Ticker

6/recent/ticker-posts

Sana'o'in Tsara Hotuna Da Zane-Zane (Graphic Design and Illustration) Da Katun (Animation)

An ciro daga littafin:

BIƊA DA TANADI A DUNIYAR INTANET
(Sana’o’i, Kasuwanci, Ƙwadago)

Na

Abu-Ubaida SANI
Abdulrahman ALIYU

Bida Da Tanadi a Duniyar Intanet (Sana’o’i, Kasuwanci, Kwadago)
Manazartar Littafi: Sani, A-U. & Aliyu, A. (2026). Biɗa Da Tanadi a Duniyar Intanet (Sana'o'i, Kasuwanci, Ƙwadago). Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-978-62480-1-1. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.21361768

Tuntuɓa Domin Samun Littafi: 
Dr. Abu-Ubaida Sani: Imel - abuubaidasani5@gmail.com | WhatsApp - 08133529736
Dr. Abdulrahman Aliyu: WhatsApp - 08036954354

Tsara Hotuna Da Zane-Zane (Graphic Design and Illustration)

A gargajiyance akwai Hausawan da suke da ƙwarewa a fannin zane-zane. Sukan yi amfani da kayan aiki daban-daban, dangogin tawada da alƙalami. Zamani da shigowar na’urori da intanet ya sa an buɗe sabon babin zane-zane. A garuruwan ƙasar Hausa, Hausawa da dama suna gudanar da aikin tsara hotuna da zane-zane a shagunan aikin kwamfuta. Su ne suke tsara katunan gayyata zuwa taron aure da sauran taruka, har ma da katunan godiya da fastocin ‘yan takarar siyasa.

Ana buƙatar aikin tsara hotuna da zane-zane domin dalilai masu yawa. Wasu daga ciki su ne:

a. Samar da katunan gayyata na aure

b. Samar da takardun sanar da gayyata zuwa tarukan ilimi ko na siyasa

c. Tsara tallace-tallacen hajoji

d. Tsara bangwayen littattafai da na finafinai

e. Tsara tambarin ƙungiyoyi da ma’aikatu da makarantu

f. Tsara tambura da hotuna a jikin kayayyakin sakawa da na amfani

Hausawa ƙwararru a fannin tsara hotuna da zane-zane suna da damar da za su iya ayyuka a kan intanet. Suna iya karɓar ayyuka daga kwastomomi na kusa da na nesa. Babban misali a nan shi ne, wanda ya tsara bangon mujallar Tasambo (Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture) na farko a kan intanet aka same shi. Shi ne kuma ya samar da ƙayataccen hoton da aka ɗora a shafin farko na kafar intanet ɗin mujallar (www.tasambo.com).

Katun (Animation)

Katun tsarin bidiyo ne a inda ake amfani da fasaha ta musamman domin samar da hotuna da zane-zane masu motsi. Yawanci akan tsara motsinsu bisa wani labari wanda hakan yake mayar da su tamkar finafinai. Akan yi amfani da fasahar 2D ko ta 3D yayin samar da katun.

Yayin da aka yi maganar katun, abin da zai fara zuwa tunanin mutane da dama shi ne Tom & Jerri. A tsakanin Hausawa kuwa, mutane da dama za su iya tuna Kiriku. Kiriku katun ne wanda aka fassara zuwa harshen Hausa. Ya yi tashe sosai a lokacinsa. Ya karaɗe garuruwan Hausawa da dama inda har aka samu sababbin kalmomi daga shirin. Daga cikinsu akwai:

Jadawali Na 7: Misalan Katun Ɗin Hausa

Kalma

Asali

Ma’ana

Kiriku

Sunan babban tauraron cikin katun ɗin Kiriku

Ƙaramin mutum mai fitina ko wayo

Karaba

Sunan bokanya a cikin katun ɗin Kiriku

Fitinanniyar mace

Tushen Bayani: Keɓantacciyar Tattaunawa[1]

Ko bayan wannan, waƙoƙi da waɗansu lafuzzan da aka samo daga cikin katun ɗin sun zamo sara. Daga cikinsu akwai:

a. “Kiriku ɗan yaro, amma shi sadauki ne!”

b. “Ruwa ya zo, ruwa ya zo!”

Duka da waɗannan suna nuni da yadda katun ɗin ya samu karɓuwa.

Tun a shekarar 2009 akwai babban yunƙuri da manazarci a matakin digiri na biyu ya yi a Jami’ar Bayero da take Kano. Ya yi nazarin ne a kan yadda za a iya mayar da tatsuniyoyin Hausa cikin katun. Yunƙuri irin wannan zai sa a tafi da zamani, tare da rage dogaro kan bidiyoyi da suke fitowa daga al’ummun da ba Hausawa ba, waɗanda kuma ba su dace da tunani da al’adun Hausawa ba. Ko katun ɗin Kiriku, ɗaya daga cikin dalilan samun karɓuwarsa shi ne kasancewar ya dace da al’adun Hausawa. Ko da ma dai, labarin ya samo asali ne daga al’adu da salon tatsuniyoyin Afirka. Fitattun masu katun ɗin Hausa a yau sun haɗa da:

a. Akili and Me - Hausa[2]

b. Baban Yellow TV[3]

c. Hausa Fairy Tales[4]

d. Muib Toons[5]

e. Official MMBSTUDIOS[6]

Katun hanya ce ta samun kuɗi cikin sauƙi. Yayin samar da bidiyoyin katun, ba a buƙatar ‘yan wasa a zahiri ko kuma kamera da haske da sauran kayan ɗaukan bidiyo. A maimakon haka, komai a cikin kwamfuta ake haɗa shi. A ciki ake samar da ‘yan wasa tare da tsara yadda bidiyon zai gudana. Wannan dama ce ga Hausawa.




[1] (A.M. Manga, keɓantacciyar tattaunawa, 4 ga watan Fabarairu 2023) da (A. Umar, keɓantacciyar tattaunawa, 7 ga watan Fabarairu 2023)

[2] Ana iya duba bidiyoyinsu a https://www.youtube.com/@AkiliHausa.

[3] Ana iya duba bidiyoyinsu a https://www.youtube.com/@Baban_Yellow.

[4] Ana iya duba bidiyoyinsu a https://www.youtube.com/@HausaFairyTales.

[5] Ana iya duba bidiyoyinsu a https://www.youtube.com/@Muibtoon.

[6] Ana iya duba bidiyoyinsu a https://www.youtube.com/@MMBStudios_ng

Post a Comment

0 Comments