Ticker

6/recent/ticker-posts

Kyauta (Dabi’a Ko Baiwa Ko Wauta?): Tsokaci A Kan Dabi’ar Kyauta A Rayuwar Bahaushe Jiya Da Yau

WANDA A KA GABATAR A TARON TALLAFAWA MARAYU A GARIN KUDAN A ZAUREN TARO (TOWN HALL) DAKE LIKORO ROAD SABON GARIN KUDAN. RANAR ASABAR 27 GA YUNI 2015, 10 GA RAMADAN 1436 DA ƘARFE 10: 00 NA SAFE.

KYAUTA (ƊABI’A KO BAIWA KO WAUTA?): TSOKACI A KAN ƊABI’AR KYAUTA A RAYUWAR BAHAUSHE JIYA DA YAU

DAGA:

DR. MU’AZU SA’ADU MUHAMMAD
 DEPARTMENT OF NIGERIAN LANGUAGES
 SULE LAMIƊO UNIVERSITY KAFIN HAUSA, JIGAWA STATE

GABATARWA

Da sunan Allah Mai rahama, Mai jinƙai, Mai kowa, Mai komai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga shugaban ma’aika, Annabi Muhammadu (S. A. W). Wannan muƙala, na da ƙudurin yin tsokaci a kan ɗabi’ar kyauta da matsayinta a rayuwar Bahaushe jiya da kuma yau. Haka kuma tare da fito da irin sauye-sauye da rayuwar Bahaushe ta samu dangane da ɗabi’ar kyauta. Bayan haka, za mu dubi dalilan da suka kawo waɗannan sauye-sauye. Ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba wajen nuna fa’idojin kyauta da kuma sakamakon da takan haifar ga mai yin kyauta da kuma al’umma. A wannan nazari, zan dubi kyauta ta ƙusurwowi uku kamar haka: A mahangar Al’adar Bahaushe, da Mahangar Addinin Musulunci, sannan ta Mahangar Zamani. Bisa wannan dalili ne yasa na yi wa wannan maƙalar take da “Kyauta (Ɗabi’a ko Baiwa ko Wauta ?)”. Na kawo taken a matsayin tambaya ne, don ya ba mu damar lalubo amsa. Tare da fatan mai karatu ko saurare zai gano ko zaƙulo amsar a ƙarshen maƙalar, don samun mafita ko a fid da jaki a duma.

FASHIN BAƘI

Ma’anar Kyauta: Na nufin wani aiki ne wanda mutum kan yi ta hanyar bayar, ko miƙa wani abin hannunsa (kuɗi ko tufafi ko abinci ko dabba, ko wani abu) zuwa ga wani. Ta hanyar miƙawa hannu da hannu, ko kuma ta hanyar aikawa da ɗan aike. Akan kira mai yin kyauta namiji da karimi, mace kuma ma’abuciyar kyauta, idan jam’i ne kuma a kirasu masu karamci.

 Ɗabi’a: Na nufin hali wanda aka san mutum da shi wanda yake aikatawa yau da kullum ya zamar masa jiki.

Baiwa: Na nufin wata ni’ima wadda Allah Ya yi wa mutum. Wannan ni’imar kuma mai ita kan yi amfani da ita a kowane lokaci, ta ko wacce fuska idan wani al’amari ya taso ya taimaka wa waninsa don samun mafita.

Wauta: Na nufin raunin hankali wanda mai shi yakan yi amfani da shi. A wani lokaci akan kira wauta da hauka.

KYAUTA A MAHANGAR AL’ADAR BAHAUSHE

Kyauta a mahangar al’ada, ana iya cewa wata ɗabi’a ce muhimmiya. Wannan yasa gaba ɗaya al’adar Bahaushe take ƙaunar kyauta da kuma mai kyauta(karimi). Tabbas mutum mai kyauta na da farin jini da kwarjini da mutunci a cikin al’ummar Hausawa. Matuƙar aka san mutum maikyauta ne, a wani lokaci har ƙoƙarin auren ‘ya’yansa ake yi, ko kuma idan shi ya nema a ba shi. A mafi yawan lokutta, kowa kan so yin ma’ammala da shi. Al’adar Bahaushe ta camfa auren maikyauta, shi yasa ake kwaɗayin aurensa ko kuma a auri ‘yarsa, don fatan a haifi ɗa ya gado shi wajen kyauta. Bisa dalilin cewa kyauta na cikin ɗabi’u da akan gada daga uwa. Haka nan kuma akan iya koyon ɗabi’ar kyauta daga abokin zama ko maƙwabci. Bahaushe ya ce: “zama da maɗaukin kanwa shi ke kawo farin kai”. Bisa wannan dalilai ne yasa Bahaushe ya ɗauki kyauta a matsayin ɗabi’a.

Kyauta dai ita ce ka bai wa wani mutum alheri ko hasafi na kuɗi, tufafi, abinci ko dabba, kai da dai sauransu. Kyauta kan ƙara ƙulla zumunci ta inda zaka samu ɗa ya yi wa iyayensa, ko yaya ya yi wa ƙaninsa, ko aboki ya yi wa abokinsa, ko maƙwabci da maƙwabci, duk kuwa inda kyauta ta ratsa ko ta gitta, to lallai zaka samu ƙauna a tsakani. Akwai wasu kalmomi da akan faɗa in za a yi kyauta, kamar ungo ko amshi ko karɓi ko ɗebi ko ɗauki ko bar shi da sauransu.

 Bahaushe ya ɗauki kyauta da muhimmanci, don kuwa Bahaushe ya ɗauketa kamar wata igiya ce da ke ƙulla zumunci ko kuma ƙara wa babba girma, da ƙauna da kwar jini ga sauran jama’a.

