DAGA:
MU’AZU SA’ADU MUHAMMAD
DEPARTMENT OF LANGUAGES
SULE LAMIƊO UNIVERSITY KAFIN HAUSA,
JIGAWA STATE
WANDA A KA GABATAR A TARON TALLAFAWA MARAYU A GARIN KUDAN A ZAUREN TARO (TOWN HALL) DAKE LIKORO ROAD SABON GARIN KUDAN. RANAR LAHADI 20 GA MAYU 2018, 4 GA RAMADAN 1439 DA ƘARFE 10: 00 NA SAFE.
1. 0. 0 GABATARWA
Da sunan Allah Mai rahama, Mai jinƙai, Mai
kowa, Mai komai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga shugaban ma’aika, Annabi
Muhammadu (S. A. W). Wannan muƙala, na da ƙudurin yin tsokaci a kan mahimmancin lokaci
a rayuwar Bahaushe. Haka kuma tare da fito da
ma’anar lokaci
da alaƙarsa da tasirinsa ga rayuwar Bahaushe jiya da yau, sauye-sauye da rayuwar Bahaushe ta gamu da su, tare da gano
hanyoyi, ko dalilan da suka jawo
waɗannan
sauye-sauye. Haka kuma maƙalar zata bayyana tasirin
baƙin al’adu a kan tunanin Bahaushe dangane lokaci. Ban da wannan kuma, za a dubi irin yadda hakan ya shafi al’adu,
da ɗabi’un
Bahaushe, har da rayuwarsa gaba ɗaya. Daga nan sai a hararo fa’idoji da kuma illolin wannan sauyin.
Bayan wannan kuma an ɗan tsakuro wasu daga cikin ɗabi’un, tare da nuna irin nauyinsu da matsayinsu a mizanin al’adar
Bahaushe. Da farko akwai kyawawan ɗabi’u waɗanda aka san mutanen ƙwarai (kirki) da su. A
wannan nazari, zan dubi lokaci ta ƙusurwowi uku kamar haka: A Mahangar Addinin Musulunci, da mahangar
Al’adar Bahaushe, sannan ta Mahangar Zamani. Bisa wannan dalili ne yasa
na yi wa wannan maƙalar take da “Me
Ka Fi, Me Ya Fi Ka, Me Kuke Daidai ?”. Na kawo taken a matsayin
matashiya ne, don ya ba mu damar lalubo mafita. Tare da fatan mai karatu ko
saurare zai gano saƙon da ake son isarwa a ƙarshen maƙalar, don samun mafita ko a fid da jaki a duma.
Fashin Baƙi
Me Ka Fi: Lokacin da ka fi, shi ne jiya, saboda ka ganta ta
wuce.
Me Ya Fi Ka: Lokacin da ya fika, shi ne gobe, saboda ba ta
zo ba ba ka ganta ba, sannan kuma ba ka da tabbas ko zaka goben ka a’a.
Me Kuke Daidai ? Lokacin da kuke ciki, shi ne yau, saboda ka
ganta ita ce kake iya yin wani abu.
Ma’anar Lokaci:
Zamani, abin da agogo, da kwanaki, da watanni,
da shekaru suke aunawa don
kintatar faruwar abu, ko halin da yake ciki, ko yadda zai
kasance a nan gaba. [1]lokaci ko sa’i, yi mulki na ƙayyadadden lokaci na
shekara huɗu, ya zauna har na
ajalin wata uku, lokaci-lokaci, ko loto-loto, ko jiƙo-jiƙo. [2] Loto ; sa’a; sa’i; sa’ili; wokaci; yayi;
zamani. [3]
Bisa la’akari da bayanai
daga masana, muna iya cewa lokaci na nufin daga hudowar rana zuwa faɗuwarta, sannan kuma daga
faɗuwarta zuwa hudowarta,
to shi ya haɗa dare da rana, wuni da
kwana.
Muhimmancin Lokaci Ga Bahaushe.
