An ciro daga littafin:
BIƊA DA TANADI A DUNIYAR INTANET
(Sana’o’i, Kasuwanci, Ƙwadago)
Na
Abu-Ubaida SANI
Abdulrahman ALIYU
2.3.6 Rabe-Raben Sana’o’i Ta La’akari Da Duniyarsu
Wannan
littafi yana da ra’ayin cewa akwai manyan duniyoyi biyu da Hausawa suke gudanar
da sana’o’i a cikinsu a yau. Duniyoyi biyu da Hausawa suke
gudanar da kasuwancinsu a cikinsu su ne:
i.Duniyar
zahiri
ii.Duniyar
intanet
2.3.6.1 Sana’o’in Duniyar Zahiri
Dukkannin
sana’o’in Hausawa na gargajiya sun kasance na duniyar zahiri. Su ne waɗanda ake
ganin su ko a taɓa su ko a shaidi sakamakon su a zahirance. Haka kuma, masu
aiwatar da sana’o’in da waɗanda suke amfana da su, duk a duniyar zahiri suke
tattaunawa. Nau’o’in su sana’o’in da zamani ya kawo wa Hausa, da dama daga
cikinsu na duniyar zahiri ne. Misalansu sun haɗa da:
a. Fawa
b. Kaɗi
c. Kisto
d. Ƙira
e. Noma
f. Rini
2.3.6.2 Sana’o’in Duniyar Intanet
Sana’o’in
duniyar intanet su ne waɗanda yayin gudanar da su, harƙallar mai saye da sayarwa
takan kasance a cikinta. Takardar Sadat (2023 sh. 708) ta tabbatar da cewa, a
yau akan yi sayayya cikin sauƙi a kan intanet. Lamari ne da yake ba wa mutum damar
sayen kaya ko ya sayar da kaya ko ya nemi wanda zai yi masa wani aiki ko shi ya
yi wa wani aiki alhali masu wannan mu’amalar ba dole ne ya kasance sun taɓa ko
da jin labarin ɓangarorin duniyar da kowannensu yake rayuwa ba.
Dahiru
et al. (2014) sun bayyana yadda masu sana’o’i da kasuwanci daban-daban a Kano
suke rungumar hanyoyin biyan kuɗi na zamani. Duk da a ƙarshe sun nuna cewa, akwai ƙarancin karɓar wannan sauyi
na zamani (Dahiru et al., 2014 sh. 9). Binciken Enejo & Ojabo (2024) ya
nuna cewa ana samun cigaba a wannan fannin. Duk da haka, binciken nasu ya gano
cewa kimanin kashi ashirin (20%) na ƙanana da matsakaitan kasuwanci a yankin
Arewacin Nijeriya ba su taɓa amfani da wani nau’in kasuwancin kan intanet ba
(sh. 92). A taƙaice ke nan, har yanzu akwai buƙatar ƙara bincike domin fito da
damarmakin da Hausawa suke da su na neman kuɗi a kan intanet.
Dogaro
da kai ta hanyar kasuwanci yana ƙara zama abu mai sauƙi a yau. Hakan yana faruwa
ne da taimakon intanet da yake bayar da damar riskar kwastomomi cikin sauƙi, da kuma sauyin tsarin
kasuwancin kansa a duniyar yau. A yau, mutane suna da damar fara kasuwanci da
kuɗi ɗan ƙalilan
kawai. Hanyoyin samun kuɗi masu sauƙi da suke ƙoƙarin mamaye dukkannin
ɓangarorin duniya sun haɗa da ƙirƙirar bidiyoyi da rubuce-rubuce domin ɗorawa a intanet.[1]
Dangane
da ayyuka a kan intanet kuwa, tsarin ya samu bunƙasa musamman bayan ɓullowar
annobar Korona. Masana’antu da hukumomi da dama sun ga damarmakin da suke
tattare da aiki daga gida (ta kan intanet) (Ringle et al., 2020 sh. 88). Daga
wannan lokaci an samu ƙaruwar rungumar tsarin ayyuka ta kan intanet. A yau ya
kasance wata alƙibla wadda kasuwancin duniya ya saka a gaba.
