An Ciro Daga: Bakura, A.R., & Sani, A-U. (2026). Zogale a ƙasar Hausa: Magani, abinci, tattalin arziki. SAS Publishers. ISBN: 978-978-63958-1-4. https://doi.org/10.5281/zenodo.22682300
Rabe-Raben Magunguna Daga Zogale
Zogale,
nau’in itace ne wanda Allah ya tsirar da shi a bisa doron ƙasa domin amfanin mutane da dabbobi da aljannu. Ita kanta ƙasa ma tana amfana da shi. Wani abin mamaki da ta’ajibi shi ne,
irin yadda halittun da suke ruwa suke amfani da saiwar zogalen da take kusa da
gulbi ko ƙorama. ‘Yanmagori da bokaye da sauran wasu daga cikin masu
sana’o’in gargajiya kamar wanzamai da masunta da makamantansu, duk suna amfani
da zogale a gargajiyance domin yin magunguna nau’i-nau’i a farfajiyar ƙasar Hausa da ma wasu sassan Nijeriya.
Ana iya
karkasa magungunan da zogale yake yi ta la’akari da yadda al’umma suke sarrafa
shi wajen biyan buƙatunsu waɗanda suka danganci rayuwar yau da kullum. Daga cikin ire-iren waɗannan buƙatun akwai:
1. Waraka
2. Kariya
3. Biyan buƙatun zuci
4. Tsafta (tsaftace ruwa)
Zogale a
Fagen Maganin Waraka
Zogale yana taka muhimmiyar rawa waje kawar da dangogin cututtuka da suke addabar jikin ɗan’adam. Ire-iren waɗannan cututtuka nau’uka biyu ne. Akwai wadda ake iya gani da wadda ba za a iya gani ba, sai dai kawai maras lafiya ya ji wasu alamomi tare da sauyawar yanayin jikinsa. Daga cikin cututtukan da zogale kan yi maganinsu akwai:
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.