Ticker

6/recent/ticker-posts

Bayani Game Da Cuta Da Kuma Bayyanar Cuta a Tsakanin Al’umma

 An Ciro Daga: Bakura, A.R., & Sani, A-U. (2026). Zogale a ƙasar Hausa: Magani, abinci, tattalin arziki. SAS Publishers. ISBN: 978-978-63958-1-4. https://doi.org/10.5281/zenodo.22682300

 Na

Adamu Rabi’u Bakura

Da

Abu-Ubaida Sani

Zogale a Kasar Hausa: Magani, Abinci, Tattalin Arziki

2.1 Bayyanar Cuta a Tsakanin Al’umma

“Cuta” kalma ce ta Hausa da take cikin jerin kalmomin suna jinsin mata. Jam’in kalmar shi ne, cututtuka ko cuce-cuce ko cutuka kamar yadda Garba (1990 sh. 29) da Abubakar (2015 sh. 81) da BUK (2006 sh. 80) suka nuna. Garba (1990 sh. 29) ya fassara kalmar da: “Rashin lafiya, mai daɗewa da nakasarwa.” Bunza (1989: 132) ya bayyana ma’anar cuta da cewa: “Cuta wata damuwa ce da ta shiga jikin ɗan’adam don raunana lafiyarsa. Ko kuma ta shafi zuciyarsa ta fuskar buƙatocinsa na jin daɗi ko ɗaukaka darajarsa da sunansa.”

Idan aka duba ma’anonin da aka bayyana na cuta da idon basira, za a iya cewa, ita ce duk wani lahani da yake haddasa rashin sukuni a cikin jiki, wanda kan haddasa rashin walwala da jin daɗi, wani zubin har yakan wanzar da raɗaɗi da zogi a jiki. Haka kuma, za a iya kallon cuta a matsayin wata damuwa ko illa da take shiga cikin jikin mutun ta raunana masa wasu ƙwayoyin halitta da suke zama garkuwa a jikin ɗan’adam, ko taɓuwar ƙwaƙwalwa da ke haifar da hauka wato taɓuwar hankali, sakamakon shan wani abu ko zuwan abu daga hukuncin Ubangijin sammai da ƙassai.

Allah buwayi gagara misali, shi ne cikin ikonsa da iradarsa ya halicci halittu masu rai da marasa rai, na ruwa da na tudu waɗanda ake iya gani da waɗanda ba a iya gani, kamar mala’iku da rauhanai da aljannu da mutane da dabbobi da tsuntsaye da ƙwari da tsirrai da duwatsu. Ya kuma halicci ɗan’adam. Ya sanya ƙasa ta kasance mazauninsa a sassa daban-daban na doron duniya. Ya ƙagi cututtuka masu ɗimbin yawa tare da sanadin wanzuwar su a tsakanin al’umma. Ya sanya magani ga kowace cuta, sai fa tsufa da mutuwa. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce:

لِكُلِّ دَاءٍ دَوَاءٌ، فَإِذَا أُصِيبَ دَوَاءُ الدَّاءِ بَرَأَ بِإِذْنِ اللَّهِ عَزَّ وَجَلَّ

Likulli dā'in dawā', fa-idhā uība dawā'u ad-dā'i bara'a bi-idhni llāhi 'azza wa jall.

Fassara

"Kowace cuta tana da maganinta. Idan aka samu maganin da ya dace da cutar, sai mai cutar ya warke da izinin Allah Maɗaukakin Sarki."

(Sahih Muslim: 2204; Sunan Ibn Majah: 3436)

Post a Comment

0 Comments