TAKARDAR DA AKA GABATAR A TARON TALLAFAWA MARAYU A GARIN KUDAN A ZAUREN TARO (TOWN HALL) DAKE LIKORO ROAD SABON GARIN KUDAN. RANAR ASABAR 5 GA YULI 2014, 8 GA RAMADAN DA ƘARFE 09: 00 NA SAFE
ROWA (HALI, WAYAU, KO CIWO?): TSOKACI A KAN ƊABI’AR ROWA A RAYUWAR BAHAUSHE JIYA DA YAU
DAGA:
MU’AZU
SA’ADU MUHAMMAD
DEPARTMENT
OF NIGERIAN LANGUAGES
JIGAWA
STATE UNIVERSITY KAFIN HAUSA
GABATARWA
Da sunan
Allah Mai rahama, Mai jinƙai, Mai kowa, Mai komai.
Tsira da amincin Allah su tabbata ga shugaban ma’aika, Annabi Muhammadu (S. A.
W).
Wannan muƙala, na da ƙudurin yin tsokaci a
kan ɗabi’ar
rowa da matsayinta a rayuwar Bahaushe jiya da kuma yau. Haka kuma tare da fito
da irin sauye-sauye da rayuwar Bahaushe ta samu dangane da ɗabi’ar rowa. Bayan haka, za
mu dubi dalilan da suka kawo waɗannan sauye-sauye. Ba za mu yi ƙasa a
gwiwa ba wajen nuna illolin rowa da kuma sakamakon da takan haifar a al’umma. A
wannan nazari, zan dubi rowa ta ƙusurwowi uku kamar haka: -
A mahangar Al’adar Bahaushe, da Mahangar Zamani, sannan ta Mahangar Addinin
Musulunci. Bisa wannan dalili ne yasa na yi wa wannan maƙalar take da “Rowa (Hali, ko Wayau, ko Ciwo?)”. Na
kawo taken a matsayin tambaya ne don ya ba mu damar lalubo amsa. Tare da fatan
mai karatu ko saurare zai gano ko zaƙulo amsar a ƙarshen muƙalar, don samun mafita ko a
fid da jaki a duma.
FASHIN BAƘI:
Rowa: Na nufin wata ɗabi’a ce wadda mutum kan yin a hana ko ƙin baiwa kowa wani abin hannunsa. A kan kira namiji da marowaci,
mace kuma marowaciya, idan jam’i ne kuma a ce musu marowata.
Hali: Na nufin ɗabi’a wadda aka san mutum da ita wadda yake aikatawa yau da
kullum.
Wayau: Na nufin kaifin tunani wanda mai shi ya kan yi amfani da shi
idan wani al’amari ya taso masa don samun mafita. A wani lokaci akan kira wayau
da dabara.
Ciwo: Na nufin wani baƙon sauyi mara daɗi mai tafe da zugi da ya
kan samu jikin mutum ko dabba, ko tsuntsu ko tsirrai. Akwai ciwo na sarari
watau na zahiri, sannan akwai ciwo na ɓoye ko na ma’ana wanda ba a iya gani da ido
ROWA (HALI, KO WAYAU, KO
CIWO?)
Bisa lura
da aka yi da wasu mutane, saboda son abin hannunsu basa ƙaunar wani ya samu. Don haka ne sai al’adar Bahaushe ta karkasa
rowa kamar haka: Ita kanta rowar watau aikin, shi mai yin ta kuwa, ana kiran
namiji marowaci, mace kuwa marowaciya, jam’i marowata.
Kashe-kashen
Rowa: Dangane da karkasuwar rowa,
sai mu ce akwai mai dalili, haka kuma akwai mara dalili.
Mai
dalili muna iya cewa saboda ƙarancin abu ko rashinsa. Ko
da yake akwai waɗanda suke da shi, amma gani suke yi idan suka bayar abin hannunsu
zai ƙare.
Game da
mara dalili kuwa, ana iya cewa, hali ne watau ɗabi’a, ko kuma sun gada, ko
kuma sun koya. Ana iya samu wasu mutane rowa halinsu ne, ko suna da wadata, ko
talauci. Ba wai su bai wa wani abu, su kansu ba su ci ba, balle iyalai ko
dangi, ballantana maƙwabta, akan kira wannan da matsolo. Shi kuwa Ibrahim Narambaɗa a waƙar Alhaji Ɗandugru Taimakon Allah ag
garai, cewa ya yi:
Jagora:
Mutanen Kaura suna hwaɗin.
Samun
wane ya zamo samun mujiya.
Mata nai
basu ci, bare danginai suci.
Yara:
Zamfara dai na faɗi ya zamo ƙaurin gada.
ɗ
Gindi:
Alhaji Ɗandurgu Taimakon Allah ag garai,
Na lura
da duniya akwai namijin arziƙi.
Rowar
gado: Wasu mutanen kuma ana iya
cewa rowa ciwo ne a gare su, don kuwa sun gada ne daga iyaye, musamman ta wajen
uwa. Domin akan tsotsi rowa, tsiya, faɗa, ko hauka a nonon uwa.
Rowar
jawo wa kai: Akwai waɗanda rowarsu ta jawo wa kai
ce, watau ta kuɗin lukudi. Lukudi wani itace ne wanda Bahaushe ya camfa, cewa duk
wanda ya haɗiyi
‘ya’yan itacen zai yi kuɗi, to amma kuma fa ba zai iya cin ko kwabo ba. Masu kuɗin lukudi ba sa ci, kuma ba
sa barin wani yaci.
Rowar
Wayau, ko ta Zamani : Bayan
wannan jerin na marowata, sai kuma jerin masu wayau, ko kuma waɗanda suka koya. Tabbas
akwai wasu mutanen da babu mai cin ko tsinkensu. A mafi yawan waɗannan mutane, rowarsu daga
rana tsaka suka fara, a dalilin zamantakewa da wasu al’ummomi.
Babu
shakka, yin mu’amala da wasu mutane kan yi tasiri matuƙa a ɗabi’unsu, dole ne sai wani ya ɗauki na wani. Turawa sun kawo mana ɗabi’un boko kuma sun koya
mana wasu daga cikin ɗabi’unsu. Akwai ‘yan boko daga cikinsu wasu sun ɗauki wayau da rowa. Shi a
tunanin wani ɗan bokon yana ganin rashin dabara ne tara iyali da ‘ya’ya da yawa.
Haka kuma a wurin wasu almubazzaranci ne ka dinga bayar da wani abu naka ba
tare da an yi ma ka wata wahala ba. A tunanin waɗannan mutanen wayau tattali ne ke sa shi yin rowa. Kuma shi ke sa
shi gudun zumunci.
ROWA A
MAHANGAR AL’ADAR BAHAUSHE
Rowa a
mahangar al’ada, ana iya cewa wata ɗabi’a ce mummuna. Wannan yasa gaba ɗaya al’adar Bahaushe
ta ƙyamaci rowa, da kuma marowaci. Tabbas marowaci ba shi da farin
jinni, ko kwarjini a cikin al’ummar Hausawa. Matuƙar aka
san mutum marowaci ne, a wani lokaci ko aure ya nema ba a ba shi. A mafi yawan
lokutta, hatta yin mu’amala ba kowa ke son yi da marowaci ba. Al’adar Bahaushe
ta camfa marowaci, shi yasa ko aurensa ba a son yi, ko kuma a auri ‘yarsa, don
gudun kar a haifi ɗa ya gado shi wajen rowa. Bisa dalilin cewa ruwan a cikin ɗabi’u da akan gada daga
uwa. Haka kuma an camfa kayan marowaci ba a ci ko da ya mutu wai don gudun kar
a ci ya yi wa mutane fatalwa.
