Ticker

6/recent/ticker-posts

Bakin Bature (Bakin Mutum Da Kan Banasare): Tsokaci A Kan Dabi’un Wasu ‘Yan Boko Masu Ra’ayin Gaba-Dai Gaba-Dai

WANDA AKA GABATAR A KWALEJIN KOYON LARABCI DA ADDININ MUSULUNCI TA SHABAB DAKE UNGUWAR DOSA KADUNA. RANAR JUMA’A 14 GA MAYU 2012.

BAƘIN BATURE (BAƘIN MUTUM DA KAN BANASARE): TSOKACI A KAN ƊABI’UN WASU ‘YAN BOKO MASU RA’AYIN GABA-DAI GABA-DAI

DAGA

MU’AZU SA’ADU KUDAN

SHIMFIƊA:

WANE NE BATURE? Bature na nufin mutumin da ya fito daga nahiyar Turai. Wannan nahiya ta ƙunshi ƙasashe irin su Ingila ko Birtaniya, Faransa, Jamus, Italiya, Holan, Esfaniya da sauransu. Waɗannan Ƙasashe sune a Turai ta yamma (western Europe). Idan muka koma Turai ta Gabas (Eastern Europe) sun haɗa da Ƙasar Rasha,Jamus,Hongiri da sauransu. Bature na nufin namiji, mace kuwa Baturiya,jam’i kuma Turawa. Ita kuwa Kalmar Nasara daga Harshen Larabci,mai asali daga kalmar nazaret da aka samo ta,daga sunan wata Ƙabila da kuma sunan wani gari a Ƙasar Isra’ila.

Baya ga waɗannan Turawa na asali, sai kuma waɗanda aka turantar da su. Waɗannan kuwa sune kamar Amurka, Kanada, a da waɗanan mutane asalinsu ba Turawa ba ne. Bisa dalilin mallakarsu da Turawa suka yi,ta hanyar mulkin mallaka. Wannan yasa aka turantar da su a inda suka rikiɗa suka zama Turawan dole. A inda har ma suka zama ‘’feƙe kafi ƙaya tsini’’. Turawan Birtaniya suka tafi Amurka suka iske indiyawan daji da kaboyi masu kiwon shanu. Waɗannan mutane suna da harsunansu na asali,amma aka cusa masu harshen Turancin Ingilishi.

Hoton Bature; shi mutum ne fari, mafi farar fata kamar zabiya mai gashin kai ƙarangiya launi ƙasa-ƙasa mai ido launi toka-toka kamar na mage. Mai baki ƙarami da matsattsen hanci mai tsini. Baturiya ita kuma tana da gashin kai har ya sauka kafaɗa, wasu kuma har gadon bayansu.

Hoton Baƙin mutum shi kuma, a nahiyar Afrika Allah ya ajiye shi. Bahaushe kuma yana cikin nahiyar Afrika sashin yammacin Afrika a Ƙasashen Nijeriya,Nijer,Gana,da wasu Ƙasashe na Afrika. Baya ga nan, duk sauran wurare da ake samun Baƙaƙen fata kuwa ban da Afrika to kai su aka yi.

GABATARWA.

Da sunan Allah Mai rahama Mai jinƙai, Mai kowa, Mai komai, Mai aikata abin da Ya so, ga wanda Ya so, a sadda Ya so a yadda Ya so, ko ana so ba a so dole bayi su so. Tsira da amincin Allah su tabbata ga shugaban halittu Annabi Muhammadu, da Alayensa da Sahabbansa.

Wannan muƙala zata ɗan taɓo, wani abu da ya shafi wata irin rayuwa da Bahaushe ya tsinci kansa a ciki. Wannan rayuwa ta kasa Bahaushe zuwa gida uku ko huɗu. Kowane daga cikinsu akwai irin nasa rayuwa,tare da dalilai da suka jefashi cikinta. Wannan yasa na kira muƙalar da suna ‘’Baƙin Bature’’ (Baƙin mutum da kan Banasare). Ma’ana gashi baƙI ne to amma tunaninsa na Bature ne. Za mu tsakuro wasu dalilan mu kallesu,don muga irin tasirin da suka yi. An ce komai bai rasa sanadi,saboda haka zuwan Turawa Afrika shi ne sila. Dogon lokaci da aka ɗauka ana tare ya taimaka a kan haka ƙwarai.

Zuwan Turawa Nahiyar Afrika,Turawan da suka fara tako Afrika ta yamma sune Turawan bincike (explorers) ku mu ce ‘yan leƙen asiri (spices). Kamar yadda aka sani ne, cewa wani Baturen Potugal mai suna Mango Park da wasu ayarin mutane huɗu, sune suka fara zuwa Afrika, wasu kuma suka ce a’a wani Baturen Ingila ne Henry the navigator shi ne ya fara zuwa.

