An Ciro Daga: Bakura, A.R., & Sani, A-U. (2026). Zogale a ƙasar Hausa: Magani, abinci, tattalin arziki. SAS Publishers. ISBN: 978-978-63958-1-4. https://doi.org/10.5281/zenodo.22682300
Ma’anar Magani
Bunza, (1990 shf.. 135)
ya bayyana kirdadon samuwar kalmar magani da ya fi karɓuwa a tsakanin masana Hausa a yau. Wannan ra’ayi ya yi daidai
da ɗaya daga cikin ra’ayoyin da suka shafi samuwar magani ga Bahaushe,
wato ra’ayin gwadawa. Ra’ayin na nuna cewa, kalmar magani ta samu ne a lokacin
da Bahaushe yake ƙoƙarin samar wa kansa magungunan cutuka
daban-daban. Yayin da cuta ta samu, sai Bahaushe ya tattaro ganyaye da saiwu da
sassaƙe-sassaƙe domin gwadawa, har sai ya samu wanda zai
samar masa da waraka. Zai ɗauki nau’in sassaƙe ko saiwa ko ganye (da makamantansu), sai
kuma ya ce: “Ma gwada wannan mu gani.” Wato dai za a gwada a gani ko
za a dace?
Sannu a hankali
har aka gajarce furucin. Daga nan aka koma cewa: “Ma yi ma gani.” Bayan tafiya
ta yi tafiya ne kuma aka sake gajarce furucin zuwa: “Ma gani.” Yayin da aka haɗe kalmomin guda biyu, su ke ba da sunan “Magani.” A bisa wannan
ra’ayi, kalmar ta “magani” gamin-gambiza ce.
Masana da dama sun yi ƙoƙarin bayyana ma’anar kalmar magani gwargwadon
fahimtarsu. Kano (2006 sh. 316) ya bayyana ma’anar magani da cewa:
Magani, yana nufin duk wani abu da ake sha ko shafawa ko
kuma ɗurawa a jiki ta hanyar yin allura, don neman samun lafiya ko kariya daga
wata cuta.
Shi kuwa Ahmad
(1984) ya bayar da ma’anar magani da cewa:
Magani shi ne, duk
wani abu da za a yi, ko wata hanya ko kuma wata dabara da aka yi don gusar da
cuta daga jikin mutum ɗungurumgun ko kuma kwantar
da ita don kawo jin daɗi ga jiki ko ga zuciya da
sauƙaƙa duk wata wahala ga jiki da damuwa da ita
cutar kan iya haifarwa.
Bakandamiyar
ma’ana ta magani ita ce wadda Bunza (1989 sh. 134) ya bayyana inda yake cewa:
Magani wata
hanya ce ta warkar da ko kwantar da ko rage wata cuta ta ciki ko ta waje ko
wadda aka samu ta haɗari. Ko kuma neman
kariya ga cuta ko abokan hamayya ko neman ɗaukaka ta daraja
ko ta iddab ta hanyar iddabaru da sihirce-sihirce na ban al’ajabi.
Gobir, ya
bayyana ma’anar magani da cewa:
Hanya ce ta
kawar da, ko kwantar da, duk wata cuta ta jiki ko ta zuciya, ko neman ɗaukaka, ko kariya daga makaru da jifa da sihiri ko siddabaru
(Gobir, 2012 sh. 224).
Wannan ma’ana
da Gobir ya bayar tana nuni da cewa, ana neman magani ne domin ɗaya daga cikin waɗannan dalilai:
a. Neman waraka
b. Kwantar da cuta
c. Neman ɗaukaka
d. Neman kariya
Lura da wannan, akan nemi magani ne domin dalilai mabambanta. A taƙaice duk wani abin da zai hana jin daɗi da walwala da nishaɗi da gudanar da rayuwa yadda ya kamata, to sunansa cuta. Hanyar da ake bi domin kawar da shi (ko kuma abin da ake amfani da shi domin kawar da wannan cuta) shi ake kira magani.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.