Ticker

6/recent/ticker-posts

Rikida a Falsafar Bahaushe

Being a mandatory Ph. D seminar paper, presented at the Department of Nigerian Languages. Faculty of Arts and Islamic Studies Usmanu Ɗanfodiyo University Sokoto, 2014

RIKIƊA A FALSAFAR BAHAUSHE

NA

SA’ADU MUHAMMAD MU’AZU
Department of Nigerian Languages.
Usmanu ƊanfodiyoUniversity Sokoto

FITATTUN KALMOMI

MA’ANAR FALSAFA

Falsafa wata kalma ce da ta samo asali daga harshen Greek (Girkanci) , watau “Philosophy”. Dangane da ma’anar wannan kalmar kuwa, wasu Masana kuwa, ga abin da suka ce: Falsafa: wani tunani ne mai ƙunshe da ilmi da nazari a kan wani al’amari (tarihi, da addini, da kimiyya da sauransu) wanda masana suka tattake wuri, tare da bayyana ra’ayinsu a kansa. [1] Ilmi ne da ke tsara ilmummukan magana da ɗabi’u, da siffar kyau da tunani na hankali, ko wani tsari na addini, ko wani fage na nihsaɗi na mutum, ko kuma aƙida, da fahimta, da matsayi na wani mutum ko na wsau jama’a. [2] Hanya ce ta tunani da ƙoƙarin samun bayanin dukkan al’amurra da suka shafi duniya da ɗan Adam da inda suka sa gaba. [3] Wani tsari ilmi ne mai alaƙa da imani, da tunani mai zurfi a kan al’amarin rayuwa da halita, da duniya, da kuma nazarin halayyar wani. [4]

 Bisa fahimtar bayanan da Masana suka yi, muna iya cewa, kalmar falsafa na nufin wani ilmi ne mai zurfi dake ɗamfare da dogon tunani. Kuma ya shafi fagagen rayuwa da yawa, wanda ya dogara kan zuzzurfan bincike wanda gogaggun masana suka gudanar. Bahaushe na irin wannan ilmin, ko tunanin game dabbobi da tsuntsaye, musamman kan barbara, da haihuwa da kuma rikiɗa.

MA’ANAR RIKIƊA;

Sauya kamannu, abu ya juye daga kamannunsa, kirarsa, ko siffarsa, ko launinsa ko a mayar da wani mutum,ko dabba,ko tsuntsu,[5] zai iya zama sauya ɗabi’a ko halaye,ko kamannu ko yanayi ko kuma a sauya wani mutun ko dabba ko wani abu. [6]Sauya kamannu daga na asali zuwa wani[7] sauyawa wani mutum ko dabba ko wani abu zuwa wani matsayi ta hanyar tsafi ko sihiri ko dabo. [8] sauyawar yanayin ƙirar jiki na ɗabi’a ko halita kamar girman jiki daga jariri zuwa riƙa (kamar kwaɗo daga gwadari zuwa tsulbu zuwa kwaɗo,ko ƙozo) ,sauyawar yanayin siffa da launi na dabi’a da wani abu kan yi kamar dutse daga ruwa ruwa zuwa sandararre ko kuma ruwa zuwa ƙanƙara,ko ƙanƙara ta narke zuwa ruwa. [9],rikiɗa na nufin jirkita abu ya koma wata siffa. misali ɗan dabo ya mayar da mutum ya zama dabba. [10] Sauya siffa ko kamannu daga ta asali zuwa wata sabuwa ta daban,musamman na dogon lokaci ko taƙaitacce. [11]

Bisa lura da bayanan masana muna iya cewa rikiɗa na nufin sauya kamannu na ƙira ko launin jiki, daga siffa ta asali. Wannan na faruwa ga mutum, ko dabba, ko tsuntsu.

GABATARWA:

A wannan muƙala za ta ƙunshi wasu bayanai, game da falsafal Bahaushe. Akan irin yadda Bahaushe ke ɗaukar dabbobi da tsuntsaye a tunaninsa, ta fuskar abin da ya shafi rikiɗa da kuma ma’anarta, da ire-iren rikiɗa kamar rikiɗar dake da alaƙa iskoki, da tsafi, da sihiri, da dabo ko rufa-ido. Haka nan kuma da dalilan da kan sanya a yi ta, tun daga Mutum, ko iska, ko dabba, ko kuma tsuntsu. Wannan irin matsayi ne har ya haifar da Bahaushe ke alaƙanta wasu dabbobi da tsuntsaye da iskoki. Za’a dubi wannan tunanin ne ta mahanga al’ada, a ƙarshe kuma sai naɗewa.

IRE-IREN RIKIƊA. Bisa ga tunanin Bahaushe game da rikiɗa ana iya cewa ya karkasa ta zuwa kashi 4, kamar haka: 1-Rikiɗa ta ɗan lokaci. 2-Rikiɗa Mai tsawo. 3-Rikiɗa ta din-din-din. 4-Rikiɗa ta ɓatar da sawu.

RIKIƊA TA ƊAN LOKACI: Akan samu rikiɗa ta wucin-gadi ne, saboda ƙwatar kai (rai). A mafi yawan dabbobi ko tsuntsaye kan rikiɗa ne cikin ƙanƙanin lokaci, domin su ƙwaci kansu daga halakarwa ko cutarwa daga abokan gaba. Ko da yake a irin wannan rikiɗa ba a cika daɗewa ba. Da zarar an wuce haɗari sai ya koma siffa ta asali. Misali hawainiya takan sauya launin jikinta, don ta saje da muhallin da ta samu kanta a ciki. Takan yi haka ne don ta kuɓuta daga mahara. Idan ta iske ganye kore sai ta rikiɗa kore, in kuma ƙasa-ƙasa ta ga ni sai rikiɗa ko kuma baƙi-baƙi. Bisa wannan dalili ne ya sa ake haɗa maganin rikiɗa da mushen hawainiya. Ita kuwa makwarwa takan ɓace a kasa ganinta, sabo da ta saje da launin ƙasa da launin gashinta. A nan ita ma Bahaushe na haɗa maganin layar zana watan layar ɓata da ita.

RIKIƊA MAI TSAWO: Dabbobi, kan rikiɗa zuwa mutane har su shiga kasuwa su yi harka tare da ‘yan Adam, a inda suke yin cinikayya. Misali barewa, da beguwa sukan rikiɗa zuwa Bafulatana. Tunku da kada sukan rikiɗa zuwa kuturu su shiga cikin mutane suna yin bara.

