumi da kayan ruwa ƙishi zai kar shi.” Wani abin armashi, marubutan ba bayanin magani ko abincin da ake sarrafawa da itaciyar zogale ko wasu sassan jikinta kawai suka yi ba. Sun yi ƙoƙarin yi wa bayanansu turke da wata mabuɓɓuga ta ilimin kimiyyar zamani, saboda su ɗaure akuyarsu a gindin magarya.

Ina kira da hukumomin lafiya da makarantu a kowane mataki da wuraren da ake sarrafa abinci a kan cewa, su nemi wannan littafi, saboda ɗimbin alfanun da yake tattare da shi.

Ina roƙon Allah Maɗaukakin Sarki ya saka wa Dr. Adamu Rabi’u Bakura da Dr. Abu-Ubaida Sani da mafificin alheri a kan wanan gagarumin aiki da suka gudanar. Allah ya ƙara musu basira da ƙwarin guiwa ta yadda za mu ci gaba da amfanuwa da ɗimbin ilimin da ya ba su.

Mal. Ibrahim Dalha
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harshe,
Jami’ar Sule Lamiɗo Kafin-Hausa,
Jihar Jigawa.
18 ga Agusta, 2026.

Post a Comment

0 Comments