Ticker

6/recent/ticker-posts

Matakan Samar Da Rabe-Raben Sana’o’i a Zamanance

An ciro daga littafin:

BIƊA DA TANADI A DUNIYAR INTANET
(Sana’o’i, Kasuwanci, Ƙwadago)

Na

Abu-Ubaida SANI
Abdulrahman ALIYU

Bida Da Tanadi a Duniyar Intanet (Sana’o’i, Kasuwanci, Kwadago)
Manazartar Littafi: Sani, A-U. & Aliyu, A. (2026). Biɗa Da Tanadi a Duniyar Intanet (Sana'o'i, Kasuwanci, Ƙwadago). Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-978-62480-1-1. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.21361768

Tuntuɓa Domin Samun Littafi: 
Dr. Abu-Ubaida Sani: Imel - abuubaidasani5@gmail.com | WhatsApp - 08133529736
Dr. Abdulrahman Aliyu: WhatsApp - 08036954354

2.3 Matakan Samar da Rabe-Raben Sana’o’i a Zamanance

Akwai ayyuka da dama da suka gabaci wannan waɗanda suka yi ƙoƙarin kawo rabe-raben sana’o’i. Mafi yawansu sun raba sana’o’i ne zuwa rukunoni biyu, (i) na gargajiya da (ii) na zamani. Daga cikin waɗanda suka bi sahun wannan rabo akwai Abdullahi (2018 sh. 23) da Nasir (2021 sh. 14-15).

Wannan binciken yana da fahimtar cewa, ba za a iya samun rabe-raben sana’o’i a kammale ba, har sai an ɗora shi bisa alƙaluma daban-daban. Sanyinnawal (2015 p 23-35) yana da irin wannan fahimta. Ya bi matakai daban-daban wajen samar da rabe-raben sana’o’i. A ciki har da jinsi da darajar sana’o’in a idon jama’a. Abdullahi (2021 sh. 70-73) ma ya yi ƙoƙarin bin matakan samar da rabe-raben sana’o’i. Ya kawo matakai da suka haɗa da lokaci da jinsi da kuma ta la’akari da abubuwan da sana’o’in kan samar.

A ɓangare guda kuwa Nasir (2021 sh. 14-15) ya rawaito inda Umar ya raba kasuwanci zuwa gida biyu: (i) Kasuwanci ta hannun dillali, da (ii) Kasuwanci kai tsaye. Daga ƙarshe kuwa, Nasir ya raba kasuwanci zuwa manyan kaso guda biyu ta la’akari da tasirin da zamani ya yi kan rayuwar Hausawa. Ya bayyana su a matsayin (i) Kasuwancin gargajiya, da (ii) Kasuwancin zamni.

Bayan nazartar ayyukan da suka gabata, wannan bincike ya yi amfani da alƙaluma daban-daban wajen samar da rabe-raben sana’o’i kamar haka:

2.3.1 Rabe-Raben Sana’o’i ta La’akari da Jinsi

Yayin da aka yi la’akari da jinsi, za a iya raba nau’o’in kasuwancin Hausawa zuwa manyan rukunoni guda uku wato:

a. Sana’o’in maza

b. Sana’o’in mata

c. Sana’o’in tarayya

2.3.1.1 Sana’o’in Maza

Waɗannan su ne sana’o’in da al’ada ta shaidi maza zalla da gudanar da su. Sun haɗa da:

a. Dukanci

b. Ɗori

c. Farauta

d. Fatauci

e. Gini

f. Jima

g. Ƙira

h. Malantar gargajiya

i. Noma

j. Rini

k. Sassaƙa

l. Su/Kamun kifi

m. Wanzanci, da sauransu

2.3.1.2 Sana’o’in Mata

Waɗannan su ne nau’o’in sana’o’in da al’adar Hausawa ta shaidi mata kaɗai da aiwatar da su. Sun haɗa da:

a. Aikatau

b. Kaɗi

c. Kitso

d. Kuku

e. Lalle/ƙunshi

f. Shiƙa

g. Sussuka

h. Ungozoma

i. ‘Yar mai ganye, da sauransu

2.3.1.3 Sana’o’in Tarayya

Wannan nau’o’in sana’o’i ne waɗanda a bisa al’adar Hausawa ta sanya maza da mata a matsayin masu gudanar da su. Sun haɗa da:

a. Arkomi

b. Dillanci

c. Fawa

d. Ginin tukwane

e. Jagale

f. Kiɗa

g. Kiwo

h. Kwarami

i. Noma

j. Roƙo

k. Saƙa

l. Waƙa, da sauransu

2.3.2 Rabe-Raben Sana’o’i Ta La’akari Da Zamani

Ana iya samar da rabe-raben sana’o’in Hausawa ta la’akari da zamanin da sana’o’in suka samu. A ƙarƙashin wannan, za a ci karo da sana’o’in da suke da daɗaɗɗen tarihi a tsakanin Hausawa, waɗanda ake gudanar da su tun shekaru masu yawa da suka gabata. Ta fuska guda kuwa, akwai sana’o’in da Hausawa suka same su a zamanance. A taƙaice, ana iya raba sana’o’in Hausawa zuwa gida biyu a ƙarƙashin wannan rukuni, wato:

a. Sana’o’in gargajiya

b. Sana’o’in zamani.

