DAGA
MU’AZU SA’ADU KUDAN
DEPARTMENT OF NIGERIAN LANGUAGES
USMANU ƊANFODIYO UNIVERSITY
SOKOTO
(07030803404)
WANDA AKA GABATAR A TARON TALLAFAWA MARAYU A GARIN KUDAN A MAKARATAR FIRAMARE DAKE KUDAN. RANAR AL’HAMIS 23 GA JANAIRU 2014, DA ƘARFE 10: 00 NA SAFE.
SHIMFIƊA:
WANE
NE MARAYA?
Maraya
na nufin yaron da uwa, ko uba, ko kuma dukkansu, suka mutu. Bahaushe kan kira
namiji da maraya, mace kuma marainiya, jam’i kuma marayu. Haka kuma Bahaushe
ya ƙara wa maraya wasu sunaye, masu alaƙa da irin
maraicin da ya samu kansa. Bisa wannan ne yasa akan kiran marayan da ubansa ya
rasu kafin a haifeshi, da audi namiji, mace kuma audinga. Shi kuma marayan da
uwarsa ta rasu bayan da ta haifeshi tun yana jariri akan kirashi da talle idan
namiji ne, ko tallafi.
MENE NE
MARAICI?
Maraici
na nufin shekarun da maraya yake rayuwa kafin ya balaga, shi ake kira maraici.
Wannan rayuwa ta ƙunshi abubuwa masu yawa,
kamar damuwa, ko kewa, da kaɗaici, da yunwa, da talauci, Tabbas sukan shafi jikinsa, ko
lafiyarsa, da tunanunsa, da tarbiyya, kai hatta irin rayuwar da zai yi in girma
nan gaba da sauransu. Waɗannan abubuwa su ne suke tauye yaro ya tsumbure, ma’ana ya kasa
girma.
GABATARWA
Da sunan
Allah Mai rahama Mai jinƙai, Mai kowa, Mai komai,
Mai aikata abin da Ya so, ga wanda Ya so, a sadda Ya so, a yadda Ya so, ko ana
so, ko ba a so, dole bayi su so. Tsira da amincin Allah su tabbata ga shugaban
halittu Annabi Muhammadu, da Alayensa da Sahabbansa.
Wannan muƙala zata ɗan taɓo, wani abu da ya shafi wata irin rayuwa da Maraya ya tsinci kansa
a ciki. Wannan rayuwa ta sanya Bahaushe ya karkasa marayun wannan zamani zuwa
gida uku ko huɗu. Kamar haka, ɗanmaraya, ko maraya mara galihu, ko kafi - mai – uba- jin - daɗi, ko uba a ka fi mu.
Kowane daga cikinsu akwai irin tasa rayuwar da yake yi,tare da dalilai da suka
jefashi cikinta. Wannan yasa na kira muƙalar da suna ‘’Maraya
da Maraici a Yau’’ (halin da Marayu suke ciki a wannan zamani). Ma’ana
gashi yana cikin ‘yan uwa da dangin uwa da na uba, to amma tunaninsu ba ya tare
da shi. Babu shakka akwai wasu dalilai da suka jawo al’ummar mu ta faɗa wannan hali. Za mu
tsakuro wasu dalilan mu kallesu, don muga irin tasirin, ko ɓarnar da suka yi. An ce
komai bai rasa sanadi, saboda haka zuwan wasu baƙin al’adu
da muka runguma su ne sila. Dogon lokaci da aka ɗauka ana tare da wasu baƙin al’ummu ya taimaka a kan haka ƙwarai.
MATSALOLIN
MARAICI A AL’UMMAR HAUSAWA
Al’amarin
maraici yana fuskanta matsaloli da dama a sakamakon faruwar sauya-sauyen da
zamani ya kawo a rayuwar Bahaushe ta yau da kullum. Kaɗan daga cikin abubuwan su
ne kamar cuɗanya da
wasu ƙabilu a in da aka samu shigowar baƙin al’adu
sannan kuma suka yi tasiri. zuwan ilimin book shi ma ya yi tasiri kwarai akan
zumuncin Bahaushe, don kuwa ya zo da wasu ɗabi’u ya kuma kawar da wasu ɗabi’u da aka gada kaka da kakanni.
Bayan ga
waɗanan kuma
sai wasu dalilai kuma da suka ƙara kawo matsaloli ga
harkar zumunci, sun haɗa da yanayi tattali arziki, cigaban zamani sannan kuma sai gurɓacewar hali da sauransu.
