Wanda aka gabatar a taron tallafawa Marayu da aka yi a zauren taro, Hanyar Likoro zuwa Kudan da ke Garin Kudan. Ranar Lahadi 7 ga Watan Ramadan 1440 Hijiriyya, daidai da 12 ga Watan Mayu 2019 Miladiyya.
DOKIN ZUCIYA BA A HAWANKA
SAI AN YI NADAMA: TSOKACI A KAN AYYUKAN SON RAI DA MUTUM KAN YI A ƘARSHE YA
RINƘA DA-NA-SANI
DAGA
MU’AZU SA’ADU MUHAMMAD
KUDAN
JAMI’AR SULE LAMIƊO KAFIN
HAUSA, JIHAR JIGAWA.
GABATARWA:
Da sunan
Allah Mai rahama Mai jinƙai, Mai kowa, Mai komai, Mai aikata abin da Ya so, ga wanda Ya so,
a sadda Ya so, a yadda Ya so, ko ana so ba a so dole bayi su so. Tsira da
amincin Allah su tabbata ga shugaban halittu Annabi Muhammadu, da Alayensa da
Sahabbansa.
Wannan maƙala na da
niyyar yin bayani a kan ɗabi’ar
son zuciya ko son rai. Nazarin zai dubi ma’anar son zuciya ko son rai, da
dalilan da kan jawo su, tare da haɗarinsa ko illoilinsa ga wanda ya yi da kuma abokin zama. Sannan da
kuma yadda son zuciya ke rusa al’umma. Kamar yadda Bahaushe yake cewa a wata
Karin Magana, “Son zuciya ɓacin
zuciya”, shi ne Bahaushe kan yi kinaya ya ce, “Dokin zuciya ba a hawanka sai an
yi nadama”. Wannan maƙala za ta fito da shawarwari ta yadda za a kaucewa hawa dokin
zuciya. Domin kaucewa faɗawa cikin
haɗari da
kuma yin nadama daga ƙarshe. Na rufe da kammalawa
da manazarta
MA’ANAR DOKI: CNHN
(2006) Dabbar gida da ta fi jaki da alfadari girma wanda ake hawa da sirdi don
tafiya ko zuwa yaƙi. Wata dabba ce mai ƙafafu huɗu da kofato, yana da
kunnuwa biyu da jela dambajejiya.
MA’ANAR ZUCIYA: CNHN
(2006) Wata curarriyar tsoka da take cikin ƙirjin
mutum ko dabba ko tsuntsu, wanda ke aika jini zuwa sauran sassan jiki.
Wata tsoka ce mai
launin ja, mai siffar ƙwai, wacce take aikin
sarrafa jini a jikin Mutum ko dabba, daga ƙirji.
Zuciya kuma ita ce muhalli inda tunani da Imani suke. Tunani na samuwa ne ta
hanyar tuntuɓa
tsakanin zuciya da ƙwaƙwalwa, domin shi hankali a kai (ƙwaƙwalwa)
yake. Akan ce in rai ya ɓace
hankali kan nemoshi.
DOKIN ZUCIYA: Wata
kalma ce da ake kira harɗeɗɗen suna. Wadda take nufin
bin son zuciya ko son rai, wato duk abin da zuciya ta riya wa mutum sai ya bi.
CNHN (2006) Son zuciya wato mutum ya aikata abin da ya ga dama. Hawa dokin
zuciya wato ya fusata.
Da Larabci ana cewa
“Hawan nafs”. Da harshen Turanci kuma ana cewa “Selfishness”.
A ƙur’ani Suratul
Nazi’at aya ta 37 zuwa 41. Inda aka bayyana cewa duk wanda so duniya
ya yi abin da yake so to jahannama ce makomarsa. Haka kuma duk wanda ya ji
tsoron Allah ya hana zuciyarsa abin da take so, to aljanna ce makomarsa. Alhaji
Aliyu Namangi Zariya na cewa:
Zuciya ita goɗiya ce,
Wanda duk ya sake ta goce,
Sai ta kai shi cikin wuta
ce,
Kar ka sau ragama ta kauce,
Ta fice da guda ta
aika ɗanya.
Bisa la’akari da wasu
abubuwa da sukan ingiza mutum ya hau dokin zuciya suna da yawa. A mafi yawan
lokuta waɗannan
guda goma su ne suka fi fazgar mutum mace ko namiji babba ko yaro, sai daga
baya ya dawo yana da-na-sani. Malamai suka ba da shawarar cewar mutum ya
yawaita faɗar:
Hasbunallahu wani’imal wakilun.