A
yanzu ‘yan kasuwa ba sa cikin takunkumin taƙaita kasuwancinsu a muhalli
ɗaya, ko da kuwa ƙaramin jari suke da shi. Wannan yana faruwa ne sakamakon
shirin game-duniya da kuma wadatuwar hanyoyin cinikayya ta kan intanet (Mishrif
& Khan, 2023 sh. 7-8). Ko ‘yan kasuwan da ba su da damar buɗe kafafen
intanet na kasuwancinsu, suna da damar haɗa guiwa da manyan kafafe daban-daban
domin gudanar da kasuwancin a kan intanet. Kasuwannin kan intanet irin su Amazon
da Alibaba da Shopipy sun yi fice a wannan fannin.
A
nan akwai manyan batutuwa biyu waɗanda suka kamata hankali ya kai gare su. Na
farko shi ne, sana’a tana iya kasancewa ta duniyar intanet kasancewar a nan ne
ake ƙulla
harƙallar
gudanar da ita. Tana iya kasancewa akwai makamanciyarta da ake gudanarwa a
duniyar zahiri. Bambancinsu a nan kawai shi ne farfajiyar gudanarwa. Misali:
a. Ɗan Nijeriya yana iya yin
aikin fassara da wani kamfani da yake Amurka, ba tare da ya taɓa jin murya ko
kallon hoton waɗanda suke magana da shi daga kamfanin ba. Komai za a gudanar da
shi ne a duniyar intanet.
b. Bauhaushe
yana
iya buɗe shagon sayar da datar waya a kan intanet. Masu yi masa ciniki za su
sayi kayayyakinsa ne kawai kai tsaye daga intanet ba tare da sanin a duniyar da
yake ba a wannan lokaci.
A ɓangare
guda kuwa, sana’a tana iya kasancewa ta duniyar intanet zamowar abubuwan da ake
sarrafawa ko samarwa a cikinta suke. Misali:
a. Mai
gina kafar intanet tamkar mai ginin gida yake a duniyar zahiri. Zai sayi fili
da sunan gida sannan ya zana filin ya fitar da ɗakuna da zauruka da sauransu.
Duk waɗannan a duniyar intanet za su kasance.
b. Wanda
ya sanya matakan tsaro a wata na’ura ko wani zaure a kan intanet, to ya yi
hakan ne a cikin wata ɓoyayyiyar duniya (duniyar intanet).
2.3.6.3 Bambance-Bambance Tsakanin
Sana’o’in Duniyar Zahiri Da Na Intanet
Akwai
bambance-bambance tsakanin sana’o’in duniyar zahiri da waɗanda ake gudanarwa a
duniyar intanet. Ɓangarorin da ake samun waɗannan bambance-bambance sun
haɗa da:
a. Abataya (Overtime) da
alawus
b. Damar
yi wa kaya kallon ƙwaƙwaf
c. Faɗaɗa
d. Hanyoyin
biyan kuɗi
e. Hulɗa
f. Lokacin
aiwatar da kasuwanci
g. Tallata
kasuwanci
h. Tsaro
i. Wuraren
ajiye kayan aiki da kayayyakin sayarwa da wurin zaman ma’aikata
j. Wurin
aiwatar da aiki
An
yi ƙarin
bayani game da su a cikin jadawali na 4 da yake ƙasa.
