An ciro daga littafin:
BIƊA DA TANADI A DUNIYAR INTANET
(Sana’o’i, Kasuwanci, Ƙwadago)
Na
Abu-Ubaida SANI
Abdulrahman ALIYU
4.1.1.4 Fassara Da Ƙirƙira (Transcreation)
Aikin fassara da ƙirƙira yana matuƙar kama da aikin fassara, musamman mai ‘yanci. Babban bambancinsu shi ne, a aikin fassara da ƙirƙira, an fi mayar da
hankali kan ƙirƙiro maganganu da suka dace da al’ada da adabin al’ummar da ake son isar wa saƙo. Wannan yana nuna cewa, za a fi mayar da hankali kan
daidaiton kalaman cikin rubutun da al’adun Hausawa da salon furta kalamansu.
Wannan ma yana ƙara jaddada buƙatar Hausawa su shiga a dama da su a ire-iren ayyukan
nan don kauce wa gurɓacewar al’adun Hausa a
hannun baubayi.
Mai aikin fassara da ƙirƙira yana da damar
ragi da ƙari mai yawa daidai
da manufar saƙon. Wannan ne yake
ba da dama saƙo ya fito ɗauke da salon magana
da falsafar zance irin na masu magana da harshen a matsayin harshen uwa. Wannan
yana nuna cewa, ana sa ran Bahaushe ya maye gurbin karin maganganun da ya ci
karo da su da na Hausawa masu makamanciyar ma’ana da na harshen da yake aiki a
kai. Aikin Mirela (2024) ya kawo cikakkiyar ma’anar ‘fassara da ƙirƙira’ da cewa:
Transcreation is a process in
the field of language services where content is not just translated from one
language to another but also creatively adapted to suit the cultural and
emotional context of the target audience. (Mirela, 2024 SL. 6).
Fassara:
Fassara da ƙirƙira wani mataki ne a
farfajiyar ayyukan da suka shafi kimiyyar harshe a inda ba wai kawai ana
fassara ƙunshiya ba ne daga
wani harshe zuwa wani, face ana yi masa kwaskwarima cikin ƙwarewa domin ya dace da al’ada da tunanin masu
harshen da ake fassara zuwa cikinsa.[1]
A duniyar ayyukan kimiyyar
harshe a yau, dole ne a bambance tsakanin ‘fassara’ da kuma ‘fassara da ƙirƙira.’ Ayyukan fassara da dama suna da tsari da ƙa’idojin da suka shafi taƙaitawa da bin harshen karɓa sawu da ƙafa. Wannan yana faruwa musamman idan ana fassarar ne
domin koyar da wata manhajar ‘ƙirƙirarriyar basira’
(AI). Yawanci kamfanonin fassara sun fi zaɓan ƙwararru yayin bayar da wannan aikin. Dole ne mai aikin
ya kasance yana da ƙwarewa a harshe da
adabi da al’ada. A taƙaice ke nan, wanda yake da gogewa a fannin harshe da
adabi da al’adun Hausawa, shi ne zai iya gudanar da wannan aiki yadda ya
kamata. A duba hoton da yake ƙasa:
Hoto Na 4.1: Kamfanin
fassara suna neman mai aikin fassara da ƙirƙira cikin
harshen Hausa
Madogara: Saƙon imel
[1] Domin
samun ƙarin bayani game da ‘fassara da ƙirƙira’ ana iya duba Katan (2016) da Carreira (2023).
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.