Bayan waɗannan kuma, sai ƙungiya ta biyu, ita ce ƙungiyar ‘yan kasuwa (traders) masu cinikin bayi (slave traders). Waɗanda suka taka muhimmiyar rawa wajen rusa nahiyar Afrika.

Daga su sai kuma ƙungiyar masu kare ‘yancin Ɗan adam da hana cinkin bayi, watau (Humanitanians) Waɗannan sun taho ne tare da ƙungiyar Turawa mishan watau (Missionaries) masu yada addinin kirista.

Ban da waɗannan kuma, sai wasu ƙungiyar watau Turawan kamfani (trader for ligetimate trade) waɗanda suka rinƙa sayan kayan amfanin gona (gyaɗa, auduga, fatu da ƙiraga, kwakwar manja, koko, ƙaro da sauransu. )

MULKIN MALLAKA (COLONIAL RULE) 1900-1960; Turawan kamfani su ne suka share wa Turawan mulkin mallaka hanya, (colonialist). Tabbas Turawan kamfani sun e suka fara rusa ko karya Daulolin mu (kingdoms and empires) kamar Daular Oyo, Benin,Etsekiri a kudu. A nan arewa kuma Daular Sokoto (Sokoto caliphate).

Bayan Turawan kamfani sun gama yin irin nasu zagon ƙasa, musamman kamfanin Royal Niger Company. Su kuma Turawan mulkin mallaka suka zo suka ƙarasa ruguza mu. Bayan sun rusa Daulolin kudu, sai suka dawo Arewa kan Daular Sokoto. A inda suka rinƙa yi masu ɗauki- ɗai-ɗai, daga shekarar 1900 suka dirarwa Bidda, Kwantagora, Keffi, sai Zariya 1902, Kano 1903 a ƙarshe Sakkwato 1903.

Bugu da ƙari, da suka ci galabar mu, sai suka kafa wani mulki mai kama da baba –na ɗaka- gemu- na- waje ko kuma cinka –nan –kashin-can. Ma’ana Sarauniyar Ingila ita ce take mulki daga can Turai, amma kuma wakilinta ke aiwatar da umarnin ta.

A shekarar 1914, sai aka ƙulla wani auren zobe (amalgamation) , inda aka haɗe sashin kudu (southern protectrate) da sashin arewa (northern protectrate) a ƙarƙashin jagorancin Pedrict Lord Lurgard. Bayan ya haɗesu (kudu da arewa) sai matarsa Florence lurgard ta raɗawa Ƙasar sunan Nijeriya wanda ya samo asali daga kogin Kwara (River Niger).

Turawan Birtaniya sun gudanar da mulkin Nijeriya, ta hanyar tsarin mulkin mai shamaki (indirect rule). A inda yake a sama Turawa ne, a tsakiya zuwa ƙasa sarakunan gargajya. Kamar haka: gwamna janar, mai binsa Resdan daga shi sai D. O (District Officer). Dukkan waɗannan Turawa ne, daga baya aka ƙara D. D. O (Deputy Director Officer) wanda ake kira baƙin Bature. Bayan su sai kuma sarakunan mu kamar haka:

Sarkin yanka (Emir) , Hakimi (District Head) , sai Dagaci (Village Head) a ƙarshe Mai Unguwa (Ward Head). Haka wannan tsari ya gudana na tsawon shekara 60 ko fiye da haka.

ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA; Wannan irin dogon zama da aka yi, na shekaru masu yawa. Shi ne ya haifar da abubuwa da yawa da suka yi tasiri a kan rayuwar Bahaushe gaba ɗaya. Shi wannan irin tasirin kuwa, zamu iya karkasa shi zuwa kashi huɗu ko kuma su mutanen kamar haka:

1. Akwai mutanen da tasiri ya yi masu jirwaye suka yi dabbare- dabbar.

2. Akwai mutane da suka yi rabi da rabi kamar ragon uda ko akuya mai gefe rabi fari rabi baƙi.

3. Akwai mutane da suka yi baƙi-baƙi.

4. Akwai mutanen da suka rikiɗe gaba ɗaya sun yi baƙiƙƙirin. Sun ƙuna ba su gudun ƙauri.

Kowane daga cikinsu baya rasa dalili da ya sanya shi zama hakan;

i. Rukunin mutane na farko su basu yi boko ba, amma sun fi ‘yan bokon zaƙewa.

ii. Rukunin mutane na biyu, ana iya samun ‘yan boko zalla watau waɗanda suka yi karatun zamani kuma suka ɗauki ra’ayin boko, amma kuma suna gaurayawa da al’adunsu.

iii. Rukunin na uku,sune boko sana’a, suna cin moriyar ta amma ba su dulmiya ba.

iv. Rukunin mutane na huɗu su ake kira boko aƙida, kuma tunanin su yafi na Bature, tun da su rayuwarsu ta yi ban –tafin- makafi da rayuwar Bahaushe da kuma musulmi.