Kyauta kan ƙara wa babba girma don kuwa har Karin Magana Bahaushe ya yi game da kyauta: “Laifin yaro ƙyuya laifin babba rowa” ko “Yaba kyauta tukwici” da dai makamantansu, misalin inda kyauta ke ƙara wa mutum girma, shi ne inda sarki ko shugaba zai bai wa talakansa ko wani mutum na ƙasa da shi kyauta, ko miji ya yi wa matarsa kyauta.

 Akwai inda kyauta kan zama don tausayawa a inda zaka ga mutum na cikin matsayi na buƙatar taimako, amma fa ya sha bamban da sadaka. Bayan wannan kuma, sai inda kyauta kan zama abin neman fada, kamar dai cin hanci ko toshiyar baki ko kuma rashawa. Ko da yake akan yi mata lulluɓi a ce mata goro, a nan kuwa ta kan taso ne a inda wani mutum yake neman wani abu a wurin wani mutum mai muƙami ko kuma yana da shari’a ko dai makamantansu.

IRE-IREN KYAUTUTTUKA. DALILIN YIN SU.

a. Hasafi - Don ciwo ko haka kurum.

b. Toshi - Don samartaka ko zawarci.

c. Barka da Sallah - Don bikin Sallah, Ranar Sallah.

d. Cin hanci. - Don neman wata alfarma.

e. Maula - Don neman girma.

f. Tukwici - Don nuna godiyar wata kyauta.

g. La’ada - Don shaidar ciniki.

h. Shara - Don cikar shekara tsakanin abokan wasa.

i. Gudunmuwa - Taimako don wani sha’ani.

j. Gyara - Don sayayya (Ciniki).

k. Tsaraba - Don tafiya.

l. Gara - Don aure.

m. Ɓantiya - Don haihuwa.

n. Ka-fi-mai- kora – Don kishiya.

o. Dannar ƙirji – Don kishiya

p. Kayan faɗar kishiya – Don kishiya

MUTANEN DA KYAUTUTTUKAN KAN SHAFE SU.

a) Hasafi - Aboki ko Ɗan’uwa ko Maƙwabci.

b) Toshi - Masoya ko Budurwa ko Saurayi ko Bazawara.

c) Barka da Sallah - ‘Yan’uwa ko Yara ko ‘Yammata.

d) Cin hanci. - Shugaba ko Mai Mulki ko Talakawa.

e) Maula - Maroƙa ko ‘Yanraraka ko Masu kuɗi.

f) Tukwici - Manya da Yara.

g) La’ada - ‘Yan kasuwa, sauran jama’a.

h) Shara - Abokan wasa ko ‘Yan’uwa.

i) Gudunmuwa - ‘Yan’uwa ko Abokai ko Mata ko Maza.

j) Gyara - Ma’auna, Masu kayan miya da sauransu.

q. Tsaraba - Baƙo da mai masauki.

r. Gara - Iyaye kan yi wa ‘yarsu in an yi mata aure.

s. Ɓantiya - Miji kan yi wa matarsa a haihuwar farko.

t. Ka-fi-mai- kora Iyaye kan yi wa ‘yarsu in za a yi mata kishiya.

u. Dannar ƙirji – Dangi kan yi wa mace in za a yi mata kishiya.

v. Kayan faɗar kishiya – Miji kan yi wa matarsa in za a yi mata kishiya.

Ga wasu dabaru na yin kyauta cikin hikima guda bakwai waɗanda Bahaushe ya gada, tun iyaye da kakanni, ko da yake a yau masu aikatasu sun yi ƙaranci matuƙa. Waɗannan ɗabi’u kuwa, su ne: -

1. Ciyayya.

2. Kawo ƙwarya.

3. Marka-marka.

4. Ɗauki.

5. Ziyara.

6. Gudummuwa.

7. Aikin gayya.

1. Ciyayya: Wata ɗabi’a ce wadda Bahaushe ya gaje ta tun iyaye da kakanni. A zamanin da, kusan dukkan magidanci yakan fito da abinci ƙofar gida, don su haɗu su ci abinci ƙofar gida. A inda shi ma maƙwabcinsa zai fito da nasa abinci, don su haɗu su ci abincin nan tare. Wannan ɗabi’a ba ƙaramin taimako take yi ba, saboda tana kyautata zamantakewar maƙwabtaka, a inda aka zama tamkar ‘yan uwa na jini. Haka kuma yana taimakon wanda bai samu yin girki ba, ko kuma mara mata (Tuzuru, ko gwauro ko baƙo), sannan da almajirai wani lokaci har da mahaukata kai har da dabbobi.

Kawo Ƙwarya: Wannan ita ma wata ɗabi’a ce wadda Bahaushe ya guje ta tun iyaye da kakanni. Waɗanda aka fi sani da wannan su ne mata a gidaje. Ɗabi’ar kawo ƙwarya na nufin idan mace ta yi girki wata ta dafa wani nau’in abinci saɓani na yau da kullum, kamar abincin marmari ko sanyin baki, sai tace da ‘yar uwan zamanta cewa kawo ƙwarya don ta zuba mata. Wannan ya fi faruwa ne ga matan daba kishiyoyi ba, a wani lokacin har yakan haɗa da maƙwabta.

Wani abin sha’awa shi ne, ko da abincin ba yawa sai a ce a bai wa yara. Ana cikin wannan tafiya ta rayuwa mai daɗi ta cuɗanni in cuɗaka.