RIKIƊA TA DIN-DIN-DIN: Ita kuma wata irin rikiɗa ta har abada. An fi samun wannan ne a wurin dabbobi irin su maciji musamman irin wanda iska ya rikiɗa zuwa shi. Haka kuma akan samu irin wannan ga irin mutanen da mayu sukan kama su mayar da su dabbobi. A mafi yawan lokutta sukan zauna a daji har abada.

RIKIDAR ƁATAR DA SAWU: Wannan irin rikiɗa akan yi ta ne, don a kawar da hankalin wasu, ko kuma a yaudaresu. Dabbobi da mutane na yinta, ta fuskar dabbobi akan samu irin su tunku, da barewa, da beguwa. Ɓangaren mutane kuwa, akan samu a wurin mayu, ko kuma ɓarayi. A lokutta, kuma a wurare da yawa, ɓarayi kan rikiɗa wata halitta, idan suka ga asiri zai tonu. Kamar yadda ya faru a garin Ilori.

Rikiɗar sauya launin jiki: Akwai rikiɗa wadda dabbobi, da kuma wasu mutane kan yi. Waɗannan dabbobi masu sauya launin jikinsu, babu kamar hawainiya. Ko da yake a wani lokaci maciji kan yi mele, saboda yawan shekaru watau tsufa, ko ya yi saɓar fatar jikinsa. Haka kuma akwai wasu dabbobin irin su ƙadangare, da danginsa sukan sauya fatar jikin su ta hanyar yin saɓa.

Rikiɗar sauya ƙirar jiki: Akwai wata rikiɗa wadda wasu dabbobi, da kuma wasu mutane kan yi. Dabbobi masu yin haka, suna da yawa, kamar barewa, da tunku, da beguwa. Ko da yake a wani lokaci maciji kan rikiɗa zuwa mutum, saboda tsufa, ko iskoki su shige shi. Haka kuma akwai wasu dabbobin irin su ƙadangare, da danginsa. Misali irin su kada, da tsari sukan sauya ƙirar jikin su ta hanyar komawa mutum.

DALILAN DA KAN SANYA RIKIƊA

 Bahaushe yakan ce komai baya rasa dalili, ko kuma zai faru ba tare da dalili ba. Don haka dalilan rikiɗa na iya kasancewa na sarari ko ɓoye tun daga dabba, ko tsuntsu har mutum ko aljani. Duk wanda ya rikiɗa zuwa wata baƙuwar siffa ta daban, saɓanin wadda aka sanshi da ita, to akwai wasu dalilai na sarari ko na ɓoye. Al’adar Bahaushe ta kalli waɗannan dalilai kamar haka: Ƙwatar rai, ko nuna buwaya, ko biyan wata bukata.

Ƙwatar rai : Akan samu rikiɗa a dalilin ƙwatar rai. Wannan kuwa na faruwa ga dabba, ko tsuntsu, ko mutum. A mafi yawan lokuta wasu dabbobin kan rikiɗa ne, don kaucewa halaka. Ma’ana saboda su da su tsira.

Nuna buwaya (Gagara) : Akan samu rikiɗa a dalilin nuna buwaya, ko gagara. Wannan kuwa na faruwa ne ga dabba, ko tsuntsu, ko mutum. Ta fuskar mutane an fi samun maharba, ko ɓarayi, ko da yake akan ɗan samu bambancin yanayin hakan.

Biyan bukata: Akan samu rikiɗa wadda kan faru a dalilin biyan wata bukata. Wannan na faruwa ne ga dabba, ko tsuntsu, ko mutum. A mafi yawan lokuta hawainiya kan rikiɗa ne, don neman abinci. Takan saje da ciyawa, ko ta haye rama ta rikiɗa launin ramar, ta rinƙa kama ƙwari tana ci. Dangane da ɓarayi kuwa, saboda su ɓatar sawu su yi sata.

ƘARAMAR RIKIƊA

Wannan rikiɗa ita ce wadda ba cikakkiyar rikiɗa ba (ƙarama ko gajerar rikiɗa). Su uku ne kamar haka: Saɓar fatar jiki, da zubar gashi, da sajewa.

Saɓa: ba cikakkiyar rikiɗa ba ce, (ƙarama ko gajerar rikiɗa). Akwai wasu dabbobi da sukan sauya kama, ta hanyar yin saɓa, a inda fatar jikin su kan saɓule, a saboda wasu dalilai. Kamar maciji kan yi saɓa ko ƙadangare, ko damo, ko tsari, da sauran danginsu.

Zubar gashi: tsuntsaye sukan sauya kamannu ta hanyar zubar gashin jikinsu. Irin wannan ya fi faruwa ne, musamman idan suna kwanci akan ƙwai kafin su yi ƙyanƙyasa. Ko da yake wasu sai in ba su lafiya ne suke zubar da gashi.

Sajewa: Ita ma kamar rikiɗa ce, sai dai ba cikakkiya ba ce, kamar inda dabba kan saje da muhalli. Misali ƙadangare in yana wuri yakan rune ya saje da launi katangar, ko ɗakin girki, haka shi ma ɓera da kuma gafiya, da wasu macizai, da kada, da tsari, da jauji.

RIKIƊA A TUNANIN BAHAUSHE TA MAHANGA AL’ADA.

A al’adance akwai wani tunani da Bahaushe ke da shi, na cewa wasu dabbobi na iya rikiɗa su koma wani nau’i na dabbobin da ba irinsu ba. Ko kuma su koma siffar mutum, misali kamar tunku Bahaushe na zargin sa da cewa yakan rikiɗa ya koma siffar kuturu kuma har ya zo kasuwa. Baya ga wannan kuma akwai iskoki da kan rikiɗa su koma siffar wasu dabbobin kamar, kare, da maciji, da ƙadangare, ko mage da sauransu. Bahaushe bai cika yarda ko amincewa da baƙin kare ba, musamman da dare. Haka wasu ƙadangaru ba, a amince masu domin ana zargin iskokin kan rikiɗa su zama ƙadangaru.

Akwai wasu mutane daga cikin masu wasu sana’u da suke rikiɗa wata dabba. Domin su nuna gagara, da ƙuƙuwa akan sana’arsu, kamar maharba, da masunta, da masu ba da magungunan gargajiya da wasu masu aikin sarki, kamar yari, da dogarai, ‘yandoka, da hauni, da wasu riƙaƙƙun ɓarayi.

Wannan tunani ya yi kaka-gida a rayuwar Bahaushe, ana samun jirwayensa a adabin baka da rubutacce. Kamar a waƙoƙI, da tatsuniya, da al’amara, da tarihi. Tunanin ya ƙara samun goyon baya daga addinin musulunci. Wannan kuwa ba ya rasa nasaba da wasu bayanai daga hadisai da suka yi magana akan al’amarin rikiɗa.

