An ciro daga littafin:
BIƊA DA TANADI A DUNIYAR INTANET
(Sana’o’i, Kasuwanci, Ƙwadago)
Na
Abu-Ubaida SANI
Abdulrahman ALIYU
Dillanci (Affiliate Marketing)
Dillanci yana ɗaya daga cikin daɗaɗɗun
hanyoyin kasuwancin Hausawa. A Ƙamusun Hausa Na Jami’ar
Bayero, an kawo ma’anar dillanci a matsayin “sana’ar da dillali ke yi.” Dillali
kuwa, an bayyana ma’anarsa a matsayin “mutumin da ke karɓar kayan mutane
don ya sayar a ba shi la’ada” (Sa’id et al., 2006 sh. 103).
M. S. Muhammad (2020 sh. 237) kuwa ya kawo
ma’anar dillanci da cewar: “Wata sana’a ce da maza da mata ke yi a
tsakaninsu, ana kiran mai wannan sana’a da Dillali in namiji ne, Dillaliya in
mace ce, akan yi dillanci a gida ko kasuwa.” Za a iya lura da cewa, ma’anar
tasa ba ta kauce wa wadda Sa’id et al (2006) suka bayar ba.
A taƙaice ke nan, dillanci
sana’a ce da ta shafi karɓar kaya da dillali ko dillaliya suke yi daga hannun
mai shi ko masu shi bisa yarjejeniyar ta musamman, tare da sayar da wannan kaya
da karɓar ladan aikinsu da ake kira la’ada. A bisa haka, dillalai suna
iya kasuwancinsu ko da ba su da jari. Nasarar kasuwancinsu ta dogara ne a kan
iya ciniki da hulɗa da jama’a da kuma sanin jama’a ɗin.
Dillancin da ake gudanarwa a kan intanet yana
kama da wanda ake gudanarwa a duniyar zahiri. Duk su biyun sun shafi yadda
dillali yake ƙoƙarin sayar da kayan da ya
karɓi dillanci domin mai kaya ya biya shi la’ada. Akwai fitattun hanyoyin
dillanci guda uku (3) a duniyar intanet. Sun kasance kamar haka:
1. Buɗe reshen kasuwanci
2. Ɗora liƙau da samfuran hajoji a kan kafar intanet ɗin dillali
3. Yaɗa liƙau da samfuran hajoji a
kafafen sada zumunta
Buɗe
Reshen Kasuwanci
Akwai manyan kamfanoni da suke ba da damar a
buɗe reshen kasuwanci a kansu. Hausawa suna iya amfani da wannan damar. Ɗaya daga cikin manyan kasuwannin hadahadar kuɗin intanet
ta duniya, Paxful, yana da wannan tsarin. Kai tsaye ya kira tsarin da
suna “dillanci.”[1] Shi kuwa wanda yake dillancin, an ba shi
suna “dillali.” Wani abin burgewa shi ne yadda aka fassara kafar Pxful zuwa
harshen Hausa. Hakan yana ƙara nuni da yadda Hausawa
suke rungumar hanyoyin neman kuɗi a kan intanet.
Hoto Na 4.11: Tsarin Dillanci a Kan Kamar
Paxful
Madogara: An ɗauko daga https://paxful.com/ha/buy-bitcoin-kiosk.
A hoto na 4.11 da yake sama, an ga yadda
Paxful suke bayar da damar a buɗe abin da ta kira “shago” a kan kafarta. Wato
zai zama tamkar wani ƙaramin shago da mai shi zai
riƙa samun kayayyakin daga ainihin uwar shagon,
wato Paxful. A taƙaice ke nan, zai yi dillanci daga asalin
babban kantin Paxful.[2]
Yayin da dillali ya buɗe reshen kasuwanci a
kan wata babbar kafa, to duk kuɗaɗen cinikin da ya yi za su tafi asusun ainihin
masu kafar ne. Shi kuma za a ba shi la’ada daga ciki. Yayin da aka dubi nazarci
lamarin, za a tarar da ya yi daidai da yadda a duniyar zahiri mutane suke buɗe ƙaramin shago sannan su dogara da masu manyan shaguna. A
irin wannan yanayi, mai ƙaramin shagon yakan ɗauko
kaya daga babban shago ba tare da yana da kuɗin biya ba. Bayan ya sayar, zai
mayar da uwar kuɗi da riba ga mai babban shagon, yayin da shi kuma zai cire
ribar da ya ɗora a sama.
[1] An fassara wannan kafa sukutum zuwa harshen
Hausa tun a shekarar 2021-2022. Yayin da aka duba fassarar da aka yi wa
shirinsu na “affiliate marketting” za a tarar an kira shi da “dillanci.”
[2] Fassara illahirin shafin zuwa Hausa na ƙara nuni da yadda Hausawa suke cikin wannan harkar dillanci a kan kafar.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.