1. Fushi
2. Ƙin karɓar gaskiya
3. Kwaɗayi
4. Haɗama / Babakere
5. Hassada
6. Mugunta / Ƙeta
7. Ƙarya
8. Yaudara / Saɓa Alƙawari
9. Girman Kai
10. Cin Amana
1. FUSHI: Bisa
mahanga ta addini fushi yana da illa, don haka Annabi (S. A. W) ya yi hani da
yin fushi, a wani Hadisi ya ce: “La tagadab” (Kar kai fushi) har sau uku. Haka
kuma wani Hadisin Annabi (S. A. W) da ya tambayi Sahabbai cewa wane ne
mai ƙarfi? Sahabbai suka ce wanda aka yi kokuwa ya yi kaye. Sai Annabi
(S. A. W) yace a’a, mai ƙarfi shi ne wanda fushinsa
ya taso, amma ya danne zuciyarsa. Duk wanda ya yi fushi aka ce ya yi haƙuri matuƙar dai ya
yi, to Allah zai taimakeshi, in kuma ya ƙi to zai
ga abin ƙi. Kamar yadda ya zo a Suratul Luƙman aya
ta 17. Inda aka nunawa mumini ya tsai da sallah, ya yi umarni da aikin alheri,
kuma ya yi da mummunan aiki, kuma ya yi haƙuri.
Bisa al’ada mutum mai
saurin fushi, Bahaushe na kiransa da kububuwa. Ba duka harkoki ake yi da shi
ba. Domin ana kallon sa mai murɗaɗɗen hali. Misali idan miji
da mata suka samu saɓani sai
aka ga ana bas u haƙuri suna ƙi, da zarar ɓarna ta auku (saki) , sai
kuma a koma nadama.
A kimiyyance, wani
Likitan ƙwaƙƙwalwa a Jami’ar New York Amurka ya ce: “Halaye huɗu kan sanya mutum yin
haukar wucin gadi: 1. Fushi. 2. Tsoro. 3. Sha’awa. 4. Zaƙuwa”.
2. ƘIN KARƁAR
GASKIYA: Haƙiƙa son zuciya ne kan hana mutum karɓar gaskiya. Ƙiri-ƙiri mutum
na sane za a faɗa masa
gaskiya amma sai ya yi ƙemudugus ya ƙI yarda.
Daga baya kuma mutum ya zo yana yin da-na-sani da ban yi ba. Aliyu Namangi
Zariya ya ce:
Tun da sauran hankalinka,
Yaƙi birnin zuciyzrka,
Nemi tanlidi kaza ka,
San su alwala da wanka,
Tun ba a aiko ma mala’ika ba.
3. KWAƊAYI: A
al’adance Bahaushe na cewa “Kwaɗayi mabuɗin wahala” ko “Idan da kwaɗayi da wulaƙanci” ko
“Mai kwaɗayi shi
ya san gidan mai rowa” ko “Duk wanda ya shiga motar kwaɗayi zai sauƙa a
tashar wulaƙanci” ko “ Idan ka ga abincinka inda bai dace ba, ka haɗiye kwaɗayinka ka wuce, idan ba ka
haɗiye kwaɗayinka ba, to kwaɗayinka zai haɗiyeka. ” Aliyu Namangi
yace:
Ka ci ka sha ka yi teɓa,
Ka mace kabari karɓa,
Ka ruɓe tsutsa ta sharɓa,
Yanzu me ya fi kyau ka zaɓa,
In ba farali da
nafila ba.
Ga shi ka tozarta kanka,
Son kuɗi ya sa ka shirka,
Da dubun miliyan gareka,
Ran da ka mutu sai a kaika,
Da tufan daba zai yi fan bakwai ba.
. Ɗabi’ar
kwaɗayi: Bayan
wannan kuma,sai ɗabi’ar kwaɗayi. Matuƙar a ka ce mutum makwaɗaici ne, mace makwaiɗiya
ce, to haƙiƙa suna cikin haɗari.
Domin Bahaushe yace : “kwaɗayi
mabuɗin wahala”ko “idan da kwaɗayi da wulakanci” ko “idan baki ya ci dole ido yai
kunya”. Da sauran maganganu da dama masu nuna illar kwaɗayi a rayuwa. To don haka duk wanda ke da kwaɗayi ƙuda ne yana iya faɗawa haɗari. Kwaɗayi
ya ƙunshi
son abin duniya (kuɗi da komatsan duniya) ,ko
kuma son cin daɗi kamar nama, ko kifi, ko kayan ƙwalam da maƙulashe. Misali yawan son abin duniya ke sa mace karɓar kyauta, ko roƙo a inda bai dace ba. An
sha samun matan da aka yiwa kyauta daga baya abin ya zama fitina. Ko kuma wasu
matan a saboda tsire ko balangu ko kaza ko kuma atamfar anko, sai su ba da
kansu. Wasu kuma a saboda kuɗi, ko a wurin talla, ko wurin aiki sai su ba da kansu a ballagazar arha.