Bisa
wannan dalili ne yasa idan marowaci ya mutu sai a kwashi kayansa a zuba a kogi
ruwa ya wuce da shi, ko kuma a kai gidan tururuwa a zuba, ko a zuba a suri
(gidan gara), ko a zubar a marabar hanya. Haka kuma, Bahaushe ya hana ɗauki yaro jariri ta baya,
don gudun kar ya yi rowa idan ya girma. Haka kuma an hana dukan yaro da bayan
hannu don kar ya yi rowa in ya girma.
Dangane
da munin rowa, Bahaushe ya yi imani cewa, idan mace na da cikin haihuwa ta roƙi wani abu, to a ba ta. Matuƙar ba a ba ta ba, za ta
haifi jariri da tabon rowa, wani baƙin abu da ya kan yi shaida
a jikin jaririn.
Haka
kuma, saboda camfa marowaci da Bahaushe ya yi, ya sanya idan har aka yi sa’a
marowacin ya baiwa wani mutum abu, sai a ce ya ɗinka laya da abin wai
maganin bakin mutane.
Bisa
al’adar Bahaushe, akan hana yaro roƙo tun yana ƙarami, don gudun kar a yi masa rowa ya ji haushi, saboda ana ƙyamar roƙo. Haka kuma akan hana shi
yin rowa musamman ga yara ‘yan’uwansa, don tsoron kar ya tashi da ita.
Bahaushe
ya ɗauki rowa
na ƙara talauci ko hana arziƙi. Haka kuma kyauta
na ƙara arziƙi kuma tana korar talauci.
Bisa wannan ne har akan ce:
“Allah
Kai mana arziƙin cin dusar sa, kar Ka ba mu arziƙin cin tsabar doki a jaka”.
Bahaushe
na nufin idan aka kawo wa sa abinci kamar dusa, da ya sanya baki zai ci, sai
ya ɗaga baki
saboda ya kori ƙuda, a dalilin haka sai ya zubar da dusar ƙadangarun su samu, kaji su samu.
Game
da cin tsabar doki a jaka kuwa, idan aka zuba masa tsaba a cikin wata jaka aka
maƙala masa, haka zai cinye ko da ƙwaya ɗaya ba za ta faɗi ba, balle wani ya samu.
Fassarar
cin dusarsa, shi ne mai arziƙi mai kyauta, shi kuwa cin
tsabar doki a jaka shi ne mai arziƙi marowaci.
WASU
SUNAYE DA AKAN KIRA ROWA DA MAROWACI
Bahaushe
kan kira rowa ko marowaci a sakaye, watau ya yi ma ta kinaya, a inda zai ƙi ambaton rowa ko marowaci kai tsaye. Wannan kan zama wata
matashiya, ko hannunka mai sanda, ko nasiha. A wani lokaci kuma ya kan zama
nuna azanci ne, ko gwanintar harshe. Kamar haka: Ƙurmusu, ko mirsisi, ko ka ci-ka-hana- kowa, ko Ɗantsako samu ka ƙi dangi, ko ƙwanƙiro, ko Tauri, ko Matsolo, ko Maƙeƙe da sauransu.
ROWA A
ADABIN BAHAUSHE.
An sami
jirwayen rowa a adabin Bahaushe, ma’ana ta yi naso a dukkan rassan adabi na
baka da rubutacce. Domin an sami karin magana, almara, tatsuniya, barkwanci, waƙar baka. Haka kuma a rubutacce akwai littattafai da aka yi kamar
zube, da wasan kwaikwayo,da rubutacciyar waƙa, kamar
matsalolin attajiri, uwar gulma, ka ƙara karatu da sauransu.
ROWA A
KARIN MAGANA
1. Ido ga na
wani ƙuda ka ci naka.
2. Mai kwaɗayi shi ya san gidan mai
rowa.
3. Laifin
yaro ƙyuya, laifin babba rowa.
4. Ci-naka
in ci nawa ba rowa ba ne (sai dai mugun zama ne).
5. Kowa ya
ci baƙon gidansa.
6. Haka ya
fi, kunun mai rowa ya ɓare a tsanya.
7. Rowa
kamar ɗan yaye.
8. Cin
tsabar doki a jaka.
9. Na-hana
sarkin rowa.
10. Zumbuli
kakan marowata.
11. Cin kayan
marowaci sai ɓarawo ko gobara.
12. Da ka ci
ka rage, gara ya kwana a rirriƙe.
13. Ɗantsako samu ka ƙi dangi.
14. Ba nawa
ba ne, masomin rowa.
15. Za ka ci?
Tayin marowata.
16. Sabon
salo, wai kaza ta ji shiƙar dare.
17. Ba
gaskiya, awo a ɗaka.
18. Inuwar
giginya na nesa kasha ki.
19. Cin goron
marowaci, sai dai a ji ƙanshin.
20. Baka son
a ba wani sai kai.
21. Na san
baka ci, riga kafin mai rowa.
22. Ni ma ba
zai isheni ba.
23. A sammun,
in sammaka sammu ta kama ni?
24. Ƙanƙan dangi maganin masu kwaɗai.
25. Kowa yaci
shi kaɗai, zai
mutu shi kaɗai.
26. Ko ƙanshi, wai mairowa na dafa dambu.
27. Wane
furar danƙo ne baya ɓamɓaro.
ROWA
A LABARUN BAKA
LABARIN
SARKIN ROWA DA SARKIN KWAƊAYI.
Akwai
wasu bayin Allah su biyu, watau sarkin rowa da sarkin kwaɗayi. Waɗannan bayin Allah, kowa na
taƙama da matsayinsa, saboda haka wata harka ta haɗa su. Wata rana sarkin kwaɗayi ya tafi gidan sarkin
rowa. Da zuwansa sai ya yi sallama, to ashe sarkin rowa yana cin abinci, sai ya
turo matarsa ta ce ba ya gidan ya yi tafiya. Sarkin kwaɗayi ya ce to sai jira shi
har ya dawo. Matar ta ce ai ba yau zai dawo ba, sarkin kwaɗayi ya ce ai ko gobe ni ina
nan saboda ina jin ƙanshin abinci daga nan.
LABARIN
SARKIN ROWA:
Akwai
wani sarkin rowa, saboda tsananin rowa sai ya ɗaurawa akushinsa (kwanon
abinci) igiya. Idan ya fito ƙofar gida yana cin abinci.
Da zarar ya ji an yi sallama, sai amsa da cewa amin aikas salamattu ja. Ita
kuma matar da zarar ta ji haka, sai ta ja igiya watau ta janye kwanon abincin
zuwa gida.
LABARIN
NA-HANA SARKIN ROWA
Akwai
wani mutum saboda tsabar rowa babu mai cin komai nasa. Wata rana ya dawo kiwo
awaki, to ashe ya manta da wata tukunyarsa ta miya bai ɗora saman rumfa ba. Haka
kawai sai wata akuya daga awakinsa ta sanya kanta a cikin tukunyar, sai kanta
ya maƙale. Na-hana ya yi iyakar ƙoƙarinsa ya fitar da kan akuyar nan ya kasa. Dole ya kira mahauta
suka sayi akuya, su yanka su cire masa tukunyar. Kash abin ka da tsautsayi sai
tukunya ta fashe. Na-hana ya yi baƙin cikin asara biyu da ya
yi. Da farko ga sayar da akuya arha, ga kuma tukunya ta fashe.