A inda suturarsu da harshensu ba su ɗauke su da muhimmanci ba. Kai har da addini, al’ada da tunani, babu wani abu muhimmi, sai wanda Bature ya yi, ko ya faɗa. Ga masu irin wannan tunani na Nasara, maganarsu, rayuwarsu da tunaninsu duk na Bature ne. Farko dai, matarsu 1, ‘ya’ya 2-3,ga baƙar rowa kamar yaro ɗan yaye, ƙin zumunci kamar ɗan tsako, kare yafi ɗan uwa, farkarsa tafi matar aure. Ya san tarihin turai, bai san danginsa ba ko na Ƙasarsa. Ƙyale dala’ ilu ka ɗauki jarida. Jikinka na Kano zuciyarka a London, shi da makwabcinsa kuwa ba ruwan wani da wani (mahaukaci ya yi baƙo) , jikinka baƙi zuciya ta Nasara.

To wannan shi ne baƙin Bature, ɗan boko ne ko ba ɗan boko ba.

MASO KAYANKA YA FI KA DABARA; Dangane da hanyoyi ko dabarun da Turawa suka bi wajen cin nasarar wannan aiki shi ne, yaudara da yaƙi da ƙwaƙwalwa (tunani) da Larabci ( gazawatul fakir) da turanci kuma (psychological warefare). A inda suka yaƙi tunani mutane ta hanyar yin amfani da ‘yan korarsu farare da baƙaƙe da barbarar yanyawa.

Haka kuma sun yi amfani da wayon rainin hankali, watau riƙe min ɗa na,ka ba ni naka in buga. A nan sukan kushe al’adunka, amma su fifita nasu don ka karɓI nasu. Su munana maka naka amma su ƙawata nasu.

Dandaƙa ko hana haihuwa; wata dabara da suka yi amfani da ita,don su rage yawan mu ta hanyar hana yin aure da wuri mazanmu da matanmu. Misali yin karatun boko a daɗe ana yi, har sai shekaru sun yi nisa. Kamar saurayi sai a iske ya kai shekaru 35-40 bai yi aure ba, mace kuma sai ta wuce budurwa ta kai uwar mata, ta kai shekara 25-30, wasu ma fiye da haka. Idan aka kwatantasu da tsararrakinsu da suka yi aure kafin su. Misali shekaru 18- 25 sai a iske sun hayayyafa kuma sun kafu. Waɗanda suka makara kuwa, al’amurra sukan kasance a murɗe. Da farko yara kan kasance kaɗan, kuma iyayen su tsufa yara basu taso ba. Haka kum ga ƙyamar haihuwar ‘ya’ya da aka cusa masu. Ɗa ɗaya kamar goɗiya. Ga ƙayyade iyali ko tazarar haihuwa da sauransu.

Gudun zumunci da ƙyamar dangi;Duk wanda ya faɗa irin wannan rayuwa, yakan koma Baƙin Bature. Haka kuma yakan koma yana ƙyamar wani ya kusance shi, daga shi sai matarsa da ‘ya’yansa ko karensa idan ma har akwai ‘ya’yan ke nan. Wannan ne ya haifar da ƙin riƙon ‘ya’yan ‘yan uwa ko ziyartar dangi watau zumunta.

Raina tunani ko fifita kansa akan waninsa; Duk wani wanda bai da tunani irin nasu, komai ya taso matuƙar dai ya saɓa da ra’yainsu, sai su ce hauka ne ko da iyayensu ne.

Sakin na hannu kamun na guje; Abin da ke faruwa a nan shi ne, irin waɗannan mutane sukan yi watsi da al’adunsu, harshensu, tufafinsu, abinci, magani da sauransu. Wanda a ƙarshen al’amari sai su tashi a tutar babu, su zama jemagu ba su a tsuntsu ba su a dabba. Da farko, su dai ba Turawa ba, kuma ga su sun guji baƙaƙe sun yi rasasa- rasasa.