Bahaushe ya ɗauki lokaci da muhimmanci don kuwa kusan kowane lokaci yana da
matsayi ko tasiri a rayuwarsa. Misali dare da rana, akwai wuni da kwana, daga
nan ake samun ranaku ko kwanaki. Kwanaki bakwai ke samar da mako guda, mako huɗu ke samar da wata ɗaya, watanni goma sha biyu
ke samar da shekara, shekaru talatin ke samar juyi, sannan shekaru ɗari ke samar ƙarni. Dukkan abin da ya faru a wannan tsakanin akan kira shi da
zamani. Kalmar jiya na nufi kwana ɗaya da ya gabata, ita kuma kalmar yau na nufin ranar ko wunin da
ake ciki. Domin haka, a wannan maƙala kalmar zamani, na nufin
wani lokaci da ake ciki, ko zai zo, ko kuma ya wuce. Zamani na yin tasiri a kan
abubuwa da yawa, masu rai ko marasa rai.
Bugu da ƙari, Bahaushe ya girmama
lokaci don kuwa kusan kowane lokaci yana da abubuwan da yake gudanarwa wannan
dalili ne yasa lokaci ya samu matsayi kuma ya yi tasiri a rayuwarsa. Misali
watanni, da yanayi ko kuma ranaku, don kuwa akwai waɗansu watanni dake da
muhimmanci kamar watan Sallah, Azumi da sauransu, ta wajen yanayi kuma kamar
kaka, da rani, da bazara,
da damuna. Sannan wajen su ranaku suna da irin tasu nasabar ga rayuwa kamar
Jumu’a, Laraba, Litinin, Asabar da sauransu.
RAYUWAR BAHAUSHE
Ana iya cewa rayuwar
Bahaushe na tafiya ne bisa ma’aunin lokaci, kusan babu abin da zai yi ba tare
da auna lokaci ba. Wato tun daga farkon samuwarsa ma’ana cikin haihuwa
zuwa ƙuruciya zuwa tsufa. Haka kuma idan muka koma kan
harkar sana’unsa nan ma abin haka yake, misali sana’ar noma. Bahaushe kan yi
amfani da wasu tsuntsaye a matsayin manunin lokaci musamman damuna, tsuntsaye
kamar ragon maza, da shamuwa. Kukan ragon maza kan zama alamun cewa bazara
ta ƙare, sannan kuma damuna ta zo. Bahaushe kan fassara
kukan kamar haka:
“A sai ƙotoci, a sai ƙotoci. ” Da ya fara sai a ce
bazara ta zo ƙarshe. Dole a fara sharar gona da sassabe da kai taki.
Idan aka yi shuka sai sauya kuka zuwa “hunn hunn,” wai haƙorinsa ne ke ciwo ba zai
iya noma ba. Da zarar Bahaushe ya ji haka, sai ya ce: an kusa ƙare noman farko za a
shiga noma na biyu wato huri. Idan aka fara huri sai ya sauya kuka zuwa “gado ɗumi-ɗumi-ɗumi-ɗumi. ” Idan gero ya fara
zare kai tumu ya zo sai ya sauya kuka zuwa “tumu-tumu-tumu-tumu,” wato
tumu ya yi. Da zarar an fara girbin gero sai ragon maza ya sauya kuka yana
cewa; “ƙwat-ƙwat- ƙwat Allah Ya kai mu baɗi. ” To ko baɗin ta yi ba zai yi ba,
wannan yasa ake kiransa ragon maza.
Haka nan ita ma shamuwa
ana amfani da zuwanta Ƙasar Hausa a shaida na matsowar damuna. Bahaushe ya
kiyaye cewa shamuwa ba ta zuwa Ƙasar Hausa, sai a watan
bakwai. Bahaushe na cewa watan bakwai maƙara rani in ba ruwa da
alamu, ko kuma komai aka yi wa shamuwa watan bakwai ya jawo mata.
Ban da wannan ma
Bahaushe na amfani da ƙwaron tuma –da-gayya, wato cinnaka mai fiffike a
matsayin alamar shigowar kaka.
MATAKAN HAIHUWA.
Matakan haihuwa na nufin mace ta ɗauki ciki na tsawon watanni
tara. A wannan tsari za a yi bayani a kan haihuwa tun daga ɓatan wata da mace kan yi
zuwa ɗaukar
ciki da laulayin ciki da goyon ciki da mace kan yi. Sannan ta yi naƙuda bayan zubar ruwan zaƙi, da fashewar faya daga
nan jariri ko jaririya ya faɗo. Sannan uwa ko mahaifa ta biya (faɗo). Duk wannan bayani zai zo ne kafin da kuma lokacin faruwar
haihuwar da kuma bayan haihuwa har ya zuwa yaye da kaciya har zuwa girman
yaro.