Gudun
zumunci da ƙyamar dangi;Duk wanda ya faɗa irin wannan rayuwa, yakan koma Baƙin
Bature. Haka kuma yakan koma yana ƙyamar wani ya kusance shi,
daga shi sai matarsa da ‘ya’yansa ko karensa idan ma har akwai ‘ya’yan ke nan.
Wannan ne ya haifar da ƙin riƙon ‘ya’yan ‘yan uwa ko ziyartar dangi watau zumunta.
HAƘƘIN 'YA'YA AKAN IYAYE.
Kamar yadda aka sani ne cewar babu abin da shari'ar Musulunci
ta ƙyale shi haka kawai. To haka harkar rayuwa tsakanin mahaifa da
'ya'yansu akwai wasu haƙƙoƙi abin kulawa don samun al'umma ta gari.
Akwai
wani hadisi da Manzon Allah (S. A. W) ya yi kashedi tun daga farkon al'amari a
inda yace ku zaɓar wa 'ya'yan kuuwa ta gari tun kafin ku haife su, in zasu yi aure
su auri ma'abociya addini, sannan kuma akwai inda ya umarci al'ummar sa da cewa
in zasu kusanci matayen su da jima'i, to su yi addu'a don neman tsari daga
shedan kar ya taba shi, ko ya halakar da shi, ga addu'ar: - "Allahumma
Jibni shaiɗan
wajibni Shaiɗani ma
razaƙata".
Bayan
wannan kuma, sai wasu haƙƙoƙi da suka rataya a kan uba, musamman, shi ne bayan an haifi
jinjiri, an so uba ya samu dabino ya tauna ya ɗiga ma jaririn ruwan
dabinon a baki don ya haɗiye, sannan kuma ya yi masa huɗuba ko a ranar da aka haife shi, ko bayan kwana uku ko bakwai, an
so ya zaɓar masa
suna mai kyau da ma'ana, kuma a ranar ta bakwai an so ya yanka haƙiƙa ya aske sumar sa ya auna nauyin gashi, ya bayar da sadaka
gwargwadon nauyin gashin.
Daga
wannan kuma, ya duƙa ke nan a wajen ciyarwa, tufatarwa da tarbiyya. Idan yaro ya kai
shekara biyu sai a yaye shi, in kuma ya kai shekara bakwai sai a yi masa
kaciya, daga nan za a umarce shi da yin Sallah, sannan kuma a raba wurin
kwanciya in sun kai biyu, in ya kai shekara goma a buge shi in yaƙi yin sallah.
Banda
wannan, a kula da ilimi da koyon sana'a, daga nan har yan balaga, watau wajen
shekara goma sha biyar zuwa ashirin. Idan ya kai haka, to ya zama mutum inda
hali sai a yi masa aure ga namiji ke nan. Amma ita 'ya mace wajibi ne da ta isa
aure a yi mata aure.
Saboda
mu samu madogara ga bayanin da ya gabata, akwai wasu hadisai da Manzon Allah
(S. A. W) yace: -
"Kullukum
ra'in, wa kullukum mas'u'lun an ra'iyatihi"
"Dukkan
ku masu kiwo ne, kuma kowane abin tambaya ne".
Banda
wannan ma, akwai wata aya a cikin Al-ƙur'ani wadda ta zama kamar
gargaɗi ce ga
musulmai muminai kamar haka: -
ياأيها الذين آمنوا قوا أنفسكم وأهليكم نارا وقود ها الناس
والحجارة أعدت للكافرين.
Ya ku waɗanda suka yi imani, ku
tsered da kanku daga wuta wadda wadda mutane da duwatsu sune makamashin ta an
tanaje ta don kafirai.
Akwai wani hadisi
da Manzon Allah (S. A. W) yace: "Kowane jariri ana haihuwar sa ne a fiɗira ta musulunci sai dai
iyayensa su mai da shi Yahudu ko Nasara ko Bamaguje.
Sannan
akwai wani hadisi da Manzon Allah (S. A. W) yace idan mutum ya mutu, duk
ayyukan sun yanke sai dai sadaƙatil jariya guda uku kamar
haka: -
1. Ko ya yi
wani abu na gina Addini kamar makaranta, hanya, gada, masallaci.
2. Ko ya yi
ilimi ya koyar da shi, ko ra rubuta littafi.
3. Ko ya
haifi ɗa salihi
wanda zai rinƙa yi masa addu'a bayan ya mutu.
