Ticker

6/recent/ticker-posts

Sana'ar Baje Haja/Koli a Kafafen Intanet Na Haya

An ciro daga littafin:

BIƊA DA TANADI A DUNIYAR INTANET
(Sana’o’i, Kasuwanci, Ƙwadago)

Na

Abu-Ubaida SANI
Abdulrahman ALIYU

Bida Da Tanadi a Duniyar Intanet (Sana’o’i, Kasuwanci, Kwadago)
Manazartar Littafi: Sani, A-U. & Aliyu, A. (2026). Biɗa Da Tanadi a Duniyar Intanet (Sana'o'i, Kasuwanci, Ƙwadago). Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-978-62480-1-1. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.21361768

Tuntuɓa Domin Samun Littafi: 
Dr. Abu-Ubaida Sani: Imel - abuubaidasani5@gmail.com | WhatsApp - 08133529736
Dr. Abdulrahman Aliyu: WhatsApp - 08036954354

Baje Haja/Koli a Kafafen Intanet Na Haya

Buɗe kafar intanet da kuma ɗaukar ɗawainiyar kula da ita ba ƙaramin aiki ba ne. Abu ne da yake buƙatar kuɗi da lokaci. A bisa wannan dalili, ba kowane ƙaramin kasuwanci ba ne zai iya ɗaukar nauyin kafar intanet. A waɗansu lokutan kuma, hajar da za a tallata ba ta da yawa yadda har za a ware mata kafar intanet mai zaman kanta. A maimakon haka, Hausawa suna iya tallata ire-iren waɗannan hajoji a waɗansu kafafen intanet mallakin waɗansu mutane na daban. Yayin da aka sayar da kaya, masu kafar sukan ɗauki wani kamasho bisa yarjejeniyar kasuwancin da aka ƙulla.

Yin haka yakan zo da waɗansu alfanu da kuma naƙasu. Daga cikin alfanun akwai:

i.Ƙarancin kashe kuɗi, sakamakon babu buƙatar gudanar da kafa mai zaman kanta

ii.Gushewar fargabar samun kutse (daga masu kutsen kan intanet)

iii.Samun damar bayyana a injunan nema cikin sauƙi da sauri[1]

Naƙasu ko ƙalubalen da suke tattare da tsarin kuwa sun haɗa da:

i.Mai kasuwanci ba shi da cikakkiyar damar sarrafa kafar zuwa sigar da yake so.

ii.A kaikaice yana ƙara tallafa wa wata kafa ne domin ta ƙara ƙarfi da sanuwa a maimakon bunƙasa kansa.

Amazon yana bayar da damar buɗe akawun da ɗora littattafan sayarwa. Duk littafin da aka sayar, mai littafin zai samu kimanin kashi 70 na kuɗin yayin da Amazon za su ɗauki sauran a matsayin ladan amfani da kafarsu.[2] Ko a kafafen intanet na Hausa, WikiHausa suna da irin wannan tsarin. Ga misalin wasu littattafan da ake sayarwa a kan kafar:

Hoto Na 4.9: Wasu Litattafan Da Ake Sayarwa a Kan Kafar WikiHausa

Sana'ar Baje Haja/Koli a Kafafen Intanet Na Haya

Madogara: https://wikihausa.com.ng/littattafai/

4.2.3 Baje Haja/Koli a Kafafen Sada Zumunta

A kullum tasirin kafafen sada zumunta ƙaruwa yake yi a tsakanin al’ummun duniya. Wannan tasiri ya shafi Hausawa da ƙasar Hausa. Adadin Hausawa da suke amfani da kafafen sada zumunta yana ƙaruwa sosai. Su ma adadin kafafen sada zumuntan ƙaruwa suke yi kasancewar ana kan ƙirƙiro sababbi. Tuni suka kasance wata kasuwa ta musamman da ake baje haja a cikinta. Hausawa ma ba a bar su a baya ba wajen cin gajiyar wannan garaɓasa.

