Ticker

6/recent/ticker-posts

Sana'ar Sarrafa Hotuna Da Bidiyoyi (Photo and Video Editing)

An ciro daga littafin:

BIƊA DA TANADI A DUNIYAR INTANET
(Sana’o’i, Kasuwanci, Ƙwadago)

Na

Abu-Ubaida SANI
Abdulrahman ALIYU

Bida Da Tanadi a Duniyar Intanet (Sana’o’i, Kasuwanci, Kwadago)
Manazartar Littafi: Sani, A-U. & Aliyu, A. (2026). Biɗa Da Tanadi a Duniyar Intanet (Sana'o'i, Kasuwanci, Ƙwadago). Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-978-62480-1-1. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.21361768

Tuntuɓa Domin Samun Littafi: 
Dr. Abu-Ubaida Sani: Imel - abuubaidasani5@gmail.com | WhatsApp - 08133529736
Dr. Abdulrahman Aliyu: WhatsApp - 08036954354

Ƙwadago Da Suka Shafi Gyaran Hotuna Da Bidiyoyi

Samar da suran mutane da halittu al’ada ce da ta daɗe a rayuwar ‘yan’adam. Hausawa ma ba a bar su da baya ba a wannan fannin. Tarihin shekaru aru-aru yana ƙunshe da sassaƙe-sassaƙe da zane-zanen surori daban-daban. Akan yi su domin cimma mabambantan manufofi da suka haɗa da:

a. Ado ko kwalliya

b. Adana tarihi

c. Bauta 

Ci gaban zamani ya buɗe sabon babi a wannan fage yayin da ɗan’adam ya samu fasahar ɗaukar hotuna da bidiyoyi. Hausawa da dama sun rungumi wannan sana’a a matsayin hanyar cin abinci. Akan je shagunansu domin a ɗauki hoto, a wanke sannan a ba wa mai shi. Haka kuma, akan gayyace su wararen taruka ko gidaje ko makarantu da sauransu, domin su ɗauki hotuna da bidiyoyi.

Samuwar intanet ya sake kawo sabon ci gaba a wannan fannin. A yau an samu hanyoyin samun kuɗi da dama waɗanda suka shafi sarrafa hotuna da bidiyoyi. Al’adar wanke hotunan kati ta fara dusashewa. Hotuna sun koma cikin wayoyi da kwamfutoci da kafafen intanet da kuma manhajoji.

A ƙarƙashin wannan, akwai manyan nau’o’in ƙwadago guda uku (3), wato:

a. Sarrafa Hotuna Da Bidiyoyi (Photo and Video Editing)

b. Tsara Hotuna Da Zane-Zane (Graphic Design and Illustration)

c. Katun (Animation)

Sarrafa Hotuna Da Bidiyoyi (Photo and Video Editing)

Ɗaukar hotuna da bidiyoyi tare da sarrafa su, sana’a ce wadda kasuwarta take ƙara faɗaɗa. A ɓangare ɗaya kuwa, kamfanonin wayoyi suna ƙara inganta kamerorin wayoyinsu. Wannan ya sa sau da dama ba a buƙatar mai ɗaukar hoto na musamman kafin samar da hotuna masu kyau. Duk da haka, bukukuwa da dama a ƙasar Hausa a yau ba sa kammaluwa ba tare da gayyato masu ɗaukar hotuna da bidiyoyi ba. Haka ma abin yake ga taruka na musamman.

Abubuwa da dama na gyaran hotuna da bidiyoyi sun koma kan intanet. Ana amfani da manhajoji daban-daban ko kafafen intanet na musamman domin yin hakan. Wannan ya shafi cire ɓangarorin da ba a so ko musanya su ko ƙara haskensu ko kuma ragewa, da dai sauran nau’o’in gyararraki masu yawa.

Waɗansu daga cikin manhajojin da ake amfani da su domin gyaran hoto su ne:

1. Adobe Photoshop (https://www.adobe.com/products/photoshop.html)

2. GIMP (GNU Image Manipulation Program) (https://www.gimp.org/)

3. Canva (https://www.canva.com/)

4. Snapseed (https://snapseed.online/)

5. Pixlr (https://pixlr.com/)

6. VSCO (https://vsco.co/)

7. Fotor (https://www.fotor.com/)

8. Affinity Photo (https://affinity.serif.com/photo/)

9. PhotoScape X (http://x.photoscape.org/)

Waɗansu daga cikin manhajojin da ake amfani da su domin gyaran bidiyoyi su ne:

1. Adobe Premiere Pro (https://www.adobe.com/products/premiere.html)

2. Final Cut Pro (https://www.apple.com/final-cut-pro)

3. iMovie (https://www.apple.com/imovie/)

4. Filmora (https://filmora.wondershare.com/)

5. KineMaster (https://www.kinemaster.com/)

6. InShot (https://inshot.com/)

7. CapCut (https://www.capcut.com/)

8. Lightworks (https://lwks.com/)

9. Shotcut (https://shotcut.org/)

A ɓangare ɗaya kuwa, Hausawa masu irin wannan sana’a suna da damar buɗe akawun-akawun a kafafen intanet da na sada zumunta. Hakan yakan kasance riba biyu a gare su. Na farko shi ne ƙara samun sanuwa wanda hakan zai kai ga sun ƙara samun kwastomomi. Na biyu kuwa shi ne kasancewar sannu a hankali kafafen nasu suna iya bunƙasar da za su kai gacin fara ɗora tallace-tallace domin samun ƙarin kuɗin shiga. Yawanci sukan ɗora samfuran hotuna da bidiyoyi da suka ɗauka a wurare daban-daban a matsayin tallatawa.

Misalan ire-iren waɗannan akawun-akawun na kafafen sada zumunta sun haɗa da:

1. Ahmed Bube (Bube Photography - Sokoto)[1]

2. Faisal H. Adam (Faisal Photography - Kano)[2]

3. Fa'iza Ibrahim Birnin Magaji (Famnoor Photography - Zamfara)[3]

4. Haruna Alengo (Alengo Photography - Bauchi)[4]

Wani ƙarin dama da ake da ita dangane da ɗaukar hotuna da bidiyo ita ce sayar da su a manyan kafafen dillancin hotuna. Hausawan da suka ɗauki hotuna masu kyau suna da damar buɗe akawun da tallata hotunan a kan intanet. Misalan kafafen intanet waɗanda ake sayar da hotuna sun haɗa da:

1. Adobe Stock (https://stock.adobe.com)

2. Shutterstock (https://www.shutterstock.com)

3. Getty Images (https://www.gettyimages.com)

4. Alamy (https://www.alamy.com)

5. Foap (https://www.foap.com)

6. Dreamstime (https://www.dreamstime.com)

7. Etsy (https://www.etsy.com)

8. Zenfolio (https://www.zenfolio.com)

9. SmugMug (https://www.smugmug.com)

10. Wirestock (https://www.wirestock.io)




[1] Akawun ɗinsa na Facebook shi ne: https://www.facebook.com/p/Bube-Photography-100066431712579/?_rdr

[2] Akawun ɗinsa na Instagram shi ne: https://www.instagram.com/faisal__photography/

[3] Akawun ɗinta na Instragram shi ne: https://www.instagram.com/famnoor_photography/

[4] Akawun ɗinsa na Instragram shi ne: https://www.instagram.com/alengo___photography/?hl=en

Post a Comment

0 Comments