An ciro daga littafin:
BIƊA DA TANADI A DUNIYAR INTANET
(Sana’o’i, Kasuwanci, Ƙwadago)
Na
Abu-Ubaida SANI
Abdulrahman ALIYU
INTANET
DA HAUSAWA DA HARSHENSU
A
babin da ya gabata, an tattauna batutuwa da suka shafi ‘sana’a’ da ‘kasuwanci’.
Wannan ya haɗa har da alaƙa da bambancinsu. Haka kuma, babin ya kawo rabe-raben
sana’o’in Hausawa tare da faɗaɗa bayaninsu. A wannan babi na uku, za a dubi
kalmar ‘intanet’ tun daga kan ma’ana har zuwa tarihin samuwa da bunƙasar intanet. Haka kuma, za
a ga tasirin intanet a kan Hausawa da kuma tasirin su Hausawa a kan intanet.
Intanet
baƙon
al’amari ne a duniya baki ɗaya. A kan haka, “kalmar intanet baƙuwa ce a fannin nazarin
Hausa” (Mukoshy, 2015 sh. 19). Asalin kalmar a Ingilishi ita ce “internet.”
An samu bambancin fahimtar kalmar da ta fi dacewa a yi amfani da ita a Hausa.
Akwai waɗanda suke ganin ya fi dacewa a yi amfani da yanar gizo ko yanar
gizo-gizo. Daga cikin masu amfani da wannan fahimtar akwai ’Yartsakuwa
(2017) da Gana (2020) da CMG Hausa (2022).
A
ɓangare guda kuwa, akwai masana da manazarta da suke da fahimtar a Hausantar da
ita zuwa “intanet.” A.H. Amfani (keɓantacciyar tattaunawa, wajajen 7 zuwa 28 ga
watan Mayu 2019) yana da irin wannan fahimtar. Ya jaddada cewa “Furta intanet
ai ba ta gagari Bahaushe ba da har za a tsaya ana kame-kame.”[1]
Rubuce-rubucen da suka yi amfani da kalmar intanet sun haɗa da BBC Hausa
(2010) da Umar (2012) da Rambo (2014) da Mukoshy (2016) da Muryar Hausa24
Online Media (2020).
Muhimmanci
da tasirin intanet ga rayuwar ɗan’adam ya sa a kullum ake samun ƙaruwar rubuce-rubuce a
wannan fanni cikin harsuna daban-daban. A shekarun baya-bayan nan an samu ƙaruwar rubuce-rubuce cikin
Harshen Hausa game da intanet. Masana da manazarta da dama sun yi ƙoƙarin ba da ma’anar kalmar
intanet. Umar ya ce:
Intanet
kafa ce wadda ta haɗa bayanai daban-daban, kuma an sauƙaƙa hanyoyin amfani da
waɗannan bayanai yadda kowa zai iya miƙa hannayensa a kowane lokaci a ko’ina. (Umar,
2012 sh. 48)
Wannan
ma’ana ta yi ƙoƙarin hasko yadda intanet yake ɗauke da tarin bayanai da
kuma yadda suke da sauƙin amfani. Wani ɗan raunin da yake cikin wannan ma’ana
shi ne, ba kowane lamarin intanet ba ne yake da sauƙi. A ɓangare guda kuwa,
ma’anar ba ta karkata ne kawai a kan bayanan da ake samu a duniyar intanet ba
tare da mayar da hankali kan salailai da sigoginsu ko hanyoyin samar da su da
sarrafa su ba.
Mukoshy
(2015) ya nazarci wasu daga cikin ma’anonin intanet da masana da manazarta suka
bayar.[2]
Daga ƙarshe
ya bayyana tasa ma’anar da cewa:
Intanet
kafar sadarwa ce ta na’urorin zamani wadda ta game duk duniya. Tana ba da damar
sadar da bayanai kowaɗanne iri, kuma zuwa ko’ina a duniya cikin ɗan ƙanƙanin lokaci. (Mukoshy, 2015
sh. 20).
Da
alama Mukoshy ya yi aron hannu ga Umar, (2012) wajen fitar da wannan ma’ana ta
intanet. Duka ma’anonin biyu (Mukoshy da Umar) suna nuna cewa, kowa na da damar
yin amfani da intanet, sannan daga kowane wuri. Ma’anar da Mukoshy ya bayar ta
zo da ƙarin
batun “na’urori” waɗanda suka kasance gishiri cikin lamuran duniyar intanet.