ALMARAR ƊANFULANI DA KAƊO.
Wata rana
an yi wa Ɗanfulani haihuwa, ranar suna sai ya gayyaci Kaɗo zuwa taron suna. Gari ya
waye Kaɗo ya
shirya ta nufi Ruga, don amsa gayyata. Bayan an yi taro an sanya wa jariri
suna, aka yi shagali aka watse. Ɗanfulani bai ba Kaɗo komai ba, sai ya ɗauko ƙahonsa, wanda aka yanka ya ce da Kaɗo gashi ka yi tururu (Ƙahon hura). Kaɗo ya karɓa ya yi godiya, bai nuna ya
damu ko ɓacin rai ba. Ashe Kaɗo ya yi alƙawarin sai ya rama. Haka
kurum, wata rana sai Kaɗo ya shirya abinci mai kyau kuma da daɗi.
ALMARAR ƊANKAMA.
Ɗankama na cikin makaɗan ban dariya, wanda shi
kuma duk kiɗan da zai
yi ko waƙa ba ya wuce abinci. Haka kuma, an san shi da raha, da wayau, da
rowa. Duk da yake Bahaushe ya san haka, amma dai yana da farin jini a wurin
jama’a. Akwai wata almara wadda aka ce matarsa ta ɗauko yayen yaro. To
ashe Ɗankama bai so ba, saboda haka sai ya tsiri wasu maganganu masu
kama da karatu ko waƙa, a zaune sai aka ji yana cewa: “Kowa ya y\o yaye ya yo awo, in
bai awo ba ya mai sasa. Ma’ana shi ne tunda matarsa ta yi yo yaye to yo awon
hatsi (ta kawo abinci) in kuwa bata yi awo ba ta mayar da yaron.
ƊANKAMA DA AGOLA
Wata rana
ne Ɗankama ya auro wata mata mai ‘ya’ya uku. Duk da yake Ɗankama bai som su amma sai ya ɓoye bai nuna ba. Kwaram sai matar ta haifar masa yaro namiji.
Domin tsabar wayau da kuma rowa, sai ya cigaba da sawo waina guda uku. Ko da
yaro ya girma sai ya sawo waina guda uku ya raba wa agololin nan guda uku, idan
uwar ta yi magana sai ya ce to kowa ya raba wainarsa biyu ya ba yaron rabi, shi
kuma ya ci rabi. A ƙarshen al’amari sai yaron
ya tashi da waina ɗaya da rabi, a inda su kuma agola sun tashi da rabin waina.
ƊANKAMA DA AGOLA.
Wani Ɗankama ne ya auro mata, to tana da ɗa, shi kuwa Ɗankama saboda rowa sannan kuma ga wayau, sai ya ce ai tare za su
ci abinci. Kullum sai an kawo masa tuwo sai ya zabga ya ji a gaban yaro. Da
zarar yaro ya yi loma, ɗaya sai ya ce ruwa, sai Ɗankama ya ba shi ruwa ana
yin haka har ya cinye tuwo, ya bar yaron.
ƊANKAMA DA BAƘIN ABOKAI.
Wata
rana Ɗankama ya yi baƙin abokai. Maimakon ya
ajiyesu a gida, sai ya kai su can nesa da gida, ya tsaresu da hira. Zuwa can
sai Ɗankama ya daidaici an gama abinci, sai ya ce zai tafi a yi masa faɗa. Domin rowa sai ya ce, in
sun ji shiru to ana yi masu faɗa kar su shigo, amma in suka ji hayaniya to su shigo an gama yi
masa faɗa. A
nan Ɗankama ya yi wayon rowa ne, saboda idan ana cin abinci ba a yin
surutu, sai dai a yi shiru. Idan kuwa ka ji ana hayaniya to an ƙoshi ne.
JIRWAYEN
RANA A WAƘOƘIN BAKA
Haƙiƙa mawaƙan baka da dama an samu naso ko jirwayen rowa a waƙoƙinsu daban-daban:
Salihu
Jan Kiɗi Gusau waƙar Bubakar Ɗan Shehu Bakadire cewa yayi:
Jagora: Wane ya
tsinkan bisa hanya,
Yana ta ɓoyo ban zo gunka ba.
Mai idon jakkai rowa yakai.
Salihu
Jan Kiɗi Gusau waƙar Ɗan Nagwamatse Gigo, cewa ya yi:
Jagora: Ɗan Nagwamatse Gigo,
koma shiri daidai don
batun.
Namijin Kutu mai ɗan kai,
Bana ya ɗauko ƙarya.
Su wane ba a da kyauta.
Sai rowa sai ƙarya,
Sai batun ƙwalama in an sanka asha gara.
Mamman
Duka Makaɗin Goge, cewa yayi:
Jagora: Muna gani
mutane.
Iri-iri a duniya.
Waɗansu na da kyauta.
Waɗansu nada rowa.
Mai arziƙin da baya kyauta.
Allah Ya maida shege dila.
Habibu
Sakarci Mai Kukuma cewa yayi:
Jagora: Ku duba wane
fa shi bai ba mu ba, ya hana ba mu,
Shi an ce ya yi roƙo ya ƙi mu je gida mu rufa talle
Sani
Sabulu Kanoma, cewa yayi:
Jagora: An ce waƙa akwai zunubi,
An ce roƙo akwai zunubi,
To mai rowa ladansa
nawa?
Ibrahim
Narambaɗa:
Jagora: Mutum ka hana
ma abu nai,
Allah in yat tashi
baka, baka yakai,
Baya bin shawarar
kowa.
Ɗanƙwairo a waƙar ‘Yan Doton Tsafe, cewa
yayi:
Jagora: Ga wani ɗansarki mai rowa,
ya kulle kwabo
yana ɓoyo.
To ba rowan mai kiɗin turu,
in dan mu a raka
ajihu.
Ɗanƙwairo a waƙar Na Amadu Baƙon Dole shi ya kashe wargi
Ali
mutanen tsafe sun ce
kai Ɗanbaki ba ka sararta.
Tun da fa baka
kyauta,
kuma ya cika dogo gemu.
Ɗanƙwairo a waƙar matawallen Adamawa:
Jagora: Naɗinka ya yi kyawu kwairanga,
kana da mutane ‘yan
kirki,
ba mutanen banza ba,
duka suna kwazan
kyauta,
wane ɗai ab bai kyauta,
mai idanun raƙuma.
Ɗanƙwairo Maradun cewa ya yi:
Jagora: Da mai kyauta
da mai rowa,
Ko can ba su zama daidai
ba.
Ɗanƙwairo a waƙar Turakin Kano:
Jagora: Zaman duniya
daɗe haka
yake,
Ga wani yace bai buƙatarka,
Bai iya ‘yamma abi
nai,
Ga wani can na murmna
ka zo yaganka,
Wai don yag ga abin
da yai ma.
Alhaji
Mamman Shata a waƙar Bakandamiya cewa ya yi:
Jagora: Wanda yake
son yai mana rowa
Allah bashi abin yin rowar,
In yai rowar mu ji zafi.
Iayakar ta dai mutum ya yi
rowar.
Ba ya hana mu shiga
aljanna.