Marka-Marka: Wannan kuma irin taimako ne na kyauta dakan wakana tsakanin aboki da aboki, watau magidanta aminan juna. Wanna kuwa yana faruwa ne da damuna idan ta kai tsakiya, ana tsululin damuwa ruwa sama ruwa ƙasa. Abin da ke faruwa shi ne, idan an wayi gari ana ruwan sama wanda ya kai har rana ana yi, ya hana mutane fita ko’ina. Ruwan saman ya takura kowa. Sai magidanci ya nufi gidan amininsa. Da zarar ya isa gidan sai ya yi sallama, idan mai gidan ya amsa, sai abokin yace da maigidan kai wane marka-marka. Shi kuma mai gidan sai ya amsa da cewa cire rama. Mai gidan ya gane cewa ruwa ya hana abokin fita neman abinci a gida. Ita kuma amsar daya mayar abokin na nufin ya zagaya bayan gida ko bayan ɗaki ya tsinki ganyaen rama. Da zarar mai gidan ya faɗi haka, to sai ya tashi ya shiga rumbun hatsi ya ɗauro masa gwanuma (rabin dami) ko na dawa ko na gero. Bayan abokin ya tsinko ganyen ramar, sai mai gida ya ba shi wannan rabin damin nan ya tafi gida a sarrafa a yi abinci dambu ko fate da sauransu.

Ɗauki: Wannan ita ma wata ɗabi’a ce wadda Bahaushe ya gaje tat un iyaye da kakanni. Ita ma wannan ta keɓanta ne ga mata kurum, saboda a cikin gida ake yenta. Ɗabi’ar ɗauki na nufin idan an samu wani abinci wanda ba mai yawa ba, musamman abincin marmari kamar nama, ko kwaɗon ganye, ko dai wani baƙon ci-maka. A mafi yawa uwar gida ce kan samu faifai, ko matankaɗi, ko tire, sai ta gutsuttsura a karkasa gwargwadon yawan mutane ko yaran gida. Bayan an kasa a faifai, to sai a kira kowa ya ɗauki kasonsa, ko kuma a kai ƙofar ɗaki a ce ɗauki, kasonki dana yaronki ko yaranki. Wannan na ƙara soyayya a tsakanin yara, a irin haka ne ake cewa kowa ya ɗauki na gabansa.

Ziyara: Na nufin ka tafi gari, ko giudan wani da nufin ku gaisa da dalili, ko babu. a wani lokaci da ‘yar tsaraba da matafiyi zai riƙa don yara. Haka shi kuma mai masauki zai tanaji abin da zai yi wa baƙonsa hidima da kuma abin sallama. Alhaji Shata Katsina na cewa:

 Farau-farau farar tabarma,

 Farin cikin mai baƙunta

Gudunmowa: Wannan wata hanya ce ta taimakawa juna wajen yi ma mutum wani hasafi(kyauta) na musamman a lokacin wani sha'anin biki kamar na aure ko suna, don a zamanto taimakwa wanda abin ya shafa. Sau da yawa a kan taimaka da hatsi, ko kuɗi, wani lokaci ma har da tufafi da dai duk wani abu mai amfani. Akwai kuma gudunmuwa da akan yi wa waɗanda suka yi gobara, ko kuma waɗanda aka yi wa sata.

Gayya: Wannan ma wata hanya ce ta kyautar ƙarfi wadda ake taimakawa juna, amma ta wajen aiki. A maimakon ya biya kuɗi, sai a yi masa kyauta. Aikin gayya ba a yin shi sai da dalili, kamar rashin lafiya ko kuma wata larura ta musamman. A kan taimakawa mutum a aikin gona, ko kuma aikin gida da sauransu. 'Yan uwa da abokan arziƙi na unguwa su ne su kan taru su taimaka.

Baya ga taimakawa da akan yi wa juna kuma, sarki ko mai unguwa yakan yi gayya don a rage masa aiki. Idan sarki ya kira gayya, to kusan ba wanda ba zai amsa wannan kira ba.

Mata su ma suna yin gayya irin ta su, misali in an yi sabon ɗaki za a yi daɓe. Duk wanda ya yi gayya, to dole ne ya yi abincin gayya saboda jama'ar da suka zo aiki su ci.

Aikin Gayya: Wannan shi ma wani aiki ne da ake taimakawa juna ta hanyar haɗuwa a yi aikin taimakon kai da kai, ko kuma idan wani bashi da lafiya ya kasa gyara gonarsa sai a yi gayyar ‘yan uwa da abokan arziƙi da ya kamata a tafi a nome masa kyauta. A irin wannan har akan yi fura da kunu ko tuwon gayya don ma’aikata su ci ko su sha. A nan ne ma har aka samu karin magana mai cewa kowa ya sha furar gayya dole ya yi aiki. Shata Katsina, sai ya ce:

 ka sha furar mutane ?

 ka ce zaka yi kwance ?

 a a ku tashi gumi na nake ci.

 Kyaututtukan Manoma.

Ga wasu dabaru yin kyauta cikin hikima guda bakwai waɗanda suka keɓanta manoma tsakaninsu masu yi masu aiki. Bahaushe ya gada, tun iyaye da kakanni, ko da yake a yau masu aikatasu sun yi ƙaranci. Waɗannan ɗabi’u kuwa, su ne: -

Galla: kyauta ce wadda manomi kan bai wa mai gonar da ya ba shi aron gona(hatsi ko kuɗi).

Tumu: kyautar sabon gero ce wadda manomi kan bai wa wani a farkon kaka don gasa a ci.

Ta-gashi: kyautar gyaɗa ce wadda manomi kan bai wa waɗanda suka yi masa aikin gona, ban da ladan kuɗi ya biyasu.

Ta-fate: kyautar masara ce wadda manomi kan bai wa waɗanda suka yi masa aikin ɓarar masara a gona, ban da ladan kuɗi ya biyasu.

 Na-kwaɗo: kyautar barkono ce wadda manomi kan bai wa waɗanda suka yi masa aikin cire barkono a gona, ban da ladan kuɗi ya biyasu.

