Shimfiɗa
Kowace
cuta tana da magani. Ruwa yana ƙasa sai ga wanda bai tona ba. Akwai hanyoyi da matakai
daban-daban da suka kamata masu hulɗoɗi a kan intanet su naƙalta domin kare kansu daga
barazanar ‘yan damfarar kan intanet. Kamar yadda aka nuna a babukan da suka
gabata, ana toshewa ne ‘yan damfara suna sake buɗe sababbin hanyoyi. Waɗanda
suke kasuwanci da sauran sha’anoni a kan intanet, sai dai su riƙa tuna maganar nan ta
Hausa: “Allah ba ya barin mutum ba aiki.” Dole ne su kasance a faɗake, sannan su ci gaba da bincike game da
hanyoyin kare kai daga duk wata nau’in damfarar kan intanet da aka ɓullo da
ita. Wannan babin ya mayar da hankali kan fito da wasu muhimman dabarun kare
kai daga damfarar kan intanet.
Nisantar
Kwaɗayi
Yana
da kyau a fahimci cewa, mafi yawan damfarar da ake yi wa mutane takan faru ne a
sakamakon kwaɗayin da suke nunawa game da samun wani abu. Kwaɗayi shi ne babban
abin da ‘yan damfara suke amfani da shi wajen ɗauke hankalin mutane da yaudarar
su. Dole ne wanda yake hawa kan intanet ya san da cewa, babu wani mutum ko wani
kamfani da haka kawai yake fitar da kyautar kuɗaɗe ko wani abu mai daraja a kan
intanet. Idan kuma wani kamfani zai fitar da garaɓasa ta musamman, to akwai
tsararrun hanyoyi da zai bi domin zaƙulo waɗanda zai bai wa garaɓasar, ba wai raba
liƙau
a kafafen sada zumunta ba.
Kullum
saƙonni
daban-daban suna zagaya kafafen sada zumunta musamman WhatsApp da Facebook
waɗanda suke yin alƙawuran ƙarya dangane da samun garaɓasa. Sukan kasance cikin sigar
kyauta ko wani kasuwancin kan intanet mai matuƙar bayar da riba cikin ƙanƙanin lokaci. Duk waɗanda
suka yaudaru suka tura kuɗinsu a matsayin rajista ko hannun jarin kasuwanci,
kuɗaɗensu sun bi shanun sarki. Idan kuwa su ne na farko-farkon shiga harƙallar, za su samu riba
yayin da za a yi amfani da su wajen jawo wasu mutane cikin harkar (ta hanyar
tsarin gayyata), waɗanda za a kulle da kuɗaɗensu. A duba misali a hoton da yake
ƙasa:
Hoto
Na 6.1: Kwaɗaitar
Da Mutane Domin Saka Hannun Jari
Madogara: Wannan ɗaya ne daga cikin saƙonnin kasuwancin damfara da
ake yaɗawa a WhatsApp
A
wannan hoton da yake sama, za a ga yadda mai turo saƙon ya yi iƙirarin cewa ya saka hannun
jari na naira dubu saba’in da biyar (₦75,000), sannan ya samu ninkin wannan kuɗi
a cikin awa ɗaya. Kwaɗayi ne kaɗai zai rufe wa mutum idanu har ya faɗa wannan
tarkon damfarar.
