Ticker

6/recent/ticker-posts

Riga-Kafi Ya Fi Magani

NA

Mu’azu Sa’adu Kudan

TAKARDAR DA AKA GABATAR A KWALEJIN NAZARIN HARSHEN LARABCI DA ADDININ MUSULUNCI TA SHABABIL ISLAM UNGUWAR DOSA KADUNA, 16 SATUMBA 2011.

SHIMFIƊA.

 Kalmar riga-kafi kalma ce mai harshen damo, watau mai ɗauke da ma’anoni fiye da ɗaya. Bahaushe kan yi amfani da wannan kalma a wurare da yawa, kuma ta fuskoki daban-daban.

RIGA: - Asalin gaɓar kalmar ta farko ta fara ne da “Riga” mai nufin ka shirya wa wani abu kafin zuwansa, watau kafin faruwar wani abu ko ciwo to ya iske ka cikin shiri, kamar ka tanaji magani kafin zuwan ciwon, ko kuma ka kawar da wani abu da zai yi sanadin ciwon, ko kaucewa wani abu da zai jawo maka ciwon. Kamar tsafta, riga-kafi ce ga cututtuka, barin gardama riga-kafi ne ga husuma (faɗa) da sauransu.

KAFI: - Gaɓar kalma ta biyu ta samo asali ne daga wani abu da Bahaushe ke yi da ake kiransa da “kafi”, shi kuwa wasu dabarbaru ne da ake yi don neman tsari musamman gida da iyali. Mai gida kan harhaɗa wasu saƙe-saƙi da ganyayyaki da sassan jikin wasu dabbobi ko tsuntsaye don haɗa wannan magani, don kariya daga ɓarawo, hari, gobara da sauran hatsararruka.

Bisa bayanin da ya gabata, muna iya cewa, idan Bahaushe yace ka yi riga-kafi, yana nufin ka ɗauki wani mataki na hana aukuwa ko faruwar wani mugun abu, kamar ciwo da makamantansu. Musamman ta fuskar Magana ko kula da rayuwa ta hanyar yin kaffa-kaffa tare da lura.

GABATARWA.

 Da sunan Allah Mai rahama Mai jinƙai, Mai kowa, Mai komai, Mai aikata abin da Ya so, ga wanda Ya so, a sadda Ya so a yadda Ya so, ko ana so ba a so dole bayi su so. Tsira da amincin Allah su tabbata ga shugaban halittu Annabi Muhammadu, da alayensa da sahabbansa.

Kamar yadda ake yin riga-kafin ciwon shan inna, ƙyanda, mai baushe (amai da gudawa) , kuturta da sauransu. Ni kuma a nawa tunanin sai na ga ya dace mu yiwa kan mu riga-kafin wasu abubuwa guda biyar, su ne kamar haka: -

1- RIGA-KAFIN CIWON HAUKA GA MATA.

1. Kasancewa cikin tsarki.

2. Lizimtar ambaton Allah.

3. Kama kai (natsuwa ko a shiga bayan ɗaki).

4. Nisantar kaɗe-kaɗe.

5. Nisantar bayyana tsiraici (jiki gaba ɗaya).

6. Kyautata niyya (Kishi da mu’amulla).

7. Lura da ƙunzugu.

8. Mayar da duk al’amari ga Allah (rungumar ƙaddara).

9. Kawar da dogon tunani.

2- RIGA-KAFIN FAƊAWA WUTA.

1. Kyautata tauhidi.

2. Mallakar zuciya.

3. Yawaita Istigfari.

4. Yawaita Karatun Ƙur’ani.

5. Girmama miji da mahaifa.

6. Gujewa butulci da rainuwa.

7. Tsare Allah.

3- RIGA-KAFIN LALACEWAR ‘YA’YA.

1. Samun uwa ta gari.

2. Ambaton Allah yayin kwanciya.

3. Kame harshe daga iyaye zuwa ga ‘ya’yansu.

4. Tarbiyya mai kyau.

5. Addu’a ta ƙwarai zuwa ga ‘ya’yansu.

4- RIGA-KAFIN MUMMUNAN KISHI.

1. Imani (Maganar Allah, Ƙaddara).

2. Nisantar jita-jita.

5- RIGA-KAFIN ZUWA GIDAN BOKA (MALAMIN TSUBBU).

 Bayan haka, wannan riga-kafi ya zama mana dole, mu kula da shi mu tsare, don ya zama kamar maganin da Bature ke ce masa “Psycho-Theraphy”, (Magani ta hanyar lallashi da shawarwari). Tabbas al’ummar mu na matuƙar buƙatar wannan magani, mazan mu da matanmu. Wannan dalili ne yasa na kira wannan Muƙala da suna “Riga-Kafi”.

 Bugu da ƙari, wannan muƙala ta ɗan taɓo wasu abubuwa ne ba wai an zurfafa ba, sai dai kawai don tunatarwa da faɗakarwa, domin kuwa dukkan abubuwan nan a sarari suke, kuma an sansu, sannan ana aikata su.

 A ƙarshe, ina fata wannan muƙala ta zama kamar allura ce ta magance waɗannan matsaloli a cikin al’ummar mu gaba ɗaya amin.



1. RIGA-KAFIN CIWON HAUKA GA MATA.

MA’ANAR HAUKA.