Akwai manyan hanyoyi guda uku da ake bi wajen tallata haja a kafafen sada zumunta. Su ne:

A. Sitatus (Status)

B.  Zauruka (Groups/Pages)

C.  Rabawa (Sharing)

Jagorar Delu Concept Services ta jaddada cewa:

Harkar internet tana taka muhimmiyar rawa wajen tafiyar da cinikayya ta kasuwanci, kuma mafi akasarin masu sayen kayanmu daga internet ne. Wani lokacin duk da mutane sun san muna yin aikin koyaushe, sai ka ga ba a saye kayan da wuri ba. Amma muna ɗorawa a internet sai ka ga nan take an saye kayan da munka yi. A.D. Aliyu (keɓantacciyar tattaunawa, 9 ga watan Satumba, 2024)

A tattaunawar da aka yi da Khadijah Muhammad (Khady Turban and More),[3] ta bayyana cewa: “Lallai intanet shi ne ginshiƙin kasuwanci a yanzu. Ta hanyar intanet ne kayan da kake sayarwa za su je wurin da kai kanka ba ka taɓa tsammanin za su je ba.” K. Muhammad (keɓantacciyar tattaunawa, 12 ga watan Satumba, 2024).

A. Sitatus (Status)

A kafafen sada zumunta, sitatus shi ne wani ɗan tsokaci ko hoto ko gajeren bidiyo da ake ɗorawa, wanda yake ɗaukar waɗansu awanni kafin ya share kansa daga akawun ɗin wanda ya ɗora shi (daidai da tsarin kafar), wanda kuma duk masu bibiyan akawun ɗin wanda ya ɗora shi za su gan shi, sai ko idan an saita wani tsari na musamman da yake hana su gani, wanda ya danganta da yadda kafar take. Da wuya a yau mutum ya duba dukkannin sitatus ɗin WhatsApp ko Facebook ɗinsa ba tare da ya ci karo da tallace-tallacen hajoji daga Hausawa ba. Hausawa masu son wani kaya da aka tallata, suna da damar yi wa mai tallen magana a keɓance domin yin ciniki.

B. Zauruka (Groups/Pages)

Kafafen sada zumunta irin su WhatsApp da Facebook suna ba da damar buɗe zauruka. Zaure wani tsari ne inda ake samun masu akawun daban-daban sun taru wuri ɗaya ta yadda za su iya karanta saƙonnin juna a lokaci ɗaya yayin da aka turo saƙonnin ta cikin zauren. Wannan ya samar da wata hanyar kasuwanci a tsakanin Hausawa. Yawaitar ire-iren waɗannan zaurukan suna ƙara nuni da yadda Hausawa suke rungumar kasuwancin duniyar intanet. A duba misali a hoton da yake ƙasa:

Hoto Na 4.10: Misalin Zauren Kasuwanci a Kafar WhatsApp

Sana'ar Baje Haja/Koli a Kafafen Intanet Na Haya

Madogara: Zauren Kasuwancin GIADE Trends Collections a Kafar WhatsApp

Yayin da aka nazarci hoto na 4.10 da yake sama, za a lura da cewa yana da mambobi da suka kai ɗari shida da ashirin da takwas (628). Duk wata haja da aka turo ta cikin zauren, ɗaukacin mambobin za su gani. Masu so suna iya tuntuɓar waɗanda suka turo a keɓance domin ƙulla ciniki.

C. Rabawa (Sharing)

Sau da dama masu kasuwanci sukan tura saƙonnin tallace-tallace ga abokansu a kafafen sada zumunta. Daga nan kuma sai su nemi abokan nasu su ma su tura wa abokansu. A haka tallar wata haja za ta yaɗu zuwa akawun ɗin mutane masu yawa. A irin wannan talla, yawanci akan sanya bayanan tuntuɓar mai sayar da kayan (misali lambar waya ko adireshi). Wannan ma wata hanya ce ta tallata haja a kafafen sada zumunta.




[1] Hajojin da aka ɗora a manyan kafafen intanet su ne suke kan gaba wajen samun damar bayyana a injunan nema cikin sauƙi. Sababbin kafafen intanet suna buƙatar a yi musu ayyuka na musamman kafin su iya gogayya da waɗanda suka riga suka yi musu nisa.

[2] A cikin shekarun 2023 da 2024, Hausawa sun mayar da hankali sosai kan wannan. Har an samu waɗanda suka gudanar da laccoci game da yadda ake samun kuɗi a Amazon.

[3] Tana sayar da sutura da kayan kwalliya.

Post a Comment

0 Comments