A
ɓangare ɗaya kuwa, ‘yan damfara suna yaɗa liƙau da sanarwar garaɓasa
iri-iri daga kamfanoni ko gwamnatoci. An fi yin haka a lokacin da ake bukukuwan
salla ko na zagayowar shekara ko samun ‘yancin kai, ko dai wani muhimmin abu da
ya shafi ƙasa
ko duniya. A duba misali a ƙasa:
Hoto Na 6.2: Garaɓasar Damfara
Madogara: An ɗauko daga zauren WhatsApp mai suna ‘Zauren Dalibai’
Wani
abin da ya kamata mutane su lura da shi daga wannan hoto shi ne, liƙau guda ɗaya aka yi ta
maimaitawa a ƙasan dukkannin nau’o’in layukan (Airtel da MTN da Glo da
9mobile). Bugu da ƙari, me ya sa garaɓasar ba za ta kasance a kan kafafen
intanet na kamfanonin sadarwar ba? Mene ne haɗin wannan kafa da su kamfanonin
sadarwar? Kwaɗayi ne yake rufe wa mutane ido, yadda waɗannan tambayoyi ba za su
zo ransu ba. A duba ƙarin misali a ƙasa:
Hoto Na 6.3: Tallafin Ƙarya Daga Gwamnati
Madogara: An ɗauko daga zauren WhatsApp na FASSARAR MAFARKI DAGA
KITABU WASSUNNA DA IJMA’IN MALAMAI
A
Nijeriya ana ci gaba da kukan talauci da yake ƙara yi wa mutane katutu. A
ɓangare ɗaya kuwa, gwamnatoci suna ci gaba da yin alƙawura (na gaskiya da na ƙarya) game da bayar da
tallafi domin rage raɗaɗin talauci. ‘Yan damfara sukan yi amfani da irin wannan
dama domin gwada sa’arsu. Kwaɗayi da talauci sukan rufe wa mutane ido ta yadda
ba za su ko bincika ingancin wannan kafa ba. Ba za kuma su yi tunanin cewa babu
abin da ya haɗa wannan kafa da gwamnati ba.
A
wani lokaci, akan tuntuɓi mutum da cewa akwai wasu kuɗaɗe da ake son turo masa
saboda Allah don an aminta da shi. Wani lokaci kuwa akan ce za a turo masa ne
saboda ayyukan da yake yi na taimakon mutane. A duba misali a ƙasa:
Hoto Na 6.4: Saƙon Imel Na Damfara Game Da Tura Maƙudan Kuɗi
Madogara: Saƙon imel (9/12/2024)
A
ire-iren waɗannan saƙonni, ya kamata mutum ya tambayi kansa cewa, a dalilin me
a cikin miliyoyin mutanen da suke duniyar intanet za a zaɓe shi domin a turo
masa maƙudan
kuɗi haka? Ƙin ƙarawa kuwa, mai turo saƙon a can wata uwa duniya
take. Babu sanayya kowace iri a tsakaninsu.
A
Lura Da Nasarar Da Ba a Nema Ba
‘Yan
damfarar kan intanet sukan tura saƙonni ga mutane kai-tsaye cewar sun yi nasarar samun
wata kyauta. Sukan tura saƙonnin ko dai ta imel ko ta lambar waya ko kuma ta kafafen
sada zumunta. Nau’o’in abubuwan da suke cewa an yi nasarar samu sun haɗa da
kyaututtuka daga bankuna ko wasu kamfanoni ko kuma wani nau’in caca.
Abu
na farko da ya kamata mutum ya tambayi kansa shi ne, me ya sa zai ci wannan
gasar ko wannan kyautar alhali bai nema ba? A irin wannan lokaci, ya kamata
mutum ya yi karatun ta-natsu, ya tantance bayanan da aka turo masa. Idan har
mutum yana son bincikar gaskiyar lamarin, to ya tura saƙo kai-tsaye ta imel ɗin
kamfanin da aka ambata. Kada ya danna liƙau ko abin da aka maƙala (attachment) a saƙon da aka turo.
Duk
mai son kare kansa daga sharrin ‘yan damfara da zamba a kan intanet, ya zama
wajibi a gare shi ya inganta tsaron akawun-akawun ɗinsa. Ire-iren waɗannan
akawun-akawun ɗin sun haɗa da:
a. Na
kafafen sada zumunta
b. Na
kasuwannin duniyar intanet
c. Na
kafafen intanet (website ko blog)
d. Na
kan manhajoji a kwamfutoci ko wayoyin hannu/salula (computer and mobile apps)
e. Imel
Matakan da mutum zai bi
domin inganta tsaronsu kuwa sun haɗa da sanya kalmar sirri mai inganci. Ingancin
kalmar sirri a nan yana nufin saka kalmar sirri mai wahalar ganewa. Abubuwan da
ya kamata a lura da su wajen zaɓen kalmar sirri mai inganci sun haɗa da:
1. Dole
ne ta kasance tana da tsawo. Aƙalla ana so ta kai gurabu takwas (8) ko sama da haka.