|
Ɓatan wata |
Laulayin ciki |
Goyon
Ciki. |
Naƙuda |
Haihuwa. |
|
Ƙauri. |
Suna. |
Yaye. |
Kaciya. |
Ƙuruciya/Yarinta. |
|
Samartaka. |
Budurci |
|
|
|
Ƙuruciya na nufin wata rayuwa dake farawa daga haihuwa zuwa
samartaka zuwa
dattijantaka da tsufa.
|
jariri/ |
Jaririya |
sabuwar Haihuwa |
|
Laɓuɓu |
Laɓuɓuwa |
wata1-6 |
|
Barden
goyo |
Barden
goyo |
wata6-24 |
|
yayayye/ |
yayayyiya, |
wata24-36 |
|
sagari/ |
Sagara |
shekara3-6 |
|
Madaci |
Ƙwaila, |
shekara6-9 |
|
Matashi |
Bera |
shekara9-13 |
|
saurayi/ |
Budurwa. |
Shekara13-17 |
|
Magidanci |
Gunduwa/uwar
mata |
shekara17-45 |
|
Dattijo |
Dattijiya |
shekara45-59 |
|
Tsoho |
Tsohuwa |
shekara 60-70 |
|
Tsoho
Tukuf |
Tsohuwa
Tukuf |
shekara70-80 |
|
Tsoho
Tukuf –Tukuf |
TsohuwaTukuf-Tukuf |
shekara80-100 |
|
Tsoho
Takwarkwasasshe |
Tsohuwa
Takwarkwasasshiya |
shekara 100-120 |
Wannan rayuwa ita ake kira yarinta, ko da yake wasu kan
kirata da cewa da farkon yarinta har zuwa tsakiya, amma zuwa ƙarshe watau samartaka sukan kirata da balaga.
Ta wata fuska ana kiran ƙuruciya da farkon rayuwa, saboda wata karin magana mai cewa “yaro
masomin babba”, ko wata karin magana mai cewa “ƙuruciya matakin farko”, “Yaro ba mutum ba sai ya girma”, In ka ga
tsohon banza daga yaron banza ya taso” da sauransu.
Gaisuwa: Bisa ga yanayin gaisuwa wasu tambayoyi ne da akan yi wa juna game da
yanayin da ake ciki, a al’adar Bahaushe za mu iya cewa, ita gaisuwa kanta Bahaushe
na girmama lokaci.
Babban dalili anan shi ne, idan an gamu da juna sai a gaisa a tambayi yanayi da mutum ya ke. A wani lokaci ko ana tare, ko ana
nesa, duk dai akan gaisa. Misali ko da a gida ɗaya ko ɗaki ɗaya aka kwana sai
ka ji ana gaisawa, haka kuma in an yi baƙo zaka ji ance zamu gaisa.
SAFIYA.
Ina kwana? /Barka da asuba/kwan lafiya? – Tambaya
i.Lafiya lau/ƙalau lafiya sumul/lumi –
amsa
ii.Ina gajiya?/yaya gajiya? – Tambaya
iii.Babu gajiya /gajiya tafi lafiya – amsa.
iv.Ya iyali? Yaya iyali? – Tambaya
v.Lafiya lau/ kalau lumi – amsa
RANA.
Barka da rana/ barka da warhaka.
Barka kadai.
YAMMACI/MARAICE.
Barka da yamma / ka wuni lafiya? Ina wuni?
Lafiya lau/ƙalau.
Bayan waɗannan tambayoyi na farko ana iya samu wasu tambayoyi da yawsa da
ba a kawosu ba a wannan tsari a wasu lokutt a inj an gama gaisuwa akan yi
sallama watau bankwani. Kamar haka.
a. Sauka lafiya
b. Sai anjima
c. A gaida gida
d. Gida ya ji
e. Sai gobe/ sai wataran
f. Allah Ya bamu alheri
g. Na barku lafiya
WATANNI.
