DA AKA GABATAR A KWALEJIN HARSHEN LARABCI DA NA ADDININ MUSULUNCI SHABAB DA KE UNGUWAR DOSA KADUNA, 25 AFRILU, 2014
SAƁALIKITA MIJIN HAJIYA (SUNƁULALLEN
UBA): TSOKACI A KAN ƊABI’UN WASU MAZAJE GAME DA
HARKAR GIDAJENSU
DAGA:
MU’AZU
SA’ADU KUDAN
JAMI’AR
JIHAR JIGAWA KAFIN HAUSA
07030803404
SHIMFIƊA
WANE NE
SAƁALIKITA?
Saɓalikita, na nufin sunɓulallen mutum, wanda bai
iya ƙullawa kansa komai, ko da shawara ce, bai iya yankewa. Watau ba
shi da ra’ayin kansa. Rayuwarsa ana kiranta da saɓulanci. Domin haka ne ake ganin duk wanda bai iya ɗaura wando a daidai ba, shi
ake kira da saɓalikita. Wannan yasa ake kiran sakin wando ƙasa-ƙasa ko saɓule wando ƙasan ɗuwawu da samari ke yi ake
cewa saɓulanci.
Haka kuma a kan kira rago, ko matsoraci da sunɓulalle. Macen da ba ta iya ɗaura zani ba, ko iya girki ba, akan ce ma ta sunɓulalliya. Ana jam’in su
kuma sunɓulallu.
MIJI:
Miji na
nufin mutum cikakke mai aure, watau magidanci. Wannan zai iya yiwuwa mace ɗaya, ko biyu, ko uku, ko huɗu. Mutum bai zama cikakken
miji har, sai ya zama jarumi, kuma tsayayye wanda ya tsare dukkan buƙatu da larurorin matarsa da na ‘ya’yansa. Dole ne ya kasance
bai da tsoro ko shakka, ba ya karaya ko nuna kasawa a dukkan al’amurran rayuwa.
HAJIYA:
Hajiya,
na nufin matar da ta tafi makka aikin hajji, amma akan kira matar mutum wadda
yake aure da hakan. Wannan suna, ana amfani da shi ne a matsayin kinaya, don
a ɓoye
sunanta tare da girmamawa. Domin ko ba ta je makka ba (Hajji) , akan kirata da
hakan. A zamanin da a kan ce mijin tace, duk dai ana sakaya sunan matar ne.
MATSAYIN
UBA:
Bisa
rayuwa ta haƙiƙa, dukkan magidancin da ya haihu, to ya zama uba. Bisa wannan
dalili yasa dole ya ɗauki wani nauyi wanda al’ada da shari’a suka ɗora masa. Watau na kula da
‘ya’yansa manya da ƙanana. Matuƙar aka ce uba ya kasa tsare haƙƙoƙin iyalinsa, wanda ya haɗa ne tun daga matarsa, watau uwar ‘ya’yansa da kuma su kansu
‘ya’yan. Matuƙar aka kuskure uba ya gaza sauke wannan nauyi, har ya bar wa wani
balle a ce matarsa. Tabbas ya zama sunɓulallen uba.
GABATARWA.
Da Sunan
Allah Mai rahama Mai jinƙa, Mai kowa, Mai komai, Mai
aikata abin da Ya so, ga wanda Ya so, a yadda Ya so, a sadda Ya so, kuma a inda
Ya so, ko ana so, ko ba a so, dole bayi su so. Tsira da amincin Allah su
tabbata ga shugaban halittu Annabi Muhammadu, da Alayensa, da Sahabbansa, da
sauran mabiyansa gaba ɗaya.
Wannan muƙala, za ta ɗan taɓo, ko tsakuro wasu daga cikin ɗabi’un wasu mazajen aure. Waɗanda Bahaushe ke ƙyama gaba ɗaya. Idan aka dubesu ta
mahanga al’ada, sun saɓawa matsayin da ake so cikakken magidanci ya kai. Haka kuma in aka
dubesu ta mahangar addinin Musulunci, a nan ma, sun saɓa wa shari’ar Musulunci. A
irin yadda ake so magidanci ya jagoranci al’amuran gida. Bayan haka kuma, ko a
hankalce abin ya saɓa wa lafiyayyen hankali. Wannan muƙala, na
nufin ta fito da wasu daga cikin waɗannan da kan sanya magidanci ya zama mijin Hajiya. Bayan wannan,
za a kawo illoli da suke biyo bayan hakan. Kasancewar wannan ɗabi’a, tsohuwar ɗabi’a ce, ta zama “Gyare
tsohon nama, yaro in baka ci ba, tsohonka ya ci”. Wannan ya sanya
harkar mjin Hajiya ta yi naso har a adabin Bahaushe na baka da rubutacce. Duk
da haka, wannan tasiri da ta yi bai hana Bahaushe ƙyamar mijin Hajiya ba.
