Ticker

6/recent/ticker-posts

Rabe-Raben Magani a Bahaushiyar Al’ada

An Ciro Daga: Bakura, A.R., & Sani, A-U. (2026). Zogale a ƙasar Hausa: Magani, abinci, tattalin arziki. SAS Publishers. ISBN: 978-978-63958-1-4. https://doi.org/10.5281/zenodo.22682300

 Na

Adamu Rabi’u Bakura

Da

Abu-Ubaida Sani

Zogale a Kasar Hausa: Magani, Abinci, Tattalin Arziki

Rabe-Raben Magani a Bahaushiyar Al’ada

Kamar yadda aka faɗa a baya kaɗan, magani abu ne mai daɗaɗɗen tarihi wanda al’ummomi daban-daban na duniya suke bin hanyoyi mabambanta domin samar da shi da kuma amfani da shi. Nau’uka ko ire-ire ko rabe-raben magani abu ne da ya ja hankalin masana al’adun Hausawa, kuma sun yi tsokaci a kan wannan batu.

Kamar yadda Sani da Jaja (2019 sh. 260) suka bayyana, a mafi yawan lokuta rabe-raben magungunan gargajiya yana tafiya ne tare da na cututtuka. Dalili kuwa shi ne, cuta da magani tare suke tafiya. Kamar yadda suke tare a zahiri, haka ma suka kasance a fagen nazari. Masana da dama sun ba da rabe-raben magungunan gargajiya. Wani abin burgewa shi ne, dukkanin ra’ayoyin na masana alƙibla guda suka dosa, amma ta fuskoki mabambanta. Bunza, (1990: 154-141) ya raba magani zuwa manyan rukunai guda biyu, wato:

i.  Magungunan cutar jiki

ii.  Buƙatocin ɗan’adam

Gobir, (2012 sh. 167-170) ya raba cutuka zuwa manyan rukunai guda biyu, (i) Cutukan jiki da kuma (ii) Cutukan zuciya. Lura da wannan rabo da ya yi, za a iya fahimtar yana da ra’ayin cewa magunguna sun rabu zuwa gida biyu manya. Na farko shi ne magunan cutukan jiki. Na biyu kuwa ya kasance magunan cutukan zuciya. Yayin da aka nazarci waɗannan rabe-rabe, za a tarar ba su ci karo da juna ba. Cutukan zuciya dai su ne buƙatocin ɗan’adam.

Shi kuwa Sarkin Gulbi (2014 sh. 86) ya kawo rabe-raben magani kamar haka:

i.  Magungunan riga-kafi

ii.  Magungunan waraka

iii. Magungunan cutarwa

iv. Magungunan biyan buƙata

v.  Magungunan camfi

A wannan rabo za a iya fahimtar cewa, wasu suna iya shiga cikin wasu. Misali, magungunan cutarwa za su iya shiga cikin biyan buƙata. Wata buƙata ce take tasowa har ɗan’adam ya ƙuduri aniyar cutar da wani ko wata ko wasu.

Kalmar Bature ta medicine tana da kamar sauƙi wurin fassara. Idan aka zo fassarar kuwa, za a tarar da cewa abin ya wuce yadda ake tsammani. Dalili kuwa shi ne, kalmar magani gama-gari ce. Ta tattara dukkanin nau’ukan hanyoyin samar da waraka da suka haɗa da na jiki da kuma na zuciya. Kowanne daga ciki kuwa yana da sunan da Hausawa suka laƙaba masa. Za a fi fahimtar yadda abin yake yayin da aka waiwaici rabe-raben magunguna manya da ƙananan da ake da su.

Wannan littafin ya yaba da hikimar da take cikin dukkannain rabe-raben da masana suka bayar kamar yadda aka zayyana a sama. Littafin ya gamsu da salon da Gobir, (2012 sh. 242) ya yi amfani da shi domin bayyana rabe-raben magani. Duk da haka, a ƙarƙashin rukunin magungunan buƙatun zuciya, wannan littafin ya ɗan sha bamban da ra’ayin Gobir. Littafin ya ɗauki rabo irin na Sani da Jaja (2019 sh. 260-261) inda suka raba magungunan biyan buƙatun zuciya zuwa Son kai da na sharri da kuma na alheri. Hakan ya zama saɓanin na Gobir da ya kawo su a matsayin na alheri da kuma na sharri.

An yi la’akari da cewa, magungunan biyan buƙata ba su tsaya kan “na alheri” da “na sharri” kawai ba. Sun haɗa har da na “son kai.” A fassarar Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero, alheri na nufin (i) Kirki ko aiki na gari, (ii) Kyauta ko baiwa, (iii) Buɗi ko riba ko albarka ko arziki ko amfani da falala. A taƙaice ke nan, alheri ya shafi farar aniya da farin aiki. Su kuwa magungunan biyan buƙata, ko dai an yi su ne domin cutarwa ko kuma wani abu da yake da dangantaka da son kai. Misali, bi-ta-zai-zai da maganin neman mulki duka son kai ne ƙarara. Wane Son kai ne ya wuce mutum ya tilasta wa wani ya so shi? Wanne ne ya wuce mutum ya nace ala tilas sai ya zama shugaba? Me zai hana shi aikata abin da za a ga cancantarsa a ba shi shugabancin?

Ga yadda rabon yake:

Misalai

 

 

Magani

Cutuka

Jiki

Ciki

Sanyin ƙashi

Ƙurjin hanji

Ciwon ƙoda

Amosani

Waje

Gwaiwa

Makanta

Gyambo

Karaya

Ƙwaƙwalwa

Taɓin hankali

Farfaɗiya

Rawar kai

Mantau

Kare kai

Sagau

Tauri

Zana

Baduhu

 

Buƙatun zuciya

Alkairi

 

Maganin kasuwanci

Tsaraka

Son kai

Bi-ta-zai-zai

Soyayya

Neman mulki

Sharri

Kurciya

Kashe rai

Firaƙi

Gumuni

Kwaikwayo Daga: Gobir, (2012 sh. 242).

Yawaitar nau’ukan magani ba ya rasa nasaba da yawan da cututtuka suke da shi. Kowace nau’in cuta tana da irin nata magani. Hanyoyin da ake samun cutuka sun bambanta, haka ma hanyoyin samar da magungunan waɗannan cutaka. 

Post a Comment

0 Comments