Watanni suna da nasu nasaba
ga rayuwar yau da kullum kamar dai yadda aka gabatar da farko, kamar watan
Azumi yana da tasiri ƙwarai don kuwa akwai
abubuwan da ake yi da suka haɗa da kira ko kamun gwauro, tashe, akwai inda ya ashafi yara a
wani ɓangaren
ma ya haɗo har da
manya. Watan Sallah akwai ƙaramar Sallah wanda in
Azumi ya ƙare ake yinta wanda akan yi ɗinke-ɗinke da dafe-dafe da
shagulgula, sai babbar Sallah ita kuma ana yin ta ne bayan watan Zulhajji ya
kwana goma, a inda a akan yanka raguna domin layya. Watan Almuharam yana da manyan al’amurra da suka haɗa da Taku-taha, cika-ciki, sai kuma shara, ita dai taku-taha yaran
sukan tafi gidajen jama’a da nufin yi musu wasa da cewa; “takutaha
sadaka, takutaha sadaka, daga wannan sai ta baɗi. ”
Cika ciki da zaran watan Muharram ya kwana goma to a daren na goma
sai a aci abinci a ƙoashi don akwai faɗan cewa in har mutum
bai ƙoshi ba a wannan shekara ba to ba zai ƙoshi ba har shekara ta dawo, ba ƙaramin cefane ake yi ba a wannan lokacin. Sannan kuma sai maganar
karɓar kuɗin shara, shi ma karɓar kuɗin shara yakan fara ne daga
goma ga watan Muharram, shi wannan al’amari yakan faru ne tsakanin abokanan
wasa kamar Ɗan mace da Ɗan namiji, sai kuma
tsakanin Bare-bari da Fulani, Buzaye da Maƙera, Kanawa, da Zazzagawa, da Gobirawa, da Katsinawa, da Katsina, da Haɗejawa da dai sauransu.
YANAYI.
Yanayi na da tasiri ga harkokin yau da kullum misali: Rani, da Kaka, da Bazara, sai kuma Damuna. Mafi yawa ana yin
bukukuwa da kaka watau bayan an girbe kayan amfanin gona, bukukuwan sun haɗa da na aure, nuna amfanin
gona, gasar kamun kifi, kalankuwa, kokuwa, dambe da sharo. Babban dalilin da
yasa aka fi mayar da hankali wajen haka shi ne lokacin ne za’a samu kuɗi kuma sannan babu ayyuka,
don haka kusan kowa zai samu halin zuwa ko bayar da wani abu kamar gudunmuwa a
nan za’a taikawa bikin.
A ƙarshe sai Damina, wannan
lokacin ne lokacin ruwan sama kamar yadda ake yi mata kirari da cewar “Damina
dare” ko kuma “Bawan Damina Attajirin Rani”, duk kusan al’amurra kusan sukan
tsaya ne saboda a kan mayar da hankali ga gona ne gaba ɗaya.
RANAKU.
Kamar yadda muka ga tasirin watanni da yanayi ga al’amurran
yau da kullum, hakanan ranaku suke da nasu tasirin don kuwa ba wata harka da za
ayi ba tare da lura da wata rana ba, don har ma ta kai ga zaɓan wata rana ta musamman
don yin wani al’amari, misali, bikin
Aure, da tafiya, ko kasuwa da dai sauransu. Don akwai
masu zaɓar ranar litinin ko jumu’a, don waɗansu na fatan samun sa’a a waɗannan lokutan. Haka kuma akan ƙi yin wasu abubuwa a waɗansu ranaku kamar Laraba ko Asabar in har basu zama dole ba, takan
kai har ma a fasa yin wasu abubuwa in suka faɗo a waɗansu ranakun. A kan yi amfani da ranaku ta wajen ƙayyade kwanaki, misalin wajen lissafi ko na shekara ko watanni.
LOKUTA MASU NASABA DA TU’AMMALI.
Su kuma waɗannan lokuta Bahaushe na yin amfani das u ne ta wajen tu’ammali da
juna, watau wajen harkokin yau da kullum ke nan, misali kamar a ɓangaren alƙawari, ƙa’ida ko kayya da kwanaki
da dai sauran harkoki, masu nasaba da ranaku kuwa
sun haɗa da: -
1. Shekaran jiya. 2. Jiya. 3. Yau. 4. Gobe. 5. Jibi. 6. Gata. 7. Citta.
Sai kuma masu nasaba da yanayin da ake ciki kamar haka: -
1. Ɗazu. 2. Yanzu. 3. Anjima.