DABBOBIN DA KE RIKIƊA.

Bahaushe na zargin wasu dabbobi da cewa sukan rikiɗa a wasu lokuta, kuma iskoki kan shige su. Su ne kamar haka: - baƙin kare, da Ƙadangare, da Kada, da barewa, da baƙar mage, maciji, da damo, da bguwa bushiya, da tsari, da tunku. Waɗannan dabbobi kan sauya kama ko kuma su rinƙa nuna wasu halaye na gagara ka buwaya.

BAƘIN KARE: Bahaushe ya camfa, kuma bai cika yarda da baƙin kare, sabo da alaƙarsa da aljannu. A wasu lokuta iska kan rikiɗa zuwa baƙin kare, ko kuma su shiga jikin baƙin kare na haƙiƙa. Don haka ne ko duka ko jifansa ba a yi. Wannan ya wuce hasashe ko zargi, saboda waɗansu hujjoji da suka tabbata a wurare, da lokutta da kuma mutane daban-daban. misalai.

Karona da wani baƙin kare

Na dawo yawo da dare na shiga wani lungu sai naga baƙin kare sai na ɗauki dutse na jefeshi, sai ya gudu ba,a ɗauki wani lokaci ba, sai naga wani mutum ya bayyanar min. Nan take sai yace kai yaro kar ka ƙara jifan kare ka ji. [12]

Baƙar mage: Bahaushe bai amince mata ba sabo da iskoki kan rikiɗa, ko shigeta. Haka kuma a dalilin, Mayu, da ɓarayi, da matsafa kan rikiɗa zuwa ita. Bayan wannan kuma akan alaƙanta baƙar mage da cewa dodo ce. Wannan ya sanya Bahaushe ba ya son ta, ko magensa ta haifi ‘ya’ya, to in har akwai baƙa, sai ya jefar da ita.

Bushiya: tana da irin nata zargin da Bahaushe ke yi mata na rikiɗa ko dibilwa. Akwai inda akan kama bushiya a rufeta da turmi, amma kafin safiya, sai a tarar ta gudu, ko kuma za aji tana kukan jariri.

Wani Yaro da wata Bushiya:

A wata shekara ne a garinmu wasu yara su biyu suka kama bushiya da dare. Bayan da suka wannan bushiya, sai suka nemi yayi da ƙirare domin su gasa. Suka dogon lokaci suna gasa bushiyar nan amma taƙi gasuwa. Ɗaya daga cikinsu watau ɗaya yaron yace, kai wannan bushiya fa mu haɗura, tun da taƙi gasuwa. Shi kuwa ɗayan yasha alwashin sai ya gasa ya ci, sai ya tafi ya samo kananzir ya zubawa bushiyar. Ƙyasta ashanarsa ke da wuya, sai kawai wuta ta kama jikinsa. Aka yi ƙoƙarin a kashe wutar nan, amma abin ya gagara. A wannan hali ne ta cinye shi ya mutu har lahira”. [13].

 Beguwa: ana zargin ta da rikiɗa zuwa mutum, watau Bafulatana. Mafarauta da yawa sun amince cewa beguwa kan rikiɗa zuwa Bafulatana har da ƙwaryar nono a kanta. Takan yi wannan ne idan ta ji motsin mutane musamman mafarauta, sai ta rikiɗa don ta kifar da su. Wasu mafarauta musamman waɗanda suke da wankin ido, sukan gane ta.

BEGUWA NA RIKIƊA ZUWA BAFULATANA.

Bahaushe na zargin beguwa mai ƙaya a jiki da cewar tana rikiɗa zuwa Bafulatana, ta shiga kasuwa da ƙwaryar nono. Maharba ne kaɗai ke iya gane ta, ta hanyar yawaita sayen rogo. A wani lokaci kuma in a cikin daji ne sai su rikiɗa fulani su jero suna hira akan hanya,,Maharba kaɗai ke ganesu. suna yin magani wannan ƙuƙuwa ne ta hanyar zuwa daji ba wando to in suka yi haka sai su harbe su su yi nasara. [14]

 TUNKU: mafarauta sun tabbatar da tunku na rikiɗa zuwa tsoho, ko kuturu, ko ƙungiyar mata. A mafi yawan lokuta in ya zo shan ruwa, ba zato ba tsammani, sai ya ji motsin mutane. Nan take sai ya zama tsoho ya tsuguna kamar zai yi wanka. Yakan zama kuturu har ya tafi kasuwa don ya yi bara, amma mafarauta na ganeshi ne ta yadda yake sayen kanwa. Da zarar aka ga kuturu na sayen kanwa, mafarauta kan yi zargin ba kuturu ba ne, tunku ne. Bayan haka yakan rikiɗa ƙungiyar mata su jero suna yin surutu kamar sun dawo biki. A nan mafaruta kan ganeshi ne ta hanyar yi masa kwanto a cikin sako da zarar suka ga mace ta gaba a jerin sai su harbeta.

Maciji: Bahaushe na zargin maciji da cewa yana rikiɗa ko kuma iskoki na rikiɗa zuwa maciji, ko kuma su shige shi. Akan samu irin wannan idan ya tsufa, inda yakan samu wani kogo itace, ko dutse, ko tsohuwar rijiya ko suri ya zauna. A wani lokaci idan maciji ya gagara ya riƙa har yakan zama guguwa ya rinƙa tashi.

Ƙadangare: Akan zargi ƙadangare cewar yana da wuyar sha’ani. Kamar yadda wani Bawan Allah yace; akwai ƙadangare iri huɗu, kamar haka: 1. Na haƙiƙa wanda iska ya shiga. 2. Wanda iska ne ya rikiɗa. 3. Da wanda yake na sihiri ne. 4. Ko kuma a sihirce shi.

Wani Aljani ya Rikiɗa ƙadangare

Wata mata ta shiga bayan ɗaki (masai) don ta biya bukata sai ta ga wani ƙadangare sai kawai ta watsa masa ruwa wai don ya gudu, bayan ta fito daga bayi sai kawai ta kasa gani watau ta makance. Aka kai ta asibitoci daban daban amma ba a ci nasara ba, sai wani yace a yi mata ruƙƙiya. Da a ka kira mai ruƙƙiya ya fara sai wani aljani ya bayyana ya fara Magana ta bakin matar da ta makance yana cewa; ‘’Ta shigo bayi ba natsuwa ni kuma ina nan sai na yi gudun kar ta ganni ta tsorata sai na rikiɗa na koma ƙadangare, amma kuma sai ta watsa min ruwa to da na haƙura amma daga baya wasu jikokina suka ƙi haƙuri akan abin da ta yi min shi ne suka rufe mata ido. Aka ci gaba da ruƙƙiya sai jikokin suka yi magana. To ashe su biyu ne Hassan da Husaini da ya ya haƙura ya fita amma daya sai da aka sha wahala amma daga baya ya fita ta warke. [15]

BAREWA; Ita ma ana zarginta da rikiɗa zuwa Bafulatana da ƙwaryar nono fara kyakkyawa. Mafarauta na gane ta hanyar lura da Bafulatanar da ta cika sayen gishiri.