A addinance an ce duk wanda
ya guji duniya kuma ya guji abin hannun mutane zai yi daraja a idon al’umma.
4. HAƊAMA KO
BABAKERE: Son kai ya yi wa mutum yawa, tare da son tara abin duniya. Son
zuciya kan lulluɓa tunanin
mutum, a inda ya kan fifita kansa ko buƙatarsa a
kan ta waninsa. Idan wani abu aka ba shi ya raba wa jama’a sai ya handame ya
hana wasu. A wani lokaci kuma sai ya tattare ya babbake ya hana wani samu da
yawa sai kaɗan.
Masu cin rashawa da soke,
Masu fince da masu tarke,
Mai ganin nassi ya take,
Zuciyarsa ba za ta warke,
Su yi nesa da cin haramiya
ba.
5. HASSADA: Son
zuciya ne kan sanya mutum ya yi baƙin ciki
don wani ɗan uwansa
ya samu alheri. Ko kuma mutum ya yi fatan arziƙi ko
alheri da wani ya samu to ya lalace. Bahaushe ya ce “Hassada ga mai rabo taki”,
“Hassada ga mai rai ba ta hana arziƙi” Kamar
mummunan kishi da mata ke da shi a wannan zamani. Domin irin wannan kishi kamar
jayayya da ƙaddara ne.
Kishi a rashin kishi: Kishin
banza (kishin mai dadaro). A inda take ƙyamar
mijinta ya ƙara aure, amma kuma yana da farka a waje. Domin son zuciya
ta ƙi zama da kishiya, amma ƙawar
Alhaji ko Amimiyarsa ko abokiyar aiki za ta zo gidan, kuma ta karɓe ta hannu bibiyu.
Duk ɓarnar da
miji zai yi indai ba maganar kishiya to daidai ne.
Bisa la’akari da bayanan da
suka gabata. Kai tsaye muna iya cewa,duk macen da ta kasance da ɗaya daga cikin waɗannan ɗabi’u da aka lissafa. To ta
zama mara wayau,kuma ba ta da tsafta, kuma ta zama ƙazama. Ta
zama Ballagaza komai ilminta,komai barikinta, tana yin ɗigirgire ko kan-tafi da
rayuwarta
6. MUGUNTA KO ƘETA: Son
zuciya ne kan sanya wani ya yi tanajin mugun abu ga wani ɗan uwa, don ya cutar das
hi. Bahaushe na cewa “In zaka gina ramin mugunta ginashi gajere”. “Mugunta
fitsarin faƙo”. A mafi yawan lokuta ana samun wasu mutane sukan shirya mugunta
amma kuma sai ta dawo kansu.
Alhaji Baba Maigyaɗa agege yana cewa:
Mun gode tabara sarki mai
kyauta,
Da yayyo bayinsa galibi
masu maganta,
Yayyo waɗansu galibi masu mugunta,
Halin ‘yan duniya na ke son
in kwatanta,
Sun fir ƙaunar
tajiri fa ba mara samu ba.
Idan ba ka da dukiya a yau
an raina ka,
Sa’o’in ;ya;yanka su sukan
riƙa takaka,
Da gangan wasu ja’irai
sukan riƙa darjeka,
Idan yai Magana a c eta
wane yana hauka,
Da ka yi shiru, sai a ce fa
wane bai cika farai ba.
7. ƘARYA: Son
zuciya ne kan sanya mutum ya shirya abin da ba a yi ba ya faɗa. Ko ya ƙirƙiri wata
Magana ya shirya ƙarya. A yau saboda son zuciya babu babban babu yaro wajen ambaton
abin da ba gaskiya ba.
A addinance Annabi
(S. A. W) yace, “Lallai gaskiya tana yin shiriya ko jagora ga zuwa aikin
alheri, shi kuma yana yin jagora zuwa aljanna. Ita ɗarya kuwa tana yin jagora
zuwa ga fajirci (Ɓarna) , ita kuma ɓarna tana yin jagora zuwa wuta. Idan mutum ya saba yin ƙarya
Allah zai sa a rubuta masa maƙaryaci a duk inda yai
Magana a ɗaukeshi
maƙaryaci.