Sai kuma masu nasaba da yanayi ko lokaci masu zuwa su tafi: -
1. Bara waccan (Bariya). 2. Bara. 3. Bana. 4. Baɗi. 5. Baɗi waccan.
Baya ga nasabar waɗannan bayani da ya gabata, to akwai lokuta da suke da alaƙa da waɗancan na farko inda sun haɗa da: -
|
Assalatu. |
Safe. |
Hantsi. |
Rana. |
Tsakar Rana. |
|
La’asariya |
Sakaliya |
Yamma |
Marece. |
Almuru |
|
Lisha. |
Dare. |
Talatanin
Dare. |
Tsakaddare. |
Asuba. |
Kusan zamu iya waigawa ga yadda yanayi, watanni da ranaku ke yin
tasiri, to su ma haka waɗannan lokuta ke da tasiri ga harkokin mu na yau da
kullum, don kuwa kowane lokaci akwai katamaimai abin da ake yi misali.
Assalatu, sau da yawa an fi yin sammako watau in za’a unguwa
ko tafiya ko kuma wasu al’amurran yau da kullum lokacin kan fara ne daga
lokacin da alfijir ya fito har zuwa da gari zai yi shi har zuwa fitowar rana.
Sai kuma hantsi yakan fara ne daga ɗagawar rana har zuwa rana ta take, har akwai kirarin da ake cewa
hantsi ya dubi ludayi, ko hantsi leƙa gidan kowa.
Da zaran rana ta take watau ta zo tsakiya watau ta fara
zafi, shi ne ake cewa tsakar rana, amma bayan wannan lokacin sai rana har ya
zuwa sunkuyawar rana, bayan rana ta sunkuya sai kuma yammaci in yammaci ya fara
bayan rana ta yi sanyi daga wannan lokacin ne sai la’asariyya, daga yammaci har
ya zuwa gaf da faɗuwar rana watau lokacin da rana ta yi jan daga nan sai lokacin da
rana ta faɗi shi ne
ake kira almuru har ya zuwa lokacin da gari zai fara duhu, to daga nan kuma sai
lisha, nan kuma shi ne mafin yawan mutane ke cin abincin dare kuma lokacin ne
yara kan fita wasa da zuwa fira daga nan sai dare, nan kuma yakan fara ne da
lokacin sawu ya fara ɗaukewa watau an fara shiga barci gari ya fara yin shiru.
YANAYI. ABUBUWAN DA AKE YI.
1. Rani. Aikin Lambu, Gine-gine, Ci-rani.
2. Bazaar. Farauta, Sharan Gona.
3. Damina. Noma, kiwo, Su, Ɗan inyi gwado, yangai aika.
4. Kaka. Girbin kayan gona, sanyi (hunturu).
Kalankuwa, wasanni, kadan raba.
TAFIYE-TAFIYEN BAHAUSHE
Akwai alamun fifita
lokaci a tafiye-tafiyen Bahaushe, tun daga lokacin fita, ko dawowa gida. Idan muka dubi kowace fita da Bahaushe kan yi, inda ya
kan bar gidansa, ko garinsa, muna iya cewa kowane da lokacin da yake ɗauka in ya fita ɗin. Bayan haka kuma, akwai irin sunan da Bahaushe ya ba shi don
rarrabewa. Haka nan kuma, a ƙarshe kowanne na ɗamfare da dalilan da kan
sanya a yishi. Bisa wannan dalili ne, ma da zarar ka ambaci irin sunan tafiya,
ko fita da Bahaushe ya yi. Tabbas za’a gane cewar lallai ga dalilin da ya fitar
da shi daga gida.
Dangane da sunaye waɗanda al’adar Bahaushe ta bai wa fitar, ko barin gida da Bahaushe
kan yi suna da yawa, sune kamar haka:
|
Ci-rani. |
Ga-aiki. |
Kaɗar
raba. |
In-yi-gwado. |
Dandi |
|
Jaura. |
Fatauci. |
Ujula. |
Kore. |
Raraka |
|
Garam. |
Kilisa. |
Rangadi. |
Zagaye
ko zage. |
|
LOKACI A ADABIN BAHAUSHE
1. Sammakon Buƙuƙuwa.
2. Dare ga mai rabo
asalatu.
3. Rana mai rabawa kowa
aiki.
4. Rana mudun aiki.
5. Ranar wanka ba a ɓoyon cibi.
6. Hantsi Leƙa gidan kowa.
7. Hantsi ya dubi ludayi.
8. Hantsi ba hatsi hatsari
ne.
9. Zuwa da wuri yafi zuwa
wuriwuri.