Malam Ibrahim Ɗanmani Mai caji Ɓukur cewa ya yi:
Jagora: Wani na
sha’awar ya ba mu,
Wani na sha’awar ya soke,
kai da kake sha’awar ka
soke,
Gobe idan Allah ya kai mu,
Ka sayo ƙiri ka kai mu kwata.
Ɗan Anace Gandi cewa ya yi:
Jagora: Ga wani ya
samu ‘yan kwababen ƙauye,
Kuma ya koma yana gudun
‘ya’yan dangi,
Mata kwankiro ɓoye abinka ba a saon komai
naka.
Haba kwankiro ɓoye abin ka ba a saon komai
naka.
Waƙar Daɓe:
Yau mai rowa tana daɓe-daɓe.
Ta ba ku tuwo.
Ba ta ba mu ba.
Ta ba ku fura.
Ba ta ba mu ba.
Ta ba ku kunu.
Ba ta ba mu ba.
Balle goro
Ba ta ba mu ba
Yau mai rowa tana daɓe
Yau mai rowa tana daɓe.
JIRWAYEN
ROWA A BARKWANCI.
Akwai
wasan barkwanci da kanawa suke yi wa zage-zagi da cewa sun cika rowa. Kamar
yadda su kan ce wai zagezagi na yin tuwonsu laɓaɓa ba kauri don kar baƙonsu ya ci da yawa. Haka
kuma kanawa na cewa zagezagi cikin ɗaki suke cin tuwo kusa da ƙafar
gadon matarsu saboda tsananin rowa. A inda su kuma suke zagezagi suke rama wa
da cewa idan Bakano ya yi baƙo sai ya tura masa ƙashi. Idan suna cin tuwo sai Bakano ya rinƙa cewa ci ƙashi baƙo. Da zarar ya tsaya cin ƙashi, sai
ya cinye tuwonsa. Haka kuma Katsinawa na cewa Nupawa inda Ɗan A’i goyon A’i mai kyautar keke amma a kaɗa ƙararawa a dawo da keken.
A
al’adance Bahaushe na zargin wasu rukunin mutane da ɗabi’ar rowa. Waɗannan mutane kuwa sun haɗa da makwaɗaici, da maroƙi, da malami, shi ma bai son ya bayar amma yana son a bashi, shi
ma malami yana son a bashi a matsayin kyauta, ko sadaka, amma shi kafin a ɓamɓari kwabo a hannunsa yana
da wuya. Masunci shi ma ana zarginsa da rowa kamar wata maganar azanci da ake
cewa: Sannu Ɗan su, yace ko ƙaya, ban roƙa ba, ya ce na hana, abin na faɗa ne yace dambe ne. Haka shi ma Bafade ana jingina masa rowa
saboda sabo da karɓa amma ba zai bayar ba. Bazawara ita ma akwai rowa sai dai a ba
ta.
A
zamanance kuwa, ana zargin mutane uku da rowa, ma’aikacin banki, da malami
(Teacher), da ‘yan sanda. Bisa lura da ɗab i’un wasu mutanen zamani da Bahaushe yayi waɗanda ba a iya cin abin
hannunsu, sai aka raba su gwargwadon tsarin rayuwarsu. Dangane da ma’aikacin
banki, ana danganta rowarsa da abubuwa kamar haka, da farko ya fi kwa sanin
darajar kuɗi, kuma
ya fi kowa iya tattali, don haka duk kwabonsa da zai fitar sai ya yi lissafin
wane alfanu zai samu. A irin wannan ƙididdigar ne zai hana shi
ya ba wani kwabonsa, a wani lokaci shi kansa ma bai ci ba. Game da malami kuwa,
shi dai ana ganin ko dai ƙarancin abin ko kuma babu,
ko kuma ƙonannen wayau. Domin shi ana ganin albashinsa bai bai kai ya komo
ba, sannan ga ɗan karan ba shi ana biyansa albashi zai wuce a bashi kuma ya koma
cin wane sabon bashin. Bahaushe kuma yace idan ruwa yazo kogi bai tarar da wani
ba, ba ya zama, kuma an ce main a sama ya ci bare jefo min? Shi kuma ɗansanda ana ganin saboda
karɓa a
hannun mutane yake kawo haka. Domin shi a ɗabi’arsa, yana son idan ka zo wurinsa ka bashi, wannan ya yi
daidai da karin maganar Bahaushe mai cewa: “Allah Ya kawo baƙon da zai cida ɗangari, ko ai wane ciki ne shi baya bayarwa sai dai a bashi. ”
ROWA A
ZAMANANCE
Rowa a
mahangar zamani, ko kuma a zamanance, ana iya cewa wata hanya ce, ko salon a
tattali. B ahaushe na kallon mutanen zamani sun ɓullo da wata dabara ta yin
rowa, koda yake su suna gani tsabar wayau ne. Bisa dalilin sauye-sauye da
zamani ya kawo waɗanda suka shafi rayuwa, tabbas mutanen zamani suna ganin rowa wata
hanyar dabara ce, ko wayau na tattali. Wannan baya rasa nasaba da sauyin tunani
da Bahaushen wannan zamani ya samu. Babu shakka tsarin rayuwa ta sauya, don
haka dole ne ɗabi’u su sauya. Bahaushen da yana ƙaunar ɗan’uwansa kuna son abin duniya bai rufe masa ido ba. A inda shi
kuma Bahaushen yanzun yake ganin kowa yayi ta kansa, sannan kuma tsabar son
abin duniya ya mamaye zukatan mu. Domin a tunaniun yau, gani ake yawaita kyauta
kamar ɓarnar
dukiya ce watau rashin tattali ne.
A wannan
zaamani akwai wasu da ke ganin cewa, wayonsu ko ƙoƙarinsu ko kuma iya tattali ke tara musu arziƙi. Wannan irin tunanin ne ke sanya wasu su riƙe kuɗI ƙamƙam, a wani lokaci ma su ba su ci ba, ba su bari wani yaci ba. Duk
da yake mun san cewa rayuwar wasu ta dogara ne daga samun albashi a ƙarshen wata. To amma bai isa ya zama hujja da zasu zama marowata
ba. Dalili kuwa shi ne, ai a da Bahaushe noma da kiwo da kasuwanci kaɗai yake yi, amma bai san
irin wannan baƙar rowar ba. Dalilin da yasa haka kuwa shi ne akwai wadatar zuci,
sannan kuma Allah Ya sanya wa abin albarka.
A zamanin
da, Bahaushe har so yake yi wani ɗan uwa ya ziyarceshi, a inda suke kwana murna ana hirar zumunci.
Yanzu kuwa zamani ya hana wannan, sai aka kopma daga ƙwauri sai gwiwa. Bahaushen yanzu bai son a zo wurinsa, su kuma
‘yan uwa basa son zuwa.
Bahaushe
manomi a da idan kaka ta yi, sai ka iske yana bayar da kyautar hatsi ga maƙwabta da danginsa. Ba komai ya kawo wannan ba, sai ƙaunar juna da son yin kyauta. Yanzu kuwa abin bahaka yake ba.
Bahaushen zamani ya fi gane ya tattare abinsa a ɗaki ya kulle.
SAUYIN
YANAYIN ZAMANTAKEWA
Haƙiƙa zamantakewar Bahaushe ta samun sauye-sauye masu tarin yawa ta
fuskoki da dama. Wannan kuwa ya kama ne tun daga yanayin hulɗarsu da jama’a da kuma
yanayin tsarin muhallinsa. Da farko in muka ɗauki hulɗarsa da sauran jama’a muna iya cewa an samu tangarɗa. Bisa dalilin cewa
Bahaushe da aka sani a zamanin da, to yanzu ba shi ne. Kamar yadda Bahaushe
yake a da an sanshi da tsare amana, da faɗar gaskiya, da zumunci, da kyautatawa abokan hulɗa, ga kyauta da taimakon
juna da sauransu.