Kishi a rashin kishi ( kishin kare) ; waɗannan mutane sukan yi kishi a inda bai dace ba, kuma su ƙi yin kishi a inda ya kamata. Miji bai kishin matar sa, bai damu da maza komai yawansu su yi hulɗa da ita ba a wani lokaci su ake aikawa su kira ta.

 Ɓangaren mata; su kuma sai aka cusa masu kishin banza (kishin mai dadaro). A inda suke ƙyamar mijinsu ya ƙara aure, amma kuma yana da farka a waje. Sun ƙi zama da kishiya, amma ƙawar Alhaji ko Amimiyarsa ko abokiyar aiki za ta zo gidan su,kuma su karɓe ta hannu bibiyu. Duk ɓarnar da miji zai yi indai ba maganar kishiya to daidai ne.

 Wata yaudarar da aka yi wa mata; Da farko bayyana tsiraci, (tun daga Budurwa har Matar aure) canza halitta (shafe-shafe don a yi fari) , ƙyamar haihuwa da son abinda duniya (dogon buri) ,sun sacewa mata kunya,sun kawar da ƙauna,tausayi da ke tsakanin Uwa da ɗanta. Suka mayar da shi tsakanin Nani (mai raino) da yaro da sauransu. Wannan kuma ita ce Baƙar Baturiya.

TO JAMA’A INA MAFITA? Matuƙar aka rutsa mage a cikin ɗaki, to dole ta nemi mafita inda zata gudu, don ta tsira da ranta ta samu ta kuɓuta. Bisa wannan dalili, ina mai yin kira ga dukkan Bahaushe da Bahaushiya, da cewa mu farka daga baccin da muke yi, mu san kanmu, mu kula da kanmu, da mu tsare kanmu.

Dukkan mai hankali a jikinsa ya kamata ya dawo cikin hayyancinsa ya tsaya ya yi wa rayuwarsa kallon natsuwa. Watau kallo irin na sayen goron tsohuwa. Wajibi ne mu sanya kishin harshen mu, al’adunum da addininmu, saboda su ne rayuwar mutum gaba ɗaya. Matuƙar aka ce mutum ya rasa su to zai yi ballagazar rayuwa mara manufa da amfani. Domin ya yi ɗigirgire ko kan-tafi da rayuwarsa,an kuwa ce kan-tafi masomin asara.

Ga wata tambaya ga masu ra’ayin nasara, shin wai sun san cewa, sauran Ƙasashe da suka ci gaba, ba irin wannan hanyar suka biyo ba?. To idan masu irin wannan tunanin ba su sani ba,to ga wani bayani: Ƙasashe da yawa da suka riƙi harshensu a matsayin harshen ma’amulla,watau Harshen Ƙasa. Suka tsare al’adarsu suka tsare addininsu, sun ci gaba nesa ba kusa ba. Misali: Sin (china) Indiya, Japan, Iran,Kyuba, Birazil da sauran su.

Matashiya ga masu irin wannan ra’ayi. Tabbas wannan magana gaskiya ce, kuma a zahiri duk mai hankali zai yarda da ita. Al’ada dai kamar riga ta ke, don haka al’adarka ita ce rigarka wadda ta ke daidai da kai. Idan kuwa har ka ɗauki rigar wani, in har ba a yi sa a ba, za ta yi maka yawa ko a tsawo ko a kauri ko faɗI. A ƙarshen al’amari ko ka sanya ba za ta yi maka kyau ba. Shi ya sa aka ce naka shi ne naka kayan aro abin shirme ne,in mai abin ya karɓi abinsa to dole zaka komo naka.

Ina kira ga masu hankali a jikinsu da su san cewa kaza ba ta zama agwagwa, haka ita ma agwagwa ba ta zama kaza. Don haka mu tsaya a inda Allah ya ajiye mu, kar mu wuce gona da iri. Domin in ba haka ba zamu yi saki na dafe, zamu zama ba Turawa ba, kuma ba baƙaƙe ba. Da farko mun watsar da al’adunmu, harshen mu waɗansu ma har da addininsu.