Na-miya: kyautar tumatur ce wadda manomi kan bai wa waɗanda suka yi masa aikin cire tumatur a gona, ban da ladan kuɗi ya biyasu.

Kan mage: kyautar auduga ce wadda manomi kan bai wa waɗanda suka yi masa aikin cire auduga a gona, ban da ladan kuɗi ya biyasu.

Tarke: kyautar dawa ce mai datti da akan kira rairaye da ƙasa-ƙasa, wadda manomi kan bar wa matan da suka yi masa aikin sussukar dawa a gona, ban da ladan kuɗi da ya biyasu.

FA’IDOJI DA KYAUTA KE HAIFARWA.

Tabbas ɗabi’ar kyauta kan haifar da wasu fa’idoji masu yawa, waɗanda suka shafi shi kansa mai yin kyautar da kuma al’umma, sannan wanda aka yi wa kyautar. Bisa lura da bayanai da suka gabata, ana iya cewa ɗabi’ar kyauta na amfanar da mai yinta watau karimi ko ya sani ko bai sani ba. Da farko kyauta takan haifar masa da farin jini da kwarjini. Kyauta na bunƙasa arziƙi na dukiya da na jama’a. Bayan haka kyauta na ƙarfafa zumunta, kyauta na sanya samun rabon lahira don tana nauyaya ma’auna (mizani). Kyauta na kai mutum aljanna, kyauta na nisanta mutum daga wuta, kyauta na kusantar da mutum zuwa ga Allah da kuma mutane. Kyauta na kawar da zargi, kuma tana sanya ƙauna.

Baya ga fa’idojin da suka shafi mai yin kyauta shi kaɗai, to haka kuma akwai fa’idojin da suka shafi al’ummar da mai yin kyauta yake cikinsu. Da farko dai kyauta na haifar da ƙauna da kawar gaba ko hassada a tsakanin mawadata masu kyauta da talakawa mabuƙata. Kyauta na haifar da kyakkyawar alaƙar zamantakewa, misali maƙwabci maikyauta da kuma maƙwabcinsa, kyauta na haifar da girmamawa ga babba ko shugaba in mai bayarwa ne, kamar malami da almajiransa, mai gida da iyalansa. Kyauta na kawar da rayuwar zaman ‘yar marina a al’umma, watau rashin haɗin kai.

Dangane da wanda aka yi wa kyauta kuwa, fa’idojin da yakan samu suna da yawa kaɗan daga ciki sun haɗa da natsuwa da kwanciyar hankali, kuɓuta daga halin ƙaƙa-ni-ka-yi da sauransu.

Jirwayen Kyauta a Adabin Baka:

Karin Magana a kan kyauta.

1. Wanda bai iya kyauta ba, ya ba mai ba shi.

2. Kar ka yi mana kyautar Ɗankama, (ƙwaryar da ta je ta dawo).

3. Kyautar koma - ɗaka kai kuka.

4. Kyautar ƙuru.

5. Ba a hana ma ba da rago fata.

6. Sarfa gandun baiwa.

7. Ungo na ƙara ƙauna.

8. Maikyauta surukin mai amsa.

9. Da babu gara ba daɗi.

10. Hasafin loma ta kaɓakin tsiya.

11. Gutsuren goro ya fi babban dutse.

12. Cin tuwon kishiya ramako.

13. Idan baki ya ci dole ido yai kunya.

14. Faɗawa mai zuciya biki ba mai dukiya ba.

15. Yaro da ungo a ke ƙara masoya.

Kyauta A Waƙoƙin Baka

Alhaji Amadu Doka Mai kukuma Kaduna a waƙarsa ta komai zaka yi rinƙa yin tunani, cewa ya yi:

 Ashe kyauta na ƙure mai waƙa,

 Waƙa na ƙure kyauta,

 Nace riga an haɗo da jamfarta,

 Na biɗi hula an haɗo da takalma,

 Na biɗi wando har agogo an ba ni,

 To ka ga kyautarka ta ƙure ni,

 Har ban san abin da zan faɗi ba.

Alhaji Amadu Doka Mai kukuma Kaduna a waƙarsa ta Matarka Iya Sa’idu jikan Alƙali, cewa ya yi:

 Matan aure iri-iri ne gangata,

 Wata mata a ba ta fan ɗari don tai komai,

 Sannan ga tuwonta mai nama ta ci,

 Sannan kuma ga zaninta ta ɗaura sabo,

 Wata kan ahu tai ta shan dukan banza.

Alhaji Mamman Shata Katsina a waƙarsa ta Gaisheka Na ‘yan leman Liman, cewa ya yi:

 Liman yake mai kwana kyauta,

 Ko’ina ya ganan yay i min kyauta,

 Suka ce mini Alhaji mai shata,

 Haka nan yake bai san rowa ba.

Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun a waƙarsa ta Sarkin Muri, cewa ya yi:

 Ran assabar sai nij je gidan Sarki,

 Ɗanƙwairoya ba ka tu tauzan,

 Daudun kiɗI da shi da Marafa,

 ko wane ga babbar rigatai,

 Mu biyu sai yab ba mu tu tauzan,

 Yaran Ɗanƙwairo goma sha uku,

 kowa riga da tu hondiren naira,

 kuɗin ƙwairo da na yara,

 sun zama fayif tauzan da siks hondiren naira.

KYAUTA A MAHANGAR ADDININ MUSULUNCI.