10. A kwana a hantse sai
kyakkyawa.
LOKACI A BAKIN MAWAƘA
Alhaji Adamu Ɗanmaraya Jos a waƙarsa ta wa ya san gobe
ban da Allah ? yana cewa:
Wa yasan gobe ban da
Allah,
In ko ka sani,
Mu ganka.
MUHIMMANCIN LOKACI A
MAHANGAR MUSULUNCI
Lokaci na da
muhimman a duk wata harka ta addinin musulunci, waɗannan bayanai sun tabbata a wurare da kuma ta fuskoki
masu yawa. Tun da farko ana iya cewa, saboda muhimmancin lokaci ne yasa Allah
subuhanahu da kanSa Ya yi rantsuwa da lokaci a wurare daban-daban. Akwai wasu
surori da ayoyi waɗanda Allah Yai rantsuwa
da lokaci don nuna darajar lokaci misali:
1. Suratul Asr (wal asar)
,
“Rantsuwa da la’asar
lokacin mutane na gudanar da harkokin rayuwa na hairan ko na sharri. Haƙiƙar mutum na cikin
hasara, sai waɗanda suka yi imani, suka
aiki na ƙwarai, suka yi umarni da gaskiya da umarni
haƙuri.. [4]
2. Suratul Duha
(wadduha) Rantsuwa da hantsi.
3. Suratul Fajar (wal
fajar) , Rantsuwa da alfijir.
4. Suratul Shamsu (was
shamsu) , Rantsuwa da rana.
5. Suratul lail (wal
laili) , Rantsuwa da dare.
Bugu da ƙari akwai wasu hadisai
waɗanda Manzon Allah (saw)
ya yi magana a kan muhimmanci na lokaci, akwai inda Manzon (saw) yace lokaci
kamar takobi ne ka yi amfani da shi kafin ya wuce. Haka kuma akwai inda ya ce
ka yi amfani da ƙuruciyya kafin tsufa ya zo, ka yi amfani da wadata
kafin talauci ya riskeka, ka yi amfani da lafiyarka kafin ciwo.
Bugu da ƙari saboda muhimmancin
lokaci ne, yasa a addinin musulunci aka keɓe lokutta na yin kowace nau’’in ibada. Sallah an ware
mata lokaci na musamman akwai salloli safe, da na rana, da kuma sallolin dare.
Azumi an ware masa lokaci kamar azumtar watan ramadana wanda ake yi na tsawon
kwanaki talatin 30 ko 29. Wato wata ɗaya ke nan. Akwai aikin hajji duk shekara, haka kuma
ga bukukuwan sallar idin azumi da na sallar idin layya. Haka kuma akwai zakka
wadda ba a yinta, sai bayan shekara ma’ana ta kai nisabi.
Haƙiƙa idan mutum ya saɓa waɗannan lokuttan da
aka ƙayyade don yin ibada, to ko ya yi ba lokacin da aka ce
a yi ibadar ba, ba ta yi ba. Kamar lokutan salla biyar mutum sai ya ƙi yi da ganar to lallai
ya yi saɓon Allah. An fi son idan
lokaci yayi a gaggauta yinta.
TASIRIN MUSULUNCI A
LOKUTAN BAHAUSHE
Bahaushe ya ce ba
a raba hanta da jini, saboda al’adun Bahaushe sun tasirantu da musulunci, har
sun zama jiki. Bisa wannan dalili yasa lokutan Bahaushe ma ba su tsira daga
wannan tasiri ba. Tun daga sunayen ranaku, da na watanni tare da wasu abubuwa
da ake yi a cikinsu.
RANAKU. TASIRINSU A RAYUWA WAJEN SUNA.
1. Lahadi. Ɗanladi, Ladi, Ladidi.
2. Litinin. Tanimu, Ɗantani, Lanti, Latai,
Lantana,
Lanto, Tine, Atine.
3. Talata. Talatu, Tatu, mai tala.
4. Laraba. Bala, Balaraba, Laraba, Balarabe.
5. Alhamis. Ɗanlami, Laminde, Lami.
6. Jumu’a. Ɗanjuma, Najume, Juma,
Jumande.
7. Asabar. Ɗan Asabe, Asibi, Asabe.
WATANNI. ABUBUWAN DA AKE YI (TASIRINSU GA RAYUWA).