Haƙiƙa waɗannan ma’anoni sun ba
da haske kan abin da ake nufi da intanet. Duk da haka, akwai muhimmin al’amari
da ya kamata bayani kan kalmar ya ƙunsa. Wannan kuwa shi ne nuna bagire ko farfajiyar kafar
sadarwar wadda ta kasance bisa hanyoyin iska waɗanda ba a iya ganin su. Tun a
shekarar 2010 Amfani ya kawo wannan cikin ma’anar da ya bayar inda yake cewa:
Intanet
tsari ne da ya haɗa duniya, ta haɗakar layin iska na kwamfutoci waɗanda ke
amfani da tsare-tsaren yanar gizo don biya wa biliyoyin masu amfani buƙatu a faɗin duniya. (Amfani
(2010) a cikin Umar (2012 sh. 48)).
Yayin
da aka nazarci waɗannan ma’anoni da ma makamantansu, za a tarar da cewa akwai
muhimman abubuwan da suka taru suka samar da kafar intanet. Za a iya kallon su
a matsayin siffofin intanet. Ko ma wace ma’ana ce ta fi kwanciya a ran
manazarci, yana da kyau a fahimci cewa:
a. Intanet
al’amari ne da ya samu a zamanance.
b. Intanet
ya kasance al’amari mai faɗi da ban mamaki. Yana ƙunshe da dukkanin wasu
fannoni da ake samu a duniyar rayuwar yau da kullum.
c. Intanet
ba ya gudanuwa sai da taimakon na’urori masu ƙwaƙwalwa (nau’o’in kwamfuta
daban-daban).[3]
d. Hulɗayyar
intanet abu ce wadda ba a gani, amma ana kallon sakamakonta ta fuskokin
kwamfutoci. Akwai kuma sakamakon da yake bayyana a gan shi a zahiri ko a ji
sautinsa ko ɗuminsa, da sauransu.
e. Intanet
yana da yaruka daban-daban. Yayin da aka tura saƙo bisa intanet, sai ya
fassaru cikin yaren da intanet yake ganewa. Daga nan kuma sai ya sake fassaruwa
zuwa yare ko sigar da masu neman sakamakon yake iya fahimta.
f. Babu
wani al’amari na intanet da yake da damar yin kansa. Komai aka gani a duniyar,
to yin sa aka yi. Duk da haka, ana iya ba wa wani al’amari a duniyar intanet
damar maimaita kansa ko sarrafa kansa zuwa wasu sigogi mabambanta.
g. Intanet
al’amari ne da ya jawo nesa kusa,[4] ya
mayar da abu mai yawa ya zama kaɗan,[5] ya
mayar da abu kaɗan ya zama mai yawa,[6]
sannan ya tsuke faɗin duniya.
h. Intanet
haɗaka ce ta tsauraran al’amura daban-daban. Sun haɗa da yarukan intanet da
gine-ginensa da hanyoyin shigarsa da sabis ko netwok wanda shi
yake ba da damar kaiwa gare shi.
Lura
da waɗannan, ba da kammalalliyar ma’anar intanet da za ta bayyana dukkanin
siffofinsa aiki ne ja. Duk da haka, ta bin sawun zaren tunanin magabata wajen
ba da ma’anar intanet, za a iya cewa:
Intanet
fasaha ce ta zamani wadda ta ƙunshi haɗakar tsauraran al’amura da suka haɗa da yaruka
da na’urori da sabis waɗanda haɗuwarsu yake samar da al’amari ko bagire da yake
tattare da hadahada da fannoni tamkar waɗanda suke duniyar yau-da-kullum, ciki
har da abubuwan da suka shafi sadarwa da makarantu da bankuna da kasuwanni da
shaguna tare da sauran halittu kamar mutane da dabbobi da waninsu.
