An Ciro Daga: Bakura, A.R., & Sani, A-U. (2026). Zogale a ƙasar Hausa: Magani, abinci, tattalin arziki. SAS Publishers. ISBN: 978-978-63958-1-4. https://doi.org/10.5281/zenodo.22682300
1.1.1 Rabe-Raben Cututtuka
Cututtukan
da sukan kama (sami) ɗan’adam iri biyu ne,
kamar yadda Abual-Rub (2003) ya zo da su:
1. Cututtukan sarari
2. Cututtukan ɓoye
1.1.1.1 Cututtukan Sarari
Cututtuka ne da
sukan kama jiki saboda wata ƙwayar
halittar jikin ɗan’adam aikinta
ya yi rauni ko kuma ta daina aiki gaba ɗaya, sakamakon
shigar wata illa (ƙwayar cuta) cikin jiki ta
hanyar ci ko sha ko shaƙar
iska ko kuma ta sanadin jima’i. Yayin da wata ƙwayar halittar jikin ɗan’adam ta kamu da illa, sai jiki ya ɗauki zafi. Wani lokaci ana iya ganin cutar da ido ƙarara ko a fahimce ta.
Akwai cutar da
ba a iya fahimta balle a gan ta ƙarara
da ƙwayar ido, sai dai wanda
cutar take addaba kawai ne zai ji jikinsa ya sauya ba ya jin wani sukuni. Wasu
lokutan har ya kasa moriyar komai. Don haka ana iya cewa, cututtukan sarari su
ne na jiki, waɗanda ake iya gani da ido ko a taɓa ko a yi bayanin yadda ake ji a jiki tare da magance su kai
tsaye. Ire-irensu su nau’uka biyu ne kamar haka:
A. Cututtuka
Masu Tsayayyen Magani
Rukunin waɗannan cututtuka, haka Allah ya halicci bayinsa (‘yan’adam da
dabbobi da wasu halittu) da su. Kowannensu ya san yadda zai magance su, ba sai
ya nemi wani ya ba shi magani ba. Cututtukan sun haɗa da: Yunwa da ƙishirwa
da gajiya da sanyi da zafi da sauransu. Ɗan’adam da dabbobi da sauran halittu masu rai duk sun san yadda za
su yi maganinsu da kansu da zarar sun kamu da su (Abual Rub, 2003 sh. 20).
B. Cututtuka
Masu Buƙatar Kulawar Mai Magani
Cututtukan da
suka danganci wannan sashe, suna buƙatar
tunani da binciken yanayin da marar lafiya yake ciki, wanda yakan
wanzu a sakamakon jin zazzafan zazzaɓi fiye da kima, ko jin
sanyi ko bushewar fatar jiki ko kuma haɗuwar dukan alamomin, kafin
a gano nau’in cutar, sannan a kai ga magance ta (Abual Rub, 2003 sh. 20). Akwai
wasu abubuwa da ba cuta ba ne, amma fa idan aka ƙi gusar da su daga cikin jikin ɗan‘adam sukan zama cuta yayin da suka yi yawa. Ire-iren waɗannan abubuwa sun haɗa da: Maniyyi
da maziyyi da fitsari da kashi da tusa da jini da amai da atishawa da hamma da
gyatsa da barci da yunwa da ƙishirwa. Idan ɗayan waɗannan ya wanzu fiye da kima a jiki yakan haifar da cuta, ba za a
samu zaman lafiya ba, sai an sami maganin kawar da shi. Wasu cututttukan kuma
sukan samu ne a sakamakon rauni/jimuwa, kamar yankan wuƙa ko taka ƙusa ko haɗari, da sauransu.
1.1.1.2 Cututtukan Ɓoye
Cututtuka ne na
zuciya, waɗanda damuwa da rashin kwanciyar hankali ne
da sukan samu ɗan’adam a sakamakon
sha’anin rayuwar yau da gobe. Hakan yakan sa a wayi gari mutun ya kasance kamar
maras lafiya, har sai lokacin da irin wannan yanayin ya kau, zai sami lafiya.
Yayin da ire-iren waɗannan cututtukan zuciya suka taso wa ɗan’adam, zai kasance cikin yanayi irin na maras lafiyar jiki. Yanayin yana iya haɗawa da damuwa da rama da rashin bacci. Abubuwan da sukan haifar da cututtukan ɓoye sun haɗa da: Sha’awa da tsoro da soyayya da hassada da kishi da ƙiyayya kamar yadda Adamu (1998 sh. 10) da Abual-Rub (2003 sh. 19) suka nuna.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.