Ticker

6/recent/ticker-posts

Sana'o'in Zamani Da Suka Shafi Bincike

An ciro daga littafin:

BIƊA DA TANADI A DUNIYAR INTANET
(Sana’o’i, Kasuwanci, Ƙwadago)

Na

Abu-Ubaida SANI
Abdulrahman ALIYU

Bida Da Tanadi a Duniyar Intanet (Sana’o’i, Kasuwanci, Kwadago)
Manazartar Littafi: Sani, A-U. & Aliyu, A. (2026). Biɗa Da Tanadi a Duniyar Intanet (Sana'o'i, Kasuwanci, Ƙwadago). Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-978-62480-1-1. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.21361768

Tuntuɓa Domin Samun Littafi: 
Dr. Abu-Ubaida Sani: Imel - abuubaidasani5@gmail.com | WhatsApp - 08133529736
Dr. Abdulrahman Aliyu: WhatsApp - 08036954354

Ƙwadago Da Suka Shafi Bincike

Kalmar bincike ba baƙuwa ba ce ga bakuna da kunnuwan Hausawa. Ta karaɗe rayuwar ɗan’adam ta yau da kullum. Kusan a kowane bagire ana amfani da ita ko kalmomin da suke zaman masu kinin ma’ana a gare ta.[1] A bisa haka, kalmar tana iya ɗaukar ma’anoni da dama mabambanta ta fuskar manufa da matakan aiwatarwa. (Bunza, 2017a sh. 22-23) ya kawo ma’anar binciken ilimi bayan nazartar jerin ma’anonin da manazarta daban-daban suka bayar. Ya ce:

Bibiyar diddigin wani abu ta hanyar taliyon mafarinsa da sabgoginsa da yanaye-yanayensa. Bincike shi ne fito da wani abu sabo daga cikin abubuwan da aka sani ko ake gani ko ake ji ko ake amfani da su...

(Mannir, 2018 SL. 4) ya ba da ma’ana makamanciyar wannan inda yake cewa: “A ilimance, bincike na nufin aiwatar da nazari kan wani al’amari ko abu domin fito da wani sabon abu ko inganta wani abu, ko kuma warware wata matsala domin cimma wani buri ko biyan wata buƙata.”

Za a iya lura da cewa akwai muhimman kalmomi da suke haɗuwa su gina ma’anar bincike. Fahimtar su a matsayin ɗaiɗaikun kalmomi tare da fahimtar alaƙar aikin da suke yi kafaɗa da kafaɗa shi zai ba da hoton zuci na haƙiƙanin ma’anar binciken ilimi. Kalmomin kuwa su ne:

i.  Matsala

ii.  Manufa/maƙasudi

iii. Matakai

iv. Dabaru

v.  Bayanai

vi. Ƙwanƙwancewa/ƙalailaicewa

vii. Sakamako/Mafita

Lura da wannan, ana iya cewa binciken ilimi yana nufin tunkarar wata matsala a ilimance cikin bin tsararrun matakai da dabaru bisa manufar tattara bayanai da bin ingantattun matakan tace su da ƙalailaice su don samun sakamako ko mafitar matsalar da ta haifar da maƙasudin gudanar da aikin.

Ko bayan binciken ilimi, akwai nau’o’in binciken da suka shafi kasuwanci ko tsaro da dai makamantansu. A yau, Hausawan da suke da ƙwarewa a fannonin bincike suna da damar yin ayyukan da suka shafi bincike a kwastomomi na kusa da na nesa. Akwai fitattun hanyoyi guda uku da ake iya gudanar da ƙwadagon da ya shafi bincike. Su ne:

1. Neman Bayanai (Data Sourcing)

Neman bayanai da tattara su wani babban mataki ne a lamarin gudanar da bincike. Binciken yana iya kasancewa na ilimi ne ko na wani nau’in kasuwanci. Dangane da misalin binciken kasuwanci, neman bayanai sun haɗa da tattaro ra’ayoyi da muradu da ɗabi’un al’umma game da wani nau’in kayan kasuwanci. Akan tattara bayanai game da ra’ayoyin al’umma (misali, Hausawa) ta hanyar kira ta waya, ko yin tambayoyi gaba-da-gaba, ko kuma ta kafafen intanet.

Dangane da binciken ilimi kuwa, ya shafi tattara bayanai game da nau’o’in abubuwa daban-daban. Sun haɗa da wurare da abubuwa da tarihi da kayan karatu da sauransu. Duk waɗannan akan nemi ƙwararrun da za su gudanar da su ta kafafen intanet. Hausawan da suke irin wannan aikin, sukan tura ta intanet, sannan a biya su ta intanet, ba tare da buƙatar sai an haɗu gaba da gaba ba.

2. Ƙalailaice Bayanai (Data Analysis)

Ƙalailaicewa ko ƙwanƙwance bayanai yana nufin nazarta tare da ƙwanƙwance bayanan da aka tattara domin fitar da sakamako. Wannan fasaha ce mai zaman kanta wadda take buƙatar ƙwarewa. Waɗanda suka nemi ilimi a wannan ɓangaren suna da damar samun ayyuka daga wurare daban-daban. Hanyoyin da ake bi domin ƙalailaice bayanai suna da yawa, sannan sun shafi nau’in bayanan da kuma nau’in binciken da ake gudanarwa. Hausawa suna da damar shiga a dama da su a wannan fage. Ana iya amfani da manhajoji daban-daban yayin gudanar da aikin. Sun haɗa da:

a.  Atlas.ti – https://atlasti.com

b.  Google Forms – https://forms.google.com

c.  NVivo – https://www.qsrinternational.com/nvivo

d.  R – https://www.r-project.org

e.  SPSS (Statistical Package for the Social Sciences) - https://www.ibm.com/spss

f.  Stata - https://www.stata.com

g.  SurveyMonkey – https://www.surveymonkey.com

3. Mataimakin Mai Bincike (Research Assistant)

A nau’o’in bincike da dama akan yi amfani da mataimakin mai bincike. Yawanci shi yake taimakawa wajen tattara bayanai da tsara su ta yadda za su yi sauƙin ƙalailaicewa da ƙwanƙwancewa. Idan binciken ya shafi ziyarar gani da ido, yawanci mataimakin mai binciken yakan kasance wani da yake da ido a yankin da za a kai ziyarar. Zai zama wanda ya san al’adunsu da harshensu. Turawa da sauran ‘yan ƙasashen waje da suke zuwa ƙasar Hausa domin bincike, sukan nemi mataimaka domin gudanar da ayyukansu cikin sauƙi. Haka kuma, manazarta da cibiyoyin binciken da suka shafi Afirka ko harshen Hausa sukan nemi mataimaka Hausawa daga lokaci zuwa lokaci.




[1] A har kullum mutane suna kan neman bayanai da suka shafi na zahiri da na baɗini. A kowace rana ba a rasa jin Hausawa sun ambaci kalmomi da suke da alaƙa da bincike (a bagiren yau-da-kullum) irin su “dubawa” ko “nema” ko “bin diddigi” ko “cigiya” da makamantansu. Bunza (2017a sh. 2) yana ganin cewa ire-iren waɗannan kalmomi ne da suka kasance takwarorin kalmar “bincike.”

Post a Comment

0 Comments