3.2 Samuwa Da Bunƙasar Intanet
Masana
da manzarta sun gudanar da rubuce-rubuce masu yawa dangane da tarihin samuwar
intanet da bunƙasarsa cikin harsuna mabambanta.[7] Sake bibiyar tarihin tiryan-tiryan zai kasance tamkar maimaici ne ga
ayyukan baya kawai ba tare da gabatar da wani sabon al’amari ko ilimi ba. Lura
da haka, wannan bincike zai fi mayar da hankali wajen zaƙulo sauye-sauye da cigaba
da aka samu a harkar intanet tun bayan ƙirƙirarta.
Bincike
da dama da suka gabata sun danganta tarihin intanet da yunƙurin wata hukumar tsaro da
take Amurka. Binciken Gerf (2004 sh. 1360) ya bayyana cewa, a shekarun 1970s ne
aka samu hoɓɓasa na kafar intanet na farko mai suna ARPANET. Wannan
bayani ya yi daidai da wanda Mukoshy, (2015 sh. 21) ya rawaito daga Deitel da
Deitel, (2009). Mukoshy ya yi ƙarin bayani da cewa, kafar intanet ta ARFA ta samu ne
bayan hukumar da aka fi sani da The Advanced Research Project Agency (ARPA)
ta gudanar da taro a shekarar 1969. Wannan hukumar ta kasance ƙarƙashin Department of
Defense in United States.[8]
3.2.1 Bunƙasar Intanet Da Yake Haɗa Na’urori
A
binciken da Romualdo & Alessandro (2007 sh. 2) suka gudanar, sun tabbatar
da cewa intanet a wancan lokaci ta shafi haɗaka ta kai tsaye ne daga kwamfuta
zuwa kwamfuta. A farko-farkon al’amarin intanet, akwai manyan matakai huɗu na
cigaba da aka samu. Sun kasance kamar haka:
a. Sambai (Linear)
Wannan
shi ne tsarin intanet na farko. Dukkanin kwamfutocin da suke haɗe da intanet
ɗin suna kan layi guda ne. Saƙo na tashi daga kwamfuta ta farko zuwa ta biyu sannan ta
uku, har ƙarshe.
Misali, saƙon
da ya tashi daga “A” sai ya je “B”, ya je “C”, ya je “D” sannan ya je “E.” A
irin wannan tsari, yayin da aka katse kwamfuta guda daga kan layi, to tamkar an
katse sauran ne. Misali, idan aka katse “C”, to “D” da “E” ba za su iya karɓar
saƙo
ba. Ga misali cikin hoton da yake ƙasa:
Hoto Na 3.1: Tsarin Intanet Mai Bin Sambai
Madogara: Romualdo & Alessandro (2007 sh. 3)
b. Zobe (Ring)
Bayan
an ɗau lokaci ana amfani da intanet mai bin tsarin sambai, cigaba da aka samu
ya sa aka fito da tsarin intanet Maizobe. A wannan tsari, saƙo na zagayawa ne cikin wani
tsari na da’ira. Saƙo daga kowace kwamfuta na iya zuwa sauran kwamfutoci. Duk
da haka, idan kwamfutar ba ita take gefen wadda ta tura saƙo ba a kan intanet, to sai
saƙon
ya bi cikin kwamfutocin da suke tsakani a cikin jerinsu kafin ya isa zuwa wadda
za ta karɓi saƙon. Ga misali cikin hoton da yake ƙasa:
Hoto Na 3.2: Tsarin Intanet Maizobe
Madogara: Pedamkar (2019 SL. 47)
c. Tauraro (Star)
Bunƙasar al’amuran intanet ya
kai ga samun cigaba zuwa tsarin haɗakar kwamfutoci cikin sigar tauraro. A
wannan tsari, babbar kwamfutar da ta haɗa sauran kwamfutoci takan kasance a
tsakiya. Saƙon
da ya tashi daga gare ta yana isa ga dukkanin sauran kwamfutoci. Idan wata
kwamfuta za ta tura saƙo ga ‘yar uwarta, dole sai saƙon ya iso cikin wannan
babbar kwamfutar. Daga nan ne saƙon zai iya kaiwa ga kwamfutar da aka aika shi. A nan, ke
nan an taƙaita
zanguna da saƙo yake yi cikin kwamfutoci kafin ya kai kwamfutar da ake
buƙatar
tura shi. Aikin Basu (2019) ya kawo hoton wannan tsari kamar haka:
Hoto Na 3.3: Tsarin Intanet Mai Zubin Tauraro
Madogara: Basu (2019 sh. 1)
d. Jigida (Mesh)
Ci
gaba da aka sake samu a sha’anin intanet ya samar da sabon salon haɗakar
kwamfutoci. A wannan tsari, kwamfutoci sukan kasance a sarƙe. Kwamfuta guda na da
damar isar da saƙo kai tsaye zuwa kwamfutoci biyu ko ma sama da haka. Abin
lura a nan shi ne, kwamfuta tana da damar isar da saƙo ne kawai ga kwamfutocin
da aka riga da aka samar da hanyar isar da saƙo tsakaninsu. Hoton da yake
ƙasa
yana ɗauke da ƙarin bayani dangane da wannan tsari.