DAMO ; iskoki ke shigar sa, mafarauta da dama sun yarda cewa, idan damo ya tsufa, iskoki kan shige shi ya rinƙa aikata wasu abubuwa na ban mamaki.

KADA; Akan zargin kada da rikiɗa ko hatsabibanci, don kuwa, akan samu kada da yakan fito wajen kogi ya rinƙa kashe mutane da dabbobi, ya kuma koma cikin kogin ko an sanya tarko ba ya kamuwa.

 KADA YAKAN RIKIƊA:

Kada kan rikiɗa zuwa tsohon mutum ko kuturu. mu mutanen Yawuri a zamanin da an rinƙa ganin abin mamaki. Domin an rinƙa samun wasu lokutta da kada,idan ya rinƙa sai ya rikiɗa ya rinƙa shigowa garin Yawuri. Babu mai gane haka sai masunta ko maharba don suna da masaniya. kamar yadda sukan ce matuƙar mutum ya gamu da tsoho wanda ba a sanshi ba watau baƙo. A kan lura da cewa ko yana da gashin gire,in har babu to lallai kada ne ya rikiɗa ya shigo gari. [16]

Rikiɗa A Adabin Bahaushe: Akwai jirwayen rikiɗa a kusan dukkan rassan adabin baka, kamar a waƙoƙinsa da tatsuniya da al’amara da tarihi.

TARIHI: WANI MACIJI DA ZAKARA A ZARIYA

A Ƙasar Zazzau kuma a cikin Birnin Zariya an yi wani shahararren Malamin addinin Musulunci, mai suna Malam shehu na Malam Na'iya. “Wata rana ana cikin karatu a azure (zawuyya) yana bayar da karatu, sai yara suka fito daga cikin gida da mushen zakara a hannunsu. A ɗaya hannun kuma da mushen maciji, sai Malam ya tambaye su ina zaku? Me ya faru?. Yara gaba ɗaya suka ce “ai wannan maciji ne ya sari zakara ya kashe shi”, sai su kuma suka kashe macijin. Abin mamaki za su fita da mushen zakara da na maciji, sai Malam yace su ajiye mushen zakaran su tafi su jefar da mushen macijin. Bayan ɗan lokaci sai kawai ana cikin karatu, sai ga wani maciji yana janye da mushen macijin da aka jefar ya shigo cikin zaure. Nan da nan kuma nan take, sai malamin nan ya sanya ɗauko mushen zakara, ya karɓa ya ajiye a gaban macijin. Malamin sai ya ce “ga ɓarnar da ya yi mana, ya kashe zakara ne mu kuma muka kashe shi?. Macijin Sai kawai aka ga ya ɗauki mushen macijin nan ya juya ya tafi. [17]

 TATSUNIYA: akwai wasu tatsunniyoyi masu yawa, da a ka samu jirwayen rikiɗa. Ga misali, kamar haka: “tatsuniyar barewa ta auri mutum”.

Gata nan gata nan ku, wata barewa ce sai ta rikiɗa ta zama mace kyakkyawa sai ta ɗauki ɗan kwatashinta ta ɗora a kanta, ta tafi tsakiyar karofi ta ajiye. Ta ce duk wanda ya jefa ‘yar tsakuwa ta buɗe kwatashin shi ne mijinta, sai wannan ya ɗauki tsakuwa ya jefa, bai buɗe ba. Wancan ya jefa tsakuwa bai buɗe ba, sai aka samu wani ya jefa ‘yar tsakuwa sai ya buɗe, sai ta ce ta samu miji shi zata aura sai suka tafi garin ita yarinya wurin iyayenta, za’a ɗaura mata aure da wannan mutumin. Da aka ɗaura masu aure ta zo ta zauna a gidan miji. Kullum ranar girkin ta sai a ce ta je, ta ciro kuɓewa a gonar miji ta yi miya. Da ta je gonar sai ta yar da zaninta, ta yi birgima a ƙasa ta zama barewa. Bayan haka sai ta yi kiran ‘yan uwanta,sai ta yi waƙa tace:

cikal-cinkal,cinkali kalaya.

Turmin ‘yankale ya yi fure,ceɗiya.

Tudu na korar tudu marina.

tudu na korar tudu da ƙaho.

Ban da kwatsakwatsan ban da ƙanƙana.

Nan da nan sai ‘yan uwanta su zo.

Su taro su ciccinye kuɓewa.

Sa’anan sai in sun gama sai tafi gida, ita kuma sai ta yi birgima ta koma mutum ta ɗauki zaninta ta ɗaaura sai ta koma gida ta dinga cewa ni da gangan aka tura nig a shin an ban samo komai ba. To ran nan sai mijinta ya bita gonar sai ya ganta tana birgima da t agama birgimar sai ya gat a rikiɗe ta zama barewa sai yaga ta yi kiran ‘yan uwanta bareyi da waƙa Bareyi suka taru a gonar jingimduk suka cinye kuɓewar sunna cikin ci sai ya fasa su sai yaga matarsa ta ganshi ya koma gida sai ta ɗauko kuɓewar ta biyo shi ta tarar das hi a gida yace wacece tace niceyace ina zakitac ɗaki zani yace a’a koma daji sai tace taƙI sai ya biyota a guje ya kora ta daji daga nan bat a sake dawowa ba. [18]

ALMARA: Akwai almarori waɗanda ke ɗauke, ko tabbatar da rikiɗa,kamar almarar biri.