2.3.2.1 Sana’o’in Gargajiya

Waɗannan su ne nau’o’in sana’o’in da suke da daɗaɗɗen tarihi a tsakanin Hausawa. Hausawa sun naƙalce su, sannan sun ci gaba da gudanar da su tun zamani mai tsawo da ya shuɗe. Misalansu sun haɗa da:

a. Dukanci

b. Farauta

c. Sassaƙa

d. Jima

e. Ƙira

f. Noma

g. Saƙa

h. Sassaƙa, da sauransu

2.3.2.2 Sana’o’in Zamani

Waɗannan su ne nau’o’in sana’o’in da Hausawa suka koya a zamanance. Cuɗanyarsu da baƙin al’ummu da kuma wayewa da sauye-sauyen zamani sun taka rawa wajen samuwa da bunƙasar waɗannan nau’o’in sana’o’i.

a. Ɗinki

b. Faci

c. Kabukabu/acaɓa

d. Kafintanci

e. Kanikanci

f. Tuƙi (mota)

g. Walda, da sauransu

2.3.3 Rabe-Raben Sana’o’i Ta La’akari Da Tasirinsu Ga Rayuwa

Kowace sana’a ta shafi sarrafa wani abu domin samar da wani abu. Abin da ake sarrafawa da wanda ake samarwa yana iya kasancewa bayyananne, na duniyar zahiri (misali saƙa kaba domin samar da tabarma). Yana kuma iya kasancewa wanda ba a gani, na duniyar baɗini wato ɓoyayyiyar gaskiya (misali sanya matakan tsaro a wani gida da yake kan intanet). Kowace sana’a tana da nau’in tasiri ko amfani da take da shi a rayuwa. Ana iya la’akari da tasirin wajen samar da rabe-raben sana’o’in Hausawa a yau. Misali:

a. Samar da abinci

b. Samar da kayan aiki

c. Samar da sutura

d. Kwalliya da gyaran jiki

e. Samar da magunguna, da sauransu

2.3.3.1 Samar Da Abinci

Waɗannan su ne nau’o’in sana’o’in da ta hanyarsu ne Hausawa suke samar da abinci tare da riskar da shi zuwa ga mutane daban-daban. Sana’o’in da suke ƙarƙashin wannan rukuni sun haɗa da:

a. Awo

b. Farauta

c. Fawa

d. Kiwo

e. Noma

f. Sakai

g. Su/kamun kifi

h. Awo, da sauransu

2.3.3.2 Samar Da Kayan Aiki

Wannan rukuni ne na nau’o’in sana’o’in Hausawa waɗanda ta hanyar su ne ake samun kayan aiki. Kayan aiki a nan na iya kasancewa na amfani a cikin gida ko a daji ko kuma waɗanda ake amfani da su wajen aiwatar da waɗansu sana’o’in na daban. Misalan sana’o’in da suke samar da kayan aiki sun haɗa da:

a. Dukanci

b. Gyartanci

c. Jima 

d. Kaɗi

e. Ƙira

f. Sassaƙa, da sauransu

2.3.3.3 Samar Da Sutura

Hausawa suna da waɗansu fitattun sana’o’in da suka shahara wajen samar musu da sutura, tun daga kan kayan sakawa da na ɗaurawa har zuwa na sanyawa a ƙafa. Waɗannan sana’o’i sun haɗa da:

a. Dukanci

b. Ɗinki

c. Jima 

d. Rini

e. Saƙa

2.3.3.4 Sana’o’in Kwalliya Da Gyaran Jiki

Akwai sana’o’in Hausawa da suke taimakawa kai tsaye wajen ado da gyaran jiki. Sun haɗa da:

a. Kitso

b. Koli

c. Ƙunshi/lalle

d. Wanzanci

2.3.3.5 Sana’o’in Samar Da Magunguna

Waɗannan su ne sana’o’in da babban amfaninsu shi ne samar da da magunguna. Magungunan nan suna iya kasancewa na wata cuta ko na biyan wasu buƙatun zuciya. Daga cikin sana’o’in akwai:

