Ticker

6/recent/ticker-posts

Abubuwan Da Masu Bayar Da Magani Ya Kamata Su Yi

An Ciro Daga: Bakura, A.R., & Sani, A-U. (2026). Zogale a ƙasar Hausa: Magani, abinci, tattalin arziki. SAS Publishers. ISBN: 978-978-63958-1-4. https://doi.org/10.5281/zenodo.22682300

 Na

Adamu Rabi’u Bakura

Da

Abu-Ubaida Sani

Zogale a Kasar Hausa: Magani, Abinci, Tattalin Arziki

Zogale A Matsayin Magani

Shimfiɗa

Itaciyar zogale tana da muhimmin matsayi a idanun duniya. Ba a wannan zamani ba har ma a ƙarnonin da suka shuɗe, ta kai matsayin ginshiƙin ginin tattalin arzikin da ake alfahari da ita . Wannan ne ya sa, al’ummomi daban-daban kamar Romawa da Girkawa da Misirawa suka duƙufa a fagen tatso mai daga ‘ya’yan zogale wanda sukan sarrafa shi wajen aiwatar da turare da man shafawa. A cikin ƙarni na goma sha tara (19), gandayen zogale da suke Yammacin Indiya sun fitar da man zogale zuwa ƙasar Turai domin yin turare da giris na na’urori.

Al’ummomin ɓangaren ƙasar Indiya sun daɗe suna amfani da kwasfan zogale wajen abinci. Shi kuwa ganyen zogale ya kasance wani muhimmin abu da ake ci a duk farfajiyar ƙasashen Afirika ta Yamma da wasu sassan Asiya. Abin ƙayatarwa ne ƙwarai da gaske, dangane da jerin nau’o’in magungunan da ake yi da zogale waɗanda suke ƙunshe da muhimman sinadarin gina jikin ɗan’adam. Sakamakon amfanin da ake yawan yi da ita ne ya sa aka gano tana maganin cututtuka da dama. Wannan ne ya haifar da mayar da hankali wajen binciken irin cutar da take magani. Wannan babi ya mayar da hankali a kan tattauna zogale a bagiren magani.

Abubuwan Da Masu Bayar Da Magani Ya Kamata Su Yi

Wajibi ne mai bayar da maganin gargajiya ko likitan zamani su aiwatar da waɗannan abubuwan kafin su ba maras lafiya magani. Yin haka shi ya fi zama maslaha da kariya gare su da kuma waɗanda Allah ya ɗora musu haƙƙin kula da lafiyarsu. Abubuwan kuwa sun haɗa da:

1. A binciki nau’i da asalin ciwo.

2. A gano dalilan da suka haifar da faruwar rashin lafiya.

3. A binciki maras lafiya bincike mai zurfi domin a gane jikinsa zai iya samar da kariyar ciwon, ko cutar ta fi ƙarfinsa. Idan har maras lafiya yana cikin kuzarinsa sosai da sosai har jikinsa yana iya yin tsayayya da cutar, a nan ba a buƙatar ba da magani.

4. A binciki matuƙar yanayin maras lafiya.

5. A binciki yanayin sauye-sauyen da maras lafiya yake fuskanta.

6. A gano adadin shekarun maras lafiya.

7. A binciki ɗabi’unsa da abin da ya saba da shi.

8. A yi la’akari da sakamakon yanayin da ake ciki.

9. A yi la’akari da asalin mazaunin maras lafiya.

10. A duba yanayi da kuma lokacin da mutum ya kamu da rashin lafiya.

11. A yi kyakkyawan nazari har a gano cutar wadda za a iya magance ta ne ko kuwa ba za a iya maganin ta ba.

12. A binciko ingantaccen maganin da ya dace wajen warkar da cutar.

13. A nemo ingantattun hanyoyin da za a yi amfani da maganin da yadda ya dace a sarrafa shi.

14. Mai bayar da magani bai taƙaita kawai ga magance cuta ba, aikinsa ya haɗa da kare aukuwar cutar da ta fi haɗari a rayuwa.

15. A zaɓa tare da rubuta magani mafi sauƙi.

16. Mai bayar da magani ya kasance ya mallaki ilimin cututtukan zuciya da na rayuwa tare da hanyoyin magance su.

17. Ya zama mai rangwame da haƙuri ga maras lafiya.

18. Ya kasance mai amfani da nau’o’in magunguna da waɗanda suka danganci ruhaniyya tare da amfani da tunaninsa. 

Post a Comment

0 Comments