 Al’amarin kyauta a mahangar addinin Musulunci, ana iya cewa baiwa ce, kuma ibada ce muhimmiya. Bisa dalilin muhimmancinta yasa Allah (S. W. T) Ya yi ummarni da yin kyauta. A ɗaya ɓangaren, sai aka kwaɗaitar da yawaita kyauta tare da bayyana fa’idojin da kyauta ke jawowa wanda ya yi ta. Akwai ayoyi da yawa waɗanda aka tsoratar da yin rowa, tare da nuna illolin da take jawo ma mai yinta, watau marowaci. Bayan ayoyin Ƙur’ani kuma, akwai hadisai masu yawa da suka nuna muhimmancin kyauta. A musulunci an kira kyauta (bayarwa) da sunaye daban daban kamar: zakka da zakkatul fitir (zakkar kono) da imfaƙi(ciyarwa) da waƙaf (bayar da gida ko gona ko makaranta) da wasiyya da layya da hadaya da sauransu.

 Kyauta Da Sadaka ;

 Kyauta da Sadaka suna da kusanci da juna matuƙa don sun yi kama, sau da yawa abin dakan bambanta su ita ce niyya.

 Manzon Allah (SAW) yana karɓar kyauta, amma ba ya karɓar sadaka. Bukhari 3. 751.

 Manzon Allah (saw) ya tabbatar cewa kar a bai wa iyalan gidan Muhammad sadaka. Muslim ya riwaito.

 Abu Huraira ya ce: wata rana Hassan ya ɗauki ƙwayar dabino. Manzon Allah ya ce kai fito da shi ba ka san mu ba ma cin sadaka ba? Fiƙhus sunna 3. 73B

 An taɓa bai wa Barira sadakar nama, amma ta kawo wa Annabi (SAW), sai Annabi ya ce: ke sadaka a gareki mu kuma ya zama kyauta. Bukhari 2. 571.

 Daga Abu Huraira ya ce: Idan aka kawo abinci zuwa ga Manzo Allah(SAW), yakan tambaya cewa kyauta ko sadaka? Idan aka ce sadaka ce, sai ya ce Sahabbai su ci, amma in aka ce ktauta ce, sai ya ci tare da Sahabbai. 3. 750.

 Zakkah: Sadaka (kyauta) ce ta wajibi watau ita farilla ce, amma ga mai wadata.

 Sadaƙatul Jariya: Manzon Allah (SAW) ya ce: Idan mutum ya mutu dukkan ayyukansa sun yanke. In ban da ayyuka uku, sadaka mai gudana da ilmin da ya koyar ake aiki da shi, sai kuma natsattsen ɗa wanda zai rinƙa yi masa addu’a. Fiƙhus Sunna 104 A.

 Daga Anas Bin Malik ya ce: Duk wanda ya dasa bishiya ko ya shuka ɗan itace ya tsira ya yi ‘ya’ya, wani tsuntsu ko dabba ko mutum ya ci daga gareta. Wannan kamar sadaka ce mai gudana. Bukhari 3. 513

 Shari’ar Musulunci ta sharɗanta wasu hukunce-hukunce don ladabtarwa, a inda ta yanke cewar a ciyar da abinci (kyauta) ko a ‘yanta baiwa. Kamar wajen kaffarar azumin watan ramalana, inda aka ce duk wanda ya karya azumi da gangar, sai ya yi azumi sittin, ko ya ‘yanta baiwa, ko ya ciyar da mutane sittin. Wannan ciyarwa alama ce ta kyauta wadda yake kishiyar rowa ce, don haka Musulunci ba ya son Musulmi ya zama marowaci. Bayan wannan kuma sai kaffarar rantsuwa, nan ma ko dai mutum ya yi azumin kwana uku, ko ya ciyar da mutane goma abincin da zasu ƙoshi.

 Bayan wannan tsari kuma, sai ɓangaren da aka umarci Musulmai da su yi kyauta, su ba da zakka da sadaka da waƙafi. Dukkan waɗannan suna korar ko kawar da rowa a tsakanin Musulmai.

 Sada Zumunci Da Kyauta:

 Ana iya sada zumunci ta hanyar yin kyauta, zumuncin zai iya kasancewa naka ko na waninka. Bayan haka kuma zai iya faruwa a tsakanin mutane rayayyu (masu rai) da matattu (waɗanda suka rasu). Haka iyaye ko mata ko yayye da sauransu.

 “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam). Ya kasance ya rinƙa bayar da kyauta zuwa ga ƙawayen Khadija matarsa ta farko ko bayan da ta rasu. A’isha (R. A. ) ta riwaito cewa: “Ban taɓa jin kishin wata mata daga cikin matan Manzon Allah ba, kamar yadda nake kishin Khadija, duk da yake ban taɓa ganinta ba. Manzon Allah yakan yawan tuna ta tare da ambatonta, kuma in ya yanka rago yakan ɗebi naman ya bayar ya ce a kai wa wasu daga ƙawayen Khadija. Wata rana na taɓa ce masa ka damu da Khadija matuƙa, tamkar ba wata mace a faɗi duniyar nan sai Khadija. Yace: “ Khadija ta yi min komai a rayuwa wanda ba wani da ya yi min kamar haka, sannan daga gareta na samu ‘ya’ya”. Bukhari 5. 166.

Akwai wani bayani wanda ya faru a zamanin Sahabbai, inda Abdullahi Ibn Umar zai tafi aikin hajji. Suna cikin tafiya da jama’arsa, sai suka haɗu da wani Balaraben ƙauye. Abdullahi Ibn Umar nan da nan, sai ya ɗauki abin hawansa da jabba ya ba shi, sannan kuma ya girmamashi. Bayan sun rabu sai aka tambayi Ibn Umar game da wannan mutumin, sai Ibn Umar yace: “Mahaifin mutumin abokin Sayyidina Umar Bin Khaɗɗaf ne”. Ibn Umar ya ƙara da cewa: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “ku sadar da zumuncin da iyayenku suke yi suna raye ko bayan sun rasu”.