 Hauka wata cuta ce da kan kama mutum a sanadiyyar naƙasar da ƙwaƙwalwa ta samu, wanda kan sanya tawaya ko raunin hankali, da na tunani, ko kuma gushewarsu gaba ɗaya. Bisa dalilin ciwon yana kama ƙwaƙwalwa ne ita kuma a kai take, sai ace ciwon ya hau kai daga nan ya koma ya hau ka = ya koma “hauka”. Mai wannan ciwo ana kiransa da mahaukaci idan namiji ne, mahaukaciya idan mace ce, mahaukata idan suna da yawa (jam’i).

Hauka nau’i – nau’i ce dangane da sanadi ko ɗabi’un mahaukaci kamar haka: -

Ire-iren hauka (Sanadoji). Ire-iren hauka (Ɗabi’un Mahaukaci).

1. Haukar Gado. 1. Haukar dariya.

2. Haukar Sammu. 2. Haukar Sambatu.

3. Haukar Iskoki. 3. Haukar kurum/kawaici.

4. Haukar camfi. 4. Haukar kuka.

5. Haukar haɗari. 5. Haukar yawo (jewaɗe).

6. Haukar Gigita. 6. Haukar hagaga.

7. Haukar Damuwa. 7. Haukar Motsuwa.

8. Haukar zamani. 8. Haukar din-din-din.

 Bisa ga al’amarin mata akan ga ciwon hauka, ana iya cewa, haukar iskoki (gamo) , ko ta sammu, ko ta kome, ko ta damuwa. Waɗannan sune aka fi samun mata masu yawa suna fama da su fiye da sauran nau’o’in ciwon hauka. Sakamakon fahimtar haka ne yasa na ga ya dace, mu ɗan tsakuro wasu matakan kare kai a matsayin riga-kafi.

 Ya kamata mata su kiyayi zuwa wurin ƙazanta ba tare da ƙwaƙƙwaran dalili ba, kuma dole ne su rinƙa bin ƙa’idojin da shari’a ta tsara game da shiga bayi da kuma wasu matakai kamar haka: -

1. Kasancewa cikin tsarki.

2. Lizimtar ambaton Allah (Zikiri).

3. Kama kai (natsuwa wajen shiga bayi).

4. Nisantar kaɗe-kaɗe.

5. Nisantar bayyana tsiraici, gashin kai da jiki gaba ɗaya.

2- RIGA-KAFIN FAƊAWA WUTA.

1- Kyautata Tauhidi: - Babban abin da ya kamata mutum Musulmi ya yi a rayuwarsa shi ne kyautata tauhidi, watau ya inganta imaninsa ta wajen kaɗaita Allah tare da kaucewa yi masa shirka, watau haɗa Allah da wani wajen bauta, ko neman taimako ko tambaya.

Wannan kuwa zai ƙudurta ne tun daga zuciya ya zuwa harshe, wato ya furta da baki, sannan kuma ya aikata da gaɓoɓinsa.

2- Mallakar Zuciya: - Mallakar zuciya na nufin mutum ya ƙirƙiri ko sanyawa zuciyarsa linzami, watau ba komai da zuciyarsa ta raya masa ba ne zai bi ko aikata ba. Dole ne ya yi ƙoƙari ya riƙa cijewa ko kaucewa tare da danne zuciyarsa musamman in yayi fushi, ya daure ya danne fushin ya yafe in aka saɓa masa, idan sha’awa ta taso masa ya dage kar ya saɓawa shari’a ya tsaya ga matarsa.

Bayan wannan kuma, idan harkar abin duniya ne da suka shafi kuɗI da sauran tarkacen duniya, kar ya bi son zuciya ya faɗawa haramun. Ya tilastawa zuciyarsa aikata alheri da sauran ayyukan ibada.

......... الا وإن فى الجسد مضغة, إذا صلحت صلح الجسد كله, وإذا فسدت فسد الجسد كله, ألا وهي القلب. رواه البخارى ومسلم.

……… To haƙiƙa a cikin jiki akwai wata tsoka, idan ta gyaru duk jiki zai gyaru, idan kuma ta ɓaci duk jiki zai ɓaci, watau ita ce zuciya. Buhari da Muslim ne suka ruwaito.

3- Yawaita Istigfari: - Mutum ya yawaita Istigafari safiya da maraice, saboda shi istigafari yana kankare zunubi kuma yana jawo alheri, sannan kuma yana sanya Allah Ya so mutum. Istigfari yana sanya mutum ya zama abokin gaba ga shaiɗan saboda shaiɗan zai rinƙa jin haushin mutum, domin ko ya sanya shi ya yi saɓon Allah sai ya tuba, watau yayi istigafari. Dama kuma Allah Yayi alƙawari cewar Yana son masu tuba, haka kuma idan mutum ya tuba da niyyar ba zai koma ga saɓo ba, to kamar bai taɓa aikata saɓon ba ne.

Haƙiƙa istigafari garkuwa ne daga faɗawa wuta, kuma Manzon Allah ya kasance yana yin istigfari sau saba’in (70) a wuni, to ina ga kai da ni da ke?

