An ciro daga littafin:
BIƊA DA TANADI A DUNIYAR INTANET
(Sana’o’i, Kasuwanci, Ƙwadago)
Na
Abu-Ubaida SANI
Abdulrahman ALIYU
Masu Zana Gini (UI UX Designers)
Kamar yadda injiniyoyi suke
zana gidaje kafin a fara gininsu a duniyar zahiri, a duniyar intanet ma akwai
masu sana’ar zana gine-ginen intanet. Ba dole ne ya kasance suna da ilimin yin
ginin ba. A maimakon haka, buƙata kawai ita ce su ƙware a fannin ƙirƙiro yadda tsarin ya dace ya kasance. Hakan yana nuna
cewa, Hausawa suna da damar shiga a dama da su a wannan fage ko da ba su ƙware a gina kafafen intanet ba.
“UI”[1] yana nufin duk waɗansu abubuwa da ake
iya gani kuma a yi mu’amala da su a kan kafar intanet. Sun haɗa da hotuna da
zane-zane da alamomi da shafuka da sauran rubuce-rubuce. A ɓangare ɗaya kuwa, “UX”[2] yana nufin tsarin
yadda masu ziyarar kafafen intanet za su yi hulɗa da kafafen. Ana iya
kwatanta tsarin da abin da yake faruwa a duniyar zahiri. Misali, idan mutum ya
je babban kanti, zai zaɓo kayan da yake son saye,
sannan ya zo wurin da zai biya kuɗin kayan.
Kwatankwacin haka abin yake a kan intanet idan kafar ta kasuwanci ce. UX ya
shafi tsara matakan yadda za a je a zaɓo kaya da yadda za a
biya kuɗinsu (da sauransu).
Kafin maginin kafar intanet
ya fara wani aiki, dole ne sai ya san abin da yake da niyyar ginawa. Matakin
farko shi ne samun bayanin dalilin samar da kafar da yadda ake son tsarin ya
kasance da mutanen da za su yi amfani da kafar. Yayin da ƙwararre a zana ginin kafar intanet ya saurari bayanan
abin da mai bayar da aiki yake buƙata, to zai iya
samar da zanen tsari mai kyau. Kai tsaye maginan kan intanet za su yi amfani da
wannan zane domin aiwatar da ginin. Masu kafafen Hausa irin su Amsoshi
da WikiHausa da Bakandamiya (da sauransu), sukan tattauna a tsakaninsu
domin ƙara wa juna sani
game da tsarin gine-ginen kafafensu.
Bayar Da Tsaro Ga Kafafen Intanet Da
Na’urori (Cyber Security)
Kamar yadda ake bayar da
tsaro a gidaje da kasuwanni da ma’aikatu a duniyar zahiri, akwai makamancin
wannan a duniyar intanet. Kowanne daga cikin kafafen intanet kimanin biliyan
biyu[3] da ake da su a yau
suna ci gaba da wanzuwa ne sakamakon ana ba su kariya. Tsaro da ake ba wa
kafafen intanet ya shafi kare su daga masu kutse waɗanda za su iya dakatar da ayyukan kafafen tare da sace
muhimman bayanai da suke kansu. Ko bayan wannan illar, masu kutse suna iya
amfani da kafafen intanet domin satar bayanan maziyarta kafafen tare da ƙoƙarin damfarar
su.
Akwai
Hausawa da suka ƙware a wannan fanni. Wani abin burgewa shi ne, “fage ne da yake matuƙar kawo kuɗi ga waɗanda
suka naƙalce shi”
J. Abdullahi (keɓantacciyar
tattaunawa, 7 ga watan Fabarairu 2023). Hakan yana da nasaba da ƙarancin gwanaye
a fannin sakamakon tsauri da wuyar sha’ani da yake da shi.[4]
Waɗanda suka yi na ɗaya da na biyu a Gasar Gwanin Kutse a Nijeriya (HackBoss
Nigeria) a shekarar 2017 duka Hausawa ne. Abdulmalik Ibrahim shi ne ya zo na
farko, yayin da Shehu Awwal ya zo na biyu (ITREALMS, 2017). Wannan yana nuni ga yadda Hausawa suka yi nisa a harkar.
[1] User
Interface
[2] User
Experience
[3]
Binciken Wise (2023) ya
bayyana biliyan biyu a matsayin ƙiyasin adadin kafafen
intanet a duniya ya zuwa shekarar 2023 (duk da cewa binciken Reboot Online (2024) ya bayar
da adadin da bai kai haka ba).
[4] Waɗanda suka zo na farko da na biyu
a gasar kutsen kan intanet ta CS2 HackBoss ta 2017 duka Hausawa ne.
Wannan yana ƙara
nuni da yadda Hausawa suke daɗa rungumar wannan fanni
na kutsen kan intanet. A duba ITREALMS, (2017).
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.