Jadawali Na 3: Bambance-Bambancen Sana’o’in Duniyar Zahiri Da Na
Intanet
|
|
Sana’o’in
Duniyar Zahiri |
Sana’o’in
Duniyar Intanet |
|
Abataya da
alawus |
Mai sana’ar
duniyar zahiri na iya buƙatar abataya
ko waɗansu alawus-alawus na tafiye-tafiye da wurin kwana da makamantansu. |
Mai sana’ar
duniyar intanet ba ya buƙatar wurin
kwana da kuɗaɗen tafiye-tafiye.[2] |
|
Damar yi wa
kaya kallon ƙwaƙwab |
A sana’ar
duniyar zahiri, kwastoma yana da damar yi wa kaya kallon ƙwaƙwaf, har ma ya taɓa ko ya jinjina, da
makamantan hakan. |
A sana’ar
duniyar intanet, wanda zai sayi kaya yana da damar kallon hoto ko bidiyon
kayan ne kawai. Ba zai iya kallon sa a zahirance ba har sai idan an kawo masa
shi (idan wanda ake kawowa ne). |
|
Faɗaɗa |
Sana’ar
duniyar zahiri tana buƙatar matakai
masu yawa kafin faɗaɗa zuwa waɗansu yankuna na nesa. Sun haɗa da ƙarin ma’aikata da ababan jigila kamar
mota ko jirgi. |
Faɗaɗa sana’a
zuwa ɓangarori daban-daban abu ne mai sauƙi ga mai sana’ar duniyar intanet. Zai
yi hakan ne kawai ta hanyar ɗora bayanansa da na kasuwancinsa a kafafen
intanet da masu neman ma’aikaci irinsa za su iya shiga. |
|
Hanyoyin
biyan kuɗi |
A sana’o’in
duniyar zahiri, ana iya biyan kuɗi hannu (takardu ko tsaba) ko a yi taransifa
ko amfani da POS ko cek da makamantansu. |
A sana’o’in
duniyar intanet ba su da zaɓin biyan kuɗi hannu-da-hannu. Bayan haka, akan
samu zaɓuɓɓukan hanyoyin biyan kuɗi masu tarin yawa. Misali, kafar Paxful tana ba da damar a biya kuɗi ta hanyoyi
sama da ɗari huɗu da hamsin (450).[3] |
|
Hulɗa |
Mai sana’ar
duniyar zahiri yana hulɗa da kwastomominsa a zahiri. Suna iya kama hannayen juna domin
gaisawa ko taɓa juna da makamantansu. |
Mai sana’ar
duniyar intanet ba ya hulɗa ta gaba-da-gaba da kwastomominsa. |
|
Lokacin
aiwatar da kasuwanci |
Yawanci mai
gudanar da sana’a yana da taƙamaiman
lokacin aiki a kowace rana ko mako. Misali, mai shagon aski na zamani yana
iya buɗewa daga ƙarfe 9:00 na
safe zuwa ƙarfe 9:00 na
dare. |
Girkakku ko
saitattun sana’o’in kan intanet suna iya aiki a kowane lokaci. Misali, wanda
ya saita shagonsa na sanyar da katin wutar lantarki, to masu ciniki na iya
sayayya dare da rana ba tare da an ci karo da wani lokaci da shagon yake rufe ba. |
|
Mai sana’ar
duniyar zahiri yana buƙatar ya yi
aiki a cikin wani ƙayyadadden
lokaci. Misali, maginin zamani (mesin) yana da damar yin gini ne daga safe
zuwa yamma kawai.[4] |
Mai aiwatar
da sana’a yana da damar
yin aiki a kowane lokaci tare da hutawa a kowane lokaci. Misali, wanda yake
fassara dogon aiki a kan Trados, yana da damar dakatawa ya huta ko ya yi wata
hidima a kowane lokaci sannan ya ci gaba da aiki a duk lokacin da ya ga dama. |
|
|
Tallata
kasuwanci |
Hanyoyin
tallata sana’ar duniyar zahiri sun haɗa da tattaunawar gaba-da-gaba da raba
takardun talla da sanyawa a gidajen rediyo da talabijin da makamantansu.[5] |
Tallata
sana’a tana kasancewa a kan intanet kai tsaye. |
|
Tsaro |
Barazanar
tsaro a wannan fannin ya shafi fasa shago ko wurin aiki da satar kaya da