a. Bokanci

b. Bori

c. Ɗori

d. Magori

e. ‘Yar mai ganye

2.3.4 Rabe-Raben Sana’o’i Ta La’akari Da Matsayinsu a Cikin Sana’o’i

Daga cikin sana’o’in Hausawa, akwai waɗanda suke tamkar bishiyoyi, inda ake samun waɗansu sana’o’in na daban sun tsira daga cikinsu. Ma’ana a nan ita ce, sukan haifar da waɗansu sana’o’in a ƙarƙashinsu. Da a ce babu su, to lallai sana’o’in da suka dogara da su za su samu koma-baya, ko ma su daina wanzuwa kwata-kwata. A ƙarƙashin wannan rukuni ana iya samun manyan nau’o’in sana’o’i guda biyu kamar haka:

i. Manyan sana’o’i

ii. Ƙananan Sana’o’i

2.3.4.1 Manyan Sana’o’i

Manyan sana’o’i sun kasance masu taimakawa kai tsaye ga waɗansu sana’o’in na daban. Akan samu sana’o’i da suka dogara da su kai tsaye, ko dai don su samar musu da kayan aiki ko kuma domin su samar musu da kayayyakin gudanar da kasuwanci. Ire-irensu sun haɗa da:

a. Kiwo[1]

b. Ƙira[2]

c. Noma[3]

2.3.4.2 Ƙananan Sana’o’i

Koma-bayan manya, ƙananan sana’o’i ba su da waɗansu sana’o’in da suka dogaro kai tsaye a kansu. Ma’ana, ba sa taka muhimmiyar rawa wajen samar da kayan aikin gudanar da waɗansu sana’o’i. A maimakon haka, yawanci al’umma suna amfani ne kai tsaye da kayayyakin da ire-iren sana’o’in suke samarwa. Misalansu sun haɗa da:

a. Dakau

b. Gyartai

c. Kitso

2.3.5 Rabe-Raben Sana’o’i Ta La’akari Da Ƙimarsu

Ƙimar sana’o’i a nan na nufin darajarsu da ta masu aiwatar da su a idon al’umma. Wannan suna da alaƙa da gudummawar da suke bayarwa ga al’umma da kuma yanayin kuɗin da sana’o’in suke samarwa ga masu gudanar da su. A wannan ɓangare ma ana iya raba sana’o’i zuwa manyan rukunoni guda biyu:

i.Masu ƙima

ii.Marasa ƙima

2.3.5.1 Masu Ƙima

Waɗannan su ne nau’o’in sana’o’in da al’umma suka fi ganin darajarsu da darajar masu aiwatar da su. Sun haɗa da:

a. Ƙira

b. Masu jima a da

c. Noma

d. Wanzanci

2.3.5.2 Marasa Ƙima

Wannan rukuni ne na sana’o’in da al’umma ba ta cika kallon su da daraja ba bisa al’adar rayuwa. Sun haɗa da:

a. Dakau

b. Gyartai 

c. Kitso

d. Ƙwadago

Yana da kyau a fahimci cewa, ƙima ko rashin ƙimar sana’a ya danganta ne da yadda al’umma suka ɗauke ta. Dangane da wannan, Sanyinnawal (2015 sh. 35) ya bayyana cewa:

Galibi sana’o’in yi wa jama’a hidima musamman waɗanda ake yi don gyaran jiki ana danganta su da sana’o’in da ba su da ƙima. Ba kuma don ba su da amfani ba, sai dai saboda ladar aikin da ake ba masu irin wannan sana’ar ba ta da wani yawa. Ire-iren waɗannan sana’o’i sun haɗa da: Wanzanci da igidi da sussuka (koda) da dakau da kitso da ƙwadago da fawa da garuwa (taula) da gyartai da faskare da ginar rijiya ko masai. Wani dalili da ke sa ake yi wa waɗannan sana’o’i kallon rashi ƙima shi ne wasu daga cikinsu talauci ko rashi ke haifar da su. Wasu kuma ɗabi’ar masu aiwatar da su ke jawo wa sana’o’in matsalar rashin ganin su da ƙima.

A nan za a iya lura da inda ya jaddada cewa, abubuwan da suke sa a ɗauki sana’a a matsayin marar ƙima sun haɗa da ɗabi’un masu aiwatar da sana’ar da kuma kasancewar talauci ne yake sa masu yin ta ci gaba da yi.




[1] Sana’o’in da suke amfana da sana’ar kiwon dabbobi sun haɗa da fawa da jima da dukanci da kiɗa da kuma ƙira.

[2] Sana’ar tana taimakawa wajen samarwa da gyara waɗansu kayayyakin noma (kamar fartanya da garma/galma) da kitso (kamar kibiya) da aski (kamar aska) da fawa (kamar wuƙa) da makamantansu.

[3] Sana’o’i da dama sun samu ne a ƙarƙashinsa, kamar su sakai da sussuka da dakau da makamantansu.

Post a Comment

0 Comments