4- Yawaita Karatun Ƙur’ani: - Yawaita karatun Ƙur’ani na kawo alherai masu yawa kamar yawan lada, ceto ranar ƙiyama, shiryar da mutum, tsare shi daga shaiɗanu, jawo arziƙi da sauransu. Allah Ya yi alƙawarin cewa duk wanda ya karanta Ƙur’ani yana da lada goma akan kowanne harafi. Bayani ya gabata a hadisai cewa Ƙur’ani zai ceci masu karanta shi a ranar ƙiyama. Haka kuma yawan karatun ka da shi yawan darajarka a aljannah. Sannan kuma Ƙur’ani na shiryar da mai yawan karatunsa, saboda Allah da kanSa Ya kirashi da cewa: “Hudan Lil Muttaƙeen”. Bayan wannan kuma, karatun Ƙur’ani kan tsare mutum daga Shaiɗanu saboda mutum ba zai fara karatu ba sai ya yi Isti’aza, watau (A’uzu Billahi Minash Shaiɗanir rajeem) ). Haka kuma duk gidan da ake karanta Ƙur’ani shaiɗanu basa zama, sannan duk wanda ya karanta Ayatul Kursiyyu da dare, to har gari ya waye babu Shaiɗanin da zai kusanceshi, haka kuma in ya karanta da safe to har rana ta faɗi babu shaiɗanin da zai kusanceshi. Karanta Ƙur’ani na jawo arziƙi da wadata, kamar wani hadisi da ya nuna cewa yawaita karanta Suratul Waƙi’a yana kawo arziƙi, watau yana maganin talauci. Bayan wannan, sai wani hadisi da ya nuna cewa idan mai gida ya dawo gidansa, to yayi sallama kuma ya karanta Ƙulhuwallahu, lallai arziƙi zai sauka a gidan.

5- Biyayyar Mace ga Mijinta (Girmama Miji) : - Biyayyar mace ga mijinta wajibi ne saboda wani hadisin da Annabi Sallallahu Alaihi Wa-Sallam yayi umarni cewa da mutum zai iya yiwa wani mutum sujada, da an umarci mace ta yi wa mijinta sujada.

To amma da yake ba a yi wa kowa sujada sai Allah. Amma shari’a ta umarci mace ta yiwa mijinta biyayya iyakar biyayya matuƙar dai bai umarce ta da ta yi saɓon Allah ba.

Da wani zai iya yi wani sujada da mata ta yi wa mijinta sujada.

وعن أبى هريرة رضي الله عنه, عن النبي صلى الله عليه وسلم قال ( لو كنت أمرا أحدا أنيسجد لأحد لإمرت المرءت أن تسجد لزوجها) رزاه الترمذى وقال حديث حسن صحيح).

 An karɓo daga Abu Hurairah (R. A) Daga Manzon Allah (S. A. W) ya ce da wani mutum zai iya wa wani sujada da na umarci mata ta yi wa mijinta. (Tirmiziy ne ya ruwaito shi. )

GIRMAMA UWA.

 Lallai ya zama wajibi a girmama uwa a matsayin ta na uwa domin saboda irin wahalar da ta sha tun daga ɗaukar ciki, kamar yadda Allah (S. W. T) Ya tabbatar da haka a Al-ƙur'ani a surori biyu watau Suratul Ahazab da Luƙman.

حملته أمه كرها ووضعته كرها

Mahaifiyar ka ta ɗauki cikin ka

حملته أمه وهنا على وهن

Mahaifiyar ka ta ɗauki cikin ka rauni bisa rauni.

 Bayan wannan kuma, sai wani hadisi da yayi bayanin girman uwa ga 'ya'yan ta don kuwa wani ya tambayi Manzon Allah (S. A. W) cewa wa zai kyautata wa? Sai Manzon Allah yace masa mahaifiyar ka har sau uku.

عن أبى هريرة رضى الله عنه قال: وحين سئل النبى صلى الله عليه وسلم من أحد أصحابه: أى الناس أولى ببر يارسول الله؟ قال أمك، قال ثم من؟ قال أمك، قال ثم من؟ قال أمك. قال ثم من؟ قال أبوك. متفق عليه.

 An karbo daga Abu Hurairah (R. A) yace wata rana wani ya tambayi Manzon Allah (S. A. W) yace Ya Rasulillahi! Cikin mutane wa zan fi kyautata wa? Sai Manzon Allah (S. A. W) yace mahaifiyar ka, ya sake tambayar Annabi har sau uku yana ce masa mahaifiyar ka, sai a na hudu ne yace masa mahaifin ka.

Bukhari da Muslim ne suka ruwaito.

GUJEWA YAWAN BUTULCI (MANCE ALHERIN DA AKA YI MATA).

 A mafi yawan lokuta sukan mance duk alheri da abin arziƙin da ka taɓa yi musu, zasu ce maka me ka taɓa yi min?. Akan wannan ne ma Manzon Allah (S. A. W) yace ya leƙa wuta ya ga mata sun fi yawa, sai ɗaya daga cikin matansa tace: “Ya Rasulillah! Saboda me? Sai Manzon Allah (S. A. W) yace saboda butulcinsu domin komai daɗewar da mutum yayi yana kyautata muku da zarar wata rana ta zo to sai aka samu saɓani, sai kuce me mutum ya taɓa yi muku?

HAƊARIN BUTULCEWA MIJI.

عن ابن عساكر، عن عائشة رضى الله عنهما: قال النبى صلى الله عليه وسلم: إذا قالت المرأة لزوجها ما رأيت منك خيرا قط فقد حبط عمنها.

 An karɓo daga Ɗan Askar, daga Aisha (R. A) tace: Annabi (S. A. W) yace: "Duk macen da ta cewa mijinta bata taɓa ganin alheri daga wurin sa ba, to haƙiƙa ta ɓata ayyukan ta.

YAWAN AIKATA ALHERI NA GYARA ZUCIYA.

 Duk wanda yake yawan aikata alheri kama mai yin wa’azi, matuƙar ya dage yana yin wa’azin ko ya samu karɓa ko bai samu ba, Allah (S. W. T) zai ƙara masa imani a inda zai gyara masa zuciya.