Kyauta Ga Maƙwabci:

 A’isha ta ce: “Ya Manzon Allah, ina da maƙwabta biyu wane zan bai wa kyauta daga cikinsu? Manzon Allah ya ce: “ki bai wa wanda ƙofarsa ta fi kusa da ke. Bukhari. 3. 767

A’isha (R. A. ) ta riwaito cewa: Manzon Allah ya yanka akuya ya rarrabar da naman, sai ya tambaya ko akwai abin da ya rage?A’isha ta ce saura karfata, sai Annabi ya ce nama na nan, karfata ce aka rasa. Tirmizi ya riwaito.

 Ladubban Kyauta a Musulunci:

Kyauta na da wasu ladubba waɗanda shari’a ta tsara don al’umma su kiyaye. Akwai na umarni da kuma na hani da na kwaɗaitarwa da na tsoratarwa da sauransu.

Abubuwa Da Suke Ɓata Kyauta Ko Sadaka

Akwai wasu abubuwa waɗanda mutum zai yi su ɓata masa kyauta ko sadakar da ya yi. Da farko akwai riya ko gori ko zobe ko tasau da sauransu.

Riya: na nufin ka yi wa mutum kyauta ko sadaka ba wanda ya sani, ka zo kana bayar da labari don a yaba maka. Tabbas riya na ɓata aiki komai yawansa.

Gori: na nufin ka yi wa mutum kyauta ko sadaka, amma daga baya ka rinƙa cewa, ashe ba na yi maka kaza da kaza ba? Haƙiƙa gori na ɓata kyauta ko sadaka saboda tana tozarta wanda aka yi wa. Wannan ya sa Manzon Allah ya hana, Allah (swt) Ya hana a cikin Alƙur’an a inda Yace: “kar ku ɓata sadakar ku da gori da zobe”

Zobe: na nufin ka yi wa mutum kyauta ko sadaka, amma daga baya ka ƙwace abin da ka bayar. Wannan shi ma shari’a ta hana, saboda ta haifar ƙiyayya a tsakanin wanda aka yi wa kyauta ko sadaka da wanda ya yi. Bisa kyakkyawar ɗabi’a duk wanda ya aikata wannan ana ɗaukarsa ƙaramin mutum. Bisa shari’a kuwa, shi ma wannan abin ƙyama ne. Akwai wani hadisi mai yin haka ya yi kama da kare. Domin kassre ya ke yin amai sannan daga baya yana dawo ya lashe abisa.

Tasau: na nufin mutum ya yi wa budurwa ko bazawara toshi (kyauta). Bayan ya yi mata toshi sai daga baya ya tayar da kyautar wato ya ƙwace. Bisa kyakkyawar ɗabi’a duk wanda ya aikata wannan ana ɗaukarsa ƙaramin mutum ma’ana mai ƙaranta. Duk wanda aka san shi wannan hali ba ya yin farin jini a gari. Bugu da ƙari ‘yanmata kan guje shi.

Raina Kyauta : A al’adance an hana mutum ya raina kyautar da aka yi masa, saboda Bahaushe ya ce: “maraina kaɗan ɓarawo ne”, ko “lomar hasafi ta fi kaɓakin tsiya” ko “da babu gara ba daɗi”.

Haka kuma ko a musulunce shari’a ta hana raina kyauta kamar a wani hadisi inda Abu huraira ya ce: Manzon Allah ya ce: “ya ku mata kar ɗaya daga cikin ku ta raina kyautar da ƙawarta ko maƙwabciyarta ko da kofatan akuya ne”. Bukhari 3. 740

Daga Abu huraira ya ce: Manzon Allah Ya ce: zan amsa gayyata walima ko da abincin kofaton akuya ne.

KYAUTAR DA MUSULUNCI KE KYAMA.

Abdullahi bn Umar da Abdullahi Abbas sun ruwaito cewa: Manzon Allah (SAW) haramun ne mutum ya bayar da kyauta ko sadaka, sannan daga baya ya zo ya ƙwace,sai tsakanin uba in y aba ɗansa. Duk wanda yayi kyauta ya koma mata ya zama kare mai yin amai ya dawo lashe. Abu Dauda 1571.

Abu umama ya ruwaito cewa: Manzon Allah y ace : duk wanda ya taimaki ɗan uwansa sannan ya karɓI wata kyauta daga gare shi to tinkari wata ƙofa daga ƙofofi riba (rashawa). 1573

Abdullahi bn Ammar bn As ya ce: Manzon Allah ya ce: ba a yarda ba mace ta yi kyauta da wani abu daga kayan mijinta ba, sai da izininsa. Abu Dauda 1575.

Nu’uman bn Bashir yace: Babansa ya tafi da shi wajen Manzon Allah, ya ce: Na baiwa ɗa na bawa, sai Manzon Allah ya tambaya ka bai wa sauran ‘ya’yanka kamar haka? Sai ya ce: a’a, Manzon Allah ya ce: karɓi kyautarka. Bukhari3. 759.

 A ƙarshe, ga wasu ƙarin hujjoji kaɗan don a sanya su a matsayin madogara. Waɗannan hujjoji sun ƙunshi ayoyin Ƙur’ani da wasu hadisai, da kuma maganganun wasu bayin Allah. Gaba ɗayansu sun yi nuni ne ga fa’idar bayarwa (kyauta ko sadaka ko zakka) a Musulunce da kuma cewa bayarwa ibada ce ga mahangar Musulunci. Bayan haka kuma baiwa ce domin kuwa sai wanda Allah Ya yarda da shi yake yin alheri.

An ambaci sadaka Suratul Baƙara aya ta 219, 270, 272, 274, 291, Ala’imrana aya ta 92, 134, Nisa’I aya ta 114, Tauba aya ta 60, 79, 103, Nur aya ta 56, Mujadala aya ta 12, 13,

An yi ummarnin yin sadaka Suratul Baƙara aya ta 271,

 An ambaci fa’idoji da falalar sadaka Suratul Baƙara aya ta 261, Anfal aya ta 60, Suratul Hadid aya ta18, Tagabun aya ta17.

