An Ciro Daga: Bakura, A.R., & Sani, A-U. (2026). Zogale a ƙasar Hausa: Magani, abinci, tattalin arziki. SAS Publishers. ISBN: 978-978-63958-1-4. https://doi.org/10.5281/zenodo.22682300
Ƙaiƙayin Ido
Zai fi
kyau mu fahimci abin da ake kira ƙaiƙayi kafin a shiga zance maganinsa.
Kalmar ƙaiƙayi, Bahaushiyar kalma ce da
take cikin jerin sunayen Hausa jinsin maza, kamar yadda Abubakar (2015) ya
bayyana. A karin harshen Sakkwatanci akan furta ta da ƙaiƙai. Yayin da a karin harshen
Katsinanci akan furta kalmar da ƙaiƙayi, kamar yadda Bargary
(1993 sh. 529) da Abraham (1975 sh. 455) suka zo da bayanin. Tana ƙunshe da ma’anoni kamar
haka:
(i) Rashin jin daɗi a jiki da kan sa mutum ya yi susa ko yanyami a
jika
(ii) Soshiyar sussukakken hatsi
wadda akan yi abincin dabbobi da ita
(iii) Ƙurar kwasfar gero ko dawa
ko shinkafa da aka cashe kuma aka sheƙe, sannan ƙurar tana jawo susar jikin
da ta sauka a kai, musamman in iska ta huro
(iv) Ciwon da yake sa fatar jiki
ta jawo sai an sosa wurin
Yayin da aka kalli ma’anonin ɗaya bayan ɗaya, za a fahimci cewa, dukkansu bakinsu ya zo ɗaya. A inda suka kira kwasfar gero ko dawa ko
dauro (maiwa/farin gero) ya karɓa sunan ƙaiƙai ko ƙaiƙayi, wani zubin har ma da
soshiyar. Wannan bai rasa nasaba da illar ko cutar da ƙurar takan haifar yayin da
ta sadu da jikin ɗan’adam. Illar kuwa ita ce
yanyamin da jikin yakan yi, har ya hana sukuni. Rashin sukunin yakan wanzar da
sai an sosa wajen akan sami sawaba. Haka masana sun aminta da cewa, ciwo ne da
yake haddasa yanyami a jikin ɗan’adam, har sai an sosa
muhallin akan sami sukuni.
Tun da mun fahimci abin da ake kira da ƙaiƙayi, sai mu dawo a kan
kalmar ido, ita kanta kalmar, tana cikin kalmomin Hausa jerin
sunaye jinsin namiji. A wani karin harshen kuwa takan kasance jinsin mace, a
inda sukan furta ta da lafazin idaniyaa., jJam’inta kuwa yakan
kasance idaanuu ko idaanuwaa ko idandunaa ko idandanii.
Wannan ya danganta ne sakamakon bambance-bambancen da yake akwai na kare-karen
harshe a tsakanin lardunan ƙasar Hausa. Kalmar tana ɗauke da ma’anoni mabambanta kamar haka:
(i) (i). Sashen da ke fuska
sama da hanci wanda ake gani da shi, daidai da ijiya, a karin harshen
Sakkwatanci
(ii) (ii). Maɓugar ruwa musamman a rijiya ko saman dutsi
(marmaro a karin harshen Sakkwatanci)
(iii) (iii). Basira da ƙoƙari a wajen karatu
(iv) (iv). Jagora ko mai
fahimtar da wani yadda ake tafi da wasu harkoki (BUK, 2006: sh, 204).
A wannan fagen nazari, ido yana nufin
sashen fuska da yake saman hanci wanda ake ganin abubuwa da shi. A
jimlace, ƙaiƙan ido a nan, ana nufin ciwon da yake wanzar da
yanyamin fatar ido da ke haddasa sai an sosa akan sami sukuni.
Ita kuwa ƙwayar ido tana da fata kala huɗu kamar haka:
(i). Farar fatar ido, wannan ta fi sauran girma da tauri.
(ii). Baƙi-baƙin fatar ido, wannan ta kasu kashi biyu kamar haka:
a. A waje akan gan ta wani
zubin ta yi kore, misali, a idon al’ummar Turawa.
b. Ta ciki da takan riƙe maganin ƙwayar ido, sai wannan da
takan riƙa tattarewa ta tsuke ko buɗe idan haske ya yi yawa ko ya yi kaɗan domin ta daidaita hasken da zai shiga cikin ƙwayar idon.
(iii). Daga waje akwai fatar ido da takan rufe ƙwayar idon a lokacin barci
ko kuma idan wani abu zai faɗa cikin idon, kamar yadda
Abdulƙadir (1990 sh. 7) ya bayyana.
Ƙura da dattin da iska takan hura a cikin idon mutum suna
iya haifar da jin zafi da ƙaiƙayi a ido, kamar yadda Abdulƙadir (1990 sh. 9) ya nuna.
A fagen magance wannan cutar ƙaiƙayin ido, sai a nemo ganyen
zogale ɗanye, a murtsuke shi, a
sami auduga (kaɗa/tauhwa) ko wani
farin ƙyalle mai tsafta. A tsoma cikin ruwan ganyen, a tatsa (matsa) ɗigo uku (3) a idon har sau
uku a rana, kamar yadda Jinju (1990 sh. 19) ya bayyana.
Shaihin Malamin ya tabbatar da ingancin maganin ta hanyar gwaji shi da kansa. Shi kuwa Samuel (2013) ya bayyana cewa yin hakan yana ƙara lafiyar idanu. Haka kuma ya bayyana cewa yana ƙara wa jiki ƙwarin garkuwa da kariya daga kamuwa da cututtuka. Axe (2016) kuwa, cewa ya yi zogale yana magance cututtukan da ƙwayoyin cutar bakteriya suke haddasawa. Wannan manuniya ce da take ƙara tabbatar da yadda itaciyar take maganin ciwon ido.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.