An ciro daga littafin:
BIƊA DA TANADI A DUNIYAR INTANET
(Sana’o’i, Kasuwanci, Ƙwadago)
Na
Abu-Ubaida SANI
Abdulrahman ALIYU
Ƙwadago
Da Suka Shafi Intanet Da Na’urori
Akwai
nau’o’in ƙwadago
daban-daban da suka shafi intanet da na’urori waɗanda Hausawa suka runguma a
yau. Mukoshy (2015) ya yi ƙoƙarin tattara wasu muhimman kalmomin kwamfuta musamman
waɗanda suka shafi intanet tare da samar da fassarorinsu. Kalmomin da ya
fassara sun haɗa da na intanet da na kwamfuta da na burauzozi da makamantansu.
A shafi na 108, ya yi kira da cewa: “Ya kamata Hausawa su shiga cikin sha’anin
nazarin fannin kwamfuta, su yi ruwa, su yi tsaki a dukkan ɓangarorinta.” Ya
nuna bunƙasa
da matuƙar
alfanu da tagomashin da harkar intanet da kwamfuta take da shi a shafuka na
107-108. Wannan ɓangare na aikin yana ɗauke da bayanai game da ire-iren
damarmaki da ake da su a wannan fannin.
Gina Kafafen Intanet (Website Design)
Idan
aka ce kafar intanet, ana nufin website ko blog a Ingilishi. Gini
ne da ake yi a kan intanet bisa tsari na musamman wanda yake ɗauke da shafi (ga
kafa mai shafi ɗaya) ko shafuka (ga kafa mai shafuka da yawa). A kullum kafafen
intanet ƙara
yawa suke yi a duniya, ciki kuwa har da na Hausa. A duniyar intanet, kafafe sun
kasance tamkar gine-gine da ake da su a duniyar zahiri. Nau’o’in gine-ginen sun
danganta ga dalilin da aka yi su dominsa. Waɗansu kasuwanni ne, waɗansu
shaguna, waɗansu kuwa wuraren shaƙatawa ne, da dai sauransu. Binciken Reboot Online (2024
SL. 4) ya bayyana cewa, a shekarar 2024, akwai kimanin kafafen intanet da suka
kai biliyan ɗaya da miliyan ɗari da talatin (biliyan 1.13).
Hausawa
da dama a yau sun riƙi gina kafafen intanet a matsayin hanyar cin abinci. Wani
abin lura shi ne, ba sai waɗanda suka karanci ilimin kwamfuta da intanet a
jami’o’i ko kwalejojin ilimi ba ne suke iya cin abinci a wannan fanni. “Ko
rukunin da suka zo na ɗaya a gasar da Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato ta saka
wanda ya shafi intanet, ba ‘yan sashen ilimin kwamfuta ba ne, duk da cewa ‘yan
sashen ilimin kwamfuta sun shiga gasar.[1]
Bugu da ƙari,
dukkanninsu Hausawa ne” A. Sani (keɓantacciyar tattaunawa, 17 ga watan Satumba
2024).
Maginan
kafafen intanet sun kasu zuwa manyan rukunoni guda uku, kamar haka:
1. Maginan Fili (Front
End Developers): Maginan
fili su ne waɗanda suke gina ɓangarorin kafafen intanet da masu ziyarar kafafen
suke iya gani. Ya haɗa da shafin farko da duk sauran shafukan da za a iya
shiga. Ya shafi hotuna da rubuce-rubuce da bidiyoyi da duk sauran abubuwan da
mai ziyarar kafa zai iya gani. Aiki ne da yake buƙatar nazari da ƙwarewa. Mai yin wannan aiki
dole ya samu ƙwarewa a kan ire-iren launukan rubutu da na hotuna da zai
yi amfani da su, da yanayin girman rubutu da gurabun da ya kamata dukkannin
abubuwan kan kafar su kasance.
2. Maginan Ɓoye (Back End Developers):
A kafafen intanet, ba
kowane nau’in bayanai ba ne mai ziyarar kafa yake iya gani. Misali, yayin da
ɗalibi zai yi rajista da kafar MIS ta Jami’ar Usmanu Danfodiyo da take
Sakkwato, to zai sanya keɓantattun bayanansa, ciki har da sunan mai akawun (username)
da kuma kalmar sirri (password). Waɗannan bayanai za su tafi rumbun
bayanai ne domin a adana su. Mai ziyarar kafar, ba zai iya ganin bayanan ba.
Mutanen da suke gina wuraren da ake adana bayanan da samar da tsarin sarrafuwar
bayanan, su ne ake kira maginan ɓoye.