 Bayan wannan, duk wanda ya tsare sallah ta zamar masa jiki ya saba, to lallai ne Allah Zai shiryar da shi, zuciyarsa zata shiryu. Kamar yadda wata aya tace: -

إن الصلاة كانت تنهى عن الفحشاء والمنكر....

Lallai sallah tana hana aikata mummunan aiki (alfasha) abubuwan ƙi….

 Akwai kuma yawaita azumi, matuƙar mutum ya lizimci azumi na farilla ko nafila, Allah (S. W. T) Zai gyara masa zuciya. Domi azumi na rage sha’awa kuma yana shiryar da zuciya.

YA KAI ƊAN’UWA! KA KIYAYE ABUBUWA SHIDA (6) KA SHIGA ALJANNAH.

 Haƙiƙa duk Musulmin da ya lizimci abubuwa shida (6) , lallai Manzon Allah zai lamunce masa shiga Aljannah. Wannan abubuwa kuwa su ne kamar haka: -

1. Faɗin gaskiya.

2. Cika alƙawari.

3. Kiyaye amana.

4. Kiyaye farji.

5. Kiyaye ido daga kallon haramun.

6. Kiyaye dukiyoyin mutane.

Baihaƙi ya ruwaito shi daga Ubadata Ɗan samit.

3- RIGA-KAFIN LALACEWAR ‘YA’YA.

ZAƁARWA 'YA'YA UWA TA GARI.

 Wajibi ne ga dukkan mahaluki mai hankali da yayi niyyar yin aure, to ya yi ƙoƙarin zaɓarwa 'ya'yansa uwa ta gari, ma'ana mai tarbiyya da son addini. Kar ya bi son zuciya ya auro mace don kyau, watau kyakkyawa, ko 'yar wane, watau mai nasaba (mai kuɗi, sarauta, muƙami). Wannan magana ta yi dai-dai da wani bayani da Manzon Allah (S. A. W) ya yi cewa ku auri mace ma'abuciyar Addini. Domin yace in ka yi aure don kyau, to lallai kyau kan ƙare in ta tsufa, ko nasaba don mulki na iya ƙarewa, amma shi Addini ba ya ƙarewa.

 Bayan haka, zaɓarwa 'ya'ya uwa ta gari kamar hutar da kai ne, domin in ka haifi yara da mace ta ƙwarai, to kamar ita ce makarantar su don zasu koyi komai na ƙwarai daga wurinta. Saboda masu hikima sun ce uwa ita ce makarantar farko ga yaro. Haka kuma in mutum ya kuskure ya auri Ballagazar mace mara tarbiya, to ya kashe kansa da kansa, kuma yaransa sun shiga uku. Babban dalili shi ne, ita ba ta da tarbiya, ba ilimi balle addini, to a nan ina makarantar farko take? Sai dai su koyi zagi da miyagun halaye.

HAƘƘIN AMBATON ALLAH

وعن معاذ رضى الله عنه قال: قال النبى صلى الله عليه وسلم: "أكثرو ذكر الله تعالى على كل حال, فإنه ليس عمل أحب إلى لله ولا أنجى لبعده من ذكر الله تعالى فى الدنيا والآخرة".

 An karɓo daga Mu'azu (R. A) yace: Manzon Allah (S. A. W) yace: "Ku yawaita ambaton Allah a kowane lokaci da hali domin cewa babu wani aiki da Allah Yafi so kamar zikiri.

HAƘƘIN RANTSUWA.

 A musulunce, haramun ne musulmi in ya tashi yin rantsuwa ya rantse da wani abu da ba Allah ba. Wajibi ne in musulmi ya tashi zai rantse, to ya rantse da Allah (S. W. T).

HAƘƘIN ADDU'A.

 A shari'ar musulunci, wajibi ne musulmi in ya tashi yin addu'a to ya roki Allah (S. W. T) kar ya roƙi wani abokin halitta, sai dai Allah. Addu'a ibada ce don haka yi wa wanin Allah shirka ne, dole ne kuma musulmi ya guji yin shirka ta kowacce fuska.

HAƘƘIN AMBATON ALLAH (ZIKIRI).

عن أبى الجوزاء مر سلا قال: قال النبي صلى الله عليه وسلم: أكثرواذ كرو الله تعالى حتى يقول المنافقون إنكم مرائون.

 An karɓo daga Jauza'iy Mursalam (R. A) yace: Manzon Allah (S. A. W) yace: "Ku yawaita ambaton Allah (zikiri) har munafukai suce ku masu riya ne.

HAƘƘIN UWA A KAN ƊANTA.

 Matsayin da uwa take da shi a wajen ɗan da ta haifa ba ƙarami ba ne. Dalilin wannan matsayi ne ya sa Allah Ya baiwa uwa muhimmin matsayi na baiwa da martaba wanda ko da baki (magana) , ba addu'a ba yake kama yaron (ɗanta). Matuƙar aka ce uwa ranta ya ɓaci a kan wani al'amari da ɗanta ya yi a wani lokaci ko ba tayi addu'a ba, duk abin da ta furta Allah kan karɓi addu'ar.

 Haka kuma matuƙar uwa ta yi wa ɗanta kyakkyawar addu'a ba zai taɓe ba a rayuwarsa. Misali wani bawan Allah mai bauta a cikin Banu Isra'ila wanda yana ibada uwarsa ta zo tana kira bai amsa ba, ranta ya ɓaci ta yi masa muguwar addu'a tace Allah Ya haɗa fuskar sa da ta karuwa, cikin ikon Allah sai da ya ga mugun abu.

