An ciro daga littafin:
BIƊA DA TANADI A DUNIYAR INTANET
(Sana’o’i, Kasuwanci, Ƙwadago)
Na
Abu-Ubaida SANI
Abdulrahman ALIYU
Gina Manhajoji (Software Programming)
Manhaja aba ce da take da siffar kafar
intanet, wanda ake iya saukewa a kan na’ura kamar waya ko kwamfuta domin amfani
da ita. Wannan yana nuna cewa, ta bambanta da kafar intanet kasancewar ita
kafar intanet, dole ne a hau ta kan burawuza kafin a iya buɗe ta. Ita kuwa
manhaja tana cin gashin kanta a inda za a iya buɗe ta kai tsaye yayin da aka
sauƙe ta a kan na’ura.
Duk da haka, yana da kyau a fahimci cewa, a
lokuta da dama manhajoji sun kasance tamkar hoto ne ko inuwar kafafen intanet.
Ma’ana a nan ita ce, akan samu kafafen intanet da aka yi wa manhajoji. A irin
wannan yanayin, manhajojin za su kasance suna tsotso bayanai ne daga kafafen.
Idan kuwa manhaja ce da take ba da dama ga ɗaiɗaikun mutane su sanya bayanai a
ciki, to bayanan da suka sanya za su tafi ne zuwa rumbun ajiyar kafar.
A yau, buƙatar samar da manhajoji tana ƙara yawaita a duniya. Ba sai an tafi shekaru da yawa baya
ba, a wajajen 2006 kaɗai “da wuya a ƙirga Hausawa biyar (5) a
birane ko ƙauyuka ba a sami ɗayansu da rediyo ba”
(Bunza, 2006 sh. 21). Ya zuwa yau (2024), tuni lamarin ya sauya zane. Hausawa
da dama sun koma amfani da wayoyin hanu wurin sauraron labarai. Lura da hakan
ya sa gidajen rediyo da na talabijin suka samar da manhajojin da za su ba da
damar kallo ko sauraron shirye-shiryensu ko da an riga da an kammala gabatarwa.
A nan sai a lura da cewa, duk gidan rediyo ko talabijin da suka yi saken kasa
sanya rigar zamani, lallai sai dai su ga ana yi. Waɗansu daga cikin manhajojin
sauraron labarai a yau sun haɗa da:
Sunan Manhaja
1. Hausa Radio
2. Freedom Radio
3. Dala FM
4. Arewa Radio
5. Izala Radio
Madogara:
Rumbun
Manhajoji Na Google (Google PlayStore)
A yau akwai Hausawa da suka shahara a wannan
fage na samar da manhajoji. Daga shekarar 2020 lokacin da Hasawa suka rungumi
kasuwancin sayar da datar waya a intanet, an ci gaba da samun ƙaruwar manhajoji mallakin Hausawa. Haka kuma, an ci gaba
da samun Hausawa da suke rungumar wannan fanni na gina manhajoji (K. Sani,
keɓantacciyar tattaunawa, 12 ga watan Ogusta 2024).
Sana’ar gina manhajoji tana matuƙar kama da ta gina kafafen intanet. Kamar yadda aka yi
bayani a baya (a ƙarƙashin 4.1.2.1), kammala
ginin ba ya nufin aiki ya ƙare. Lokaci zuwa lokaci za
a buƙaci gyararraki. Wannan yana nuna cewa, yayin
da mutum ya gina manhajoji masu yawa a kamfanoni da ɗaiɗaikun mutane, to yana
da tabbacin ci gaba da samun kuɗin shiga.[1]
[1] Ya zuwa watan Agustan shekarar 2024, manhajojin da suke cikin Google PlayStore kaɗai sun kai miliyan biyu da dubu ɗari uku (miliyan 2.3) (Ceci, 2024).
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.