A al’adance duk inda
mutum ya kasance maƙaryaci to ana ɗaukarsa mutumin banza. Ba ma haka ba, ko da yawan santu mutum ya
cika yi, akan ce maganar wane ka ji ta hauka barta a nan. A maganganun yau da
kullum a kan ce “Ai wane durum ne uban ‘yan ƙarya”, ko
“ƙarya
kamar kuɗin duba”,
ko “ƙarya kamar guntun yaƙi”,
Ibrahim Narambaɗa na
cewa:
Na bar ƙarya ko
ina kiɗi,
Nai sittin saba’in naka
jira,
Mai saba’in ƙarya ana
ta zunɗai nai.
A wannan zamani ƙarya
ba ɗauketa
laifi ba, musamman da wayar hannu ta zo. Domin son zuciya da raina zunubi sai
mutum ya kantara ƙarya da waya ba kunya ba tsoron Allah.
8. YAUDARA KO SAƁA ALƘAWARI: Son
zuciya ne ke sanya mutum yin yaudara. Wato ya san abu ba zai yiwu ba, amma sai
ya nuna zai yiwu, daga baya ya fasa. Tun da farko shi wanda aka yi wa alƙawarin
zai sakankance da al’amarin, a ƙarshe ya
yaudareshi ya saɓa alƙawari.
A al’adance Bahaushe
na cewa: “Wani ya faɗa ya
cika, ya faɗa bai
cika ba Allah ya tsinewa mai ƙarya.
Dalilin da yasa ake ɗaukar
mayaudari a matsayin maƙaryaci kuwa shi ne, tun a zuciyarsa ya san ba zai yi ba, amma sai
y ace zai yi. Duk wanda bai cika alƙawari na
kallonsa ba dattijo ba ne. Aƙilu Aliyu yana cewa:
Malam nemi ɗiyar dattawa,
sanda kake riya neman
aure,
Ba mai gemu ko saje ba,
Ba mai faffaɗar riga ba,
Ba mai mota ko babur ba,
Mai Magana ka ji
tamkar ƙyaure.
A addiniance kuwa,
ana ɗaukar
mayaudari a matsayin munafuki mai fuska biyu. Kamar a wani Hadisi da Annabi (S.
A. W) yake cewa: “Alamun munafuki uku ne: 1. In yai Magana ya yi ƙarya. 2.
In aka amince masa, ya ci amana.
3. Idan ya yi alƙawari ya
saɓa.
9. GIRMAN KAI: Wannan
munguwar ɗabi’a
babu abin da ke sanya wa a yita, sai son zuciya. Zuciyar mutum za ta riya mashi
cewar ya fi kowa, sai shaiɗan ya rinƙa tunkuɗashi. Girman kai ne kan
sanya mutum ƙin karɓar nasiha
ko shawara, ko wa’azi, saboda yana ganin shi ya fi ƙarfin a
faɗa masa
Magana. Shaiɗan kan raɓe ne a bayan wani matsayi
da mutumin yake da shi. Misali, mulki, wato shugabanci, ko wadata kamar dukiya
ko ilimi. A irin nan sai shaiɗan ya rinƙa nuna
masa ai kowa na ƙasa da shi. Alhali kuwa a Alƙur’an Suratul
Luƙuman aya ta 13 zuwa 19 an
nunawa mumini yadda zai girmama iyaye, da kuma yadda zai yi tafiya ban da taƙama, da
yadda zai yi magana ban da ɗaga murya wato hargowa. Alhaji Aliyu Namangi Zariya yana cewa:
Shi fa girma kai hali ne,
Wanda ke cutar mutane,
Shi tafarkin gargara ne,
Wanda ko ke bi shi ƙone,
Ba san mafita a lahira ba.
A addinnance Allah ya
haramta girman kai. Domin Annabi (S. A. W) ya ce: “Duk wanda ya mutu da girman
kai a zuciyarsa daidai da ƙwayar zarra ba zai shiga
aljanna ba. ”
A al’adance Bahaushe
na cewa “Girman kai rawanin tsiya, don ya kan hana hanyar arziƙi”. A
mafi yawan lokuta mutum mai girman kai bai cika yin kwarjini ba a cikin
al’umma.
10. CIN AMANA: Son
zuciya wato son rai, shi ke sanya mutum ya ci amana bayan an yarda das hi, amma
kuma ya yi cuta. Akwai inda a kan samu cin amana ta fuskoki da yawa kamar: Karɓar ajiya ta dukiya ko kaya
ko mutum ko dabba. Rike sirri ko rufa asirin wani na Magana ko na wani aiki.