 A wannan matsayi ina kiran 'yan uwana da mu lallaɓa mahaifan mu ko rayuwarmu ta yi kyau. Su kuma iyaye su danne fushinsu, su daina furta miyagun maganganu ga ‘ya’yansu don samun kyakkyawar al’umma nan gaba.

TARBIYYAR ‘YA’YA YA RATAYA WUYAN IYAYE.

 Nauyin yiwa ‘ya’ya tarbiyya ya rataya ne a wuyan iyaye watau uba da uwa. Wanda ya haɗa da: -



1. Sanin Allah.

2. Son Annabi da Alayensa.

3. Karatun Ƙur’ani.

4. Sallah.

5. Girmama na gaba.

6. Koyar da magana.

7. Koyar da tafiya.

8. Koyar da cin abinci.

9. Koyar da kwanciya.

10. Koyar da kunya.

11. Gudun kwaɗayi.

12. Barin hassada.

13. Koyar da ƙwazo.

14. Koyar da tsafta.

15. Koyar da tattali.

16. Koyar da zumunci.

17. Koyar da tausayi.

18. Koyar da kallo.

19. Koyar da tsare amana.

20. Gujewa ƙarya da gujewa gaskiya.



FALALAR RAINON 'YA'YA MATA.

 Akwai wata garaɓasa wadda Allah (S. W. T) ya tanadarwa duk mutumin da ya raini 'ya'ya mata har zuwa girmansu kuma suka yi aure. Wannan kuwa ya bayyana a wani hadisi da Manzon Allah (S. A. W) ya yi bayani a kan haka.

Kamar haka: -

 "Manzon Allah (S. A. W) yace dukkan wanda ya ɗauki nauyin 'ya'ya mata guda biyu ko uku ko 'yan uwa biyu ko uku har suka girma (suka yi aure) , ko kuma ya mutu ya bar su, zan kasance ni da shi a cikin Aljannah kamar haka, sai yayi nuni da hannunsa manuni da wanda yake binsa. Kuma zai samu ladar mai jihadi don ɗaukaka kalmar Allah, wanda yake azumi da sallar dare a wurin jihadin. Sai wata mace tace har 'ya ɗaya? Sai Manzon Allah (S. A. W) yace har da mai 'ya ɗaya. "

وعن أنس رضى الله عنه، عن النبى صلى الله عليه وسلم قال: من عال جاريتين حتى تبلغا جاء يوم القيامة أنا وهو كهاتين.

 An karɓo daga Anas (R. A) yace, daga Manzon Allah (S. A. W) yace, duk wanda ya raini (riƙe) yara mata biyu har suka girma, watau suka balaga, ranar ƙiyama zai zo ni da shi haka…..

عن عبد الرحمن ابن مرقع رضى الله عنه قال: قال النبى صلى الله عليه وسلم: إنه لا وعاء إذا ملئ شر من بطن، فإن كنتم لا بد فاعلين، فاجعلوه ثلثا للطعام وثلثا للشراب، وثلثا للريح أو النفس.

الإمام السيوطى.

 An karɓo daga Abdurrahman Bin Marka'a (R. A) yace: Manzon Allah (S. A. W) yace: "Babu wata jaka da za a cika ta fiye da ciki, in ya kasance babu makawa ku masu aikata haka ne, ku sanya shi kashi ɗaya don abinci, kashi ɗaya domin abin sha (ruwa) , kashi ɗaya domin shaƙar iska ko numfashi.

Suyuɗi ya ruwaito.

1. An hana yin mugun ci.

2. An hana cin abinci mai zafi.

3. An hana hura abinci da baki.

4. An hana da an gama cin abinci a kwanta.

5. An hana cin abinci ham-ham, (hannau baka hannu ƙwarya).

6. An hana cin abinci har sai an ji yunwa.

7. An hana surutu in ana cin abinci.

4- RIGA-KAFIN MUMMUNAN KISHI.

IM ANI.

 Imani shi ne yarda da abu, watau yarda da ƙaddara. Abin da yasa Bahauhshe yake cewa haka shine, imani yana da rassa shida sune: -

ü Imani da Allah.

ü Imani da Mala’iku.

ü Imani da LittattafanSa.

ü Imani da ManzanninSa.

ü Imani da tashin ƙiyama.

ü Imani da Ƙaddara mai daɗi da mara daɗi, (mai kyau da mara kyau. )

 Bugu da ƙari, Allah Yace: “Ku shiga Addini gaba ɗaya”. Sannan Yace: Zaku yi imani da wani sashe na Ƙur’ani ku kafirce wani sashinsa? Allah (SWT) da kanSa yake cewa musulmai su yi aure, sannan kuma da mata biyu ya fara yin umarni sannan uku, sannan huɗu, sai a ƙarshe ne aka ce ku auri mace ɗaya in kuna tsoro ba zaku yi adalci ba a tsakaninsu.

KYAKKYAWAR ƊABI’A.

HARAMCIN ƘAURACEWA MIJI A SHIMFIƊA.

 Shari’ar Musulunci ta yi hani ko haramta mace ta ƙauracewa mijinta a shimfiɗa, watau lokacin kwanciya in ya buƙace ta, ma’ana ya kira ta, saboda zata shiga fushin Allah, Mala’iku zasu yi ta tsine mata har sai gari ya waye.

وعن أبى هريرة رضى الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: إذا دعا الرجل امرأته إلى فراشة فلم تأته فبتا غضبان عليها العنتها الملائكة حتى تصبع. متفق عليه.

