An ciro daga littafin:
BIƊA DA TANADI A DUNIYAR INTANET
(Sana’o’i, Kasuwanci, Ƙwadago)
Na
Abu-Ubaida SANI
Abdulrahman ALIYU
4.1.1.2 Fassara
(Translation)
Fassara
babban fage ne a fannin kimiyyar harsuna. Kasuwarsa ta daɗe tana ci, sannan
kullum ƙara
bunƙasa
take yi. Duk da yawan rubuce-rubuce da aka yi dangane da fassara, ma’anarta ba
ta kasance mai ruɗani ko janyo muhawara ba. Abbuwan da ake da bambancin ra’ayi
game da su sun haɗa da matakan gudanar da fassarar da yiwuwar samun
ingantacciyar fassara da makamantansu. Sulaiman (2013 sh. 201) ya nazarci
ayyukan Malumfashi (2012) da Yakasai (2012) da Sarɓi (2012) sannan ya fitar da
ma’anar fassara da cewa: “... na nufin mayar da ma’anar wani bayani ko kalma
daga harshen bayarwa zuwa harshen karɓa.”
A
sauƙaƙe ana iya cewa, fassara
tana nufin aikin da ya shafi fasahar bin tsararrun matakan samar da ma’anar
kalma ko kalmomi ko jumloli ko bayanai da aka yi a cikin wani harshe (wanda ake
kira harshen bayarwa) zuwa wani harshe (wanda ake kira harshen karɓa)[1] ba
tare da salwantar da ainihin ma’anar kamar yadda take a harshen bayarwa ba,
bisa la’akari da muhimman abubuwan da suka haɗa da bambance-bambancen al’adu da
tsarin ginin jumla da suke tsakanin harsunan biyu. Musa da Sani (2010) sun
jaddada cewa: “Mai fassara masani ne na harasa fiye da ɗaya, amma ƙwararre a harshen uwa. Don
haka, kowane mai fassara da irin basirarsa ta fahimtar harshe daidai gwargwado.
(Musa & Sani, 2010 sh. 104).
Ayyukan
fassara suna taimakawa ta fuskoki daban-daban. Ko bayan samar da aikin yi ga
masana harshe, sukan taimaka ta fuskar bunƙasa fannonin da suka shafi
addini da adabi da harshe da kimiyya da fasaha.[2]
Sarɓi (2010 sh. 84-85) ya nazarci yadda ayyukan fassara suka taimaka matuƙa wajen samar da cigaba a
duniya. Bisa wannan ne yake ganin ya kamata a samar da makarantun fassara na
musamman domin bincike da fassara ayyukan kimiyya da fasaha kamar yadda aka yi
a cibiyar da ake kira House of Wisdom[3] a Bagadada.
A
cikin dukkannin nau’o’in ayyukan da suke ƙarkashin kimiyyar harshe, za a iya cewa aikin
fassara ya fi yawa. Wannan yana daga cikin dalilan da suka sa aka fi kiran
kamfanonin da suke gudanar da ayyukan da suka shafi kimiyyar harshe da suna
‘kamfanonin fassara’.
A ƙwadagon fassarar kan
intanet, an fi yin lissafin kuɗin aiki cikin dala. Bugu da ƙari, ana biya ne
kalma-kalma ba kuɗin goro ko shafi-shafi ba. Farashin kowace kalma ya danganta
kan alƙaluma
da suka haɗa da:
a. Harsunan fassara (na bayarwa da na karɓa)
b. Yanayin kamfanin
c. Yanayin ƙunshiyar abin da za a
fassara (wahalarsa ko sauƙinsa ko darajarsa)
d. Ƙwarewar mai aikin fassarar
e. Yawa ko ƙarancin abin da za a
fassara
A
aikin fassara daga waɗansu harsuna zuwa harshen Hausa, yawanci kuɗin yana
kamawa daga dala 0.03 zuwa 0.8 ga kowace kalma. Wannan ya kama wajajen naira
arbain da takwas zuwa ɗari da ashirin da takwas (N48 – N128) ga kowace kalma.