Wannan
dalili ne, yasa na kira muƙalar da sunan “Saɓalikita Mijin Hajiya. Kuma Sunɓulallen Uba”. Bayan
haka, wannan muƙalar riga ce ba wuya. Duk wanda ya huda yasa, to ya zama mijin
Hajiya.
HATTARA
DAI MAGIDANTA!
Ina kira
ga dukkan magidanci, watau wanda yake da aure. Da cewa, ya yi hattara da
al’amarin mace, saboda al’amarin mace, yana da wuya. Haka kuma mace sai Allah,
Wanda Shi Ya halicce ta. Bahaushe kan yi ma mace kirari kamar haka: “Mace
mai sa ka ci rance, ta cinye ta mance, tun ba ka biya rancen ba”. Bayan
wannan kuma, yakan ce: “Mata na inna dangin shaiɗan, in baku ba gida, in kun
yi yawa gida ya ɓaci”. Haka kuma
Bahaushe ya ce, ba a baiwa abubuwa uku amana, su ne mace, da kogi, da doki.
Dalili kuwa shi ne, mace ba ta da tabbas komai daɗewarku da ita, kuma ko me ka yi mata, wata rana sai ta butsare ta
ce me ka taɓa yi min?
Haka shi ma kogi, kana iya wuce shi lafiya lau, amma kafin ka dawo, sai ka
tarar ya cika, baƙon ruwa (Kwazari) ya zo, ka kasa wucewa. Game da doki shi ma,
komai ɗadewarku
da shi, haka kawai wata rana, sai ya abauce maka ya ƙi sarrafuwa, dole ka ƙyale shi.
Ya kai
magidanci, waɗannan bayanai a sarari suke, kuma a bayyane. Don haka, ina kira
gare ka da ni kaina da sauran magidanta da cewa, hattara dai dangin warki.
Da farko,
a fahimce ni, kar a yi min bahaguwar fahimta. Ba wai nace kar magidanci
ya ɗauki
shawarar matarsa ba ne, a’a, abin da nake so in ce, shi ne, ko da mace ta ba ka
shawara, to ka tsaya ka duba ta sosai. Ka yi ma ta dubi irin na sayen goron
tsohuwa, ka juya, ka ƙara juyawa, sannan ka
aiwatar. Idan kuwa ka ga matsala a ciki, to ka watsar. Bahaushe ya ce, shawarar
mace guda uku ne, ba a ƙin ɗauka: -
• In tace tsaya ka ci aninci, to tsaya.
• Ko tace zo ka yi wanka.
• Kai yaro makaranta, to ka kai shi.
Dalili
kuwa, a mafi yawan lokuta daga ɗaukar shawararsu ake faɗawa cikin tarkon zama mijin Hajiya.
Bugu
da ƙari, wannan haɗarin bai ƙyale duk wani namiji mai
aure ba. Domin kamar yadda Bahaushe ya rarrabasu, kowanne an bashi suna
daban-daban kamar haka: -
• Mai tsayuwar gauraka, ko mai langa (Mai mace ɗaya).
• Mai ƙafar kaza (Mai mata biyu).
• Mai murhu (Mai mata uku).
• Mai ƙafar doki (Mai mata huɗu).
Dukkan waɗannan, ma’aurata ba wanda
ya tsira daga faɗawa, ko zama mijin Hajiya. A wani lokaci mai mace ɗaya kan zama mijin Hajiya,
amma mata biyu kan fi zama mijin Hajiya. A dalilin karkata da yayi wuri ɗaya, ko uwar gida, ko kuma
ita amarya da tazo daga baya. A kan rinƙa juya shi kamar ƙosai a man gyaɗa. Wani mai mata ukun, shi ma akan same shi a cikin irin hakan. A
wani lokaci uwar gida ke jan ragamar gida, ko kwarin tsakiya, ko amarya. Haka
shi ma mai mata huɗu, akan samu wani ya faɗa cikin wannan hali. A wani lokaci uwargida, ko kwari, ko kwarin
tsakiya ko amarya ita ke mulki.
HAƊARINSA A SHARI’AR MUSULUNCI.
Akwai
babban haɗari,
magidanci ya zama mijin Hajiya a shari’ar Musulunci. Domin a shari’a, ana ƙyamar magidanci ya saki nauyin ko ya wulaƙantar da haƙƙin da Allah Ya ɗora masa. A Ƙur’ani, Allah Ya ce: “Arrijalu Ƙawwamuna Alan Nisa’i”. Lallai
maza na gaba da mata, don haka su ne shugabanni. Kamar yadda wani hadisi ya
nuna Manzon Allah (S. A. W) ya ce: “Dukkan al’ummar da suka baiwa
mace shugabanci, ba za su taɓa cin nasara ba”. A nan,
malamai suka ce al’umma na farawa daga gida ne, saboda lallai ne duk wanda ya
zama mijin Hajiya, ba zai ci nasara ba.
