An ciro daga littafin:
BIƊA DA TANADI A DUNIYAR INTANET
(Sana’o’i, Kasuwanci, Ƙwadago)
Na
Abu-Ubaida SANI
Abdulrahman ALIYU
4.1.1.5
Fassarar Kan Sikirin (Subtitling)
Fassarar kan sikirin fassara ce da
ake yi na maganganu da sautukan da halittun cikin bidiyo suke furtawa, tare da
sanya su yadda za su riƙa bayyana a kan
sikirin ɗin na’urar da ake kallon bidiyon a daidai inda ake
samar da wannan sautin ko ake furta maganar.[1] A yau da duniya ta
rungumi kallo da sauraro sama da karatu, bidiyoyi suna ƙara yawaita a duniya. Yayin da shirin game-duniya yake
ƙara kankama, a
kullum duniya tana ƙara buƙatar fassarar kan sikirin. Kamfanoni da ma’aikatu da gwamnatoci sukan sanya fassarar kan sikirin a
bidiyoyin da suke tallata haja ko manufofinsu domin saƙonnin su kai ga al’ummu daban-daban a
faɗin duniya. A duba misali a hoton da yake ƙasa:
Hoto Na 4.2: Bidiyon Hausa da fassarar
kan sikirin cikin Ingilishi
Madogara: https://www.youtube.com/watch?v=0dQn93P8ZiM
Wannan waƙa ce ta Nazifi Asnanic (Nazifi Abdulsalam Yusuf) da
Ali Jita (Ali Isah) da kuma Naziru Sarkin Waƙa (Naziru M Ahmad). Tana da taken “Nonon Uwa Na
Farko”. Za a lura da cewa, an yi mata fassarar kan sikirin cikin harshen
Ingilishi.
Ko bayan waɗannan, ana samun bidiyoyi masu tarin yawa
cikin harshen Ingilishi ɗauke da fassarar kan
sikirin cikin harshen Hausa. Haka kuma, akwai dubbannin bidiyoyin Hausa waɗanda suke ɗauke da fassarar kan
sikirin cikin Ingilishi.[2] Wannan ya samar da
wata kasuwa ga ‘yan ƙwadagon kan intanet
waɗanda suka ƙware a fannin samar da fassarar kan sikirin.
4.1.1.6 Gyaran Rubutu (Editing)
Gyaran rubutu wani babban
reshe ne na ayyukan ƙwadagon kan intanet
da suka shafi kimiyyar harshe. A wannan mataki, ana son tabbatar da cewa an
gyara duk waɗansu kurakurai da suka shafi
ƙunshiyar rubutun. A
Hausa, ya haɗa da daidaita jumloli domin
dacewa da yadda Bahaushen ƙwarai zai faɗe su, da kuma
tabbatar da rubutun bai kauce wa al’adar maganar Hausawa ta yau da kullum ba.
Aikin gyaran rubutu yana iya
cin gashin kansa. Haka na faruwa ne idan rubutun da za a gyara a cikin harshe ɗaya yake (misali
Hausa). A nan, mai gyaran zai bi rubutun ne domin daidaita zaman jumloli da
yadda aka ƙulla zaren tunani a
cikinsa.
A ɓangare ɗaya kuwa, aikin
gyara na iya biyo bayan wani aikin kimiyyar harshe da aka kammala. Misalan
wannan sun haɗa da gyaran rubutu bayan
kammala aikin fasara ko aikin fassarar kan sikirin, da dai sauran makamantansu.
A irin wannan yanayi, akwai buƙatar mai gyara ya
nazarci rubutu cikin harsuna biyu.[3] A duba misali a
hoton da yake ƙasa:
Hoto Na 4.3: Kamfanin fassara na Game
Lang suna neman wanda zai yi aikin gyaran rubutu
Madogara: Saƙon imel daga
kamfanin fassara na Game Lang
‘TEP’ a aikin fassara yana
nufin “Translation, Editing, and Proofreading”, wato fassara da gyaran
rubutu da kuma karatun bita. A cikin wannan hoto da aka kawo a sama, za a ga
cewa kamfanin suna neman wanda zai iya waɗannan ayyuka game da
harshen Hausa. A irin haka ne waɗanda ba Hausawa ba
suke amsa gayyatar yayin da aka rasa Hausawa ƙwararru a kusa.
[1] Domin ƙarin bayani game da ‘Fassarar Kan Sikirin’ (Subtitling), ana iya duba Ishika (2023).
[2]
Bidiyoyi masu tarin yawa a kan TikTok da YouTube (da sauran kafafen makamantansu)
suna ɗauke da fassarar kan
sikirin.
[3] Domin ƙarin bayani game da aikin gyaran rubutu, ana iya duba Saldanha & O’Brien
(2014) da Cadwell et al. (2018).
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.