Ina yi wa Bahaushe albishir, idan bai sani ba ya sani cewa, Allah ya yi wa harshensa da ala’dunsa ɗaukaka a duniya. Domin a yanzu harshen Hausa ya karɓu ƙwarai, tufafin Bahaushe na da kwarjini a ko ina a duniya, sannan addinisa na musulunci ya gagagara a duniya. Duk da irin tsangwama da Turawan yamma da Yahudawa suke yi masa, shi ne a sama cikin ikon Allah. To dama Bahaushe ya ce “an so kare da gwaiwa Allah ya bai wa rago” don haka mu taru mu yi kishin kan mu, saboda wasu Hausawa sun ɓata biyu ɗaya ba ta gyaru ba. Su dai ba harshen Turancin, kuma sun saki Hausar a ƙarshe sun saki reshe sun kama ganye. Haka ita ma al’adar sun bar ala’adar Bahaushe sun ɗauki ta Bature, sai dai kuma ba a Turai suke ba. Gashi kuma Turawan ba za su karɓe su ba, sai su ƙare a rasasa-rasasa. Alhali kuwa masu hikima sun kasa ribar rayuwa mataki uku zuwa huɗu kamar haka:

1. san samu (mutum ya samu alherin duniya da na lahira)

2. samu rasa (mutum ya samu alheirn duniya ya rasa na lahira)

3. rasa ka samu (mutum ya rasa alheri duniya ya samu na lahira)

4. rasasa-rasasa (mutum ya rasa alherin duniya da na lahira)

Allah ya tsare mu amin.

KAMMALAWA;

A ƙarshe wannan takarda, ta tsakuro wasu halaye ne na wasu mutanen mu waɗanda Turwa suka yaudaresu suka kuma sake su a igiyar ruwa. Irin waɗannan mutane ana samunsu a maza da mata. Don haka akwai baƙin Batutre, akwai baƙar Baturiya, ko baƙin mutum da kan Banasare da kuma baƙar mace da kan Banasariya. Kamar yadda bayani ya gabata cewa, an ɗan taɓo ne. Domin abubuwan suna da yawa. Ina fatan al’umma su fahimci inda wannan muƙala ta sanya gaba. Manufar ita ce mutum ya san shi wane ne, kuma mene ne matsayinsa?Don ya yi kishin kansa, saboda an ce’’ da uba aksse ado, in don riga ko a kasuwa sai a saya’’.

Mun riga munji irin illolin da Turawan nan suka yi mana, ta fuskoki marasa iyaka kuma ta kusurwoyi daban daban. Domin wasu har halitarsu suke sauyawa, daga baƙi zuwa fari ta hanyar shafe-shafe (bleaching) ko dasa gahin kai, nuna tsiraici da sauransu. Allah Ya tsare mu Ya bamu ikon gyarawa amin. Assalamu alaikum

KIRARIN BATURE

1. Bature manta sallah mai fitsarI a tsaye.

2. Huntu ubangijin mai riga.

3. Goga ka fi kyau tsira- tsira.

4. Ka ci gari ka kwana a daji.

5. Bature mai ture mutum a hanya ta ƙwarai.

6. Nasara asarar duniya.

7. . Nasara jar akuya mai kaI ga yara ɓarna.

8. Na Ingila ba ku daɗin gaba.

9. Na Jamus ɓata Ƙasa.

10. Na Faransa a bi ku a huta.

11. Shirinya raɓi ki kashe.

12. Mishau bad da musulmi.

13. Kowa ya daka taku zai yi nadama.

14. Kori tsohonka ka girmama kare.

15. Kori matarka ka kwana da farka.

16. Gaida kwartonka ka ba shi abinci.

17. Ƙadda baƙon dole, ana ba wuri kana kafa ɗaki.

18. A ci tuwo da kai, ai tsadar kai kwano.

19. Nasara ba ku yi don Allah, kun fi son ku yi suna.

20. Nasara ba ka cin hatsi sai rayis.

21. Nasara ba ka aikin banza.

22. Faransa romon jaɓa.

23. Na faransa mai kisa ba shiri’a

 

 

 

 

 MANAZARTA

OniS. (1980) West African History 100 Questions And Answers. University Press Ibadan

Brian C. (1968) A Map History of the Modern World second edition Heimann Educational Books Ltd. Lodon

Lempert. L. O. (1968) A History of Africa 1918-1967 Printed in the U. S. S. R.

Sarki H. A. (2000) Zuwan Musulunci a Afirka da shigowarsu

 Ƙasar Hausa. G. A. Computer Centre. Ikere – Ekiti, Ekiti State.

Adam M. Tahir (1997) Asalin Hausawa da Harshen su. Kano Nigeria.

Madauci I. (1963) Al’adun Hausawa. Northern Nigerian Publication Company Zaria.

Shagari S. A. (1975) Waƙar Najeriya. Northern Nigerian Publication Company, Zaria.

 Bunza A. M. (2006) Gadon feɗe al’ada. Tiwel Nigeria Limited Surulere, Lagos.

 Ladan Y. (1980) Zaman Duniya Iyawa ne. Northern Nigerian Publication Company, Zaria. 

 Hausa Post

Post a Comment

0 Comments