An ciro daga littafin:
BIƊA DA TANADI A DUNIYAR INTANET
(Sana’o’i, Kasuwanci, Ƙwadago)
Na
Abu-Ubaida SANI
Abdulrahman ALIYU
Ɗora Liƙau Da Samfuran Hajoji a Kan Kafar Intanet Ɗin Dillali
Wani salon dillanci a duniyar intanet wanda
Hausawa suke cin gajiyarsa shi ne yaɗa liƙau da samfuran hajoji a kan
kafafen intanet. A wannan nau’in dillanci, dillali yakan kasance yana da kafar
intanet tasa ta kansa. A kan wannan kafar ne zai ɗora liƙau ɗin wata haja. Masu ziyartar kafar tasa suna iya latsa
liƙau ɗin domin ya kai su wurin da za su sayi
kayan. A duba misali cikin hoto na 4.12 da yake ƙasa:
Hoto Na 4.12: Liƙau Lulluɓe Cikin Hoto Domin Dillanci
Madogara:
An
ɗauko daga kafar Amsoshi (www.amsoshi.com).
Akwai tsarin da ake yi wanda zai ba su damar
kammala sayayyar ɗungurungum ɗinta a kan kafar intanet ɗin dillalin. Akwai kuma
tsarin da liƙau ɗin kai tsaye zai mayar da su kan ainihin
kafar intanet ɗin mai kayan ne. Ko ma yaya abin ya kasance, na’urorin za su
kundace rahoton cinikin da aka yi sakamakon biyowa ta liƙau ɗin. Yayin da aka kammala sayayyan wani kaya, to
dillali zai samu kasonsa na riba, wato la’ada.
Yaɗa Liƙau Da Samfuran Hajoji a Kafafen Sada
Zumunta
Hausawa waɗanda ba su da kafafen intanet ma
suna da damar shiga a dama da su a harkar dillancin duniyar intanet. Za su iya
hakan ne ta hanyar yaɗa liƙau ɗin a akawun-akawun
ɗinsu na kafafen sada zumunta. Wanda zai yi irin wannan dillanci, da farko zai
buɗe asusu da kamfanin da zai yi wa dillancin. Daga nan za a ba shi liƙau wanda ya keɓanta gare shi. Wannan liƙau ɗin ne zai riƙa yaɗawa a kafafen sada
zumunta.
Yayin da aka bi liƙau ɗin dillali aka sayi wani kaya ko aka yi rajista, to
za a keɓe masa la’adarsa. A irin wannan nau’in dillanci, dillali yana iya buƙatar ‘yan uwa da abokansa su taya shi yaɗa liƙau ɗin. Ma’ana dai, bai zama dole ya kasance a kan akawun
ɗinsa na sada zumunta ba, zai iya kasancewa a kan na kowa. Abu mai muhimmanci
kawai shi ne ya kasance liƙau ɗin nasa ne wanda aka ba
shi bayan ya buɗe asusu da kamfanin masu kaya.
Hausawa da yawa sun samu kuɗaɗe daga
dillancin da suka fito daga kamfanonin:
a. Chipper Cash
b. Kuda
c. Manhajar Abeg
d. PalmPay, da makamantansu[1]
[1] A. Sani (Keɓantacciyar Tattaunawa, Maris 6, 2023).
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.