Ticker

6/recent/ticker-posts

Sana'ar Baje Haja/Koli a Kafar Intanet Mallakin Mai Kaya

An ciro daga littafin:

BIƊA DA TANADI A DUNIYAR INTANET
(Sana’o’i, Kasuwanci, Ƙwadago)

Na

Abu-Ubaida SANI
Abdulrahman ALIYU

Bida Da Tanadi a Duniyar Intanet (Sana’o’i, Kasuwanci, Kwadago)
Manazartar Littafi: Sani, A-U. & Aliyu, A. (2026). Biɗa Da Tanadi a Duniyar Intanet (Sana'o'i, Kasuwanci, Ƙwadago). Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-978-62480-1-1. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.21361768

Tuntuɓa Domin Samun Littafi: 
Dr. Abu-Ubaida Sani: Imel - abuubaidasani5@gmail.com | WhatsApp - 08133529736
Dr. Abdulrahman Aliyu: WhatsApp - 08036954354

Baje Haja/Koli

A nan, baje haja ko baje koli yana nufin bayyanawa ko gabatarwa ko baza kayan da ɗankasuwa yake sayarwa domin kwastomomi su gani su saya. A kullum Hausawa suna ƙara rungumar intanet a matsayin kasuwar baje hajojin da suke sayarwa. Wannan yana ɗaya daga cikin misalan harƙallolin da ake gudanarwa a duniyoyi guda biyu (na zahiri da na baɗini). Tun a shekarar 2021, (Oyekanmi, 2021 SL. 3) ya bayyana cewa rahoton National Bureau of Statistics (Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa) ta nuna cewa kashi 22% na masu ƙananan kasuwanci ne suke amfani da intanet wajen gudanar da kasuwancinsu.

Hausawa masu ƙanana da manyan kasuwanci da dama suna amfani da kafafen intanet daban-daban domin tallata kasuwancinsu. Waɗansu suna amfani da kafafen sada zumunta (WhatsApp, Facebook, Instagram, TikTok, da sauransu).[1] Waɗansu kuwa sukan buɗe kafafensu na kansu ko su haɗa guiwa da wasu masu kafafen intanet domin a sama musu gurabun baje hajojinsu. A ƙarƙashin nau’o’in kasuwancin kan intanet da suka shafi baje haja, akwai manyan rukunoni guda uku, wato:

1.  Baje Haja/Koli a Kafar Intanet Mallakin Mai Kaya

2.  Baje Haja/Koli a Kafafen Intanet Na Haya

3.  Baje Haja/Koli a Kafafen Sada Zumunta

Baje Haja/Koli a Kafar Intanet Mallakin Mai Kaya

A yau, masu manyan kasuwanci sukan buɗe kafafen intanet domin baje hajojinsu. Yakan kasance wani abu mai kama da manya da ƙananan kantuna da kuma kasuwannin duniyar zahiri. Yayin da aka ɗauki matakin duniya, fitattun kafafen sayayya sun haɗa da Amazon (https://www.amazon.com) da Alibaba (https://www.alibaba.com). A Afirka kuwa, Jiji (https://jiji.ng) da Jumia (https://www.jumia.com) sun kasance zakarun gwajin dafi. Hausawa ma ba a bar su a baya ba wajen amfani da wannan cigaban zamani. Masu nau’in kasuwanci daban-daban sukan buɗe kafafen intanet domin baje hajojinsu. Amfanin kafafen sukan haɗa da:

a.  Tallata haja domin samun kwastomomi na kusa da na nesa

b.  Bayar da damar cinikayya ta kan intanet

c.  Adana muhimman bayanai game da kasuwanci

Misalan kafafen intanet na baje haja mallakin Hausawa sun haɗa da:

a.  A.Y.M. Shafa Holdings Limited (https://aymshafaholdings.com/)[2]

b.  Dangote Sugar (https://dangote.com/our-business/sugar-refining/)[3]

c.  Hikaya Bakandamiya (https://hikaya.bakandamiya.com/)[4]

d.  Misau Model Academy (https://misaumodel.com.ng/)[5]

e.  Rano Rice Mill (https://aarano.org.ng/services/rano-rice-mill/)[6]




[1] Da wuya mutum ya karaɗe sitatus ɗinsa na WhatsApp ba tare da cin karo da hajojin da Hausa suke tallatawa ba, irin su tufafi, turare, na’urori, da sauransu.

[2] Yana kasuwancin abubuwa daban-daban. Ɗaya daga ciki shi ne man fetur.

[3] Kamfanin da yake samarwa da sayar da sikari. Reshe ne na kamfanin Dangote Industries Limited.

[4] Hajar da suke bajewa ta shafi littattafai da suke saya daga wurin marubuta daban-daban. Masu karantu sukan biya kuɗi domin a ba su damar karanta littattafan.

[5] Wannan kafar intanet ce ta makarantar kuɗi.

[6] Shinkafa ake tallatawa. Wani reshe ne na kamfanin AA RANO Nigeria Limited.

Post a Comment

0 Comments