1. Muharram. Cikar Shekara, Cika ciki, Shara.
2. Safar.
3. Rabi’ul Auwal. Maulidi, Sallar Gani, Takutaha.
4. Rabi’us Sani.
5. Jimada Auwal.
6. Jimada sani.
7. Rajab. Azumin Tsofaffi.
8. Sha’aban. Sallar Tsofaffi.
9. Ramadhan. Azumi, Tashe, Kiran Gwauro.
10. Shawwal. Ƙaramar sallah, Yawon
Sallah.
11. Zul’iƙidah. Bawan sallah, tafiya hajji.
12. Zulhijjah. Aikin hajji, Layya.
Sadaƙatul Jariya: Manzon Allah (SAW) ya ce: Idan mutum ya mutu dukkan ayyukansa sun
yanke. In ban da ayyuka uku, sadaka mai gudana da ilmin da ya koyar ake aiki da
shi, sai kuma natsattsen ɗa wanda zai rinƙa yi masa addu’a. Fiƙhus Sunna 104 A.
Daga Anas Bin Malik: ya ce:
Duk wanda ya dasa bishiya ko ya shuka ɗan itace ya tsira ya yi ‘ya’ya, wani tsuntsu ko dabba ko mutum ya
ci daga gareta. Wannan kamar sadaka ce mai gudana. Bukhari 3. 513
A Musulunci, an fifita mai bayar da kyauta a kan wanda yake karɓa. kamar wani hadisi day
ace: Hannun sama (Mai bayarwa) yafi hannun ƙasa (mai
karɓa)
daraja. Duk wannan ana nuna kyawun kyauta fiye da rowa da kuma kwaɗayi.
Ibn Abbas ya ce, Manzon
Allah shi ne mafi alheri (Kyauta) a mutane. Ya fi yin kyauta a watan azumi, ya
fi iska kyauta. 1. 1
Abdullahi Bin Amr ya ce, wani mutum ya tambayi Annabi cewa: Wane
aiki ne ya fi a musulunci? Sai ya ce ka ciyar da talaka, sannan ka yi sallama
ga wanda ka sani da wanda ba ka sani ba. Bukhari 1. 11.
LOKACI A MAHANGAR ZAMANI
A wannan zamani da
muke ciki, tun bayan zuwan Turawa, lokacin Bahaushe ya tasirantu da al’adun
Bature. Wannan kuwa ya bayyana tun daga sunayen ranaku zuwa na mako zuwa na
watanni. Muna iya alaƙanta wannan da dalilin aiki da agogo, da kalandar
Nasara wato watan ‘yan albashi. Bisa la’akari da muhimmancin lokaci ne yasa
Bature ya ƙirƙiro agogo, saboda tantance lokacin ma’amalla ta yau da
kullum. Tabbas agogo na taimakawa wajen sanin tafiyar lokaci a wuni. Ita kuma
kalanda na taimakawa ne, wajen ƙididdige kwanakin wata
da lokacin biyan albashi, da sauran ayyukan yau da kullum.
Zuwan agogo ya kori yin amfani wasu lokuta masu nasaba da yanayin da ake ciki kamar haka: -1. Ɗazu.
2. Yanzu. 3. Anjima.
Kwatsam sai
Bahaushe ya koma amfani da ƙarfe, da minti, ko awa,
kamar haka: Ƙarfe 1: 00, 2: 00, 3: 00, 4: 00, 5: 00, 6: 00, 7: 00,
8: 00, 9: 00,10: 00, 11: 00, 12: 00. Awanni 12 ke samar da wuni ɗaya, awanni 24 ke samar
da kwana ɗaya.
RANAKUN BATURE.
1. Monday. Mande
2. Tuesday. Cusde
3. Wednesday. Wenesde
4. Thursday. Tasde
5. Friday. Firayid
6. Saturday. Sati
7. Sunday. Sande
WATANNIN BATURE
1. January. Janairu
2. Febuary. Feburairu
3. March. Maris
4. April. Afirulu
5. May. Mayu
6. June. Yuni
7. July. Yuli
8. August. Agusta
9. September. Satumba
10. October. Oktoba
11. November. Nuwamba
12. December. Disamba
Waɗannan awanni, da ranaku,
da watanni na Bature, haƙiƙa sun yi tasiri a mafi yawan harkokin rayuwar Bahaushe
a yau. Wannan kuma ya haɗa da ‘yanboko, da
ma’aikatan gwamnati ‘yan albashi, da waɗanda ba su ba. Ana iya cewa kusan bukukuwan mu da
tarurrukanmu, da alƙawuranmu sun koma kan doron waɗannan lokuta na Bature ne saɓanin namu na da wanda muka gada.