Bayan
haka, a harkokin addini gaba ɗaya, namiji shi aka sani da jagoranci. Domin haka, duk wanda ya
sanya tsarin ta hanyar bai wa mace jagoranci, to ya saɓa. Haƙƙin ciyarwa da shayarwa, da tufatarwa, da mahallin zama, duk yana
kan maigida ne, ko da mace na da dukiya, ba a ɗora ciyarwa a kanta ba, sai
dai shi miji ya ciyar da ita. Banda wannan, saki da sadaki, da izinin fita, duk
suna hannun miji, wajibi ne ya tsare su. Wanda duk ya kasa, to ya zama mijin
Hajiya.
Akwai
inda darajar ta ƙara bayyana a sarari, kamar
wajen bashi kaso biyu in aka zo rabon gado. Haka kuma inda aka ce aljannar mace
tana ƙarƙashin dugadugin mijinta. Sannan ko azumin nafila za ta yi, sai ta
sanar da shi, ko ta nemi izini. Haka kuma ga limanci da bayar da aure, zuwa
jana’iza da sauransu, dukkansu namiji ne ake so ya jagoranci harkar.
To don
Allah, ya kai bawan Allah, wace irin wauta ce za ta saka ka yi watsi da irin waɗannan darajoji da Allah Ya
baka ka bar wa mace? Haƙiƙa mijin hajiya ya yi watsi da darajojin nan, saboda ya baiwa mace
jagorancin gidansa. Wannan, ba ƙaramin haɗari ba ne, saboda ba zai
tsaya a kansa ba shi kaɗai, sai ya shafi sauran al’umma kamar wata waƙa da Alhaji Aƙilu Aliyu ya yi wa Ɗandaudu, inda yake cewa: -
“Da falle
biyu ce daraja tasa,
Ya watsar
ya riƙe falle ɗai.
Ga wani
ya bar gaba domin baya,
Ya ɓatawa mazaje suna.”
Duk da
yake da Ɗandaudu ake yin magana a waɗannan baitotci. To kuma ya yi daidai da mijin hajiya.
YA WUCE
WAI, BAI ZAN WAIWAI BA.
Tabbas,
harkar mijin ta ce, ko mijin hajiya, wani al’amari ne daɗaɗɗe, wanda ba yanzu aka fara
ba. Ana iya cewa wannan al’amari an gaje shi ne tun iyaye da kakanni. Bisa wani
nazarin adabin Bahaushe nabaka, da rubutacce da aka yi, yana iya zama hujja ko
madogara akan haka.
Idan muka
dubi adabin bakan Bahaushe, akwai wasu daga cikin rassansa da aka samu jirwayen
mijin tace. Misali, wasu almarori guda uku sanannu a Ƙasar Hausa, waɗanda suka tabbatar da samuwar ko faruwar wannan al’amari. Kamar
almarar mai ɗebo tsamiya.
“Wani
manomi ne zai tafi zuwa gona, sai matarsa tace in zaka dawo ka ɗebo mana tsamiya, shi kuma
sai ya ce ba zai ɗebo ba. Ita kuma sai ta ce to ka dawo, zuwa can sai ya ce to in
na ɗebo ba zan ɓare ba. ”
Almara ta
biyu kuwa, ita ce, almarar malami.
“Wani
malami ne yana bayar da karatu a azure ga almajirai da yawa. Zuwa can sai
matarsa ta aiko a ce ana kira a cikin gida. Ko da aka faɗa masa, sai ya ce, ku je ku
ce ba zan zo ba. Bayan yaran sun tafi, jimawa kaɗan, sai malam ya ce bari mu
gani in bi yaran nan cikin gida, ko sun faɗa cewa ban zuwa?
Almara ta
uku kuwa:
“Wani
sarki ne yana zaune a fada ana fadanci, sai ga jakadiya ta zo kusa da kunnensa
ta ce uwar gida na kira. Maimakon sarki ya yi Magana, sai kawai ya girgiza kai
da nufin cewa ba za a je ba. Jakadiya ta koma cikin gida ta faɗa, ba a daɗe ba, sai jakadiya ta ƙara dawowa. Ai sarki na ganinta, sai ya yi wuf ya tashi, kamar zai
buge ta, ita kuma da ta ga haka, sai ta ruga da gudu. Sarki ya bi ta kamar ya
yi fushi, ashe ya tafi wurin kiran nan na farko ne da matar ta aiko, amma sai
ya yi barazanar zai bugi jakadiya. ”
Dangane
da karin magana, da kirari, da maganar azanci, ana iya cewa dukkansu an samu
jirwayen mijin tace a cikinsu. Misali kamar haka: -
• Mijin tace.
• Mijin Hajiya Mijin banza/in ba kuɗi ba aiki.
• Bita zaizai.
• Sauyar sala.
• Santilaɓi.
• Soloɓiyo.
• Je ka ka dawo.
• Gaso rogo a baka ɓawo.
• Za ta unguwa.
• Ta more miji.
• Gwamma talla da biko.
• Bautar mata kowa da irin tasa.
• Ana tsoronka kana tsoron hajiya.
• Bari in tambayota.