 An tsoratar a kan ƙin yin sadaka Suratul Suratul Isra’il aya ta 28, ayoyi da surori masu yawa a Ƙur’ani mai girma :

 Suratul Isra’il aya ta 29. Kar ka maƙe hannunka ka zama marowaci, kar kuma ka zama almubazzari don kar ka zama abin zargi, ko ka talauce.

A cikin Suratul Laili. Da Suratul Ma’uun, da cikin Suratul Hadid.

Abu Huraira ya ruwaito Annabi ya ce: “mai kyauta yana kusa da Allah, kuma kusa da Aljannah, kuma kusa da mutane. Amma marowaci kuwa yana nesa da Allah, kuma yana kusa da wuta. Jahili wanda yake yin kyauta ya fi kusa da Allah fiye da mai ibada marowaci. Tirmizi: 580:

Aliyu Ɗan Abi Ɗalib yace: Malami saboda iliminsa yana iya zama mai kyauta. A inda mai dukiya saboda son dukiyarsa yana iya zama marowaci.

A Musulunci, an fifita mai bayar da kyauta a kan wanda yake karɓa. kamar wani hadisi day ace: Hannun sama (Mai bayarwa) yafi hannun ƙasa (mai karɓa) daraja. Duk wannan ana nuna kyawun kyauta fiye da rowa da kuma kwaɗayi.

 Ibn Abbas ya ce, Manzon Allah shi ne mafi alheri (Kyauta) a mutane. Ya fi yin kyauta a watan azumi, ya fi iska kyauta. 1. 1

Abdullahi Bin Amr ya ce, wani mutum ya tambayi Annabi cewa: Wane aiki ne ya fi a musulunci? Sai ya ce ka ciyar da talaka, sannan ka yi sallama ga wanda ka sani da wanda ba ka sani ba. Bukhari 1. 11.

KYAUTA A MAHANGAR ZAMANI.

Kyauta a mahangar zamani, ko kuma a zamanance, ana iya cewa, kallon da ake ya canza. A yau ɗabi’ar kyauta ta yi ƙaranci, saboda ana ganin yenta wauta ce, amma ruwa wata hanya ce, ko salon tattali. Bahaushe na kallon mutanen zamani sun ɓullo da wata dabara ta yin rowa, ko da yake su suna gani tsabar wayau ne. A inda suke fakewa da kalmar babu, ko kuma a ce maka gobe ka dawo, saboda yaudara. Bisa dalilin sauye-sauye da zamani ya kawo waɗanda suka shafi rayuwa, tabbas mutanen zamani suna ganin rowa wata hanyar dabara ce, ko wayau na tattali. Wannan ba ya rasa nasaba da sauyin tunani da Bahaushen wannan zamani ya samu. Babu shakka tsarin rayuwa ta sauya, don haka dole ne ɗabi’u su sauya. Bahaushen da yana ƙaunar ɗan’uwansa, kuma son abin duniya bai rufe masa ido ba. A inda shi kuma Bahaushen yanzun yake ganin kowa ya yi ta kansa, sannan kuma tsabar son abin duniya ya mamaye zukatan mu. Domin a tunanin yau, gani ake yawaita kyauta kamar ɓarnar dukiya ce watau rashin tattali ne, ko kuma wauta.

A wannan zamani akwai wasu da ke ganin cewa, wayonsu ko ƙoƙarinsu ko kuma iya tattali ke tara musu arziƙi. Wannan irin tunanin ne ke sanya wasu su riƙe kuɗi ƙamƙam, a wani lokaci ma su ba su ci ba, ba su bari wani ya ci ba. Duk da yake mun san cewa rayuwar wasu ta dogara ne daga samun albashi a ƙarshen wata. To amma bai isa ya zama hujja da zasu zama marowata ba. Dalili kuwa shi ne, ai a da Bahaushe noma da kiwo da kasuwanci kaɗai yake yi, amma zaka iske yana yin kyaututtuka da dama, bai san irin wannan baƙar rowar ba. Dalilin da yasa haka kuwa shi ne akwai wadatar zuci, sannan kuma Allah Ya sanya wa abin albarka.

A zamanin da, Bahaushe har so yake yi wani ɗan uwa ya ziyarceshi, a inda suke kwana murna ana hirar zumunci. Yanzu kuwa zamani ya hana wannan, sai aka koma daga ƙwauri sai gwiwa. Bahaushen yanzu bai son a zo wurinsa, su kuma ‘yan uwa ba sa son zuwa.

Bahaushe manomi a da idan kaka ta yi, sai ka iske yana bayar da kyautar hatsi ga maƙwabta da danginsa. Ba komai ya kawo wannan ba, sai ƙaunar juna da son yin kyauta. Yanzu kuwa abin ba haka yake ba. Bahaushen zamani ya fi gane ya tattare abinsa a ɗaki ya kulle.

SAUYIN YANAYIN ZAMANTAKEWA

Haƙiƙa zamantakewar Bahaushe ta samu sauye-sauye masu tarin yawa ta fuskoki da dama. Wannan kuwa ya kama ne tun daga yanayin hulɗarsu da jama’a da kuma yanayin tsarin muhallinsa. Da farko in muka ɗauki hulɗarsa da sauran jama’a muna iya cewa an samu tangarɗa. Bisa dalilin cewa Bahaushe da aka sani a zamanin da, to yanzu ba shi ba ne. Kamar yadda Bahaushe yake a da an sanshi da tsare amana, da faɗar gaskiya, da zumunci, da kyautatawa abokan hulɗa, ga kyauta da taimakon juna da sauransu.

