An ciro daga littafin:
BIƊA DA TANADI A DUNIYAR INTANET
(Sana’o’i, Kasuwanci, Ƙwadago)
Na
Abu-Ubaida SANI
Abdulrahman ALIYU
MATASHIYA
GAME DA BIƊA DA TANADI A DUNIYAR YAU
Tun farkon samar da halittu a doron duniya
ake samun sauye-sauye a kusan dukkannin ɓangarorin rayuwa. Mahangar addini da
ilimin kimiyya da fasaha da kuma hankalin tuwo duk sun tabbatar da hakan.
Sauye-sauyen da ake samu sun haɗa da: (i) waɗanda suke aukuwa bisa tsarin
halittar duniya (misali girma da duniya take ƙarawa[1] da raguwar girman jiki da tsawon rayuwar
mutane) da (ii) waɗanda suke faruwa sakamakon ayyukan halittu (misali samuwar
na’urori da sababbin gine-gine da makamantansu).[2]
Biɗa da tanadi suna da gurbi na musamman a
rayuwar Hausawa. Yanaye-yanayensu suna sauyawa da ƙara samun cigaba daga lokaci zuwa lokaci. Hausawa sun
biyo waɗansu matakai tun daga kan furfure/musanye na tsarin ba ni gishiri in
ba ka manda, har zuwa matakin saye da sayarwa da fatauci. Samuwar hanyar
rubutu da karatu ya buɗe musu wani sabon babin damar rubuta sunaye da farashin
kayayyakin kasuwanci tare da samar da allunan talla. An sake samun cigaban
zamani yayin da rediyo da talabijin suka samu. Su kansu sun kasance hanyoyin
neman kuɗi a zamanance ta hanyar yin aiki tare da gidan rediyo ko talabijin.[3] A ɓangare ɗaya kuwa, sun samar da sababbin
hanyoyin tallata haja ga masu sana’o’i da kasuwanci daban-daban.
Samuwar intanet babban sauyi ne da duniya ta
samu a ƙarni na ashirin (Ƙ 20). Hakan ya ƙara tabbata, yayin da a yau
ake mayar da lamuran hulɗoɗin yau da kullum zuwa intanet. Harkar biɗa da tanadi
suna daga cikin nau’o’in hulɗoɗin da suke ƙara samun gindin zama a duniyar intanet.
Sannu a hankali tallace-tallace suna ci gaba
da komawa kan intanet. Daɗin daɗawa, intanet ɗin karan kansa ya zo da sababbin
damarmakin kasuwanci ga Hausawa. Sun haɗa da gina kafafen intanet da kasuwancin
kuɗin intanet da buɗe gidajen talabijin a kafafen intanet, da dai sauran
damarmakin samun kuɗi waɗanda kai tsaye intanet ne ya zo da su.[4]
Samuwar intanet a shekarar 1983 ya zo da
gagarumin sauyi a ɓangarorin rayuwa daban-daban a faɗin duniya. Da wuya a samu
wani al’amari da ya yi tasiri a kan rayuwar al’umma tamkar intanet. A yau, babu
wani ɓangare na rayuwar ɗan’adam wanda intanet bai taɓa ba.[5]
Duk da an samar da intanet tun a ƙarni na ashirin (Ƙ 20), ƙarni na ashirin da ɗaya (Ƙ 21) ya zo da sababbin abubuwa a fannin da suka girgiza
duniya. Bunƙasar kasuwancin duniyar intanet da samuwar ƙirƙirarriyar basira
(Artificial Intelligence (AI)) sun sauya alƙiblar rayuwa baki ɗaya. Tuni hankalin manyan ‘yan kasuwar
duniya ya karkata kan wannan fage.
