Naƙaltar Matakan Tantance Kafafen Intanet Na Gaskiya
Yana da kyau mutum ya kiyaye sosai game da
tura keɓantattun bayanansa a kan intanet. Kafin tura wani bayani, ya zama dole
mutum ya tantance kafar intanet ɗin ko imel ɗin da aka tuntuɓe shi da shi. Dole
ne mai kasuwanci a kan intanet ya naƙalci dabaru da hanyoyin
tantance kafafen intanet na gaskiya da na boge. Wasu daga cikin hanyoyin da ake
bi domin gane kafafen intanet na gaskiya su ne:
1. Lura da https://:
Kowace kafar intanet da take ta haƙiƙa kuma take da tsaro, to takan fara ne da https//.
Waɗanda ba su da tsaro yawanci sukan kasance ba tare da “s” ba, wato http://
kawai. A duba misali a cikin hoton da aka kawo a ƙasa:
Hoto Na 6.7: Kafar
intanet ɗauke da https:// a cikin liƙau ɗinta
Madogara: Shafin
farko na kafar intanet ɗin AMLAS[1] (www.amlas.amsoshi.com) (29/12/2024)
A cikin wannan hoto, za a ga cewa liƙau ɗin ya fara da https://. Yana da kyau
a lura cewa, wannan kaɗai ba hujja ba ce da take nuna cewa kafar intanet
amintacciya ce. Kafin tabbatar da ingancinta, dole ne sai an nazarci sauran alƙaluman da suke nuna aminci da ingancin kafafen
intanet.
2. Alamar Rufaffen Kwaɗo: Kafa mai aminci takan zo da
alamar rufaffen kwaɗo a gurbin rubuta liƙau ɗin burauza (address
bar). Wannan ya danganta da nau’in burawuzar da aka hau. A duba misali a
hoton da aka kawo a ƙasa:
Hoto Na 6.8: Alamar
rufaffen kwaɗo a farkon gurbin rubuta liƙau a burawuza
Madogara: Shafin
farko na Amsoshi (www.amsoshi.com)
a kan burawuzar Mozilla
3. Cikakkiyar Lura da Abajadin
Sunan Kafar Intanet Ɗin:
‘Yan damfara suna iya ƙirƙirar kafar intanet da suna mai matuƙar kama da na wata sananniyar kafa. Sukan sauya
abu ɗaya kawai a cikin abajadin. Misali, za su iya rubuta bakandemiya.com ko
bakondamiya.com a maimakon bakandamiya.com.
4. Ƙaramar Kafa (Subdomain)
Ƙarin da ake yi wa sunan kafa domin fitar da ƙaramar kafa a farko ake yin sa (kafin asalin
sunan kafa), ba a ƙarshe ba. Misali, buy.amsoshi.com
zai iya zama sunan ƙaramar kafar amsoshi.com,
amma amsoshi.buy.com wani abu ne na daban. A har kullum ƙarin yana zuwa ne kafin asalin sunan kafar?
5. Kurakurai a Cikin Kafa
Yawancin kafafen intanet da aka yi don damfara suna ƙunshe da kurakurai. Akan samu kurakuran rubutu
da na tsarin kafar kanta. Yayin da kafa ta tuntuɓi wani mutum a matsayin cewa
kafar kasuwanci ce, to ya kamata ya nazarci yadda ɓangarorin kafar suke. Idan
ya ci karo da kurakuran rubutu, to lallai akwai alamar tambaya a kan wannan
kafa. Dalili kuwa shi ne, kafafen intanet na kasuwanci sukan yi matuƙar ƙoƙari wajen ganin sun yi aiki da ƙwararru da za su tace dukkannin bayanansu kafin
ɗorawa a kan intanet.
6. Bayanan Tuntuɓa
Kafafen intanet na gaskiya sukan sanya cikakkun bayanan tuntuɓa na
haƙiƙa. Duk wata kafa da ta ɓoye bayanan tuntuɓarta,
lallai akwai alamun tambaya a kan wannan kafar. A bisa wannan, ɗaya daga cikin
hanyoyin tantance ingancin kafa shi ne a duba idan suna da shafin “Tuntuɓe Mu”
wanda yake ɗauke da gamsassun bayanai.