Dangane da fuska ta biyu kuwa, sai mu ce hatta tsarin muhalli wanda aka san Bahaushe na da shi a wannan zamanin ya sauya. A zamanin da, an san Bahaushe da zaman gandu, a inda za a iske gida ɗaya yana ƙunshe da kaka, da uba tare da uwa, ga ɗa tare da matansa har da ‘ya’yansa, watau jikoki ke nan. Haka kuma ga ‘ya’yan riƙo da agola wani lokacin har da barori.

Bahaushe yace zama da maɗaukin kanwa shi ke kawo farin kai. Tabbas wannan Karin Magana ita ce ta faru ga rayuwar Bahaushe a yau. Dalili kuwa shi ne, mu’amulla da baƙin al’ummu da Bahaushe ya yi, shi ya haifar da sauyin tunanin Bahaushe. Wannan sauyin tunanin da Bahaushe ya samu, to shi ne ya sauya hulɗa ko mu’amular gaba ɗaya. Babbar illar da Bahaushe ya samu a irin wannan baƙon tunani kuwa, shi ne tsabar son abin duniya, da ƙaryar talauci wanda kuma shi ya haifar masa da baƙar rowa. Ɗabi’ar kyauta ta zama wauta mai yin ta ya zama wawa.

SHAWARWARI

Bisa lura da bayanai da suka gabata, ana iya cewa an ji kuma da fatan an gamsu. Don haka akwai buƙatar a ɗauki matakin rungumar ɗabi’ar kyauta, sannan kuma mu kare kai daga faɗawa cikin tarkon rowa. Ya dace mu bai wa juna shawarar neman mafita. Ga wasu shawarwari waɗanda ya kamata mu ɗauka su ne: Yaƙar zuciya, da kuma shaiɗan, mu sanya wadatar zuci, da kyautata tauhidi, tare da neman rabon gobe ƙiyama, sannan mu kyautata zumunci, a ƙarshe mu rage son abin duniya. Don haka mu sani cewa abin da ka bayar shi ne naka, wand aka tara na magada ne, ko kuma wanda ka ci ya zama kashi.

 KAMMALAWA:

A ƙarshe wannan takarda, ta tsakuro wasu al’amura da suka shafi zamantakewarmu. An kawo ma’anar kyauta da ire-irenta tare da dalilan yin waɗannan kyaututtuka da waɗanda suka shafa. A al’adance kyauta ɗabi’a ce don har akan gajeta daga iyaye, sannan kuma akan koya daga abokin zama. A addinance kuwa kyauta baiwa ce, sai wanda ya yarda da shi ne yake iya yin kyauta. A zamanance kuwa kyauta wauta ce, sai mara wayau ne zai yi ta. Mun ga wasu abubuwan alhairai da ɗabi’ar kyauta ke jawo wa al’umma, a zamanin da. Bayan haka kuma mun ga irin halin da muka tsinci kanmu a wannan zamanin. Haka kuma mun ga yadda ɗabi’ar rowa ta gurɓata halayen wasu daga cikinmu. Bayan wannan kuma, ga masu rauni daga cikinmu, sannan da marayunmu waɗanda aka sake su a igiyar ruwa. Irin waɗannan marayun ana samunsu a maza da mata, duk da yake ga dangin uwa da uba. Duk da yake ga sauran jama’a masu hannu da shuni, suna tare da su, amma kowa ta kansa yake yi. Watau rayuwar daga ni sai ɗa na, ko daga ƙwauri sai gwiwa. Don haka akwai bukatar, kowanne mutum ya dawo da hankalinsa jikinsa ya taimakawa maraya da marainiya. Ina fatan al’umma su fahimci inda wannan muƙala ta sanya gaba. Manufar ita ce mutum ya san shi wane ne, kuma mene ne matsayinsa? Don ya sani shi kansa yana iya mutuwa, saboda haka me yake nufi da ‘ya’yansa?.

Domin haka muna fata mu koma ga halaye da muka gada tun iyaye da kakanni, na kyautatawa junanmu, Allah Ya tsare mu Ya bamu ikon gyarawa mu rungumi kyauta mu gujewa rowa amin. Assalamu alaikum

 MANAZARTA.

Alhassan H. D (1982) Zaman Hausawa. Islamic Publication Bureau, Lagos.

Bunza A. M. (2006) Gadon feɗe al’ada. Tiwel Nigeria Limited Surulere, Lagos.

Ɗangambo A. (1984) Rabe-Raben adabin Hausa da Muhimmancinsa ga rayuwar Hausawa. Triunph Publication Kano.

 Ɗahiru B (2007) Tafsirin Watan Ramadan. Rediyo Najeriya Kaduna.

Madauci I. (1963) Al’adun Hausawa. Northern Nigerian Publication C ompany, Zaria.

Sadiya G. Y. (2005) Talauci Hauka ne? Super Prints Press, Kano.

Zindani A. A. (2000) Human Development. Muslim World League Printing Press. Saudi Arabia.

Sarki H. A (2000) Zuwan Musulunci a Afirka da shigowarsu Ƙasar Hausa.

 G. A. Computer Centre. Ikere – Ekiti, Ekiti State.

Gora Y. C. (1989) Matsayin camfi a Al’ummar Hausawa,M. A. Hausa Bayero University Kano.

Gusau. S. M. (1980) SarkinTaushi Salihu Jan kiɗi, (Tarihinsa da waƙoƙinsa) Kaduna Baraka Pubisher Ltd.

Gora Y. C. (1989) Matsayin camfi a Al’ummar Hausawa,M. A. Hausa Bayero University Kano.

Gusau. S. M. (1980) SarkinTaushi Salihu Jan kiɗi, (Tarihinsa da waƙoƙinsa) Kaduna Baraka Pubisher Ltd. 

 Hausa Post

Post a Comment

0 Comments