2. Ana
so ta ƙunshi
manya da ƙananan
harufa. Yana da kyau a tuna cewa, gurabun kalmar sirri sukan
fito ne a sigar da ake kira da suna ‘case sensitive” a Ingilishi, wato
babban baƙi
daban yake da ƙaramin baƙi. A bisa haka, idan mutum ya sanya /y/ a madadin /Y/, to
za a nuna masa cewa kalmar sirrisirrin ba daidai take ba.
3. Ana
so kalmar sirrisirrin ta ƙunshi lambobi. Sanya harrufa kaɗai a matsayin kalmar
sirri ba shi da inganci kamar yadda yake idan an haɗa da lambobi.
4. Ana
so kalmar sirri ta ƙunshi alamomi, misali “%” ko “#” ko “&” ko “*” ko “@”
ko “>” ko “}” da sauransu.
5. Ba
a so jerin harrufan da suke cikin kalmar sirri su kasance suna da alaƙa da mai akawun ɗin. Wannan
yana nufin, mai suna ‘Adamu Kabir’, ba a so a kalmar sirrinsa a samu “Adamu’ ko
kuma ‘Kabir.’
6. Ba
a so lambobin da suke cikin kalmar sirri su kasance masu alaƙa da mai akawun ɗin. Wannan
yana iya kasancewa shekarun haihuwa ko lambar ɗalibta ko lambar waya,
da makamantansu. Misali, a kwatanta cewa akwai wani mai suna ‘Salihu Aliyu’
wanda aka haifa a shekarar ‘2004.’ Idan ya sanya kalmar sirri ‘Salihu2004’ ko
‘Aliyu2004’ ko ‘salihu2004’ ko ‘aliyu2004’ ko ‘2004salihu’ ko ‘2004Salihu’ da
sauransu... duk za su kasance masu sauƙin ganowa ta hanyar yin canki-canka.
7. Yana
da kyau kalmar da mutum zai rubuta ta bayar da wata ma’ana a gare shi. Wannan
ba dole ba ne, amma yana da muhimmanci wajen taimaka masa domin hardacewa cikin
sauƙi
tare da tunowa a duk lokacin da yake so. Duk da haka, akwai buƙatar mutum ya
adana a wani wurin da babu wanda zai iya bincikowa ba tare da izininsa ba.
8. A
kiyaye amfani da kalmar sirri iri guda ga akawun mabambanta. Idan mutum yana
yin haka, to za a iya yin kutse a dukkannin akawun ɗinsa da zarar an gano
kalmar sirrinsa.
9. A
bisa waɗannan bayanai, misalin kalmar sirri mai inganci za ta iya kasancewa: Now$1is>#1000?Ops!.
Abin da aka rubuta a nan shi ne: Now 1 dollar is greater than 1,000 naira?
Ops!. Wanda yake amfani da wannan salo a yayin rubuta kalmomin sirrinsa,
zai iya tunowa da yadda kalmar sirri take da zarar ya tuna abin da ya rubuta a
salon rubutun yau da kullum. Zai tuna ɗin ne kasancewar ya san yadda yake taƙaita kalmomi yayin rubuta
kalmar sirri.
Wani
abin da zai ƙara
taimakawa shi ne ƙara matakin tantancewa na biyu, wato two-factor
authentication (2FA). Wannan tsari ne wanda idan an kunna shi, akan turo
lambobin tantancewa zuwa imel ko lambar wayar mutum yayin da aka yi ƙoƙarin shiga akawun ɗinsa
musamman a kan sabuwar na’ura. Wani lokaci kuwa akan tura saƙo ne zuwa ga wayarsa inda
za a buƙaci
ya danna abin da yake nuni da cewa shi ne yake ƙoƙarin shiga akawun ɗin a kan
wata na’ura ta daban. Wannan tsarin yana taimakawa wajen ƙara wa akawun ɗinsa tsaro
da tabbatar da cewa babu wanda zai yi ƙoƙarin shiga akawun ɗin ba tare da mai shi ya
samu sanarwa ba.