MATASHIYA
Tun da yake jiya ta
wuce, mun san abin da muka yi, gobe ba ta zo ba, ya zama wajibi mu yi
tattalinta. Shi kuwa wannan tattali ba zai yiwu ba, sai mun dage. Domin haka,
yau ce muke ciki, a ita ne zamu yi tanaji zuwan gobe. Wannan gobe tana iya zama
ta kwana ɗaya ko kuma gaobe ta
ranar kiyama, tilas ni da mu yi wa kan mu guzuri kyakkyawa kuma mai kauri.
Bisa lura da bayanai da suka gabata, ana iya cewa an ji kuma da
fatan an gamsu. Don haka akwai buƙatar a ɗauki lokacin da muhimmanci, sannan kuma mu kare kai daga faɗawa cikin tarkon shagala. Ya dace
mu bai wa juna shawarar neman mafita. Ga wasu shawarwari waɗanda ya kamata mu ɗauka su ne: Mu yaƙi son zuciya, da kuma shaiɗan, wadatar zuci, da kyautata tauhidi, tare da neman rabon
gobe ƙiyama, a ƙarshe mu rage son abin
duniya. Don haka, mu sani cewa abin da ka bayar shi ne naka, wanda ka tara na
magada ne, ko kuma wanda ka ci ya zama kashi.
Dukkan mai hankali a jikinsa ya kamata ya dawo cikin hayyancinsa
ya tsaya ya yi wa rayuwarsa kallon natsuwa. Watau kallo irin na sayen goron
tsohuwa. Alhali kuwa masu hikima sun kasa ribar rayuwa mataki uku zuwa huɗu kamar haka:
1. san samu (mutum ya samu alherin duniya da na lahira)
2. samu rasa (mutum ya samu alheirn duniya ya rasa na lahira)
3. rasa ka samu (mutum ya rasa alheri duniya ya samu na lahira)
4. rasasa-rasasa (mutum ya rasa alherin duniya da na lahira)
Allah ya tsare mu amin.
KAMMALAWA:
A ƙarshe wannan maƙala ta kawo wasu
al’amura da suka shafi mahimmancin lokaci
a rayuwar Bahaushe. Haka kuma tare da fito da
ma’anar lokaci
da alaƙarsa da tasirinsa ga rayuwar Bahaushe jiya da yau, da sauye-sauye
da rayuwar Bahaushe ta gamu da su, tare da gano
hanyoyi, ko dalilan da suka jawo
waɗannan
sauye-sauye. Haka kuma an kawo bayyanin yadda baƙin al’adu suka taɓa tunanin Bahaushe game da lokaci. Ban da wannan kuma, an dubi
irin yadda hakan ya shafi al’adu, da ɗabi’un Bahaushe, har da rayuwarsa gaba ɗaya.
MANAZARTA
Bargery,
G. F. (1993) A Hausa-English Dictionary and English-Hausa Vocabulary. Zaria:
Amadu Bello University Press.
(2006) Ƙamusun Hausa Na Jami’ar Bayero Kano.
Madauci I. (1963) Al’adun Hausawa. Northern Nigerian Publication
Company, Zaria.
Ladan Y. (1980) Zaman Duniya Iyawa ne. Northern Nigerian
Publication Company, Zaria.
Roxana M. N. (1997) An English Hausa Dictionary.
LearnAfrica P. LC. Lagos
Sarki H. A. (2000) Zuwan Musulunci a Afirka da shigowarsu Ƙasar Hausa. G. A. Computer Centre. Ikere – Ekiti, Ekiti State.
Adam M. T (1997) Asalin Hausawa da Harshen su, Kano Nigeria.
[1]. Ƙamusun Hausa Na Jami’ar Bayero (2006) ,
[2] Roxana
MaNewman (1997) An English Hausa Dictionary.
[3] Bargery
G.P. (1993) Ahmadu Bello University Press LTD.
[4] Tafsir Ibn Kasir. Translated by Muhammad Anas Gad Khalil. Dar-AL-Mannah (2007) vol 4.pg 2553
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.