A ɓangare guda kuwa, a yau rayuwar duniya
baki ɗaya tana ƙara karkata a kan intanet. Wannan ne ya ja
hankalin Clement (2020 SL. 4) inda ya ce: “By now, a world without the
internet is unimaginable.” Ma’ana: “A yanzu, ba za a iya kwatanta yadda
duniya za ta kasance ba idan aka ce babu intanet.” Tawagar Pandora FMS
(Pandora, 2023 SL. 1-18) na da fahimta makamanciyar wannan, inda har suke ganin
cewa da wuya rayuwa ta gudana a yau idan babu intanet. Ire-iren waɗannan iƙirari ba romon baka ba ne kawai, domin kuwa a yau an wayi
gari:
a. Kasuwanci ba zai haɓaka ya yi gawurtar
a-zo-a-gani ba, sai an haɗa da intanet.
b. Makaranta ko cibiyar ilimi ba za ta kai ƙololuwa a fice ba, sai ta gwane wajen sarrafa intanet.[6]
c. Ƙasa ba za ta samu bunƙasa da ƙarfin ikon faɗa-a-ji ba,
har sai ta nuna wa duniya ita ba kanwar lasa ba ce a sha’anin intanet.
d. Muryar malamin addini ba za ta karaɗe duniya
ba, har sai an haɗa da intanet.
e. Al’adu da tadojin wata al’umma ba za su yaɗu
a haƙiƙanin siffofi da sigoginsu
ba, sai idan masu su sun auri intanet.
Yana da kyau a san da cewa, kafafen intanet
na ɗaya daga cikin hanyoyin kasuwanci a zamanance. An samu ƙaruwar kafafen intanet na Hausa musamman daga wajajen
shekarun 2015 zuwa yau (2026). Babban ƙalubalen shi ne, wasu daga
cikin waɗannan kafafen intanet ba Hausawa ne suke jagorantar su ba. Hausawan ma
da suke jagorancin kafafen sun kasance ba masu ilimin harshe da al’adun Hausa
ba.[7]
Shehu (2013) ya nuna damuwarsa game da yadda
waɗanda ba Hausawa ba suke ci da harshen Hausa. Bugu da ƙari kuma, sau da dama sukan kawo naƙasu ga Hausar musamman ta fuskokin da suka shafi ƙa’idojin rubutu da gurɓata al’ada. A bisa haka ne ma yake
ganin cewa ya zama wajibi ga malaman Hausa da su yi yunƙurin kare harshen kamar yadda takwarorinsu suke yi a
harshen Ingilishi da Faransanci da makamantansu. Ya ce:
A tashi tsaye gadan-gadan domin a tsawata a
tabbatar da cewa an kare mutunci da martabar wannan harshe na Hausa ta hanyar
nuna wa ma’aikatan gidajen rediyo na ƙasashen waje ire-iren
kura-kuran da suke yi a wajen rubutunsu na Hausa, musamman ma ta yadda suke
tura shi a yanar gizo-gizo da kuma yadda suke tura wa jama’a a wayoyinsu na
tafi-da-gidanka (salula). (Shehu, 2013 sh. 64)
Farfesa Aliya Adamu tana da irin wannan
ra’ayi dangane da yawaitar rubuce-rubucen Hausa a kafar intanet musamman na
labarai. A. Adamu (keɓantacciyar tattaunawa, 7 ga watan Mayu 2019) wadda ta
kasance manazarciyar ƙagaggun labarai ta ce:
Mu ne ya kamata mu yi wani ƙoƙari na bincike tun da wuri,
domin mu gano tare da tantance inganci da rashin ingancin labaran Hausa da ake
ɗorawa a kafafen intanet. Idan ba mu yi haka ba, kafin mu farga an yi musu
gagarumar illa.[8]
La’akari da waɗannan bayanai, a har kullum
abu ne mai muhimmanci a yi hoɓɓasa wajen samar da kyakkyawan wakilcin al’adun
Hausawa a duniyar intanet. Kamar yadda Bahaushe yake cewa: “Sai bango ya tsage ƙadangare yake samun mafaka.” Yayin da aka nuna halin
ko-in-kula game da bayyana wa duniya haƙiƙanin al’adun Hausawa, an ba da ƙofa ga mutane na daban domin aikata yadda suka ga dama.