Bayan
waɗannan, akwai buƙatar mutum ya riƙa sabunta manhajojinsa a duk lokacin da
sababbin siga (new versions) suka fito. Yayin da kamfani suke ƙoƙarin fito da sabuwar sigar
manhaja, sukan tabbatar da sun toshe duk wasu hanyoyin da ‘yan damfara da kutse
a kan intanet suka buɗe domin illata masu amfani da manhajojin. Idan mutum ya
ci gaba da amfani da tsohuwar manhajar, hakan yana nufin zai iya fuskantar
barazanar ‘yan damfara da masu kutse a kowane lokaci.
Dole ne mutum ya riƙa sabunta manhajojin na’urorinsa a duk lokacin da sabon sigar
na’urar ta fito. Yawancin sababbin sigogin sukan zo da ƙarin tsaro tare da toshe wasu ƙofofin da suka fahimta
waɗanda za a iya shigo da damfara ta cikinsu. Bugu da ƙari, a kullum ana kan fito da baros iri-iri. Duk sabon baros da
aka fito da shi wanda zai iya yin tasiri a kan manhaja, dole ne masu manhajar
su sabunta fasaharta ta yadda za ta iya kauce wa wannan ƙalubale ko haɗari. Sabunta manhajar zai taimaka wajen tabbatar da
cewa mutum yana aiki da wadda take da cikakken tsaro bisa alƙaluman tsaro na lokacin.
Fahimtar
Take-Taken ‘Yan Damfara
Duk
wani salon damfara da aka fito da shi, za a tarar da cewa akwai wani tsari na
musamman da ‘yan damfarar suke amfani da shi. Duk da haka, akwai abubuwa na
gama-gari da za a iya lura da su a cikin saƙonnin ‘yan damfara. Daga
cikinsu akwai:
1. Akan
samu kurakurai a cikin saƙonnin da suke turowa waɗanda ba su dace a same su ba idan
sun kasance ne daga kamfani na haƙiƙa.
2. Akan
samu maimaicin zance a cikin saƙonnin sama da ƙima domin jaddadawa da jan hankali da ƙoƙarin nuna gaskiyar saƙon.
3. Akan
samu kwalliya sama da ƙima a cikin saƙonnin. Wannan ya shafi amfani da imoji da
launukan rubutu daban-daban. A duba misali cikin hoton da aka kawo a ƙasa:
Hoto Na 6.5: Kwalliya Sama Da Ƙima A Rubutun Saƙon Damfarar Kan Intanet
Madogara: An ɗauko daga zauren WhatsApp na ACCESS REAL INVESTMENT
(29/12/2024)
A cikin wannan hoto da
aka kawo a sama, za a ga cewa kwalliyar da aka yi wa rubutun ya wuce ƙima. Ya koma salon jan hankali na masu rubutu a kafafen sada
zumunta kawai. Kafaffen kamfani mai kyakkyawan tsari ba zai yi irin wannan
rubutun ba. A duba ƙarin misali a ƙasa:
Hoto Na 6.6: Rasitin damfara a saƙon imel
Madogara: Saƙon imel (10/12/2024)
Akwai abubuwan lura masu
yawa a wannan hoton. Da farko dai an turo saƙon ne daga imel ɗin da
ba na kamfani ba,
wato an nuna cewa saƙon daga kamfanin McAfee
yake. Babu yadda za a yi wannan kamfani su turo rasiɗi ta amfani da wani imel
wanda ba na kamfaninsu ba. Haka kuma, yadda aka turo saƙon bai yi tsari ba. Babu wani tsararren bayani da yake nuna ƙwarewa (professionalism) wajen tura saƙon. Duk ire-iren waɗannan misalai ne na abubuwan da mutum zai lura
da su domin gane saƙonnin ‘yan damfarar kan intanet.
Manazarta:
Sani, A-U., Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.