Misali, mutum ya daɗa maka
wata Magana a matsayin sirri y ace amana kar wani ya ji. Kai kuma sai ka tafi
ka bad a labara, to ka ci amana. Haka kuma idan aka baka ajiyarr wani abu, sai
aka zo karɓa
maimakon a sameshi yadda yake, son zuciya sai ya sanyaka ka ɓata shi ko ka cinye. Aliyu
Namangi na cewa:
Kar ka so bidi’a ta zamna
Zuciyarka balle
hinaya,
kar ka zam mai so ka raina,
‘yan uwa ka tsare
amana,
ka bi sunna ba da kangara
ba.
11. SAƁON
ALLAH: A mafi yawan lokuta son zuciya ko bin son rai shi ne kan ingiza
wasu mutane aikata saɓon Allah,
Shaiɗan da
zuciya su ne ginshiƙan da suke tura mutane yin saɓon Allah. A nan ne ake hawa dokin zuciya sai daga baya mutum ya
dawo yana nadamar abin da ya aiakata na ɓarna. A Suratul Hashri aya ta 16, inda Shaiɗan kan tura mutum ya yi saɓo, sai bayan ya aikata sai
Shaiɗan yace:
ba ruwa na da kai, ni ina tsoron Allah. Aliyu Namangi Zariya ya na cewa:
Ko da dai laifi tudu ne,
Naka wanda ka tattara ne,
Ke hawa ka gano na wane,
Ga mutum mai gargaɗI ne,
Bai bar saɓon Ubangiji ba.
Mu Kaucewa Aikin Da Zai
Jawo Mana Zargi:
An samu
wani Hadisi a muwaɗɗa a babin
ittiƙafi, wanda ya yi bayanin cewa: Annabu (S. A. W) yana Ittiƙafi a
masallaci, sai ɗaya daga
cikin matarsa ta kawo masa ziyara. Ko da Annabi (S. A. W) ya fi to zai raka ta,
sai wasu samarin Madina suka zo wuce wa, suka yi masa sallama suka wuce. Bayan
har sun wuce, sai Annabi (S. A. W) ya kirasu, ya ce, “Zainab bintu Jashim, yace ni ne Muhammadu Ɗan Abdullahi wannan kuma
Zainab mata ta. sai Annabi (S. A. W) ya ce, “a’a kamar yadda jini ke yawo yana
zagayawa a jikin mutum, to haka Shaiɗan yake yawo a jikin mutum.
Wannan Hadisi ya
koyar da mu abubuwa kamar haka: Idan mutum yana ittiƙafi
matarsa za ta iya kawo masa ziyara. Dole ne mutum ya yi ƙoƙarin
kaucewa duk wani abu da zai sanya zargi a zuƙatan
mutane. Wannan ya ƙara nuna mana haɗari ko
illar keɓewa da
mace don zai sanya ƙaiƙayi a zukatan mutane. Dole ne mutum ya guji tsayawa da mace a inda
za a iya zarginsa, ko da matarsa ce.
Alaƙar mace da shaiɗan abu ne da yake a bayyane, wanda kuma aka yi bayanin
haka a wurare da dama tun daga Al-ƙur’ani mai girma har ya zuwa hadisan Manzon Allah (S. A.
W) , da kuma maganganun magabata. Baya ga wannan, ko a maganganun mu nay au da
kullum a kan ci karo da karin maganganu, maganganun azanci da sauransu.
Tun
farkon al’amari in muka dubi abin da ya faru tsakanin Annabi Adamu da Hauwa’u a
Al-jannah, shaiɗan bai rinjayi Annabi Adamu ba sai ta hanyar Hauwa’u ya
ci galabarsu ya yi sanadiyyar fitar su daga Al-jannah.
Suratul
Baƙara: aya 36.
Bayan wannan kuma, saboda alaƙar da ke tsakanin mace da shaiɗan, Manzon Allah (SAW) ya yi hani da a keɓe da mace, saboda da zarar sun keɓe to na ukun su shaiɗan ne, nan da nan kuma ba zai bar su ba sai ya yi sanadin
da suka yi ɓarna. Haka kuma shaiɗan kan yi amfani da mace a matsayin wata kibiya da yake
harbin mumini da ita. Yana da kibiyoyi guda biyu, in har ya harbi mutum da kuɗi ya ga bai same shi ba, to sai yasa ɗayar kibiyar ita ce mace. Shaiɗan kan yi amfani da mace a matsayin tarko na kama wasu
mutane ta hanyoyi da yawa.
12. KAUCEWA CIN
HARAM: Haƙiƙa an hana musulmai cin abin da yake haramun. Akwai wanda aka samu
ta hanyar haram, kamar ta hanyar sata, ko ƙwace, ko
yaudara. Haka kuma akwai wasu nau’o’in abincin da suke haramun ne, kamar wasu
dabbobi da giya da wasunsu.