Dangane
da fuska ta biyu kuwa, sai mu ce hatta tsarin muhalli wanda aka san Bahaushe na
dashi a wannan zamanin ya sauya. A zamanin da, an san Bahaushe da zaman gandu,
a inda za a iske gida ɗaya yana ƙunshe da kaka, da uba tare
da uwa, ga ɗa tare da matansa har da ‘ya’yansa, watau jikoki kenan. Haka kuma
ga ‘ya’yan riƙo da agola wani lokacin har da barori.
Bahaushe
yace zama da maɗaukin kanwa shi ne kawo farin kai. Tabbas wannan Karin Magana iat
ta faru ga rayuwar Bahaushe a yau. Dalili kuwa shi ne, mu’amulla da baƙin al’ummu da Bahaushe yayi shi ya haifar da sauyin tunanin
Bahaushe. Wannan sauyin tunanin da Bahaushe ya samu, to shi ne ya sauya hulɗa ko mu’amular gaba ɗaya. Babbar illar da
Bahaushe ya samu a irin wannan baƙon tunani kuwa, shi ne
tsabar son abin duniya, wanda kuma shi ya haifar masa da baƙar rowa.
Dangane
da ɗayar
fuskar kuma, ana iya cewa tsarin muhallin da Bahaushe ya gada a yau kusan ya
ragu ko ya watse. To shi ma ba a rasa wasu dalilai da suka haifar da hakan ba.
zamani ya kawo aikin gwamnati dana gwamnati dana kamfanoni da sauransu. A inda
za a ɗauki
mutum daga garinsu ko mahaifarsa a kais hi wani garin na daban, inda bai san
kowa ba. Bisa wannan kuma, gashi yayi nisa da danginsa, ziyara ma kanta
sai ƙarshen mako ya tafi a gurguje saboda lokacin taƙaitacce ne, ba abin daya kawo wanna sai zamani. Hatta tsarin
gidajen ya sauya daga zaman gandu zuwa daga ni sai ‘ya’ya na ko daga ƙauri da gwiwa. Ko ba rowan wani da wani wai mahaukaci yai baƙo. Tsari irin na zamanin da wanda za a iske maƙwabci da maƙwabci ana hira da juna ko
ciyayya. A yanziu wannan ya kau, saboda sauyin zamani. Bisa dalilin sauyin
zamani a yanzu ana iya samun maƙwabci da maƙwabci su yi wata da watanni ba a gaisa ba. An kewaye gida da
doguwar Katanga babu mai kula wani, saboda wai kowa na da ‘yanci don kar wani
ya shiga ‘yancin wani. Haƙiƙa wannan tunanin shi ya haifar da wata rayuwa ta ci-naka in ci
nawa ba rowa ba ne. To amma Bahaushe ya ce ai mugun zaman ne.
ROWAR
ZAMANI HALI KO HALI?
Idan muka
dubi rowa a wannan zamani ana iya cewa akwai alamar tambaya akan mutanen yanzu.
An san cewa wasu mutanen babu ce ke hana su yin kyauta, to amma kuma wasu bayan
rowa ce, suna da halin wadata, sai dai su ƙi yi. Don
haka sai mu ce abin hali ne watau ya zama ɗabi’ar su.
Bisa
nazarin yadda abubuwa ka kaiwa suna komowa, sai muce rowar wannan zamani hali
ne na ɗabi’a
wanda muka koya da rana tsaka daga wurin baƙin
al’ummu. Babban dalili kuwa shi ne, a yanzu wannan zamani akwai wadata ba laifi
a kan zaman da. Duk da haka sai aka fi samun marowata fiye da da.
A wannan
zamani, saboda rowa ta zama ɗabi’ar mu, sai a iske ɗa na yi ma mahaifansa rowa. Wani abin mamaki da ban haushi sai a
iske har yana da wata ƙaryar da zai yi don ya kare
kansa. A tunaninsa wai shi nan wayau ne, saboda rowa ta zama halinsa, ba wai
hali ne baya da shi ba.
A ƙarshe, in muka dubi bayanin da ya gabata, sai mu ce ga hali na
wadata ga arziƙin, amma hali na ɗabi’a ya hana yin kyauta. Haka kuma an ce wani abu ke jawo wani, a
dalilin wannan baƙar rowar da Bahaushen wannan zamani ya ƙirƙiro, sai kuma aka samu ɓullowa ko yawaitar marasa gaskiya, da makwaɗaita, da maroƙa, da ‘yan damfara, da sauran ɓata gari. Waɗanda a zamanin da, basu kai haka ba. Don haka, rowar nan bata da
fa’ida, dole ne mu sake hali, mu rungumi juna.
Bahaushe
yace zamani ba kan ji magani, ko zamani riga ce, ko mai laya kiyayi mai zamani.
Dukkan waɗannan
Karin maganganu suna nufin ƙarfi ko tasirin da zamani
kan iya yi wa kowa da komai.
Babu
shakka, zamani ya zo da al’adu bisa dalilin da Bahaushe yayi da wasu baƙin al’ummu. A kan wannan sai mu kowa ya tuna bara bai ji daɗin bana ba. Abin nufi a
nan, shi ne, waɗannan baƙin al’adu ko ɗabi’u da suka iske
Bahaushe, sai suka yi naso a rayuwarsa gaba ɗaya. Ana iya cewa wasu cikin gaggawa Bahaushe ya ɗauke, wasu kuma sannu a
hankali, sai dai kawai Bahaushe ya wayi gari ya ga yana aikata su.
Tabbas,
zamani ya iske Bahaushe da wasu kyawawan ɗabi’u, kuma na-san barka waɗanda tilas ne mutum ya yaba dasu. Kash! Sai dai kuma zamanin ya yi
wa wasu daga cikin ɗabi’u korar kare saboda tasirin boko ko rayuwar Turawa. Ga wasu
guda goma waɗanda
zamani ya kora, ko bai kore su duka ba, a yau masu aikatasu sun yi ɗaranci matuƙa. Waɗannan ɗabi’u kuwa, su ne: -
1. Ciyayya.
2. Kawo ƙwarya.
3. Marka-marka.
4. Ɗauki.
5. Riƙo ko goyo.
6. Zumunci.
7. Ziyara.
8. Gudummuwa.
9. Aikin
gayya.
10. Zaman
gandu.
1. Ciyayya: Wata ɗabi’a ce wadda Bahaushe ya gaje tat un iyaye da kakanni, amma
yanzu ta ɓace. A zamanin da, kusan dukkan magidanci yakan fito da
abinci ƙofar gida, don su haɗu su ci abinci ƙofar gida. A inda shi ma maƙwabcinsa zai fito da nasa abinci, don su haɗu su ci abincin nan tare.
Wannan ɗabi’a
ba ƙaramin taimako take yi ba, saboda tana kyautata zamantakewar maƙwabtaka, a inda aka zama tamkar ‘yan uwa na jini. Haka kuma yana
taimakon wanda bai samu yin girki ba, ko kuma mara mata (Tuzuru, ko gwauro ko
baƙo), sannan da almajirai wani lokaci har da mahaukata kai har da
dabbobi.