Bayan
wannan kuma, in muka kalli rubutaccen adabi, ko muce adabin zamani. Akwai
littattafan zube, da na wasan kwaikwayo, da aka samu jirwayen tace a cikinsu.
Kamar a magana jari ce, littafi na uku a labarin sususu da shashasha. Inda
matansu suka sanya suka zama abin dariya a gari. Matar ɗaya daga cikinsu watau
sususu, ta ce yace ba shi da lafiya, ya kuma yarda, ta ce ai ya mutu, ya kuma
yarda, da ya mutun. Shi kuma ɗayan, watau shashasha matarsa tasa shi ya yi yawo tsirara, wai ta
saƙa masa riga da wani zare da ba kowa ke iya ganinsa ba, shi kuma ya
yarda. Haka kuma a littafin Ruwan Bagaja, an samu jirwayen mijin tace. A inda
matar Malam Zurƙe ta dinga zuga shi har sai da ya tashi suka tafi daji don yin faɗa da wami mutum (Alhaji
Imam). “Ita kuwa, ta yi ta turara mai gidanta da ƙarairayi har sai da ya tashi biɗi kulki ya nufi daji tare da ita”….
Haka
kuma, a wani littafin wasan kwaikwayo mai suna Uwar Gulma, shi ma akwai nason
mijin hajiya. Kamar inda uwar gulma dillaliya take cewa: “Ai ku kuke ƙyale maza suke rena ku, ni namiji in ya yi min, ai ma haɗu a gado”….
DALILAN
DA KAN SANYA HAKA.
Bisa lura
da kuma nazarin rayuwa, tare da sauye-sauye da akan samu. Tabbas akwai wasu
dalilan da kan sanya wasu mazaje suke zama mijin tace, ko mijin hajiya, kamar
haka: -
• Karayar zuci.
• Son abin duniya
• Matsanancin son mace.
• Baƙuwar Al’ada.
• Sihiri ko tsafi.
• Kissa da kisisina.
• Karayar arziƙi.
• Auren Gadara.
• KARAYAR ZUCI:
Karayar
zuci, na nufin mutum ya yanke ƙauna ga cin nasara, ko cire
rai ga cimma burin rayuwa. A wata fuskar kuma, ana iya cewa gazawa, ko kasawa a
gudanar da wasu al’amura. Sannan kuma ana iya cewa tsoro, ko razana. Ba shakka,
karayar zuci tafi karayar ƙafa, kamar yadda Bahaushe
ke cewa. Domin idan ka karye a ƙafa, ana iya ɗora ka ka warke. Shi kuma
karayar zuci in aka karye ba ta ɗoruwa. Kusan ana iya cewa duk wanda ya samu karayar zuci, to ya
zama “Talasuru” mai matacciyar zuciya, ko kuma raƙumi da
akala, sai inda aka juya shi. Ma’ana ba shi da wani ra’ayin kansa. Duk wanda ya
faɗa wannan
hatsari, to babu makwa zai zama mijin hajiya.
• SON ABIN DUNIYA:
Son abin
duniya na nufin kwaɗayi na dukiya, ko wasu kayayyaki, ko kadara da sauransu. Kwaɗayi kan sanya wasu mazaje
su faɗa haɗarin zama mijin hajiya.
Domin akwai wasu mazajen da sukan aure mace saboda dukiyarta, ko dukiyar
iyayenta. Akan kira wannan aure da cewa auren jari, ko auren hange-hange. A
wani lokacin akan samu wasu mazajen da sukan zama tuwon tushe, watau ba su da
kataɓus akan
harkar gidansu. Wannan na faruwa ne a dalilin gudun kar ya saɓawa matar nan ko don
dukiyarta, ko kuma abin da take yi masa na hidimar gida ta daina. Haka kuma
idan iyayenta ke da dukiyar, kar su daina taimaka masa.
Bugu
da ƙari, irin wannan hali ne ke sanya mai gida ya zama kamar baran
gida. Domin a wani lokaci, matar kan aike shi kasuwa, ko wasu wurare, ko talla.
A wasu gidajen ba ɗan aike mijin hajiya ke zama ba, abin ya kan kai har tana daka
masa tsawa. Bayan wannan, hatta ‘ya’yan cikinsa kan raina shi, sannan kuma ba
shi da iko a kansu. Ko da aure ‘ya’yansa mata za su yi, dole sai wanda uwarsu
take so za su aura. In ba haka ba, ba za a yi auren ba. Wani mijin hajiyan
hatta cefanen gida ita ke yi, ko kuma ka iske tana yi masa ɗinkin sallah.
• MATSANANCIN SON MACE:
Wasu
mazajen, tsabar soyayye da suke nunawa mace ke sawa su zama mijin hajiya. Kamar
yadda Bahaushe kan ce: “So hana ganin laifi”. Bisa matsancin so da miji ke da
shi a kan matarsa. A wani lokaci, bai iya cewa komai. Irin wannan, shi ke
haifar da kishin saraku, watau kishi a tsakanin uwar miji da matar ɗa, ko ya haifar da kishin
sauri, watau kishi a tsakanin matar ƙani da matar wa (yaya).