Akwai Hadisin day a
nuna cewar duk jikin day a ginu da haramun, to ƙarshensa
wuta. Duk wanda ya ginu da haramun, ba za a karɓi addu’arsa ba. Duk da sanin haka sai son zuciya ya sanya wasu cin
haram.
13. SHAWARWARI: Zamu fara
da wata aya daga Ƙur’ani mai girma, mai cewa: Ita dai zuciya ba a bin ta. A Suratul
Yusuf aya ta 53. Innan nafsa la’amaratu bi su’i, illa man rahima
Rabbi. Lallai zuciya ta kasance mai ummarni da yin ɓarna, sai wanda ya tsare. A
wata ayar kuma a Suratul Nazi’at aya ta 41, aka ce: “man hafa
maƙama
rabbihi wanahan nafsun anil hawa fa’inaj jannati hiyal ma’awa. ”. Duk wanda ya
ji tsoron Allah ya ƙI bin son zuciyarsa, to aljanna ce makomarsa.
A al’adance kuwa,
Bahaushe na cewa: “Daga ƙin gaskiya sai ɓata”. Wanda wannan ne nufin
duk aiki mara kyau ya ƙi ji ya bi son zuciyarsa,
to zai kasance mai yin nadama. Kamar inda Bahaushe kan ce “Kowa ya ƙi jib a
zai ƙi gani ba” ko wanda bai ji bari bay a ji hoho. Wannan na ƙara nuna
mana illar bin son zuciya.
Dole ne mu faɗawa kan mu gaskiya, haƙiƙa akwai
wasu dabaru ko abubuwa waɗanda
Bahaushe ya yi tanaji don sarrafa doki na haƙiƙa. Domin
haka shi ma dokin zuciya akwai wasu dabaru ko abubuwa a ake amfani da su don
sarrafashi. Ga guda uku daga ciki kamar haka: Linzami, da dabaibayi, da tarnaƙi.
1. Linzami na hana
doki gudu ko tafiya, shi ne kamar birki ga abubuwan hawa na zamani. To shi ma
dokin zuciya yana da linzami, shi ne kamar hakai hakuri da azzakar wato
Ambato\n allah. Idan an ɓata maka
rai ka ji fushi ya taso maka, to ka tuna Allah ka ambaceshi ta hanyar yin
a’uzubillahi minas shaiɗanur
rajim. Ko ka yi wata addu’a, sannan kuma ka yi haƙuri domin
an ce “Haƙuri maganin zaman duniya”.
2. Dabaibayi, yakan
hana doki yawo ko ya yi nisan kiwo. To shi ma akwai abubuwan da dokin zuciya
kan hana shi yawo har ya ja mutum zuwa ga halaka. Dabaibayi kuwa shi ne barin
yin garadama, wato jayayya, Bahaushe na cewa: “Gradama matsirar sababi an bar
gamata ran wani bai ɓaci ba.
Haka kuma an ce ja-in-ja shi ke kawo tsinkewa. Don haka duk inda ka lura
gardama za ta kunno kai to ka kauce mashi.
A addinance Annabi ya hana
jayayya ko gardama. Akwai inda yace ka bar gardama ko ta addini ce. Kamar yadda
Aƙilu aliyu
yake cewa:
‘Yan uwa ga shawara, In
muna son gafara,
To mu yarda da ƙaddara,Sai
mu gaskata lahira,
Kar mu ruɗu da duniya.
To mu juya gargaɗI, wanda shi ne zai biɗi,
Taimako in farfaɗi, aibukanta, na bankaɗi,
‘Yan kaɗan daga Duniya.
Kar ka dinga yawan fushi,
Ban da kai wani babu shi,
Wanda zan auraniya.
Mu’azu Sa’adu Kudan yana
cewa:
Ya Allah ka tsaremu da
sharrin nan uku,
Sharrin Shaiɗan da kuɗi da na zuciya,
TUNA MUTUWA NA RAGE DOGON
BURI:
A wani
Hadisi da ya zo a Littafin Kitabu Ahadis y ace: Mumini ya rinƙa tuna
mutuwa, yawan tuna mutuwa na sanya mutum ya rage dogon buri.
DOGARO GA ALLAH: Matuƙar mumini
ya dogara ga Allah, ya mayar da al’amuransa zuwa ga Allah to zai samu nutsuwa,
kuma zai samu wadatar zuci, tare da samun mafita a rayuwarsa. Kamar yadda ya zo
a Alƙur’ani mai girma: Duk wanda ya dogara ga Allah to Allah ya isar
masa. Kuma duk wanda ya ji tsoron Allah zai samar masa mafita.