Kwaram
sai zamani yayi fatali ko jifar matacciyar mage da wannan ɗabi’a. a yau mafi yawa kowa
yana cin abincinsa ne a cikin gida ko ɗaki a inda ake ajiye masa a kula da shi kaɗai. A yanzu zamani ya koya
mana ci naka in ci nawa ba rowa bane, to amma Bahaushe yace mugun zama ne.
2. Kawo Ƙwarya: Wannan ita ma wata ɗabi’a ce wadda Bahaushe ya
guje ta tun iyaye da kakanni. Waɗanda aka fi sani da wannan su ne mata a gidaje. Ɗabi’ar kawo ƙwarya na nufin idan mace ta
yi girki wata ta dafa wani nau’in abinci saɓani na yau da kullum, kamar abincin marmari ko sanyin baki, sai
tace da ‘yar uwan zamanta cewa kawo ƙwarya don ta zuba mata.
Wannan ya fi faruwa ne ga matan daba kishiyoyi ba, a wani lokacin har yakan haɗa da maƙwabta.
Wani abin
sha’awa shi ne, ko da abincin ba yawa sai a ce a bai wa yara. Ana cikin wannan
tafiya ta rayuwa mai daɗi ta cuɗanni in cuɗaka. Kwatsam sai zamani ya kori wannan ɗabi’a, inda ya kawo rayuwar
ba-ni in baka, kar ka-ba-ni. Haƙiƙa wannan rayuwa ta ɓata zumunci ga ɗan karan rowa da ta koya wa Bahaushe.
3. Marka-Marka: Wannan kuma irin taimako ne na kyauta da kan wakana tsakanin aboki
da aboki, watau magidanta aminan juna. Wanna kuwa yana faruwa ne da damuna idan
ta kai tsakiya, ana tsululin damuwa ruwa sama ruwa ƙasa. Abin da ke faruwa shi ne, idan an wayi gari ana ruwan sama
wanda ya kai har rana ana yi, ya hana mutane fita ko’ina. Ruwan saman ya takura
kowa. Sai magidanci ya nufi gidan amininsa. Da zarar ya isa gidan sai ya yi
sallama, idan mai gidan ya amsa, sai abokin yace da maigidan kai wane
marka-marka. Shi kuma mai gidan sai ya amsa da cewa cire rama. Mai gidan ya
gane cewa ruwa ya hana abokin fita neman abinci a gida. Ita kuma amsar daya
mayar abokin na nufin ya zagaya bayan gida ko bayan ɗaki ya tsinki ganyaen rama.
Da zarar mai gidan ya faɗi haka, to sai ya tashi ya shiga rumbun hatsi ya ɗauro masa gwanuma (rabin
dami) ko na dawa ko na gero. Bayan abokin ya tsinko ganyen ramar, sai mai gida
ya ba shi wannan rabin damin nan ya tafi gida a sarrafa a yi abinci dambu ko
fate da sauransu. Dangane da wannan ɗabi’a a yau zamani ya kore ta, sai ta zama tarihi. Domin kuwa ana
iya cewazai yi wuya a samu mafi yawan gidajenmu. Zamani ya sanya ana fyaɗe hatsi tun a gona a ɗaure a buhuna, sannan ga baƙar rowa da zamani ya kawo saboda son abin duniya. Kowa gani yake
tattalinsa shi zai sa yayi arziƙi.
4. Ɗauki: Wannan ita ma wata ɗabi’a ce wadda Bahaushe ya gaje tat un iyaye da kakanni. Ita ma
wannan ta keɓanta ne
ga mata kurum, saboda a cikin gida ake yenta. Ɗabi’ar ɗauki na nufin idan an samu wani abinci wanda ba mai yawa ba,
musamman abincin marmari kamar nama, ko kwaɗon ganye, ko dai wani baƙon ci-maka. A mafi yawa
uwar gida ce kan samu faifai, ko matankaɗi, ko tire, sai ta gutsuttsura a karkasa gwargwadon yawan mutane
ko yaran gida. Bayan an kasa a faifai, to sai a kira kowa ya ɗauki kasonsa, ko kuma a
kai ƙofar ɗaki a ce ɗauki, kasonki dana yaronki ko yaranki. Wannan na ƙara soyayya a tsakanin yara, a irin haka ne ake cewa kowa ya ɗauki na gabansa. Sauyin
zamani yazo yayi fatali da wannan ɗabi’a, a mafi yawa sai dai a yi ƙurmusu watau a cinye a ɗaki. Don haka wannan wani salon rowa ne da zaman ya kawo.
Riƙo Ko Goyo: Riƙo ko goyo shi ne wani mutum ya riƙe ɗan wani tun daga yarinta har zuwa girma, in
yaro namiji ne, a wasu wurarern a kan mayar da shi wurin ubansa, in kuwa mace
ce, da zarar yarinya ta isa aure, to daga nan shike n
an, riƙo ko goyo ya ƙare ke nan, riƙo ko goyo ya kan gudana a
tsakanin ɗan'uwa da ɗan uwa ko kuma aboki da aboki, ana yinshi ne,
saboda wasu dalilai da suka haɗa da: - Zumunci,
da haihuwa, da ƙauna, da tausayi, da moriya.
Zumunci: Da zarar an ambaci kalmar zumunci a al’ummar Hausawa,
babu abin da zai zo masu a zuciya da wuce wata dangantaka ta musamman dake
tsakanin mutum da mutum wadda ta shafi dukkan fannonin rayuwa. Zumunci wata alaƙa ko dangantaka,ko
nasaba,ko jituwa ce dake ƙulluwa ko haɗa mutane daban-daban kan
harkokin da suka shafi rayuwa ta yau da kullum.
Nau’o’in Zumunci: Al’amarin zumunci a al’ummar Hausawa abu ne
da za’a ce yana da rassa ko yana yaɗuwa fiye da kowace ƙabila ko al’ummar dake maƙwabtaka da Hausawa.
1. Zumunci na jini (haihuwa ko zuriyya): - Wannan kan ƙunshi mutane irin su uwa da
uba, 'ya'yan tsatso, 'yan uwa, 'yan uba, kawu, inna, gwaggo, baffa, yaya, ƙani da sauransu.
2. Zumunci na aure (auratayya): - wannan kan shafi mutane
irin su miji da mata, suruki, suruka, agola, ɗan riƙo.
3. Zumunci na zamantakewa (maƙwabtaka): - wannan kan
shafi mutane a wurin maƙwabtaka na gida, ko kasuwa, ko gona, da sauransu.
4. Zumunci na mu'amulla (sana'a, moriya) : - wannan kan
shafi mutane masu sana'a iri ɗaya ko kuma abokan ciniki,
barantaka, almajiiri, ɗalibta da sauransu.
5. Zumunci na ra'ayi (tunani): - wannan kan shafi mutane da
suka yi tarayya a ra'ayi kamar addini, ko siyasa, ko kulob, ko wasanni da
sauransu.
5. Ziyara: Na nufin ka tafi gari, ko giudan wani da nufin ku gaisa da dalili,
ko babu. Ana iya cewa wannan al’ada ko ba a daina to Bahaushe ya rage yenta
matuƙa. Wannan kuwa baya rasa dalili na sauyin zamani. Domin zamani ya
kawo abubuwan sufuri ba za a yi tafiya sai da kuɗin mota, a wani lokaci da ‘yar tsaraba da matafiyi zai riƙa don yara. Haka shi kuma mai masauki zai tanaji abin da zai yi wa
baƙonsa hidima da kuma abin sallama. To yanzu son abin duniya da
ganin gari dab aƙar rowa sun hana ziyartar juna. Kowa sai ya fake da babu, ana iya
samun ‘yan uwa na jini sun yi shekara da shekaru ba ziyarci ba. Ba wai waɗanda suke garuruwa
daban-daban ba, a a hatta waɗanda suke gari ɗaya.