ALMARAR BIRI

Akwai inda aka ce wata Bafulatana ce ta dawo kasuwa sai yaronta yana jin kashi, ko da ta sauke shi ya yi kashin ya gama, sai ta ɗauko waina daga cikin kayanta. Bayan da ta ɗauko sai ta karya biyu ta share masa kasha da wainar nan take sai ya zama biri. Daga nan ya kama tsalle ya faɗa daji da gudu, ya bar tan an tsaye tana mamaki kuma tana kuka. [19]

WAƘOƘIN BAKA: Akwai mawaƙan baka da suka yi waƙoƙi da a ka samu jirwayen rikiɗa. MISALI: Danlami Nasarawa a waƙar Maigari Amadu

 Gindi: In ɓarawo ya zama kura

Mai gari zai zama zaki

In ɓarawo ya zama ɓera

Mai garizai zama kyanwa

In ɓarawo ya zama tsuntsu

Mai gari zai zama shaho

 Jagora: Ya buge shi ya ɗaure

: ya buga masa ankwa

: Ya miƙa ga yari.

: Ya shigo yana yin shawagi

 Gindin: Haka ne yara, duniya,

 zaman ‘yan marina ne

 Mai komo Dan Tudun Doki (ilaje)

Ilaje ya ga mugun zaki

ko da ya harbe shi

Mugun zaki ya zaburo

 zai kasshi Ilaje ya zam dawa

Gambu mai kiɗin ɓarayi (Nazaƙi ) inda Inuwa Ɗan Maɗacci ya tare shi akan hanya a lokacin da suke tafiya tare tudun

 Jagora: kora jakkai kora jakkai

 Nic ce ga kura can tsugunne

 Yac ce, bar su su wuce kar ka damu

 Ai ba kura ta ba Gaambo

 Muhd inuwa na ka bi na

 Duk bai da rabo ɗiba ga baina,

 Sai dai wata rana na gaya ma.

 Duk bar shi ya ƙare ƙuƙuwa tai,

 Sai ya hita hili in buge shi,

 In bar shi ga kolaye su canye.

RIKIƊA A RUBUTATTACCEN ADABIN BAHAUSHE;

Al’amarin rikiɗa a tunanin Bahaushe ba ƙarami ba ne. Domin kuwa wannan tunani ya yi naso a rayuwar Bahaushe gaba ɗaya. Wannan kuwa ya haɗa har da rubutaccen adabi. Kamar zube watau ƙagaggun labarai. Akwai littattafai irin su Magana jari ce na 1 da 2 da na 3.

Labarin ‘Yan birni da Ɗan ƙauye,

Wani Baƙauye ne ya shigo gari da jakinsa,sai ya ga wani mai wasan nakiya da garma (ɗan hoto) ya ta yin wasa. Baƙauyen nan ya saki baki yana kallo yana riƙe da jakinsa. zuwa can sai wasu yan birni suna zaune. wani daga cikin yan birnin nan ya ce yanzu ƙwace jakin can wuri muzin can ba zai yi wuya ba. Abokansa suka ce haba wannan ba zai yiwu ba wane kai saboda a ƙarfi dai ba zaka iya ƙwacewa a hannunsa ba, kuma yan zu rana ce ba dare ba. shi kuma sai yace ku biyoni da isarsu sai ya saɓule igiyar dake ɗaure a wuyan jakin Baƙauyen nan ya rataye a wuyansa. Ya miƙawa ‘yan uwansa jaki suka tafi da shi. Baƙauye bai san abin da ke gudana ba. Ko da Ɗan birni ya lura abokansa sun ɓace, sai ya fara daddagewa yana turjewa Baƙauye kuwa sai jan igiya yake yi. Bayan da ya ji abin ya gagara,sai ya waiwayo da niyyar ya bugi jakinsa sai ya ga mutum ɗaure da igiya a wuya mamaki ya kama shi. Baƙauye ya ka da baki y ace me yake faruwa? Dan birni ya buɗe baki yace ;Ni ne jakinka,tun farko ni mutun ne wataran haukar ƙuruciya ta ɗebe ni na sha giya na zagi mahaifiyata,sai ta tsine min shi ne na koma (rikiɗa) jaki ina ganin ta yafe min ne Baƙauye ya ji tausayinsa ya sake shi yace kar ka ƙara irin wannan. [20]

RIKIƊA TA BAIWA DAGA ALLAH:

Akwai rikiɗa ta baiwa daga Allah kamar Mala’iku da iskoki da kuma wasu dabbobi ko tsuntsaye. Rikiɗa ta baiwa, Allah (SWT) Ya bai wa Mala’iku wata baiwa ta sauya (rikiɗa) halittarsu ta asali zuwa wata halitta ta daban. Kamar in da suka rikiɗa zuwa mutune. Haka kuma su ma iskoki suna da wannan baiwar sauya halittarsu ta asali zuwa mutum, ko dabba, ko tsuntsu. Kamar irin su tunku da barewa,da beguwa,da hawainiya da makwarwa.

DANGANTAKAR DABBOBI DA ISKOKI.

 Iskoki a wajen Bahaushe wasu halittu ne masu kama da mutane ta fuskar halittarsu, da surarsu, da ayyukansu, da al’adunsu, daɗabi’unsu, da harshensu, da siyasar rayuwarsu, da dai makamantansu. Bahaushe ya yi imni da samuwarsu a kowanne tudu, da rahi na bangon duniya, wuraren da ake samun ‘yan Adam, da wuraren da ba’a samun su. [21]

Bisa ga bayanan da suka gabata, muna iya cewa, iskoki wasu halittu ne waɗanda Bahaushe ya yi imani da su, duk da yake ba ya ganinsu. Al'adar Bahaushe ta tabbatar da samuwarsu, tun kafin zuwan musulunci. Haka kuma, addinin Musulunci ya zo, sai ya tabbatar da samuwar su. Wannan ya ƙarawa Bahaushe ƙarfin gwiwa a kan tunaninsa, a game da iskoki.

“ Hausawa na danganta dabbobi da yawa da iskoki saboda irin siffarsu,da ɗabi’unsu, da ayyukansu. Iskoki kan sauya siffarsu zuwa manyan dabbobi ko ƙanana. Waɗannan dabbobi Bahaushe na yi masu kallon iskoki ko wakilansu: a. Baƙin kare. b. Baƙar karya. c. Farin kare. d. Baƙar mage. e. Baƙin Jaki. f. Farar kura. g. Ayyu. h. Tsohon Kada. i. Tsohon Damo. j. Ani. Idan manyan Maharba ko Masunta suka karo da waɗannan dabbobi sukan ɗan raga masu,gudun kada su faɗa masu iska ya ɗauki fansa. Duk watadabbar da ake has ashen iskokina shigar burtu da siffarta,idan za’a farauceshi sai an shirya”. [22]

 Bahaushe na da hasashen cewar akwai wata alaƙa a tsakanin iskoki da wasu dabbobin gida da dabbobin daji. Wannan dagantaka akwai ta sarari akwai kuma ta ɓoye. A al’adance akwai wasu dabbobi da ke da wasu halaye da suka saɓa da na sauran dabbobi. Akwai wasu tattabaru da iskoki sukan shige su, sai mai su yakan gane. Bisa ga bayani game da alaƙar dabbobi da iskoki ana iya raba su kashi-kashi ko fuska-fuska, kamar haka: A wani lokaci iska kan rikiɗa ta koma wata halitta, don ta tsoratar da wani, ko don ta ɓatar da kama. A wasu lokutta akan gane sabo da ɗabi’a da ta saɓa da ita irin dabbar da iskar ta koma, amma a wasu lokuttan ba a gane su. Haka kuma, iska kan shige dabba ko tsuntsu, saboda sha’awar da dabbar ta ba su, ko a sanadin zama wuri ɗaya da iskar ko kuma tsufa.