JIRWAYEN SON
ZUCIYA A ADABIN BAHAUSHE:
Akwai inda aka samu
jirawayen son zuciya a adabin Bahaushe da dama. Kamar a Karin Magana, Alal
Misalai: -
v
Dokin zuciya mutum biyu ba sa hawanka.
v
Son zuciya ɓacin
zuciya.
v
Ba a bin son zuciya don ba ta ƙashi.
v
Zuciyar mutum burinsa.
v
Ƙafa ba ta
zuwa inda zuciya ba ta je ba.
v
Zuciya mai mugun nufi.
v
Saurin fushi na kawo da-na-sani.
v
Karayar zuciya mafi karayar ƙafa
lalacewa.
v
Zuciya kin fi tukunya tafasa.
v
Sunɓulalle
marar kishin zuciya.
v
Dokin zuciya ba ka jin linzami.
v
Aikin da zuciya ta ɗauka ba a jin nauyinsa.
WASU ABUBUWAN LURA:
Babu wani
abu mai yi wa dokin zuciya zagi, wato jagora, kamar shaiɗan ko wakilansa. Ana iya
samun na sarari ko na ɓoye,
Misali, Aljani ko mutum, mace ko namiji. Da zarar mutum ya hau Dokin zuciya zai
kasance ba ya sauraron kowa, ba ya jin nasiha, a lokacin kuma ko an ba shi haƙuri ba
zai yi haƙuri ba.
Duk wanda ya hau
dokin zuciya ya kan rasa wasu abubuwa, kamar haƙuri, da
kunya, da hankali. Ma’ana yakan yi haukar wucin gadi a wani lokaci ma har
tunani yakan rasa. Amma kuma yana sauka daga dokin zuciyar, sai ya dawo
hayyacinsa a ƙarshe ya fara nadamar aikin da ya aikata.
Duk wanda ya hau
dokin zuciya zai iya cin mutuncin kowane ne, babu maganar ragowa domin idanunsa
sun rufe.
Duk wanda ya hau
dokin zuciya bai san ya kamata ba. A wurinsa ba babba ba yaro. Mahanar tausayi
ko haƙuri babu.
Duk wanda ya hau
dokin zuciya bai damu da muhallin da yake ba. Babu ruwansa da kunyar kowa zai
yi abin da yake so, sai ya biya buƙatarsa
shaiɗan ya
sake shi, sai ya fara nadama. Mafi yawan masu aikata laifi ba sa sauraron
nasiha, sai a ƙarshe sun faɗa hannun
hukuma ko an kai kotu, sannan su kan yi nadamar cewar, ai wane abokina ne ya ja
shi suka aikata laifin. Aliyu Namangi Zariya:
Haka zai riya ma da sata,
Hassada, kushe da ƙeta,
Sa ƙazaf da
yawan mugunta,
Manta sallah a lokacinta,
Zunubi ne ba abin musu ba.
Yawancin masu waɗannan ayyuka, shaiɗan ne kan ƙawatawa
zuciya ita kuma ya ingiza mutum ya aikata, shaiɗan kan sanyawa mutum asurka a hancinsa ya yi masa jagora har sai
ya aikata ɓarna
sannan ya kauce ya bar shi yana nadama. Bayan shaiɗan
RIYA: Yin aikin
alheri don wani ko wasunsu don su gani su yabawa mutum. Ko kuma bayan an yi
aikin alherin mutum ya rinƙa bayar da labari, don a ji
a yaba masa. A Suratul Baƙara aya
ta 264, inda aka hana mumini yin gori, da zobe, da riya, saboda
dukkansu suna ɓata aikin
alheri.
ROWA: Ƙin bayar
da wani da mutum ya mallaka ga kowa. Rowa ita ce kishiyar kyauta, rowa na
haifar da ƙiyayya da ƙyamar juna.
RAINI: Na nufin
rashin girmama kowa da ganin fifiko a kan kowa raini kan sanya mutum ya ƙi
sauraron kowa ta fuskar nasiha ko shawara balle kuma wa’azi. Duk wanda yake da
raini a ransa to bai ganin darajar kowa, babu wanda ya isa sais hi. Duk mai
raina mutum za ka sameshi da ɗagawa wato girman kai. A wurinsa tunaninsa ya fi na kowa, duk
wanda ya yi wani aiki ko wani tutiya faɗi wata Magana in ba shi ba to ba daidai ba ne.