Gudunmowa: Wannan wata hanya ce ta taimakawa juna wajen yi ma mutum wani
hasafi na musamman a lokacin wani sha'ani kamar na aure ko suna, don a zamanto
taimakwa wanda abin ya shafa. Sau da yawa a kan taimaka da hatsi, ko kuɗi, wani lokaci ma har da
tufafi da dai duk wani abu mai amfani. Akwai kuma gudunmuwa da akan yi wa waɗanda suka yi gobara, ko
kuma waɗanda aka
yi wa sata.
Gayya: Wannan ma wata hanya ce ta taimakawa juna, amma ta wajen aiki.
Aikin gayya ba a yin shi sai da dalili, kamar rashin lafiya ko kuma wata larura
ta musamman. A kan taimakawa mutum a aikin gona, ko kuma aikin gida da
sauransu. 'Yan uwa da abokan arziƙi na unguwa su ne su kan
taru su taimaka.
Baya ga
taimakawa da a kan yi wa juna kuma, sarki ko mai unguwa ya kan yi gayya don a
rage masa aiki. Idan sarki ya kira gayya, to kusan ba wanda ba zai amsa wannan
kira ba.
Mata su
ma suna yin gayya irin ta su, misali in an yi sabon ɗaki za a yi daɓe. Duk wanda ya yi gayya,
to dole ne ya yi abincin gayya saboda jama'ar da suka zo aiki su ci.
6. Aikin
Gayya: Wannan shi ma wani aiki ne
da ake taimakawa juna ta hanyar haɗuwa a yi aikin taimakon kai da kai, ko kuma idan wani bashi da
lafiya ya kasa gyara gonarsa sai a yi gayyar ‘yan uwa da abokan arziƙi da ya kamata a tafi a nome masa kyauta. A irin wannan har akan
yi fura da kunu ko tuwon gayya don ma’aikata su ci ko su sha. A nan ne ma har
aka samu karin magana mai cewa kowa ya sha furar gayya dole ya yi aiki. Shata
Katsina sai ya ce ka sha furar mutane kace zaka yi kwance a a ku tashi gumi na
naka ci. Zamani ya zo yayi ɓarin makauniya da wannan ɗabi’a. A yau komai sai dai kuɗinka ya baka ko yasa a yi maka. Bahaushe ya tabbatar da wannan a
inda ya ƙirƙira wata magana mai cewa: “Nasara ya hana aikin banza”. Ko kuma:
“Kowa tashi ta fisshe shi”.
7. Zaman
Gandu: Wani zama ne da ake yi, a
inda za a iske kaka, da ubada da uwa, da ɗa da matarsa, da jikoki duk a gida ɗaya ga ɗakin wannan ga na wannan. A
irin wannan zama ana kasancewa komai tare ake yi. Da damuna za a tafi gona ta
mai gida da ake kira gonar gandu a wurin aiki. Bayan an dawo, maigida ne zai
ciyar da kowa, ko da kuwa ɗansa yana da mata da ‘ya’ya, dole shi ne zai ciyar da su. Irin
wannan rayuwa tana da daɗi matuƙa, domin ana taimaka wa juna a harkokin rayuwa ta fuskoki da yawa.
Ba a farga ba, zamani ya zo ya yi tafiyar ya ji da wannan ɗabi’a. Musamman samuwar
aikin gwamnati, a inda za a ɗauki mutum ya koma wani garin da ba nasa ba, ko kuma ko yana gari,
sai ka iske ya ware gidansa shi kaɗai wai kar a dame shi. A nan ne ake rayuwa irin ta daga ƙwauri sai gwiwa, ko kuma mu ce ba rowan wani da wani wai mahaukaci
ya yi baƙo. baa bin da wannan yake koyarwa sai ‘yar karen rowa.
ILLOLI DA
ROWA KE HAIFARWA.
Tabbas
rowa kan haifar da illoli masu yawa waɗanda suka shafi shi kansa marowaci da kuma al’umma. Bisa lura da
bayanai da suka gabata, ana iya cewa ɗabi’ar rowan a cutar da mai yenta watau marowaci ko ya sani ko bai
sani ba. Da farko rowa ta haifar masa dabaƙin jini ko rashin kwarjini.
Rowa na tauye arziƙI na dukiya da na jama’a. rowa yanke zumunta, rowa hana samun
rabon lahira don tana tauye ma’auna (mizani). Rowa na kai mutum wuta, rowan a
nisanta mutum da Allah da kuma mutane. Rowa na sanya zargi.
Bayan ga
illolin da suka shafi marowaci shi kaɗai, to haka kuma akwai illolin da suka shafi al’ummar da marowacin
yake cikinsu. Da farko dai rowan a haifra da ƙiyayya ko gaba a tsakanin mawadata marowata da talakawa mabuƙata. Rowa na haifar da mummunar alaƙar
zamantakewa, misali maƙwabci marowaci da kuma maƙwabcinsa, rowan a haifar da rashin girmama na gaba ko shugaba in
marowaci ne, kamar malami da almajiransa, mai gida da iyalansa. Rowa na haifar
da rayuwar zaman ‘yar marina a al’umma, watau rashin haɗin kai. Domin kowa na ƙoƙarin tashi-ta-fissheshi, wanda yake irin wannan irin rayuwa na
wargaza al’umma.
ROWA A
MAHANGAR ADDININ MUSULUNCI.
Al’amarin
rowa a mahangar addinin Musulunci, ana iya cewa ciwo ne mummuna. Bisa dalilin
muninsa yasa Allah (S. W. T) Ya yi hani da yin rowa. A ɗaya ɓangaren, sai aka kwaɗaitar da yawaita kyauta
tare da bayyana fa’idojin da kyauta ke jawowa wanda ya yi ta. Akwai ayoyi da
yawa waɗanda aka
tsoratar da yin rowa, tare da nuna illolin da take jawo ma mai yenta, watau
marowaci. Bayan ayoyin Ƙur’ani kuma, nuna munin
rowa.
Tabbas
marowaci ne kaɗai bai yin kyauta, kuma baya bayar da sadaka sannan kuma ya hana
zakka.
Shari’ar
Musulunci ta sharɗanta wasu hukunce-hukunce don ladabtarwa, a inda ta yanke cewar a
ciyar ko a ‘yanta baiwa. Kamar wajen kaffarar azumin watan ramalana, inda aka
ce duk wanda ya karya azumi da gangar, sai ya yi azumi sittin, ko ya ‘yanta
baiwa, ko ya ciyar da mutane sittin. Wannan ciyarwa alama c eta kyauta wadda
yake kishiyar row ace, don haka Musulunci baya son Musulmi ya zama marowaci.
Bayan wannan kuma sai kaffarar rantsuwa, nan ma ko dai mutum ya yi azumin kwana
uku, ko ya ciyar da mutane goma abincin da zasu ƙoshi.
Bayan
wannan tsari kuma, sai ɓangaren da aka umarci Musulmai das u yi kyauta, su bada zakka, da
sadaka, da waƙaf. Dukkan waɗannan suna korar ko kawar da rowa a tsakanin Musulmai.