Haka kuma, shi ke haifar da mummunan kishi a tsakanin matan mutum ɗaya (Kishiyoyi). Domin ya
kan sakar wa mowa, watau matar so ragamar gudanar da harkar gida, wanda zai sa
sauran matan su zama ‘yan bora (waɗanda ba a damu da su ba). Duk matsannacin son mace ke sanya haka.
Bugu da ƙari, ko an nuna masa haka, sai ya rufe idonsa ya ƙi karɓar gyaran.
• BAƘUWAR AL’ADA:
Haƙiƙa, hulɗa da baƙin al’ummu daga wasu sassan duniya. Baƙaƙe da farare, da Bahaushe ya yi, to ya haifar da tasiri mai yawa.
Waɗannan
al’ummu, sun bar al’adunsu Bahaushe ya ɗauki wasu, haka su ma sun ɗauki wasu al’adun Bahaushe. A al’adar al’ummar ba sa saɓawa matarsu, sai abin da
take so, za ta yi. Misali, Turawa sun kawo ilmin boko, wanda Bahaushe ya
rungume shi. Don haka ya yi tasiri matuƙa a kan wasu mazaje.
Da farko,
wasu mazaje ‘yan boko ba sa wuce mace ɗaya, sannan kuma sun sakar ma ta ragamar gudanar da komai na gida,
ba duka ɗan boko ke faɗa a ji a gidansa ba, musamman idan matar ta yi ilmin boko mai
yawa, ko a ce ta fi shi yawan karatu. Ko kuma tana kan wani babban matsayi, ko
muƙami a wurin aikin ta (ofis). Bayan wannan kuma, wani ɗan bokon, matarsa ko izinin
zuwa unguwa ba ta tambayarsa, wannan kuma bai sa ya damu ba, kuma bai iya yi ma
ta magana. A tunani irin na Bature, shi ne, ai tana da ‘yanci, saboda haka kar
ya takura ta. Wannan kuwa, ai baƙuwar al’ada ce don ba
al’adar mu ba ce. Daga irin haka, ana iya faɗawa ramin mijin hajiya.
• SIHIRI KO TSAFI:
Kalmar
sihiri, baƙuwar kalma ce daga harshen Larabci “Sihir”. Kalmar asali ta
Bahaushe ita ce tsafi. Dukkan wasu kalmomi ko sunaye da akan yi amfani da su,
kamar makaru, ko sammu, ko jifa, ko magani, ko tambaya, ko asiri da sauransu,
ana yi ne don sakaya sunan tsafi. Haƙiƙa wasu mata kan yi amfani da tsafe-tsafe da dama, ta fuskoki masu
yawa, saboda su mallaki mazajensu. Akwai matan da kan tafi wurin bokaye, da
malaman tsibbu, da ‘yan bori don a haɗa masu abin da zai sanya su mallaki mazajensu. To daman an ce:
“Tsafi gaskiyar mai shi”. Waɗannan ƙulumboto da mata kan yi, ko
suke sawa a haɗa masu don mallake mazajensu, suna da yawa. Kaɗan daga ciki sun haɗa da: Miɗis, da Bi-ta-zaizai, da
Bi-ni kamar kare, da Kar-ka- tsallaka, da bar shi kurum da sauransu.
Mazaje da
yawa kan zama mijin hajiya a sakamakon tsafin da matansu suka yi masu. A inda
sukan zama raƙumi da akala, ana juya su kamar maburgin miya a hannun mata a irin
wannan ne akan ce, ai wane matarsa ta shanye shi, ko a ce ta wanke masa hannu a
ka, ko ta kafe shi da sauransu.
• KISSA DA KISISINA:
Wannan,
na nufin halaye ne, ko dabaru waɗanda wasu mata kan yi, saboda su mallake mazajensu. Wasu mata sun
iya nuna soyayya da kyautatawa ta ƙarya ko na yaudara. Suna
iya zama na magana ko wajen biyayya, ko nuna ƙaunar danginsa, ko ‘ya’yansa, amma na ganin ido. Idan aka ce mace
tana da kissa, ko kisisina, ko hila, to ta kan mallake mijinta gaba ɗaya. Bisa wannan dalili,
sai magidanci ya zama bai son kowa, kuma ba ya ɗaukar maganar kowa sai na
matar. Wasu matan su kan shiga tsakanin miji da iyayensa (Surukai) , ko
tsakaninsa da danginsa, ko abokai, ko maƙwabta. Daga nan ya zama
mijin hajiya.
• KARAYAR ARZIƘI:
Rashi,
ko ƙarancin abin hannu, kan haifar da magidanci ya zama mijin hajiya a
mafi yawan lokuta. Ko da yake an fi samun attajirai, ko masu dukiya waɗanda suka karye, watau arziƙin su ya karye. Sau da yawa, wasu harkokin da sukan gudanar a da,
sais u gagare shu a daloilin rashi. Sakamakon irin wannan halin da suka tsinci
kansu a ciki sai al’amura su koma hannun matar. Haƙiƙa irin haka, kan sa mai gida ya zama mijin hajiya. A wani lokaci
matar kan koma miji, shi kuma ya koma matar.