GORI: Ka yi wa
mutum kyauta ko wani alheri ko taimako sannan daga baya ka goranta masa. Ka rinƙa cewa
“ka ga kamar ban yi masa kaza ba, ko ni na ba shi kaza ba”. Tabbas gori
na ɓata aikin
alheri. A Suratul Baƙara aya
ta 264, inda aka hana mumini yin gori, da zobe, da riya, saboda
dukkansu suna ɓata aikin
alheri.
ZOBE: Bayan
mutum ya yi wa wani mutum kyauta, sai kuma daga baya ya dawo ya ƙwace. Duk
wannan na faruwa a sakamakon son zuciya. Musamman na bayan an ɓata wa mutum rai wato ya yi
fushi. A Suratul Baƙara aya
ta 264, inda aka hana mumini yin gori, da zobe, da riya, saboda
dukkansu suna ɓata aikin
alheri.
ZUGA: Ingiza
wani don ya aikata wani mugun aiki, ta hanyar faɗa masa wasu kalmomi da za su tunzura shi. A ƙarshe sai
a samu tashin hankali a tsakanin mutane.
GANGANCI: Yin wani
abu bisa kasada ko da kuwa an san mutum zai cutu sai ya aikata saboda son
zuciya. Aliyu Nmangi Zariya y ace a Littafinsa na Infiraji:
Kar ku yarda da cin amana,
Ko mutum mai son hiyana,
Ko gani balle ka zauna,
Wanda ka san fasiƙina,
Ba a yarda kuyi abokantaka
ba.
Annabinmu y ace da tsoka,
Ɗaya mutum
a cikin jikinsa,
In ta ɓaci duk jikinka,
Ma’ana ko zuciya ya duba.
Zuciya ita goɗiya ce,
Wanda duk ya sake ta goce,
Sai ta kai shi cikin wuta
ce,
Kar ka sau ragama ta kauce,
Ta fice da guda ta
aika ɗanya.
Gyaruwanta barin ayyuka,
Masu janye ƙafa su
kaika,
Nan da nan a cikin tarukka,
Wanda ko a zatonka,
Ba ka riski abin da kai
nufi ba.
Shi fa girma kai hali ne,
Wanda ke cutar mutane,
Shi tafarkin gargara ne,
Wanda ko ke bi shi ƙone,
Ba san mafita a lahira ba.
Masu cin rashawa da soke,
Masu fince da masu tarke,
Mai ganin nassi ya take,
Zuciyarsa ba za ta warke,
Su yi nesa da cin haramiya
ba.
KAMMALAWA:
A ƙarshe dai
wannan muƙala ta yi nazari ko bayani a kan son zuciya ko son rai wanda aka
yi masa kinaya da abokin zuciya. An kawo ma’anar son zuciya da dalilan da kan
jawo haka, haɗarin haka
ko illolin. Nazarin ya kawo wasu shawarwari da za su taimaka domin samun
mafita. Muƙalar ta ɗora
bayananta a kan mahangar addini, sannan da mahangar al’adar Bahaushe, da kuma
bayani a kimiyance.
MANAZARTA:
Aliyu A (1976) , Fasaha
aƙiliya. Northern Nigerian Publishing Company. Zaria
Bunza AM (2000) Muhallin
Hankali Da Bagiren Hauka A Hausance” Muƙala cikin
mujallar Hausa Studies22: 122 Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya Jami’ar
Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato.
Gumi A. (1980) Fassara
Arba’unna Hadis. Northern Nigerian Publishing Company Zaria.
Gumi A (1970) Fassara Hausa
Alƙur’ani
mai girma, Hadimaini Haramaini Makka.
Namangi A (2012) ,
Waƙoƙin Infiraji a kammale Juz’ul na 1-9. Northern
Nigerian Publishing Company, Zaria.
Harold. I. K. (1994)
Synopsis Psychiatry Behavioural Sciences/Clinical Psyciatry. Eight Edition.
Imam A (1989) , Magana
Jari ce. Littafi na ɗaya. Northern Nigerian Publishing Company Zaria.
Tafida U (1870) , Jiki
Magayi. Northern Nigerian Publishing Company Zaria
Imam A (1939) , Ruwan
Bagaja. Northern Nigerian Publishing Company Zaria.
Sa’adu M (2010) , Zuciya
Sarauniya Ce. Unpublish Book.
Lawrence M. B. (1960)
Therapeutic Counseling and Psychotherapy. PrintedIn Engfewood Cliffs New Jesey
USA.
Malik I (Ba Shekara)
, Muwaɗɗa
Malik. Darul Fika Beirut Lebanoon.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.