RIKIƊA MAI ALAƘA DA ISKOKI

Iska ba abin da zai yi idanun mutane su gan su ba ne ƙuru-ƙuru. Iskoki idan suna son su ziyarci mutane cikin siffar da ba zasu tsorata su ba,suka rikirkiɗa da yawa. Ba Bahaushe kaɗai ke da imanin cewa, iskoki na rikiɗa. Labarawa,da Turawa, da mutanen Asiya,da dukkanin Ƙabilun duniyar baƙar fata suna da wannan tunanin. Iskoki suna sauya kama su yi shigar burtu su kutsa cikin mutane da siffa irin ta: a. Mutane,b. Dabbobi, c. Kwari. [23]

Akan samu dabbobi, ko tsuntsaye su rikiɗa su sauya halitta daga tasu ta asali zuwa wata ta daban. Wannan bai rasa nasaba da hulɗa da iskoki, da farko iskoki kan shiga jikin wasu dabbobin, sai su zama gagararru, ko shu’umai. Bahaushe na zargin dabbobi irin su baƙin kare, da ƙadangare, da baƙar mage, da maciji, da sauransu.

Mafarauta sun tabbatar da cewa duk a cikin namun daji babu mai hatsabibanci irin gwanki. Domin idan aka harbeshi ba ya faɗuwa sai ya yi gudu mai nisa. Ko da kuma in ya faɗin, sai a tarar yana zaro harshe yana lasar ƙasa, ko ciyawa, kamar bai mutu ba. Ko ka ga ƙudan zuma na fitowa daga kunnensa, ko kuma kan gwankin ya ƙi yankuwa da dai sauransu. A waƙoƙin bakan Bahaushe, akwai mawaƙa da suka nuna hakan. Misali: Alhaji Mamman Shata a waƙar Widi Ɗan Usman Salgare yace;

 Jagora: Baba kan kada mai ƙwari,

 : kan gwanki mai rangwagwan,

Gindi: Widi Ɗan Usman Salgare.

Wasu dabbobin idan suka tsufa, shekarunsu suka yi yawa iskoki kan shigesu. Kamar raƙumi, da maciji, da ƙadangare, da kada, da tsari. A mafi yawan lokuta, idan waɗannan dabbobi suka tsufa sai a rinƙa nuna wasu halaye na daban. Kamar maciji da zarar ya tsufa sai ya zama gamsheƙa ba wuya iskoki sun shigeshi. Daga nan sai ya zama masha-ruwa ko bakan-gizo a inda zai samu wata tsohuwar rijiya ko suri. Haka kuma wani macijin yakan zama guguwa shi ma alaƙar iskokin ne.

ISKOKI KAN RIKIƊA ZUWA DABBA.

 Allah Ya bai wa iskoki wata baiwa,wadda zasu iya rikiɗa komai suka ga dama. Domin sukan rikiɗa zuwa mutum, ko dabba, ko tsuntsu.

WANI ANGO DA WANI MACIJI

A zamani Manzon Allah Annabi Muhammadu (SAW) An fita da sahabbai ana aikin gayya, sai wani matashi Ango wanda bai daɗe da yin aure ba. Ya nemi izini daga wurin Manzon Allah (SAW) cewar yana son zuwa gida. Annabi (SAW) Ya ba shi izinin, ya tafi gida ke nan sai ya tarar da amaryarsa a waje tana tsaye. Da isowarsa, sai ya tambaye ta meke faruwa ya ganta a waje? Amaryar tace ya shiga ɗaki maciji ne. Ko da ya shiga,sai ya ga wani maciji ya yi gammo a kan gado. Wannan matashi yana fita sai ya ɗauko sanda,don ya kashe maciji. Bayan ya kai wa maciji duka da sanda. Ba a san wanda ya riga mutuwa ba tsakanin maciji da Angon ba. Wannan labarin na isowa wurin Annabi (SAW) sai ya ce, ku guji kashe macizai a garin [24]

RIKIƊAR MUTUM ZUWA DABBA

Akwai rikiɗa wadda wasu mutane kan yi daga mutum zuwa dabba. Wannan rikiɗa kan faru ne a sanadiyyar, ƙwatar kai, ko nuna buwaya, ko ɓatar da sawu. Mutanen da aka fi sani da irin wannan hali, su ne, kamar haka: Maharba, da mayu, da masu dabo da sauransu. Akwai wasu mutane da ya zama masu al’ada, su rikiɗa zuwa dabba. Kowanne dalilan da kan sanya su haka ya bambanta. Kamar a Ƙasar Birnin gwari akwai ƙabilar Kamukamawa (kamuku) , da ƙabilar Katafawa su duka a jihar Kaduna, sukan rikiɗa zuwa kura. A Ƙasar Katsina kuma a gundumar Ɗanmusa, da akwai masu rikiɗa kura. A Ɗandume akwai mutane idan suna biki sukan rikiɗa kura, ko zaki ko kuma yaro ya koma tsoho tukuf. A Ƙasar Gaidam a jihar Yobe, nan ma akwai masu rikiɗa kura da dai sauransu.

WATA MATA TA RIKIƊA BAREWA

A wani ƙauye a Ƙasar Ilori ta jahar kwara wani maharbi ya fita farauta a daji, sai kawai ya ga wata barewa. Nan take sai ya harbe ta, ta ɗan ƙara gudu kaɗan sai ta faɗi. Shi kuwa ya nufi barewa da ta faɗi tana shure-shure da ƙafafunta. Da isarsa sai kuma barewa ta rikiɗa tsohuwar mace. Maimakon ya ga barewa sai ga mace tsohuwa matacciya. Nan da nan ya ruga da gudu zuwa gidan sarki. Bayan da sarki yaji abin da ya faru sai ya tura maharbin nan zuwa ofishi ‘yan sanda. Ya yi wannan dabarar ne don gudun kar jikokinta su ɗauki fansa ta hanyar kai masa hari don su kasheshi. [25]

 RIKIƊAR SIHIRI, TSAFI, DABO, DA RUFA-IDO.