Akwai
manyan nau’o’in fassara guda biyu; (a) fassara zuwa harshen karɓa da (b) mayar
da fassara zuwa harshen bayarwa. An kawo bayaninsu a ƙasa, kamar haka:
a. Fassarar Gaba (Front
Translation): Wannan
shi ne nau’in fassarar da aka fi sani da sabawa da shi. Ya shafi yin fassara
kai tsaye daga harshen bayarwa zuwa harshen karɓa. Misali shi ne fassara daga
Ingilishi zuwa Hausa, ko daga Larabci zuwa Hausa.
b. Fassarar Baya (Back
Translation): Wannan
nau’in fassara ne a inda ake sake mayar da fassara zuwa harshen bayarwa. Ma’ana
ke nan, bayan an yi fassara daga harshe na ɗaya zuwa harshe na biyu, sai kuma a
sake mayar da shi daga harshe na biyun zuwa harshe na ɗaya. Idan aka yi
la’akari da misalan da aka bayar a sama a ƙarƙashin “a” da yake ƙasan “4.1.1.2”, to wannan
nau’in fassarar zai kasance sake mayar da abin da aka fassara zuwa harsunan
farko (wato daga Hausa zuwa Ingilishi da Larabci).[4]
4.1.1.3 Daidaita Fassarori (Harmonization)
Wannan
ma ɗaya ne daga cikin nau’o’in ayyukan fassara waɗanda suka shafi harshen
Hausa. Kamar yadda sunan ya nuna, daidaita fassarori yana nufin nazartar
fassarorin da masu fassara biyu ko sama da haka suka yi domin samar da
ingantacciyar fassara daga cikinsu. A kowane yankin fassara, za a ɗauki wadda
ta fi dacewa, ko kuma a ɗauko ɓangarori (misali farkon fassara ta farko da ƙarshen fassara ta biyu)
domin samar da fassara mafi nagarta. Aikin daidaita fassara yana tasowa
sakamakon manyan dalilai guda biyu kamar haka:
a. Bayar da fassara kai
tsaye ga masu fassara daban-daban: Ana iya ba wa mutane daban-daban fassara tun a karon
farko domin muhimmancin abin da ake son fassarawa, ko don wani dalili na daban.
Daga ƙarshe
kuma, sai a samu wani ƙwararre na daban domin daidaita fassarorin da suka samar.[5]
b. Fassarar baya: A duk lokacin da aka bayar
da fassarar baya (misali mayar da Hausa zuwa Ingilishi), to za a duba domin
tabbatar da cewa ba a samu gurɓatar ma’ana ba a fassarar gaba da aka yi. Idan
an samu gurɓacear ma’ana, to za a tafi matakin daidaita fassara. A wannan
gaɓar, za a samu ƙwararren da zai nazarci fassarorin biyu (ta gaba da ta
baya) da kuma asalin harshen karɓa (source language) domin daidaita wuraren da
suke da matsala.
[1] Ko bayan wannan suna
(harshen bayarwa da harshen karɓa), akwai waɗansu sunayen da ake musu. Sun haɗa
da (a) harshe na ɗaya da harshe na biyu, ko (b) harshen aiki da harshen mai
aiki.
[2] Domin ƙarin bayani, a duba Sarɓi
(2013 sh. 145).
[3] Domin samun bayanin House
of Wisdom, a duba Sarɓi (Sarɓi, 2010 sh. 79-83).
[4] Yana da kyau a fahimci
cewa, idan kai tsaye aka bayar da aikin fassara daga Hausa zuwa Ingilishi ko
Larabci, to wannan ba fassarar baya ba ce. Za ta kasance fassarar baya idan aka
sake buƙatar
fassara abin da yake cikin harshen Ingilishi da Larabcin zuwa Hausa. Ana yin
fassarar baya ne domin tabbatar da cewa ma’anar saƙon da aka fassara bai
salwanta ko ya gurɓace ba yayin da aka yi fassarar gaba. Yayin da aka lura da
gurɓacewar ma’ana, to akwai buƙatar wani sabon aiki mai suna Daidaita Fassara (Harmonization).
An tattauna wannan a ƙasa a ƙarƙashin 4.1.1.3.
[5] Sau da dama Hausawa da suka goge a aikin fassara sukan yi ƙorafin yadda suke cin karo da gurɓatattun fassarori waɗanda a bayyane suke cewa ba Hausawa na haƙiƙa ba ne suka yi su.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.