• AUREN GADARA:
Auren
dadara na nufin mutum ya yi alwashi sai ya auri wata mace mai mnatsayi iri
kaza, alhali kuwa yasan cewa tafi ƙarfinsa, ko kuma ya auri
‘yar gidan su wane mai babban matsayi bayan kuma Bahaushe ya ce: “Ko
yaro ya san matar aurensa”. Ko “Linzami ya fi ƙarfin bakin kaza”. Tabbas
wasu mazan sukan yi irin wannan auren ne, don kawai su rinƙa yin gadara da cewar ai mata iri kaza yake aure, ko ‘yar gidan
wane kaza yake aure. Wasu kuma don abokinsu ya auri wata mata daga wata
zuriyya, to shi ma sai ya dage sai ya aura, don ya rinƙa yin alfahari da hakan.
Bugu
da ƙari, a irin wannan halin, wasu mazan sukan daure da duk irin wulaƙanci, tare da wahalar da su da matar ke yi, ba sa nunawa, balle su
yi magana. Domin Bahaushe ya ce: “Sa-kai ya fi bauta ciwo”. Mafi
yawan mazajen da suka shiga irin wannan yanayi, suka faɗa ramin zama mijin hajiya
cikin sauƙi.
BAUTAR
MATA KOWA DA IRIN TASA:
Babu
shakka, ana iya cewa kowane namiji da irin hidima, ko ɗawainiyar da yake yi wa
matarsa to, amma shi mijin hajiya, nashi matsayin ya zarce hankali, idan muka
dubi al’amarin zaman aure, ana iya karkasa shi gidaje, ko mazaje, ko magidanta
zuwa kashi huɗu, kamar haka: -
• Gidan Ilmi (Malamai na Addini da na zamani).
• Gidan Sarauta (Sarki, ko Shugaba, ko Jagora).
• Gidan Wadata (Mai kuɗi, ko Ɗan Kasuwa).
• Gidan Talauci (Talaka, ko Matalauci)
• Gidan Ilmi:
Gidan
ilmi, na nufin gidan malamai, inda ake samun wasu malamai a gidajensu, sun faɗa cikin matsalar tace. Ko
da yake dalilan da kan sanya wasu malamai su zama mazan tace, kan bambanta.
Wasu malaman a dalilin bin shari’a da dokokinta ke sawa su zama haka.
Sharia’r
Musulunci, ta sharɗanta a tausaya wa mace, kuma a kyautata ma ta. A sanadiyyar haka,
sai matansu su fi ƙarfinsu, su riƙa juya su. Wasu malaman kuma, a saboda rashin lokaci na gudanar da
wasu harkokin gida, sai su sakar wa matansu. To daga haka, sai mazan su zama
mazan tace, wasu kuma a dalilin ganin mutuncin iyayen matar, watau surukai.
Da farko,
ba za yi ma ta magana ba, ita kuma sai ta yi amfani da wannan damar, ta rinƙa juya mijin. Don haka, waɗannan na daga kaɗan daga cikin dalilan da kan sanya a samu mijin tace a cikin
malamai, duk da yake ga ilmi.
• Gidan Sarauta:
Gidan
sarauta, na nufin gidan sarki, ko wani shugaba a kowane matsayi. Tabbas, ana
samun mijin tace a cikin wasu daga sarakuna, da shugabanni na da, da na zamani.
A mafi yawan lokuta, akan sami wani sarki, ko shugaba matarsa na juya shi
kamar ƙaramin yaro. Komai mulkinsa, ko ɗamararsa, bai hana mace ta
juya shi kamar sitiyarin mota. Misali:
“Wani
babban soja ya dawo gida, har an buɗe masu get (ƙofa) , sai ya ce madam na
ciki?” Mai gadi ya ce: “Tana ciki”. Sai ya ce wa direba: “Yi ribas mu
koma”. Za a iya samun wani sarki
ko shugaba ana matuƙar tsoronsa a waje, ko a fada da kuma ofis. Idan kuma ya koma
gida, shi kuma yana tsoron hajiya shi ne ake cewa: “Ana tsoronka kana tsoron
Hajiya”.
• Gidan Wadata:
Gidan
wadata, na nufin gidan wasu masu kuɗi, masu hannu da shuni. Akwai mawadata masu yawa, da suka zama
mazajen hajiya. Ko da yake akwai dalilai da suke jawo hakan. Wasu masu kuɗin sukan sakar wa matansu
ragamar gudanar da harkokin gida. Abin kamar wasa, sai ya zama ya wuce ƙa’ida, wanda daga nan, sai mai gida ya zama mijin hajiya. Wasu
suna ganin isa ce, ko ƙauna, ko wayewa ke sa masu
kuɗi na
barin harkokin gidansu zuwa ga matansu. Akwai masu ganin harkokin neman dukiya
ko tafiye-tafiye, ba zai bar su har su lura da wasu abubuwa ba. A ƙarshe, sai su bar wa matansu, su kuma su yi ta damawa, da mai
tanka masu, ko a dangi, ko a abokai, balle kishiyoyi idan ma har akwai su.