Kalmar sihiri baƙuwar kalma ce daga harshen Larabci, mai asali daga “sihir. ” Wannan kalma na nufin aikata wani abu wanda ya saɓa wa rayuwa ta haƙiƙa. A da can Bahaushe na kiran sihiri da sunaye masu yawa da suka haɗa da tsafi, ko dabo, ko rufa-ido, ko kanbulku da sauransu. Akwai misalai da yawa da suka shafi rikiɗa da suka faru a wurare da yawa. Misali:

MUTANE MASU RIKIƊA ZUWA BUNSURU

Muna garin Patakwal akwai wasu ‘yan Arewa waɗanda sukan rikiɗa zuwa taure (bunsuru). Abin da yake faruwa kuwa shi ne, idan suka ga kirsimati ta matso, kuma ba su da kuɗi, sai su shirya a tsakaninsu wani ya rikiɗa zuwa bunsuru. Ɗaya daga cikinsu sai ya ɗaura masa igiya yana zagayawa a cikin gari a matsayin talla. Idan har wani ya sayi bunsurun ya kai gidansa ya ɗaure, sai kawai dare ya kwance kansa ya gudu. Irin wannan abu ya sha faruwa a garin Patakwal. [26]

RIKIƊAR MASU DABO: Rikiɗa masu dabo, ana iya cewa ta kasu kashi biyu, akan rikiɗar da wani abu ya koma dabba, ko tsuntsu. Ko a rikiɗar da wata dabbar zuwa wata, ko tsuntsu ya koma wani tsuntsu ta hanyar dabo. Akwai kuma inda su da kansu sukan rikiɗa su koma zuwa dabbar ko tsuntsu. Duka wannan na faruwa ne bisa dalilin nuna buwaya ko gagara. Misali.

ANA MAYAR DA TUSHIYAR DAWA ZAKARA

Tabbas irin wannan ta sha faruwa ko kuma ince yana faruwa har ya zuwa yau. Matuƙar a kace sallah ta kusa an fara hada-hadar sallah. Lallai in mutum bai yi sa’a ba to zai sayi tushiyar dawa a matsayin zakara. Abin da ke faruwa shi ne, akwai wasu mutane da suka ƙware wajen dabo. Waɗannan mutane sukan samu tushiyar dawa, sai su cika kwando su yi wani sidabaru. Nan take sai tushiyoyin dawar nan su koma zakaru. Wani abin mamaki kuma shi ne ko mutum ya sayesu, ba za su koma tushiyar dawa ba, har sai ya kai gida. [27]

RIKIƊAR KANBULKU: Wata irin rikiɗa ce da wasu mutane ke yi mai kama da rufa-ido. A inda zaka ga wata dabba ta nufoka, amma kuma ba ita ba ce. Wannan rikiɗa akan yi ta ne don nuna gagara da kuma firgita abokan gaba. Wasu lokuta akan yi ta ne a wararen tararruka na biki, kamar kalankuwa, taron daba, ko bikin nuna amfanin gona, ko farauta tsakanin wani gari da wani gari. Ko da yake akan yi irin wannnan rikiɗa ne a Ƙasar Hausa da maƙwabtansu. To amma kuma akan samu ‘yan bambance bambance daga wannan gari zuwa wancan.

a

RIKIƊAR MATSAFA: Akwai rikiɗa wadda matsafa kan yi idan suka tashi yin tsaface-tsafacensu. Wani lokaci sukan yi ne don nuna buwaya, ko fifiko ga junansu. A wani lokaci kuma sukan yi domin neman biyan bukata ga iskokai ko abin bauta. Akwai wasu matsafa waɗanda kan rikiɗa da daddare zuwa wata dabba ta hanyar surkulle ko saddabaru, da sukan yi.

RIKIƊAR MAYU: Mayu kan rikiɗa zuwa wata dabba, ko kuma su rikiɗar da kurwa wani mutun da suka kama zuwa wata dabba ko tsuntsu. Akan samu irin wannan ne idan maye ya so ya ɓatar da sawu, sai ya sanya kamannu ya rikiɗa zuwa wata dabba kamar kura, ko zaki, ko mage, da sauransu. Bayan wannan mayu kan rikiɗar da kurwar mutumin da suka kama, idan basa son cinyeshi sai su mai da shi wata dabba ko tsuntsu. “Ni ina zama kura ne, shi kuma yana zama zaki”. Sule Butu wushishi (2012) D V D Plate mai kama mayu da cire maita.

RIKIƊAR MAHARBA: Akwai wata rikiɗa mai dangantaka da sihiri, ko tsafi, ko dabo, wanda Maharba kan yi, don su kuɓuta daga wani haɗari da suka tsinci kansu a ciki. Misali in suka gamu da wata dabba mai haɗari. A wani lokaci kuma idan maharbi ya so ya nuna gagara ko kuma wani maharbi na son ya faɗa masa ko halakashi,sai ya rikiɗa ya koma wata dabba don ya tsira daga shairin abokin a dawa.

RIKIƊAR ƁARAYI: Ɓarayi da suka riƙa (gagara) , kan rikiɗa wata dabba. Akwai dalilan da kan sanya su rikiɗa, kamar shiga runtsi (hatsari) kamar zasu halaka sai su rikiɗa. Wasu kuma in suka so shiga wani gida sai su nuna buwaya. Wasu kuma sai an kama su sai su ɓace. Tunanin Bahaushe game da rikiɗa da dabbobi kan yi zuwa wata dabba ko iskoki su rikiɗa zuwa dabba, ko mutane su rikiɗa zuwa dabba. Babu jayayya akan haka,saboda abin har yanzu yana faruwa.

SHIGAR BURTU: Ita wannan ba za’a kira ta rikiɗa ba, sai dai a ce ba-saje. Domin abin dake faruwa shi ne, maharba kan samu kan wani tsuntsu wanda ake kira burtu. Bayan sun ɗaura shi a jikin wata sanda sai kuma su ɗaura a kansu sannan su lulluɓe jikinsu da wani mayafi. Dabarar da suke yi a nan ita ce, zasu rinƙa duƙawa suna duƙar da kansu kamar yadda tsuntsaye ke yi. Irin wannan shiga kan yaudari tsuntsaye su saki jikinsu su yi zaton wani tsuntsu ne ɗan uwansu yake yin kiwo. A irin wannan lokacin ne maharba kan mamayi tsuntsaye su harbesu, su kamasu. A wani lokaci kuma idan maharba suka shirya biki sukan yi wasan burtu, don kawai su nuna buwaya da kuma cewa su ‘yan gado ne.