Tunda
yake haihuwa rahama ce, ashe kuwa duk wanda ya same ta, ya zama wajibi ya
tarbiyantar da yaransa maza ne ko mata, don in suka zama mutanen kirki, sun
zama abin alfahari ga musulunci. Wannan shi ya tuna mana da wani hadisi da
Manzon Allah (S. A. W) yace: -
"Ku
yi aure ku hayayyafa in yi alfahari da yawanku…"
Bugu
da ƙari, wata falala da garaɓasa da iyaye suka samu a dalilin tarbiyantar da yara musamman 'ya
mace, Manzon Allah (S. A. W) yace duk wanda ya raini 'ya mace har ta girma ta
shiryu ta yi aure, to sakamakonsa Aljannah.
Sai
kuma wani da ya ce duk wanda ya ilmantar da 'ya mace, to ya ilmantar da al'umma
ne.
HAƘƘIN TARBIYYA YA RATAYA GA WUYAN IYAYE.
Nauyi
yi wa 'ya'ya tarbiyya ya rataya ne a wuyan iayye watau uba da uwa.
Wanda ya
haɗa da: -
ü Sanin Allah.
ü Son Annabi da Alayensa.
ü Karatun Al-ƙur'ani.
ü Sallah.
ü Girmama na gaba.
ü Koyar da magana.
ü Koyar da tafiya.
ü Koyar da cin abinci.
ü Koyar da kwanciya.
ü Koyar da kunya.
ü Gudun kwaɗayi.
ü Barin hassada.
ü Koyar da ƙwazo.
ü Koyar da tsafta.
ü Koyar da tattali.
ü Koyar da zumunci.
ü Koyar da tausayi.
ü Koyar da kallo.
ü Koyar da tsare amana.
Riyadus
Salihin – Pg. 202.
ZAƁARWA 'YA'YA UWA TA GARI.
Wajibi ne ga dukkan mahaluki mai hankali da yayi niyyar yin aure,
to ya yi ƙoƙarin zaɓarwa 'ya'yansa uwa ta gari, ma'ana mai tarbiyya da son addini. Kar
ya bi son zuciya ya auro mace don kyau, watau kyakkyawa, ko 'yar wane, watau
mai nasaba (mai kuɗi, sarauta, muƙami). Wannan magana ta yi
dai-dai da wani bayani da Manzon Allah (S. A. W) ya yi cewa ku auri mace
ma'abuciyar adini. Domin yace in ka auri don kyau to lallai kyau kan ƙare in ta tsufa, ko nasaba don mulki na iya ƙarewa, amma shi addini ba ya ƙarewa.
Bayan
haka, zaɓarwa
'ya'ya uwa ta gari kamar hutar da kai ne, domin in ka haifi yara da mace
ta ƙwarai, to kamar ita ce makarantar su don zasu koyi komai na ƙwarai daga wurinta. Saboda masu hikima sun ce uwa itace makarantar
farko ga yaro. Haka kuma in mutum ya kurkure ya auri Ballagazar mace mara
tarbiya, to ya kashe kansa da kansa, kuma yaransa sun shiga uku. Babban dalili
shi ne, ita ba ta da tarbiya, ba ilimi balle addini, to a nan ina makarantar
farko take? Sai dai su koyi zagi da miyagun halaye.
TANAJIN
DA MUSLUNCI YA YI WA MARAYA
Haƙiƙa shari’ar Musulunci ta yi wa maraya tanaji mai yawa, saboda a
kare shi daga tozarta. An yi wannan tanajin ne kuwa ta hanyar bayar da ummarni,
kyautata masa, ko hanin cutar da shi. Duk wannan ya zo ne a cikin ayoyin Alƙur’ani mai girma, da hadisai masu yawa. Ga wasu misalai kamr haka:
HAƘƘIN MARAYA A KAN WALIYYIN SA.
Dukiyar
da maraya ya gadan wajibi ne a sanya ta hannun wani waliyyin sa wanda zai tsare
ta ya lura da ita. Wannan waliyyi shi ne zai riƙa ɗaukar nauyin sa wajen
ciyarwa, tufatarwa da tarbiyantarwa, wannan ya haɗa har da ilimi.
An
sharɗanta cewa
a rinƙa juya kuɗin don gudun kar zakka ta cinye, a bisa wannan ne shari'a ta tsara
waliyyin maraya na iya amfani da kuɗin marayan nan idan ba mai wadata ba ne. amma kar ya yi da ɓarna.