• Gidan Talauci:
Gidan
talauci, na nufin talakawa. Akwai talakawa da yawa da suke zaman mazan hajiya.
Su ma talakawan da akwai dalilai da suke jawo hakan. Matuƙar magidanci ya tsare nauyin da ke kansa, abu ne mawuyaci ya zama
mijin Hajiya. Idan kuma ya zama talasuru ya gaza sauke nauyin da ke kansa, haƙiƙa zai iya zama mijin hajiya. Ko da yake akwai waɗanda kan shiga wannan hali
bisa dole. Domin babu, babu abin da ba ta sawa. Wasu bisa dole ‘ya’yansu kan yi
talla, saboda ko na cefane ba su da halin bayarwa, ita matar ce ke ƙuƙƙulawa ta san yadda za ta yi. Domin haka, sai ragamar gudanar da
harakokin gidan ya koma hannun matar. Daga nan sai ‘ya’yansu su fara gagararsa,
ba sa saurarornsa balle su yi shawara da shi.
GWANO BA
YA JIN WARIN JIKINSA:
Wani abin
mamaki, da ban haushi, da takaici, game da al’amarin mijin tace, shi ne, ko da
iyaye, ko dangi, ko abokai sun gane irin halin da yake ciki. Ko da sun yi ƙoƙari su nuna masa, ko su ƙwato masa haƙƙi, sai ya bijire ya ƙi sauraronsu. Kai in har
aka matsa masa, sai ya ce: “Kar ku dame ni” “Ai bautar mata kowa da irin tasa”,
ko ya ce: “Gwamma talla da biko”, da dai sauran maganganu masu nuna cewa ba
ruwan ko da da shi.
Wani
mijin hajiya ma ko ya ɗauki shawarar da aka bashi. Da zarar ya koma gida ya faɗa ma ta, sai ya fasa
ya ƙi ɗaukar shawarar.
ILLOLIN
DA KAN BIYO BAYA:
Sakamakon
faruwar waɗancan
dalilai, da suka sanya wasu mazajen suka zama mazan hajiya. Babu shaka, akan
samu wasu illoli da sukan biyo baya. Waɗannan illoli kuwa, sukan cutar da al’umma gaba ɗaya. Kaɗan daga cikinsu sun haɗa da:
• Zubewar mutunci.
• Gurɓacewar tarbiyya.
• Ɓata zumunta.
• Taɓarɓarewar al’umma.
• Zubewar Mutunci:
Babu
shakka, matuƙar aka ce mutum ya zama mijin tace, mutuncinsa kan zube gaba ɗaya. Dalili kuwa, duk mijin
tace ba ya yin magana ɗaya. Domin in ya yi magana ko alƙawari,
sai hajiya ta yarda, in ba ta yarda ba, sai ya fasa. Bisa wannan dalili, sai ya
zamanto ba ya magana ta tabbata. A ƙarshe, al’umma za su ɗauke shi ba shi da dattaku,
to a nan mutunci ya zube. Kamar yadda Alhaji Aƙilu Aliyu
yake cewa:
“Malam
nemi ɗiyar
Dattawa,
Sanda
kake riya neman aure.
Ba mai
gemu ko saje ba,
Ba mai
mota ko babur ba.
Ba mai
faffaɗar riga
ba,
Ba mai
gogaggen wando ba,
mai
magana ka ji tamkar ƙyaure.
In ya ce
i, ba ya a’a,
Wanda
yake da kula da shari’a’,
Wanda a
zuci yana da ƙana’a,
Ba nauyi
ba kawai ga jama’a.
Ba kanari
ba kurum ɗan kare. ”
Haƙiƙa waɗannan baitoci, sun nuna mana hoton dattijo, kamannunsa da ɗabi’unsa. Don haka, duk
wanda ya saɓawa waɗannan abubuwa, ko ya rasa
su, to shi ba dattijo ba ne, kuma mutuncinsa ya zube. Bisa wannan dalili, mijin
hajiya ba shi da mutunci, sai dai na riga ko muƙami.
• Gurɓacewar Tarbiyya:
Sakamakon
rashin iko na faɗa a ji, ko tsawatarwa kan haifar da hukunci ya koma hannun mace,
ko da ya ga ɓarna, baida ikon hanawa. ‘Ya’yansa maza da mata kan zama
sangartattu, kuma su zama ‘ya’yan mace. A zahiri, Bahaushe kan ce wa zai auri
‘yar mace? Ko ya ce: “Wane ai ɗan mace ne”, ma’ana ubansa bai da iko akansa. Don haka, ya samu
rauni a tarbiyyarsa. A bisa rayuwa ta haƙiƙa, ana son duk yaro ya tashi tsakanin uwa da uba, kuma kowanne
cikinsu yana da irin gudummuwar da zai bayar ta fuskar tarbiyya. Kamar yadda
aka sani ne bisa al’ada, yara sun fi tsoron iyaye maza fiye da iyaye mata.