makamantansu. |
Barazanar
tsaro a sana’o’in duniyar intanet ya fi shafar kutse da tatsar bayanai ta
bayan gida. |
|
Wuraren ajiye
kayan aiki da kayayyakin sayarwa da wurin zaman ma’aikata |
Wanda yake da
sana’ar da ta bunƙasa, misali
kafintan ƙasa, to yana
buƙatar wuraren
ajiye kayan aikinsa da wuraren ajiye kayayyakin sayarwa (gadaje da kujeru da
sauransu, waɗanda aka haɗa domin a sayar) |
Wanda yake sana’a a duniyar intanet ba ya buƙatar wurare a zahirance na ajiye
kayayyakin sayarwa. A maimakon haka, yakan ajiye su ne a duniyar intanet
cikin tsarin da ake kira hosting ko storage. |
|
Wurin aiwatar
da aiki |
Yana iya
kasancewa yana da wuri na musamman da ake gudanar da shi (kamar maƙera domin ƙira ko masaƙa domin saƙa) |
Mai sana’a ko
masu sana’a suna iya kasancewa a ko’ina. Farfajiyar aiwatar da
sana’ar ita ce intanet (misali kafar Proz da ake ɗaukar hayar ma’aikata) |
|
Yana iya
kasancewa ma’aikaci sai ya je wurin da ake buƙatar aiwatar da aikin domin ƙera wani abu ko gyara wani abu
(misali kafintan sama sai ya je gidan da aka gina kafin ya yi rufin kwano). |
Mai sana’a ba
ya buƙatar ya je
wurin da ake buƙatar aiwatar
da aiki (misali mai gina zaure a kan wata kafar intanet zai yi hakan a duk
inda yake, alhali waɗanda zai yi wa aikin za su ga ya kammala a kan intanet). |
Madogara: Lura ta kai tsaye da nazarin ƙwaƙƙwafi
2.4
Naɗewa
Kafin
wannan littafin, yawancin rubuce-rubuce sukan raba sana’o’in Hausawa ba tare da
la’akari da mabambantan matakai da alƙaluma wajen samar da rabe-raben ba. Bayanan
da aka kawo a cikin wannan babi na biyu sun cike wannan babban gurbi da aka
bari a ɓangaren bayanin sana’o’in Hausawa. Kamar yadda bayanai suka gabata a
cikin babin, an yi la’akari da alƙaluma da suka haɗa da ‘zamani’ da ‘jinsi’ da ‘daraja’ da
‘amfani’ (da sauransu) wajen samar da rabe-raben sana’o’in Hausawa. Haka kuma,
babin ya tattauna shigar giragizai da ake samu tsakanin ‘sana’a’ da
‘kasuwanci’.
[1] Waɗanda suka ɗora abubuwa
a intanet suna da damar yin kasuwanci ko dai ta hanyar sayar da su abubuwan
kansu, ko kuma ta hanyar ɗora tallace-tallace a kafafe da shafukansu.
[2] A maimakon abataya
(overtime), ana iya samun kuɗin gaggawa ko kuɗin uzzurawa (rush
fee).
[3] Domin samun ƙarin bayani, ana iya duba
su kai tsaye a kafar: https://paxful.com/university/new-payment-methods.
[4] Akan samu lokutan da ake
gudanar da ire-iren ayyukan nan har cikin dare. Hakan ba zai yiwu ba sai an yi
waɗansu tanade-tanade na musamman, kamar samar da wadataccen haske da sauransu.
[5] Yana da kyau a fahimci cewa, a yau ana amfani da kafafen intanet domin tallata sana’o’in duniyar zahiri. Duk da haka, abin ba kamar na sana’o’in duniyar intanet yake ba. Dalili shi ne, sana’o’in duniyar zahiri ba su cika shafar al’ummomi da suke nesa da mai sana’a ba. Misali, kafintan ƙasa da yake Kano a Nijeriya, ba zai yi tunanin tallata hajarsa ga ‘yan Amurka da Burtaniya da Kanada ba (sai dai idan ya bunƙasa sosai da sosai).
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.