 An karɓo daga Abu-Hurairah (R. A) , yace Manzon Allah (S. A. W) yace: Idan miji ya kira matar sa zuwa shimfiɗarsa, watau ya nufi ya kwanta da ita amma ta ƙI, ma'ana ta ƙi yarda da shi, har shi mijin ya yi fushi da ita, Mala'iku zasu yi ta tsine ma ta har zuwa asuba. Bukhari da Muslim suka ruwaito.

KYAKKYAWAR ƊABI’A. (HANIN CUTAR DA JUNA. )

Shari'ar musulunci ta yi hani tare da cutarwa a kan ɗan uwa musulmi ya cutar da wani ko ta wacce irin fuska kuma komai ƙanƙantar abu, in dai zai cutar da ɗan'uwa, to aguje shi. Babban misali shi ne, ba wani aiki ba ko magana, hatta kallo ba a yarda ka yi wa ɗan'wan ka ba. Ku zama kamar jiki guda in wata gaɓa ta kama ciwo, to sauran ma su amsa. Ku zama masu ƙaunar juna. Ga wani babban misali, shi ne a wani hadisi: -

 عن أبى هريرة رضى الله عنه، أن النبى صلى الله عليه وسلم قال: ولا تحاسدوا، ولا تناجشوا، ولا تباغضوا، ولا تنابروا، ولا يبع بعضكم على بيع بعض، وكونوا عباد الله إخوانا. المسلم أخوالمسلم، لايظلمه، ولايخذ له، ولا يكذبه، ولا حقره، التقوى ههنا، وبشر إلى صدره ثلاث مرات. بحسب أمرئ من الشر أن يحقر أخاه المسلم غلى المسلم حرام، دمه وماله، وعرضه. رواه مسلم.

 An karɓo daga Abu hurairah (R. A) yace: Manzon Allah (S. A. W) yace: "Kada ku yi wa juna hassada, kuma kada ku yi wa juna ƙyashi, kuma kada ku yi ƙiyayya, kuma kada ku yi wa juna ruɗi a ciniki, kuma kada waninku ya yi ciniki a kan cinikin waninsa. Ku zama bayin Allah 'yan uwan juna. Musulmi ɗan uwan musulmi ne, kada ya zalunce shi, kuma kada ya taɓar da shi, kuma kada ya yi masa ƙarya, kuma kada ya wulaƙanta shi. Tsoron Allah a nan yake, (ya faɗi haka sau uku yana nuna ƙirjinsa). Ya isa sharri ga mutum ya wulaƙanta musulmi ɗan uwansa. Musulmi, jininsa da dukiyarsa da mutuncinsa haramun ne. " Muslim.

NISANTAR JITA-JITA.

 Jita-jita na nufin ɗauka ko yarda da labarai ko maganganu barkatai daga bakin mutane ba tare da bincike ba. Misali akwai labarin cewa mijin ki yayi kaza, ko yace kaza, ko an ganshi da wata ko a wani wuri da sauransu.

 Allah Yace idan fasiƙi ya kawo labari to ku bincika. Domin duk wanda ake kawo masa labari ba tare da yayi bincike ba, kuma har ya ɗauki mataki to zai yi nadama wataran.

5- RIGA-KAFIN ZUWA GIDAN BOKA (MALAMIN TSUBBU).

BOKANCI.

 Bokanci wata daɗaɗɗiyar hanyar binciken cututtuka da nazarce-nazarcen itace da ƙwari da dabbobi da halittun sama da ƙasa, da na sarari da na ɓoye (iskoki) domin samar da magani da warkarwa da mabuƙata. Babu wanda ya san lokacin da Bahaushe ya fara sarrafa magungunansa.

 Bayan Boka, akwai magori da ‘yar maiganye shi magori wani mutum ne da yake ɗaukar jaka da ake kira jakar magori, mai ɗauke da saƙe-saƙI, ganyayyaki, guraye, layu, fatun sassan jikin wasu dabbobi da tsuntsaye da sauransu don yin talla layi-layi kwaro-kwaro, ita kuma ‘yar mai ganye tana yawo da Kwando cike da tarkace saƙe-saƙI, ganyayyaki kamar dai magori. Tana shiga gidaje don yin talla.

 Bayan waɗannan, sai sarkin mayu wanda shi ma yana tallar magani da jakarsa, kuma har yakan fitar da ƙanƙarar maita daga cikinsa.

 Magani: - asalin Kalmar ya samo ne daga sha-ma-gani, sha-mu-gani, gwada-mu-gani, sai ya koma sha-mu-gani, magani sai da gwaji. Magani sai Allah don itace sinadari ne.

TSUBBU.

 Tsubbu wata kalma ce da ta samo asali daga harshen larabci wadda ake kira “Ɗibbu” mai nufin magani. Bahaushe sai ya ɗauki wannan kalma ya bata wata ma’ana mai nufin magani ta hanyar addini da aka harmutsa ta hanyar duba, watau ilmin taurari ko kuma a haɗa jiƙe-jiƙen magunguna da rubuce-rubuce ta hanyar amfani da wasu ayoyi ko surori daga Alƙur’ani, ko kuma a zaɓo wasu laƙuna da asirai daban-daban.

ƊIBBU.

 Malamai masu ɗibbu ba su da ilmi da yawa galibinsu sai Alƙur’ani kaɗai suka sani, wasu kuwa sai su fara da karatun huru’a kawai, kamar su Ahalari da ishimawi da su Ƙawa’idi har Risala. Amma su waɗanda suka yi zurfi, wani lokaci suna yawo da ‘yan ƙullinsu, watau almajiransu, waɗanda suka isa sai a iske su a gidajensu.