Hoto Na 3.4: Tsarin Intanet Mai Zubin Jigida
Madogara: Keary (2024 SL. 52)
Lura
da duk waɗannan, lallai Hausawa sun yi gaskiya da suka ce: “Sannu ba ta hana
zuwa, sai dai a daɗe ba a je ba.” A zuwa yau, tsarin intanet ya samu bunƙasa da ya wuce dukkanin
waɗannan matakai. A yanzu kwamfutoci suna haɗe ne cikin wani tsari mai sarƙaƙiyar gaske. Kowace kwamfuta
tana iya haɗuwa da ‘yar uwarta tare da tura mata saƙo kai tsaye. Misali, “A” na
haɗe da “B” da “C.” “B” na haɗe da “A” da “C.” “C” na haɗe da “A” da “B.” A taƙaice, ba a buƙatar saƙo ya bi ta cikin wata
kwamfuta kafin ya kai ga wata.[9]
[1] Wannan bincike ya fi
karkata a kan amfani da kalmar intanet a maimakon yanar gizo. An
yi wannan zaɓin ne kasancewar:
a. Ta fi riƙe bakin Hausawa.
b. Ta fi hasko hoton abin
da ake nufi kai tsaye domin kamancen sauti da take da shi da furucin kalmar internet
a Ingilishi.
c. Ta fi zagaya kafafen
intanet da manhajojin fassara na ƙasa-da-ƙasa.
[2] Sun haɗa da ma’anonin da
suka fito daga Almajir (2008) da Muhammad (2011) da Umar (2012).
[3] Yana da kyau a tuna cewa,
kwamfuta tana zuwa cikin sigogi da dama. Wayoyin hannu da agogwannin dijita da
talabijin ɗin dijita duk suna iya shiga cikin jerin nau’o’in kwamfutoci da ake
da su.
[4] Misali, wanda yake zaune a
ƙasar
Hausa zai iya yin magana da wanda yake birnin Sin yayin da suke kallon juna.
Zai kuma iya taya shi wani aiki da yake gudanarwa a kan intanet a wannan
lokaci.
[5] Misali, kafar intanet guda
za ta iya ɗaukar dubban miliyoyin manyan littattafai waɗanda idan ɗakin karatu
za a gina domin adana su, abin sai wanda ya gani.
[6] Idan za a ba da wata
sanarwa ta amfani da jarida ko wasiƙa, ana buƙatar buga takardu masu matuƙar yawa domin rarrabawa ko
lilliƙawa
a wurare domin amfanin saƙonnin su kai ga jama’a. Ta hanyar amfani da intanet,
rubutu guda zai iya wadatarwa ba tare da an yi ta maimaitawa ba.
[7] Rubuce-rubucen da suka
kawo tarihin intanet sun haɗa da Leiner et al. (1997) da Romualdo &
Alessandro (2007) da Jonathan (2008) da Mukoshy (2015).
[8] A ƙasar Hausa kuwa, intanet ya
fara shigowa a wajejen 1990 kamar yadda Mukoshy (2016 sh. 27) ya rawaito daga
Almajir (2009). Duk da haka, bai bunƙasa ba sai a wajejen 1998.
[9] Duk da haka, akan yi wannan tsari (na sanya wata kwamfuta a matsayin mai karɓar saƙo da tura shi zuwa kwamfutar da aka aika shi) musamman yayin da ake buƙatar tara saƙonni da tace su a wani mataki kafin a wuce da su zuwa sauran kwamfutoci.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.