A ƙarshe, ga wasu hujjoji kaɗan don a sanya su a matsayin madogara. Waɗannan hujjoji sun ƙunshi ayoyin Ƙur’ani da wasu hadisai, da
kuma maganganun wasu bayin Allah. Gaba ɗayansu sun yi nuni ne ga munin rowa a Musulunce da kuma cewa rowa
ciwo ce ga mahangar Musulunci.
Suratul
Isra’il aya ta 29. Kar ka maƙe hannunka ka zama
marowaci, kar kuma ka zama almubazzari don kar ka zama abin zargi, ko ka
talauce.
A cikin
Suratul Laili. da Suratul Ma’uun, da cikin Suratul Hadid.
Jabir bin
Abdullahi ya ruwaito. An kira rowa da cewar mummunan ciwo ne Sahihul Bukhari:
5. 666.
Hindu Bint
Utba matar Abu Sufyan ta kira shi da marowaci (Matsolo). Sahihul Bukhari:
9. 291.
Amru
Bin Shu’aib ya ruwaito Annabi yace bayan dawowa daga yaƙin Hunain ba zaku same ni marowaci ba. Muwaɗɗa: 21. 22.
Abu
Huraira ya ruwaito Annabi yace mai kyauta yana kusa da Allah, kuma kusa da
Aljannah, kuma kusa da mutane. Amma marowaci kuwa yana nesa da Allah, kuma yana
kusa da wuta. Jahili wanda yake yin kyauta ya fi kusa da Allah fiye da mai
ibada marowaci. Tirmizi: 580:
Abu Dhar
yace Annabi (SAW) yace babban marowaci a cikin ku shi ne wanda yaƙI yi min salati a lokacin da aka ambaci sunana. Fiƙhis Sunnah: 138:
Aliyu Ɗan Abi Ɗalib yace: Malami saboda
iliminsa yana iya zama mai kyauta. A inda mai dukiya saboda son dukiyarsa yana
iya zama marowaci.
Mai rowa
da mai gori ba zai shiga Aljannah ba. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.
A
Musulunci, an fifita mai bayar da kyauta a kan wanda yake karɓa. kamar wani hadisi day
ace: Hannun sama (Mai bayarwa) yafi hannun ƙasa (mai
karɓa)
daraja. Duk wannan ana nuna kyawun kyauta fiye da rowa da kuma kwaɗayi.
SHAWARWARI
Bisa lura
da bayanai da suka gabata, ana iya cewa an gani kuma an gamsu. Don haka akwai
buƙatar a ɗauki matakin kare kai daga faɗawa cikin tarkon rowa. Ya dace mu bai wa juna shawarar neman
mafita. Ga wasu shawarwari waɗanda ya kamata mu ɗauka su ne: Yaƙar zuciya, da kuma shaiɗan, mu sanya wadatar zuci,
da kyautata tauhidi, tare da neman rabon gobe ƙiyama, sannan mu kyautata zumunci, a ƙarshe mu rage son abin duniya.
KAMMALAWA:
A ƙarshe wannan takarda, ta tsakuro wasu al’amura da suka shafi
zamantakewarmu. Mun ga wasu abubuwa da ɗabi’ar rowa ta jawo wa al’umma a wannan zamanin. Haka kuma mun ga
yadda ɗabi’ar
rowa ta gurɓata
halayen wasu daga cikinmu. Bayan wannan kuma, ga masu rauni daga cikinmu,
sannan da marayunmu waɗanda aka sake su a igiyar ruwa. Irin waɗannan marayun ana samunsu a
maza da mata, duk da yake ga dangin uwa da uba. Duk da yake ga sauran jama’a
masu hannu da shuni, suna tare da su, amma kowa ta kansa yake yi. Watau rayuwar
daga ni sai ɗa na, ko daga ƙwauri sai gwiwa. Don haka
akwai bukatar, kowanne mutum ya dawo da hankalinsa jikinsa ya taimakawa maraya
da marainiya. Ina fatan al’umma su fahimci inda wannan muƙala ta sanya gaba. Manufar ita ce mutum ya san shi wane ne, kuma
mene ne matsayinsa? Don ya sani shi kansa yana iya mutuwa, saboda haka me yake
nufi da ‘ya’yansa?.
Mun riga
mun ji irin illolin da wannan muguwar ɗabi’a ta yi mana, ta fuskoki marasa iyaka kuma ta kusurwoyi daban
daban. Domin haka muna fata mu koma ga halaye da muka gada tun iyaye da
kakanni, na kyautatawa junanmu, Allah Ya tsare mu Ya bamu ikon gyarawa mu
gujewa rowa amin. Assalamu alaikum
MANAZARTA.
Alhassan
H. D (1982) Zaman Hausawa. Islamic Publication Bureau, Lagos.
Bunza A.
M. (2006) Gadon feɗe al’ada. Tiwel Nigeria Limited Surulere, Lagos.
Banbale
M. B. (1994) Kukan Kurciya. Ibramud Nigeria Limited, Zaria.
Ɗangambo A. (1984) Rabe-Raben adabin Hausa da Muhimmancinsa ga
rayuwar Hausawa. Triunph Publication Kano.
Ɗangambo A. (1983) Kitsen
Rogo. Triunph Publication Kano..
Ɗahiru B (2007) Tafsirin
Watan Ramadan. Rediyo Najeriya Kaduna.
Imam A.
(1937) Magana Jar ice na 1, da 2, da 3. Northern Nigerian Publication Company,
Zaria.
Madauci
I. (1963) Al’adun Hausawa. Northern Nigerian Publication Company, Zaria.
Sadiya G.
Y. (2005) Talauci Hauka ne? Super Prints Press, Kano.
Williams
B. (1979) Human Design. Harvard University Printed USA.
Yaro Y.
I. (1971) Tatsunniyoyi da Wasanni. Oxford University Press, Ibadan.
Zindani
A. A. (2000) Human Development. Muslim World League Printing Press. Saudi
Arabia.
Sarki H.
A (2000) Zuwan Musulunci a Afirka da shigowarsu Ƙasar Hausa. G. A. Computer Centre. Ikere – Ekiti, Ekiti State.
Ɗanfodiyo S. U. (2002) Faɗakar da ‘Yan’uwa a kan halayyar Ƙasar Sudan. (Fassara) Muhammad Mode Shuni. C. I. S Usman Ɗanfodiyo University, Sokoto.
Rowa (Hali, Wayau, Ko Ciwo?): Tsokaci A Kan Dabi’ar Rowa A Rayuwar Bahaushe Jiya Da Yau
TAKARDAR
DA AKA GABATAR A TARON TALLAFAWA MARAYU A GARIN KUDAN A ZAUREN TARO (TOWN HALL)
DAKE LIKORO ROAD SABON GARIN KUDAN. RANAR ASABAR 5 GA YULI 2014, 8 GA RAMADAN
DA ƘARFE 09: 00 NA SAFE
ROWA (HALI, WAYAU, KO CIWO?): TSOKACI A KAN ƊABI’AR ROWA A RAYUWAR BAHAUSHE JIYA DA YAU
DAGA:
MU’AZU
SA’ADU MUHAMMAD
DEPARTMENT
OF NIGERIAN LANGUAGES
JIGAWA
STATE UNIVERSITY KAFIN HAUSA
WANDA A
KA GABATAR A TARON TALLAFAWA MARAYU A GARIN KUDAN A ZAUREN TARO (TOWN HALL)

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.