3. Maginan Komai-Da-Ruwanka
(Full-Stack Developers): Akwai waɗanda suke samun ƙwarewa a dukkannin fannonin
guda biyu, wato ginin bayyane da na ɓoye. Waɗannan su ne ake kira maginan
komai-da-ruwanka.[2]
Akwai
nau’o’in harsuna (programming languages) da ake yin amfani da su yayin gina
kafafen intanet. Sun kasance tamkar bulo-bulo da sauran kayan gini a duniyar
zahiri. Yadda nau’in gine-ginen da za a yi a zahirance suke buƙatar kayan aiki na
musamman, haka abin yake a lamarin ginin kafafen intanet. Dole ne Bahaushe ya
naƙalci
waɗannan harsuna kafin gogewa a fannin. Ginin da za a yi, shi yake nuni ga
nau’in harsunan da za a yi amfani da su. Duckett (2011 sh. 172-193) da Niederst
Robbins (2018 sh. 93-200) sun yi bayanin harsunan intanet da yadda ake amfani
da su. Misalansu sun haɗa da:
a. HTML (HyperText Markup Language)[3]
b. CSS (Cascading Style Sheets)[4]
c. JavaScript[5]
d. PHP (Hypertext Preprocessor)[6]
e. Python[7]
f. TypeScript[8]
Akwai
Hausawan da suka rungumi sana’ar gina kafafen intanet wa kwastomomi na kusa (local
programming). A ɓangare ɗaya kuwa, akwai waɗanda suka duƙufa wurin neman aiki a kan
kafafen intanet (online sourcing).[9] Kafafen intanet da suka
kasance kasuwannin baje haja ga maginan kafafen intanet sun haɗa da:
a. Fiverr (https://www.fiverr.com)
b. Freelancer (https://www.freelancer.com)
c. Guru (https://www.guru.com)
d. PeoplePerHour (https://www.peopleperhour.com)
e. Upwork (https://www.upwork.com)[10]
Wani
abin burgewa ga sana’ar gina kafafen intanet shi ne, duk kafar da maginin ya
gina, to za ta ci gaba da kawo masa kuɗi na tsawon lokaci. Hakan yana faruwa ne
sakamakon akwai gyare-gyare da sabunta bayanai da masu kafar za su buƙaci maginin ya yi. Yayin
gudanar da sauye-sauyen kuwa, to za a biya shi wasu kuɗaɗe na musamman. Ko
bayan wannan, lokaci zuwa lokaci akan samu sabuntawa na gama-gari da za a yi.
Shi ma sai an biya maginin kafin ya aiwatar. Akan yi aiki a kan kafar intanet a
bisa dalilai da dama. Wasu daga ciki su ne:
a. Buƙatar sauya wasu bayanai (rubutu ko hotuna ko
bidiyoyi) a kan intanet
b. Sabunta biyan kuɗin rumbun ajiye bayanai
(hosting)
c. Sabunta biyan kuɗin sunan kafar intanet
(domain name)
d. Bunƙasa/girman ƙunshiyar intanet da zai kai
ga buƙatar
ƙarin
girman rumbun ajiye bayanai
e. Gyara wata matsala da za ta iya ɓullowa
f. Muradin sauya fasalin shafukan kafar
intanet
g. Samuwar sababbin fasahohi sakamakon
cigaban zamani
Lura
da duka waɗannan, sana’ar gina kafafen intanet ta kasance mai maiƙo wadda take ci gaba da
kawo wa mutum kuɗi ko bayan kammalawa. Ana iya kwatantan shi da ginin gidan
duniyar zahiri a ƙasar Hausa. Yayin da aka gina gida, hakan ba ya nufin an
kammala aikin dindindin. Lokaci zuwa lokaci za a kira mai fenti ko kafinta ko
fulamba domin gyara wani abin da ya ɓaci. Haka abin yake ga kafafen intanet.
[1] Waɗanda suka yi na ɗaya
sun fito ne daga Tsangayar Nazarin Fasahar Magunguna da Sashen Kiyon Lafiya (Faculty
of Pharmaceutical Science da College of Health Sciences).
[2] Domin ƙarin bayani game da ayyukan
gina kafafen intanet, ana iya duba Myers (2024) da Zeldman & Marcotte
(2024).
[3] An fi amfani da shi wajen tsara ƙunshiyar
kafafen intanet.
[4] Ana amfani da shi wajen ba
wa shafuka tsari da launi da girman rubutu.
[5] Da shi ake samar da tsarin
hulɗayya tsakanin masu ziyara da kafafen intanet (misali shi yake ba wa kafar
intanet damar gane sunan maziyarci) da kuma sauyawar abubuwa da kansu (kamar
motsawar rubutu ko hotuna).
[6] Ana amfani da shi wajen
gina fannonin da suka shafi 'ginin ɓoye.'
[7] Shi ma ana amfani da shi
wajen gina fannonin da suka shafi 'ginin ɓoye.'
[8] Harshe ne mai aiki irin na
JavaScript, sai dai ya fi JavaScript bunƙasa. An fi aiki da shi a manyan kafafe da
manhajoji masu sarƙaƙiya.
[9] M. Bello (keɓantacciyar
tattaunawa, 20 ga watan Janairu 2024). Ya kasance Bahaushe wanda ya dogara da
gina kafafen intanet a matsayin sana’a. https://misaumodel.com.ng ɗaya ce daga cikin
kafafen intanet da ya gina (Kafa ce ta Misau Model Academy). Ya bayya cewa:
“Ana cin wannan kasuwa da Hausawa masu yawa.”
[10] A cikin waɗannan kafafe, akwai Hausawa masu yawa. Wannan yana nuni ga yadda Hausawa suke da damar shiga a dama da su a wannan fannin.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.