An ciro daga littafin:
BIƊA DA TANADI A DUNIYAR INTANET
(Sana’o’i, Kasuwanci, Ƙwadago)
Na
Abu-Ubaida SANI
Abdulrahman ALIYU
Hadahadar Kuɗin Intanet
Kuɗin intanet (crypto currency) wani nau’in
kuɗi ne da ya samu a zamanance, wanda ba a ganin sa a dunyar zahiri sai dai a
cikin intanet.[1] Kuɗaɗen intanet nau’o’i na kuɗin baɗini
waɗanda hadahadarsu take wanzuwa a duniyar intanet. Buhari (2024 SL. 8) ya
bayyana shi a matsayin “kuɗi da ake amfani da su a cikin kwamfuta wanda za a
iya saye da saidawa da su a cikin hanya mai sauƙi.” Wani muhimmin abu game da su shi ne, ana iya sayen
kuɗin intanet ta amfani da kuɗin zahiri. Ana kuma iya sayen su ta amfani da
wani nau’in kuɗin intanet na daban.
Tun a shekarar 2022, ƙididigar Triple-A (2022 SL. 5) ta nuna cewa kashi goma da
ɗigo talatin da huɗu (10.34%) na ‘yan Nijeriya sun mallaki kuɗin intanet.
Binciken Statista (2024) ya nuna cewa, ya zuwa shekarar 2025, kimanin ‘yan
Nijeriya milayan biyu da dubu ɗari takwas da sittin (miliyan 25.86) ne za su
kasance cikin hadahadar kuɗaɗen intanet (SL. 9).
Kuɗin intanet na farko shi ne Bitcoin[2] wanda aka samar tun a shekarar 2008 (Reiff,
2024 SL. 32) sannan aka fara amfani da shi a shekarar 2009 (Batey, 2024 SL. 9).[3] Ya zuwa yau akwai nau’o’in kuɗaɗen intanet
daban-daban waɗanda a kullum suke ƙara yawa saboda sababbi da
ake samarwa. Pi yana ɗaya daga cikin waɗanda suka fi ƙaurin suna tsakanin Hausawa, inda har aka samu waƙoƙi[4] da maganganun malamai da masana
daban-daban game da shi. Bayan haka, akwai bidiyoyi masu tarin yawa dangane da ‘Yan
Pi Netwok.
Hadahadar kasuwar intanet ba ta rago ba ce.
Sana’a ce ta jajirtacce wanda ya san darajar lokaci kuma yake amfani da shi.
Sana’a ce ta mutanen da suke shirye su sadaukar da lokacinsu wurin bincike da
karance-karance, tare da bin diddigin sababbin sauye-sauyen zamani a-kai-a-kai.
An samu Hausawa da dama da suke bayani game
da lamuran da suka shafi kasuwancin kuɗin intanet. Yawanci sukan yi ne a
tashoshin kan intanet masu zaman kansu. Wasu kuwa sukan buɗe makarantu na
musamman a inda ake koyar da hadahadar kuɗaɗen intanet. Makarantun sukan
kasance ko dai a duniyar zahiri ko a kan intanet, ko kuma duka biyu.
Sunusi Danjuma Ali tasha yake da ita a kan
YouTube mai suna SunusiCryptoTV. Ya zuwa 10 ga watan Octobar shekarar
2024, kimanin mutane dubu ashirin da huɗu da ɗari ɗaya (24,100) ne suke bibiyar
wannan tashar tasa. A duba hoton da yake ƙasa:
Hoto Na 4.13: Tashar Koyar Da Hadahadar
Kuɗin Intanet a Kan YouTube
Madogara: https://www.youtube.com/@SunusiCryptoTV/videos
Ƙarin misalai na Hausawa da
suke koyarwa ko gabatar da laccoci na musamman game da kuɗin intanet sun haɗa
da:
a. Abdul Kabo[5]
b. Aminu Sirajo[6]
c. Injiniya Mujahid Muhammad Manga[7]
d. Umar Isma'il Muhammad[8]
e. Yusufuddee. A. Yusuf[9]
Makarantun Hausawa na koyar da hadahadar
kuɗaɗen intanet waɗanda suke azuzuwa a duniyar zahiri sun haɗa da:
a. Arewa Trading Academy[10]
b. HydarFX Academy Kano[11]
c. SMT Academy Kaduna[12]
Hoto Na 4.14: Wasu Ɗalibai a Ajin Koyon Hadahadar Kuɗin Intanet a Makarantar Arewa
Trading Academy
Madogara: https://www.tiktok.com/@yahaya_crypto
[1] Duk da haka, akan samu yunƙuri da shawarwarin a samar da waɗansu daga cikinsu a
duniyar zahiri. Idan aka yi haka, lallai sunansu da manufofinsu za su iya
sauyawa.
[2] Binciken Reiff (2024) ya nuna cewa, kafin
Bitcoin an yi yunƙurin samar da waɗansu nau’o’in kuɗin intanet
waɗanda ba su yi dogon zango ba. Sun haɗa da eCash (wanda David Chaum ya tsara
a cikin shekarar 1983), E-Gold (wanda Dr. Douglas Jackson da Barry Downey suka
samar a shekarar 1996), Bit Gold (wanda Nick Szabo ya samar), B-Money (wanda
wani da ya sakaya sunansa da Wei Dai ya samar a shekarar 1998), da kuma
Hashcash (wanda aka samar a shekarun 1990 zuwa 1999).
[3] Wanda ya samar da Bitcoin ya bayyana sunansa
a matsayin Satoshi Nakamoto. Sai dai har yanzu ba a san mai wannan sunan ba. Ba
a ma san mutum guda ne ko ƙungiya ce ba. Domin samun ƙarin bayani, a duba Batey (2024).
[4] https://www.amsoshi.com/2021/12/yan-pi-network.html
[5] Yana koyar da abubuwa daban-daban da suka
shafi kasuwancin duniyar intanet. Sunan Tasharsa a YouTube Abdulkabo Tech
(https://www.youtube.com/@Abdulkabo__tech).
[6] Sunan Tasharsa a YouTube Aminu Tech (https://www.youtube.com/@aminutech).
[7] Ya shahara wurin gabatar da laccoci a
shafinsa da yake kan kafar TikTok. An fi sanin sa da suna Abumaher.
[8] Shi ne yake da tashar Umar Top TV
YouTube (https://www.youtube.com/@umartoptv).
[9] Shi ne yake da tashar YDEEN a YouTube (https://www.youtube.com/@iam_ydeen/videos).
[10] Za a iya duba su a https://www.tiktok.com/@yahaya_crypto.
[11] Za a iya duba su a https://www.tiktok.com/@hydarfx.
[12] Kafar intanet ɗinsu ita ce: https://smtacademy.org/index.html.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.