Wajibi
ne waliyyin maraya ya aurar da yarinya/marainiya in ta isa aure, kuma ya bi
wasiyya da mahaifi ya bari, ko kuma ya shawarce ta, amma ba zai yi mata auren
dole ba. In ya kasance maraya ne, watau namiji idan ya balaga ya kawo ƙarfi, ya zama mai hankali, to sai a miƙa masa dukiyar sa tare da shaidu, amma in wawa ne (saluhu) to shi
za a rinƙa kula masa da dukiyar.
وءات اليتمى أموالهم ولا تتبدلو الحبيث بالطيب،
ولا تأكلوا أموالهم إلى أموالكم، إنه كان حوبا كبيرا.
Kuma ku
bai wa marayu dukiyoyin su, kuma kada ku musanya mugu da mai kyau. Kada ku ci
dukiyoyinsu zuwa ga dukiyoyin ku. Lallai shi, ya kasance zunubi ne mai girma.
FALALAR
KULA DA MARAYA.
Matashiya.
Allah
(S. W. T) Ya yi kira kuma tare da tsoratarwa a kan harakar maraya, wannan
kashedi da aka yi wa musulmai a kan kula da maraya, in mutum ya ji ya bi don
kansa, in kuma ya ƙi, to ga dai sakamakon da
zai tarar gobe ranar ƙiyama. Allah Ya tsare mu
amin.
"إن
الذين ياكلون أموال اليتامى ظلما إنما يأكلون فى بطونهم نارا وسيصلون سعيرا.
Lallai waɗanda suke cin dukiyar
maraya da zalunci, lallai suna cin wuta ne a cikinsu, da sannu a jefa su cikin
wutar sa'ira.
ولاتقربوا مال اليتامى إلا بالتى هي أحسن حتى يبلغ
أشده
Kar ku
kusanci dukiyar maraya sai da kyautatawa, sai sun isar ga ƙarfi, watau sun kawo ƙarfi.
ومن كان غنيا فليستعفف ومن كان فقيرا فليعكل
بالمعروف
Wanda ya
kasance mai wadata ne, to ya sauƙaƙa, amma wanda ya kasance mabuƙaci ne, to ya ci amma da
kyautatawa ko da tsoron Allah.
وعن ابن عباس قال: قال رسول الله صلى الله عليه
وسلم: من ضم يتيما من المسلمين إلى طعامه وشرابه حتى
FALALAR
RAINON MARAYA.
Akwai wata garaɓasa wadda Allah (S. W. T)
ya tanadarwa duk mutumin da ya raini maraya har zuwa girmansa kuma ya yi masa
aure. Wannan kuwa ya bayyana a wani hadisi da Manzon Allah (S. A. W) ya yi
bayani a kan haka.
Kamar
haka: -
يغنعه الله تعالى أو جب الله له الجنة إلا يعمل
ذنبا لا يغفر. وقل صلى الله عليه وسلم: من مح رأسه يتيما لا يمسحه إلا الله كان له
بكل شعرة مرة عليها يده حسنه. ومن أحسن إلى يتيم أو يتيمة عنده كنت وأنا وهو هكذا
فى الجنة.
An karɓo daga Ɗan Abbas yace: Manzon Allah (S. A. W) yace: "Duk wanda
ya ɗauki
maraya na musulmi na daga abincinsa ko abinsha har sai da Allah ya azurta shi.
Allah (S. W. T) Ya wajabta mai Aljannah, sai dai in ya aikata wani zunubi da ba
a gafartawa.
Manzon
Allah (S. A. W) yace: Duk wanda ya shafa (dafa) kan maraya, bai shafa kan don
komai ba sai don Allah. Yana da lada gwargwadon yawan gashin kansa (suma) da
hannunsa ya taɓa. ni da shi muna kamar haka a Aljannah.
فى البخارى: أن رسول صلى الله عليه وسلم قال: أنا
وكافل اليتيم فى الجنة هكذا. وأشار با لسبا بة ووالوسطى وفرج بينهما.
Ya zo
cikin Bukhari:
Manzon Allah (S.
A. W) yace: Ni da mai rainon maraya a Aljannah haka muke. Sai ya yi nuni da
yatsunsa biyu ɗan Ali da babba na tsakiya. Ya gwame su.
وفى صحيح مسلم عنه صلى الله عيه وسلم قال: كاقل
اليتيم له أو لغيره أنا وهو كها تين فى الجنة. وأشار بالسبابة والوسطى.
Ya zo a
Sahihu Muslim:
Manzon Allah (S.