 Malaman ɗibbu su sukan yi rubutun sha, maganin farin jinni da na tsautsai, da sauran irinsu, kuma sukan yi ɗibbu su rubuta laya su ba mutane, su kuwa mutanen su basu kuɗi. wannan shi ne iyakar batun ɗibbu.

MALLAMI.

 Kalmar malami ita ma kalma ce da ta samo asali daga harshen larabci mai cewa: “Mu’allimu ko Mu’allim”. Bahaushe ya datse ya komar da Kalmar zuwa Mallam, mai ma’anar masani watau wanda ya san ilmi a fagage da yawa.

MALLAMIN TSUBBU.

 Na nufin malamin da ya san ilmin taurari (ilmin nujum) , da kuma wasu asararru da wasu malamai suka ciro daga littattafai da Ƙur’ani da hadisai. Amma wasu suka fara haɗawa da ƙulunboto da aljani da sauransu.

HAƊARIN ZUWA GIDAN BOKA (TSUBBU)

 (Mu kiyaye mu samu tsira da mutunci da imani).

 Bisa dogaro da wasu hujjoji na zahiri kuma bayyanannu da suka faru a garuruwa da dama, sannan a lokutta daban-daban. Waɗannan abubuwa da suka faru, sun shafi mutane daban-daban. Ga dukkan mai hankali wannan bayani ya wuce jayayya in dai ba a sa son zuciya ba.

 Akwai haɗurra masu yawa da ake iya gamuwa da su, ko faɗawa ciki, a dalilin zuwa gidajen bokaye da ‘yan tsubbu. Tun da farko dai zuwa gidansu tare da gaskata su saɓawa Manzon Allah ne. domin yace duk wanda ya tafi wurin boka ya kuma gaskatashi to an saɓa wa (Annabi (S. A. W) ).

Haɗarin zuwa gidan Boka da Malaman Tsubbu.

· Kaɗaicewa.

· Tonewa kai asiri.

· Asarar dukiya.

· Shirka.

· Jayayya da Allah.

· Ridda.

· Zina.

· Cin Amana.

· Kome.

· Tozarta/Nadama.

 Bayan wannan kuma, sai wani saɓon shi ne keɓewa da mace da namiji su biyu, bayan kuwa Annabi ya hana, to ashe yin haka shi ma saɓawa Annabi ne.

 Bayan wannan sai tonawa kai asiri, domin zaki tonawa kan ki asiri ta hanyar bayyana sirrinki da na mijinki ga wani, wanda kin roƙi Allah ke da shi ki yi addu’a ko aikata wani aiki na alheri ko lada sai ki yi tawassuli da aiki ki yi addu’a. akwai asarar dukiya da za ki yi, domin wasu ba sa yin wani aiki ko roƙon Allah da akan ce, sai dai kawai su yi maki wayau su karɓe maki kuɗi, wanda waɗannan kuɗi da kin bar su kin yi wa mahaifanki wani aikin alheri ko abokan mahaifa ko wasu gajiyayyu, ko yara marayu ko maƙwabta, kai ko mijinki ki bai wa sadaka ko kyuta zaki samu lada a wurin Allah kina kuma iya yin tawassuli da aikin a wurin addu’a.

 Akwai wani mummunan haɗari da ake iya gamuwa da shi a dalilin zuwa gidan boka shi ne haɗarin shirka. Matuƙar boka ya riƙa baya aiki shi kaɗai sai da taimakon shaiɗanu ko iskoki wanda su ba sa yi maka aiki sai kai ma ka yi masu wanda yayi kama da bauta ko haɗa Allah da wani.

 Wasu dalilai da suke kai mata wurin boka sun haɗa da neman haihuwa, korar kishiya ko mallamakar miji.

 Game da maganar haihuwa, kowa ya san Allah ke bada haihuwa ba boka ba, don haka ki roƙi Allah don Shi ke bayarwa. Tafiya nema wurin wani kuskure ne.

 Dangane da maganar kishiya, korar ta ko hana ta zuwa gidan mijinki. Dukkan Musulmi yayi imani da ƙaddara, don haka abin da Allah ya ƙaddara, ba boka ba, in duk duniyar nan zaki tara don su taimake ki ba za su iya ba. Haka kuma wani bai haihuwar ɗan wani, Allah Ya rubutawa mijinki ‘ya’ya 10 ko 15, ke kin haifi 7 ko 9, to kina tsammanin sauran ba zasu zo ba ne? to gaskiyar al’amari shi ne kowa an rubuta abin da zai Haifa tun alimiz zarri, don in kika ce wai baki yarda ba, to kina jayayya ne da ƙaddarar Allah.

 Haka kuma al’amarin da ya shafi mallakar miji kuwa, boka bai kai yadda ke zaki yi ki samu kan mijin ki ba. Matuƙar ki ka gyara halayenki da dabaru na nuna ƙauna ko tsare amana da sauran abubuwa, suna iya baki matsayin mallakar miji ba boka ba. Shi dai zai sa ki cikin halaka da shirka. (Hikayar mai macizai).

 Bayan haka, kuma boka yana iya sanya ki kiyi ridda ba tare da kin sani ba. Akwai wasu bokaye da sukan haɗa ƙulonboto tare da sunan Allah ko ayoyin Alƙur’ani, sai kuma su saki ki sanya wata laya a cikin najasa, masai (shadda) , juji, kwata, suri ko tsohuwar rijiya, ko ace ki sa a cikin mushen jaɓa. duk mutumin da ya aikata wannan ya wulaƙanta ayar Ƙur’ani don haka ridda ne. ban da wannan kuma, in kika yi wa wata sihiri (tsafi) ta haukace, to duk saɓon da ta yi haƙƙin na kanki, in kuma mutuwa ta yi, to kin yi kisan kai. Allah kuma yace “Duk wanda ya kasha mumini da gangar sakamakonsa Jahannama mai dauwama a cikinta”…….. in wani ciwo ne kika sanya mata ki saurrari naki ko akan ‘ya’ya ko jikoki a matsayin komen sammu.