Wannan, bai rasa alaƙa da kasancewarsu tare da iyaye mata a ko da yaushe.
• Ɓata Zumunta:
Idan aka
yi rashin sa’a, mace ba ta son zumunci da dangin miji, sannan kuma mijinta ta
shanye shi, ma’ana mijin hajiya. Tabbas zumunci zai ɓaci, saboda ba za ta bar
shi ya yi hulɗa da danginsa ba, balle har ya kyautata masu. Idan ba a yi sa’a
ba, sai dai ya yi da danginta. A irin wannan ne, mata kan ce: “Dangin miji ba
ku san abin arziƙI ba” ko “Dangin Miji ba ‘yan goyo ba ne”. Bayan wannan kuma,
hatta zumunci na cikin gida ɗaya a tsakanin mai gida da ‘ya’yansa, ko mai gida da sauran
matansa, watau kishiyoyi ke nan. A bisa dalilin zama mijin tace da mai gida ya
yi, shi yasa ake samun ‘yan ubanci, inda mai gida kan ware wasu daga cikin
‘ya’yansa a matsayin ‘ya’yan so (waɗanda ake kyautatawa) , wasu kuma a ƙyamace su, ba a son su, irin wannan wariya, shi ke haifar da ‘yan
ubanci a cikin ‘ya’yan mutum ɗaya, amma uwarsu kowa da tashi, watau ‘ya’yan turaka (‘ya’yan
kishiyoyi). Ta fuskar kishiyoyi kuwa, mai gida mijin tace ya kan fifita matar
so, wannan zai iya kasancewa uwar gida ko na ‘yar mowa da ‘yar bora ba za a
samu zaman lafiya ba ballantana har a yi zumunci.
• Taɓarɓarewar Al’umma:
• Taɓarɓarewar al’umma, na nufin lalacewa, ko susucewar al’umma. Wannan na
iya samun al’umma, ko ƙasa, ko gari, a dalilin
yawaitar mazajen hajiya. Idan aka rasa kakkyawar tarbiyya a gida, dole ne ya
shafi sauran gidajen, watau maƙwabta, da zaran aka ce
marasa tarbiyya sun yawaita, to dole al’umma ta lalace, al’amurransu su taɓarɓare.
KAMMALAWA
A ƙarshe, wannan muƙala ta ɗan taɓo wasu daga cikin ɗabi’un wasu mazaje ko
magidanta. A inda aka fito da dalilai da illoli, tare da nuna matsayin mijin
hajiya ko mijin tace. Idan muka kalli bayanan da suka gabata, sai mu ce dalilan
da sukan sanya magidanci ya zama haka, sun bambanta daga wannan magidanci zuwa
wancan, ko daga wannan gida zuwa wancan. Haka kuma, mun ga irin hanyoyi ko
dabaru waɗanda wasu
matan kan bi su jefa mazajensu wannan rami
Bayan
haka, wannan muƙala ta kawo shawarwari ga mazaje a inda aka yi hannunka mai sanda
ga mai hankali, saboda a gudu tare, a tsira tare.
Ina fatan
wannan muƙalar ta zama matashiya gare mu mazaje, a nan ma ya haɗa har da ni.
Alhamdu
Lillahi. Allah Yasa mu dace, amin.
MANAZARTA
Aƙilu A (1985) Fasaha Aƙliya Northern
Nigerian Publication Company Zaria.
Imam A
(1939) Magana Jari ce na uku. Northern Nigeria Publication Company
Zaria.
Imam A.
(1937) Ruwan Bagaja. Northern Nigeria Publication Company Zaria.
John T.
U. (1989) Jiki Magayi. Northern Nigeria Publication Company Zaria.
Maƙarfi S. (1970) Jatau na Ƙyallu. Northern
Nigeria Publication Company Zaria.
Sada M.
(1969) Uwar Gulma. Northern Nigeria Publication Company Zaria.
Hauwa A.
(2010) Don Iyalai. Jaridar Nasara
Sadiyya
I. B. (2008) A Gani na. Jaridar Gaskiya Tafi Kwabo.
Imam S.
(2014) Hira da shi a gidansa. Bakin Kasuwar Sati Unguwar Dosa Kaduna.
Sarki A.
(2014) Hira da shi Kasuwar Sati, Unguwar Dosa Kaduna 23/2/2014
Jiƙamshi S. (2014) Hira da shi Kasuwar Sati, Unguwar Dosa Kaduna
27/2/2014.
Is’haƙa A. (2014) Hira da shi a gidansa Layi Mai Anguwa Unguwar Dosa
Kaduna
23/2/2014.
Lawal M.
(2014) Hira da shi a gidansa Layi Mai Anguwa Unguwar Dosa Kaduna
23/2/2014
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.