A. W) yace: Mai rainon maraya nashi ne? watau danginsa ko na waninsa nin da shi
haka muke a Aljannah. Sai ya yi nuni da yatsun sa ɗan Ali da babba na tsakiya.
An
kwaɗaitar da
kula da kyautatawa maraya ta kowacce hanya a wurare da yawa tun daga
Ayoyin Ƙur'ani har zuwa
Hadisai
kamar a cikin Suratul Ma'un. 1-2.
أرءيت الذى يكذب بدين. فذ1الك الذى يدع اليتيم.
Shin ka
ga wanda ke ƙaryatawa game da ranar sakamako?. To, wannan shi ne ke tunkuɗe maraya daga haƙƙin sa.
Suratul
Fajr.
كلا بل تكرمون اليتيم.
A aha! Ba
haka ba, ai baku girmama maraya!
Suratul
Insan.
...... مسكينا ويتيما وأسير.
Ga
matalauci da maraya da kamamme.
Suratul
Ma'un.
فذالك الذى يدع اليتيم.
To,
wannan shi ne ke tunkuɗe maraya daga haƙƙin sa.
ويطعمون الطعام على حبه مسكينا ويتيما وأسيرا.
Suna
ciyar da abinci ga mabuƙata, miskinai bayi da
marayu don neman yardar Allah.
12. 3 KYAUTATA WA
NA ƘASA DA KAI.
Manzon
Allah (S. A. W) ya umarni da akyautatawa na ƙasa,
watau mutum ya kyautata wa wanda duk ke ƙarƙashin sa, tun daga mata, ya'ya, barori, kai hatta dabbobi, banda
ma umarni, shi da kansa ya aikata an gani. Akwai wani abu da ya faru a kan wani
yaro Bahayude mai yin hidima a gidan Manzon Allah (S. A. W) , a lokacin da ya
tashi bashi da lafiya, sai Manzon Allah (S. A. W) ya tashi da kansa ya tafi
gidan yaron don kawai ya gashe shi. Ko da ya isa gidan ya shiga ya duba yaron,
sai yace masa ka yi imani, sai yaron yana kallon Annabi kuma yana kallon
babansa, a ƙarshe sai baban yace ma yaron ka yi wa baban Ƙasim ɗa a, ma'ana ya bi abin da Annabi yace masa, nan take kuwa ya yi
imani, sai aka zare ransa. Sahabbai suka ga Annabi ya fito yana fara'a, sai
suka tambaye shi, sai Manzon Allah yace madalla da Allah Ya shiryar da shi.
Akwai
wani hadisi da Manzon Allah (S. A. W) ya yi umarni cewa ku kyautatawa bayin ku,
ku ciyarn da su abin da kuke ci, ku tufatar da su abin da kuke tufata, ku
tausasa musu don suma suna da rai kamar yadda kuke da shi.
Sai kuma
wani hadisin da yace bashi tare da mu wanda bai ji tausayin na ƙasa da shi ba, bai kuma girmama na gaba ba.
Haka kuma
wani hadisin cewa ya yi, duk wanda ya ciyar da ɗanyar hanta Allah na kallon
sa.
KYAUTATA
WA MUMINI.
Manzon
Allah (S. A. W) ya yi bayanin cewa mu kyautata wa juna don Allah na son masu
kyautatawa. Bayan wannan kuma, sai wani hadisin da ya yi bayanin cewa duk wanda
ya kyautatawa mumini sau ɗaya to Allah (S. W. T) Zai kyautata masa sau saba'in, haka kuma
wanda duk ya munanawa mumini sau ɗaya, to Allah sai ya munana masa sau saba'in.
Banda
wannan, sai wata maganar da tace: duk wanda ya yaƙi mumini
(waliyyi) , haƙiƙa zai yi yaƙi da Allah.
وعن ابن عمر رضى الله عنهما، أن رسو الله صلى الله عليه وسلم قال:
المسلم أخو المسلم، لايظلمه، ولا يسلمه. من كان فى حاجة أخيه كان الله فى حاجته،
ومن فرج عن مسلم كربه،لا فرج الله عنه بها كربه من كرب يوم القيامة. ومن ستر
مسلما، ستره الله يوم القامة.
HAƘƘIN MARAYA AKAN AL'UMMA DA HUKUMA.
Maraya na nufin
yaro/yarinyar da iyaye uwa ko uba suka mutu suka bar shi bai balaga ba.