 Wani babban haɗarin da mata kan gamu da shi a dalilin harka da bokaye shi ne faɗawa tarkon zina, saboda sau da yawa wasu mata sukan faɗa tarkon da bokaye ke yi musu ta hanyar sihiri ko dabaru har sai sun yi zina da su. Akwai wasu matan har cikin shege suke samu a sakamakon zina da bokaye. An samu shaidun faruwar haka a garuruwa a kafafen watsa labarai, kamar rediyo da talabijin da jaridu, kuma har yanzu wasu basu bari ba.

 Wani haɗarin shi ne, zuwa wurin boka na jefa mata cikin cin amanar mazajensu, kamar ya yarda da ita, amma da zarar ta fara zuwa wurin boka zata fara ha’intarsa, don kuwa babu izininsa zata tafi, ta tona asirinsa ga wani ya ba ta wani magani ko laya ta sa masa a abinci ko filo (matashin kai) , ko a takalmi da sauran wurare na ha’inci kuma a munafunce, saboda ba zata so ya sani ba.

 Akwai wani haɗarin da mata kan gamu da shi, saboda zuwa gidan boka, shi ne kome, kome na nufin mutum yayi sammu ko makaru don ya cutar da wani, to in aka yi rashin sa’a sai ya komowa wanda yayi. A irin nan ne ake samun haukar kome da ake cewa aniya makomiya, ko aniya-bi-aniya, ko ƙaiƙayi koma masheƙiya.

 Bayan wannan, sai tozarta tare da nadama da mata masu zuwa gidan boka kan gamu da su. Mafi yawan mata dake hulɗa da bokaye asirinsu kan tonu, a wani lokacin ma basu ci nasara ba, mazajensu su kore su, kuma a yo kishiya har ta haihu, ita kuma ba ɗan, kuma bata mallaki mijin ba, ga saɓon Allah da ManzonSa ga asarar kuɗI da mutunci (ta yi rasasa-rasasa).

 Aƙarshe ina kira da babbar murya mata har da maza ma da mu kiyayyi bokaye don gudun kar mu yi saki-na-dafe, ba tsuntsu ba tarko, Allah Ya tsare mu.

KAMMALAWA.

 Wannan ɗan ƙaramin bincike ya kammala cikin ikon Allah. Domin ƙoƙarin gano wasu hanyoyi ko dabaru waɗanda nake ganin za su taimakawa al’umma ta fuskar kare kai a matsayin riga-kafi daga faɗawa ko kamuwa da wasu abubuwa a rayuwar mu gaba ɗaya.

 Da farko dai mun ga taken da na baiwa wannan Muƙala tare da dalilai na, domin na kalli abin ta fuskoki da dama, kuma ina fatan an karɓi wannan take da na sanya.

 Bugu da ƙari, in aka kalli wannan Muƙala ana iya cewa ta yi harshen damo, ko kuma ace mata hatsin bara, bisa dalilin ta shafi al’ada, ta kuma shafi addini, koda yake daman abubuwa ne guda biyu da ba mai ‘iya raba su don sun yiwa juna shigar giza-gizai, haka kuma ta shafi duniya da lahira da kuma lafiya da tattalin arziƙi da sauransu. Ina fatan Allah ya taimaka mana amin. Alhamdu lillah.

MANAZARTA.

Sa’adu M. M (2007) HAUKA DA IDON BAHAUSHE. Kundin bincike digiri na biyu M. A-Hausa. Usman Ɗanfodiyo University, Sokoto.

Saulawa M. I. (2000) Jagorar Fahimtar Ciwon taɓin hankali.

 Al’sam Printers Katsina.

Bunza A. M. (2006) GADON FEƊE AL’ADA.

 Tiwal Nigeria limited suru lere Lagos.

Bunza A. M. (1995) MAGUNGUNAN HAUSA A RUBUCE (Nazarin Ayyukan Malaman Tsibbu) ,Kundin digiri na uku Phd Hausa,

 Bayero University Kano.

Bunza A. M. (1990) “Hayaki fidda na kogo” (Nazarin sihiri da siddabarun hausawa)

 Kundin digiri na Biyu M. A. Hausa.

 Bayero University Kano.

Abubakar Gumi (1980) FASSARAR HADISAI ARBA’IN.

 Northan Nigeria publishing company. Zaria

Ibni Hajar Askalani (1988) BULUGUL MARAMI.

 Darul Fikr Bairut Lebenon.

Suyudi A ( ) JAMI’UL HADITH.

Zaid A. A. ( ) RISALA FASSARAR HAUSA.

Abubakar M. G. (1980) ALƘUR’ANI MAI GIRMA.

 Hadimul Haramainish-Sharifaini Makka.

Malik. I. (1970) MUWAƊƊA MALIK.

 Darul Fikri Beirut Lebanon.

Annawawi. I. ( ) RIYADUSSALIHIN.

 Darul Fikr Beirut Lebanon.

Imam Z. ( ) KITABUL KABA’IR.

 Darul Fikr Beirut Lebanon. 

 Hausa Post

Post a Comment

0 Comments