NAƊEWA.

A wannan muƙala ta ƙunshi wasu bayanai, a kan irin yadda Bahaushe ke kallon rayuwar dabbobi da tsuntsaye. Ta fuskar abin da ya shafi rikiɗa a tunaninsa. Wannan irin matsayi ne har ya haifar da Bahaushe ke alaƙanta wasu ɗabi’u waɗanda akan yi tarayya tsakanin ɗan Adam da dabbobi da tsuntsaye. Bayan wannan muƙala ta kawo bayanai game da ma’anar rikiɗa da ire-irenta, tare da dalilan dake yin sanadinsu. Haka kuma muƙalar ta dubi irin yadda Bahaushe yake alƙanta tasirin iskoki ga dabbobi da tsuntsaye.

Bisa dogaro da wasu hujjoji da aka samu ta fuskar al’ada, da addinin Musulunci sun ƙara ƙarfafa tunanin Bahaushe. Bayan haka kuma tare da duba wasu rassa na adabinsa, don ƙara wa bayanan da aka kawo a wannan bincike, turaku. Wannan muƙala ta fito da wasu abubuwa waɗanda a baya ba a damu da su ba. Waɗannan abubuwa kuwa sun haɗa da: rikiɗa, da ire-irenta, da dalilai da kan sa a yi, da rikiɗar dabo, da kanbulku. Tare da gano cewar ana yin magani da naman wasu dabbobi ko tsuntsaye don a rinƙa rikiɗa. Misali naman wasu dabbobi kamar hawainiya, da kuma tsuntsaye irin makwarwa.

 MANAZARTA.

Abraham R. C. (1947) Dictionary of the Hausa Language, London Hodder &Stoughton

Bargery. G. F. (1993) A Hausa-English Dictionary andEnglish-Hausa

 Vocal Amadu Bello University Zaria.

Bello M (2011) Mahaɗin Dabbobi A Magungunan Hausawa M. A. Hausa Jami’ar Usman Fodiyo Sakkwato.

Bukar. B. A. ( 2008) Mu Yangidan sarautar Macina,muna da alaƙa ta jini da

 Jaridar Leadership Hausa.

Bunza A. M. (2006) “Gadon Feɗe Al’ada”,Tiwel Nigeria Limited Lagos.

Bunza A. M. (2009) “Narambaɗa”,Ibrash Islamic Publication Centre Limited Lagos

Bunza A. M (2011) “Kura a ma’aunin Adabin Hausa”, Muƙala.

 Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua a Katsina

Haruna A. (2010) “Maharbi ya harbe wata tsohuwa a matsayin

 Barewa”. Jaridar Aminiya.

Kutama. M. (2008) Wata budurwa ta rikiɗa zuwa macijiya a Fatakwal.

 Jaridar Aminiya.

MaiYama. U. H. (2008) Sata a zamantakewar Hausawa. Nazari a kan Waƙoƙin Ɓarayi Na Muhammadu Gambo Fagada. Ph. D. Hausa.

 Usman Ɗanfodiyo university Sokoto.

Mu’azu. A. H. (2009) Gurbin Dabbobi da Ƙwari a cikin Waƙoƙin Baka na Hausa”. M. A Hausa Proposal. Usman Ɗanfodiyo University, Sokoto.

Mahe I. A (2008) Amfani da Dabbobi a fagen gina Adabin Hausa”.

 M. A. Hausa. Bayero University Kano.



[1] Encarta Softwire English Dictionary (2009) :

[2] A dubi Ƙamus mai suna Almaurid na Ingilishi zuwa Arabiyya. AlƊaba’at Al-Hadiyata Asharat (eleventh edition) , 1977, Shafi na 681.

[3] A dubi A.A.Dunfawa “Tunanin Bahaushe a cikin Littafin Ruwan Bagaja” Shafi na biyu cikin Special Research Project in Humanities,2013, U.M.YU.Katsina.

[4] Oxford Advanced Learner’s Dictionary Oxford New York (6th edition) 2000, pg 872,

[5].Bargery, G. F. (1993) A Hausa-English Dictionary and English-Hausa Vocabulary Ahmadu Bello University Zaria.

[6] Encyclopedia Britanica Volume iv page 350

[7] A English-Hausa Dictionary Skinner (1970) N.N.P.C. Zaria.

[8] Hornby.A.S (2006) Oxford Advanced Learner’s Dictionary University Press NewYork

[9] ENCARTA Softwire English Dictionary2009

[10] Ƙamusun Hausa B.U.K. ( 2006).

[11]Oxford Advanced Learner’s Dictionary Oxford New York (6th edition) ( 2000) 739

[12] Sa’idu Abubakar hira da shi a bakin Kasuwar Sati Kaduna 18/6/2012.

[13] Sulaiman Muhammed hira da shi a Kasuwar sati Unguwar Dosa Kaduna laraba 17/4/2013.

[14] Baturen Dutse Wusasa Zariya Sarkin Baka KSMC Rediyon jahar Kaduna

[15] Alasan Muhammad Kano hira da shi a garin Sokoto.22/7/2004

 

[16] Muhammad Dahiru Yawuri hira da shi a Runji Sambo Sakkwato.10/1/2013.

[17] Hira da Idris Shu’aibu Gimba a Kwalejin Tunawa da Sardauna Kaduna 23/6/2009

[18] Yahaya I.Y. (1971) “Tatsunniyoyi da Wasanni”, Oxford University Press,Ibadan.

[19]Yusuf Sadau hira da shi a Bakin Kasuwar Sati unguwar Dosa Kaduna 23/8/2012

[20] Abubakar Imam Magana jari ce littafi na I,1937.N.N.P.C.Zaria.

 

[21] Dubi Littafin Gadon Feɗe al’ada na Bunza AM (2006)

[22] Bunza AM (2006) Gadon Feɗe al’ada

[23] Dubi littafin Gadon feɗe al’ada BunzaAM (2006)

[24] Imam Malik littafin muwaɗɗa malik

[25] Haruna A. (2010) “Maharbi ya harbe wata tsohuwa a matsayin Barewa”. Jaridar Aminiya.

[26]Jauro Muhammad hira das hi Unguwar D osa 17/12/2012

[27] Malam Jafaru Kano hira das hi a kasuwar sati Unguwar Dosa Kaduna 13/10/2012

Hausa Post

Post a Comment

0 Comments