Maraya
na da wasu haƙƙoƙi da suke rataye a wuyan waliyansa, watau dangin sa na jini ko
'yan uwa musulmai ko hukuma. Dole ne ɗaya daga cikin ƙungiyoyin nan uku su kiyaye
haƙƙoƙin har girman marayan in namiji ne ya balaga ya mallaki
hankalinsa, inda zai iya dogara da kansa. Idan mace ce kuwa (marainiya) har
zuwa girman ta ta yi aure.
Dangane
da rayuwar maraici, wasu na ganin cewa wanda ya rasa uba (mahaifi) shi ne
maraya, amma wanda uwar sa ta rasu shi ba maraya ba ne. wasu kuma na ganin da
wanda ya rasa uwa ko uba duka maraya ne.
Bugu
da ƙari, waɗannan haƙoƙi wajibi ne a kula da su tun daga dangin maraya, sauran al'ummar
musulmi har ya zuwa ga hukuma. Domin kula da wannan bin umarni ne na shari'ar
musulunci. Saboda Allah Ya yi umarni a Ƙur'ani.
Haka Mazon Allah (S. A. W) ya yi umarni a hadisai masu yawa.
TO
JAMA’A INA MAFITA? Matuƙar aka rutsa mage a cikin ɗaki, to dole ta nemi mafita inda zata gudu, don ta tsira da ranta
ta samu ta kuɓuta. Bisa wannan dalili, ina mai yin kira ga dukkan Musulmi da ya
farka daga baccin da muke yi, mu san kanmu, mu kula da kanmu, da mu tsare
kanmu.
Dukkan
mai hankali a jikinsa ya kamata ya dawo cikin hayyancinsa ya tsaya ya yi wa
rayuwarsa kallon natsuwa. Watau kallo irin na sayen goron tsohuwa. Wajibi ne mu
sanya kishin al’adunmu da addininmu, saboda su ne rayuwar mutum gaba ɗaya. Matuƙar aka ce mutum ya rasa su to zai yi ballagazar rayuwa mara manufa
da amfani. Domin ya yi ɗigirgire ko kan-tafi da rayuwarsa, an kuwa ce kan-tafi masomin
asara.
KAMMALAWA;
A ƙarshe wannan takarda, ta tsakuro wasu halaye ne da wasu marayunmu
waɗanda aka
sake su a igiyar ruwa. Irin waɗannan marayun ana samunsu a maza da mata,duk da yake ga dangin uwa
da uba. Bayan haka ga sauran jama’a masu hannu da shuni, suna tare da su, amma
kowa ta kansa yake yi. Watau rayuwar daga ni sai ɗa na, ko daga ƙwauri sai gwiwa. Don haka akwai bukatar, kowa ne mutum ya dawo da
hankalinsa jikinsa ya taimakawa maraya da marainiya. Kamar yadda bayani ya
gabata cewa, an ɗan taɓo ne. Domin abubuwan suna da yawa. Ina fatan al’umma su fahimci
inda wannan muƙala ta sanya gaba. Manufar ita ce mutum ya san shi wane ne, kuma
mene ne matsayinsa? Don ya sani shi kansa yana iya mutuwa, saboda haka me yake
nufi da ‘ya’yansa?.
Mun riga
munji irin illolin da waɗannan mugayen ɗabi’u suka yi mana, ta fuskoki marasa iyaka kuma ta kusurwoyi
daban daban. Haka kuma mun ji irin tanajin da musulunci ya yi wa maraya da kuma
duk wanda ya kulak o ya kyautatawa maraya. Domin haka muna fata mu koma ga
halaye da muka gada tun iyaye da kakanni, na kyautatawa marayu, Allah Ya tsare
mu Ya bamu ikon gyarawa amin. Assalamu alaikum
MANAZARTA
A
SuyuɗI ( )
Jami’ul Hadisi
S. Aliyu
(2001) Addu’a’u min kibabi was’sunnah
Maktabatu
Anwaru Abdullahi, Kurmi Market, Kano.
Abdullahi
Fodiyo ( ) Sabiblil Najati. Jafaru Bin Alhaji,
Hussaini
Alkamawa Sakkwato.
Zaid A. A
( ) Risala Fssarar Hausa. Kurmi Market, Kano.
Gumi A M.
(1980) Al-ƙur’ani mai girma,Tarajamar Hausa.
Hadimil
haramaini, Sharifaini Makkah.
Malik I.
(1970) Muwaɗɗa Malik.
Darul fikri, Beirut Lebanon.
Annawawi
I. ( ) Riyadus salihin. Darul fikri, Beirut Lebanon.
Imam Z. ( ) Kitabul
Kaba’ir, Darul fikri, Beirut Lebanon.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.