7. Bincikar Daɗewar Kafar
Intanet
Ana iya duba lokacin da aka ƙirƙiri kafar intanet ɗin ta amfani da kafafe irin
su Who is Lookup by ICANN (https://lookup.icann.org/) da ViewDNS.info
(https://viewdns.info/).
Idan ya kasance kafar intanet ta daɗe sosai tana aiki, to akwai yiwuwar ta
gaskiya ce. Idan kuwa ya kasance kafar intanet ba a daɗe da buɗe ta ba, to
lallai ya kamata a ƙara takatsantsan da ita
matuƙa. A duba misali a cikin
hoton da yake ƙasa:
Hoto Na 6.9: Duba
Daɗewar Kafar Intanet Ta Amfani Da Shafin lookup.icann.org
Madogara:
https://lookup.icann.org/en
A nan za a ga yadda shafin farko na wannan kafa yake. Wani abin
bugrewa shi ne, mutum yana da damar zaɓen harshen da yake buƙatar amfani da shi daga cikin jerin harsunan da
aka zayyana a saman shafin. Yayin da aka sanya adireshin wata kafar intanet, to
za a samu bayanai masu muhimmanci waɗanda za su bayyana lokacin da aka buɗe
kafar. A duba misali a hoton da yake ƙasa:
Hoto Na 6.10: Wani
Ɓangare Na Sakamakon Da Aka Samu Bayan Duba
Bayanan www.amsoshi.com
Madogara:
https://lookup.icann.org/en
Wannan wani ɓangare ne na sakamakon da aka samu yayin da aka ziyarci shafin www.amsoshi.com.. Za a iya ganin cewa, an buɗe wannan kafar
intanet tun shekarar 2017. Hakan yana nufin ta daɗe tana aiki. Daga nan mai
bincike yana iya yanke hukuncin cewa akwai ƙamshin kafa ce ba ta damfara ba. Da a ce ta
damfara ce, ba za ta daɗe haka ba ba tare da an samu rahotanni game da ita ba a
kan intanet.
Duk da haka, sakamakon nan kaɗai bai wadatar ba. Bai zama abin da
za a dogara a kansa shi kaɗai ba. A maimakon haka, shi dai kawai ya kasance ne
ɗaya daga cikin matakan da mutum zai iya bi domin ƙoƙarin fahimtar ingancin kafar intanet ɗin da yake
hulɗa da ita.
8. Bincikar Tsokaci Game Da
Kafar Intanet
Ana iya hawa intanet domin nemo
tsokacin da mutane suka yi dangane da kafar (sai a lura da tsokacin boge kamar
yadda aka yi bayani a ƙarƙashin 2.1.6).
Naɗewa
Dangane da damfarar kan intanet, yanzu sai dai a ce gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah. Wanda gemun ɗan uwansa ya kama da wuta, kamata ya yi da shi ya shafa wa nasa ruwa. An damfari mutane masu yawa a kan intanet ya zuwa yau, wanda wannan littafin ya kawo misalai masu yawa game da nau’o’in damfarar. Bugu da ƙari, littafin ya kawo hanyoyi da dabarun kare kai daga sharri da barazanar ‘yan damfara. Idan har aka yi amfani da waɗannan dabaru yadda ya kamata, lallai ana iya kauce wa harin da ‘yan damfara suke yi a kafar intanet. Yaya gara takan yi da dutse? A koyaushe sai dai a ce musu “kifi na ganin ka mai jar koma!” Allah ya kiyashe mu da sauran mutanen ƙwarai baki ɗaya daga ‘yan damfarar kan intanet. Amin!
[1] Amsoshi Language Services, kamfanin ayyukan da suka shafi harshe da kimiyyar harshe ne musamman na kan intanet, wanda yake Nijeriya. Ayyukan da suke samarwa sun haɗa da fassara da tafintanci da gyaran rubutu da sauransu.
Manazarta:
Sani, A-U., Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.