Rubuce-rubuce game da hanyoyin neman kuɗi a
kan intanet za su taimaka wajen haska wa Hausawa sababbin hanyoyin biɗa da
tanadi. Hakan zai yi matuƙar taimaka wa ɗaiɗaikun
mutane wajen samun aikin yi da rage zaman banza. Zai kuma taimaka wajen bunƙasa tattalin arziki da cigaban ƙasar Hausa da ma ƙasa baki ɗaya. Garba (2013
sh. 125) ya jaddada hakan inda yake cewa, bunƙasar Hausa a intanet zai taimaka wajen bunƙasar harshen da kuma cigaban yanki da ƙasa baki ɗaya.[9]
[1] Ƙur’ani mai tsarki da ilimin
kimiyyya duk sun tabbatar da cewa duniya tana ƙara girma. A duba Ƙur’ani (51:47) da Gohd
(2024).
[2] Yana da kyau a lura da cewa, sauye-sauyen da
suke faruwa a duniya suna kasancewa bisa wani sarƙafaffen tsari mai alaƙa da juna. Misali a nan shi ne, yau da gobe da sauyin
yanayi na tilasta wa mutane ƙirƙirar sababbin hanyoyin sauƙaƙa rayuwa. A ɓangare guda
kuwa, sababbin hanyoyin sauƙaƙa rayuwa na yin tasiri tare da samar da sauyi ga yanayin
duniya (kamar tiriri da hayaƙin ababen hawa da
masana’antu da suke haifar da ɗumamar yanayi).
[3] Aiki a gidan rediyo ko talabijin bai taƙaita ga aikin jarida ba kawai. Ya haɗa da ɗaukar hotuna
da bidiyoyi da gyara sauti ko bidiyo da tsara shirye-shirye da kula da na’urori
da dai sauransu. Duk waɗannan hanyoyin samun kuɗi ne da suka zo wa Bahaushe a
zamanance.
[4] Yana da kyau a lura da cewa, wannan littafin
ya mayar da hankali ne a kan biɗa da tanadi a kan intanet. Kasancewar
hanyar samun kuɗi tana da alaƙa da harshe ko adabi ko
kimiyya da fasaha ko ilimin gama-gari, ba shi yake nuna cewa ya fita daga
bagiren al’ada ba. Al’adar da take ciki ita ce kasancewar Hausawa suna ƙara rungumar waɗannan hanyoyin samun kuɗi tare da dogaro
da su. Hakan bai fita daga farfajiyar biɗa da tanadinsu ba, wanda ya tabbatar
da shi a matsayin wani ɓangare na al’adunsu da suka samu sakamakon tasirin
zamani.
[5] Duk wani ɓangare na rayuwa da al’amuran
zamantakewa da aka duba, sai an ci karo tasirin intanet ko dai kai tsaye, ko a
kaikaice. Bayan taron watan Maris na shekarar 2010 da BBC ta shirya kan Tasirin
Fasahar Intanet, ta wallafa a shafinta cewa: “Fasahar intanet fasaha ce da wasu
masana suke cewa ta sauya fasalin yadda ake gudanar al'amuran rayuwa a duk faɗin
duniya.” A duba BBC Hausa (2010 SL. 1).
[6] Yayin da makaranta ko cibiyar ilimi take son
ta yi fice a duniya, dole ta kasance ta yi amfani da intanet yadda ya kamata. A
ciki za ta baje hajarta. Hakan zai sa mutane daga ko’ina a faɗin duniya su ci
karo da ayyukan da makarantar ko cibiyar take gudanarwa. Haka kuma, ayyukan
malaman makarantar za su yi fice a duniya ne kawai idan sun kasance a kan
kafafen intanet fitattu.
[7] Yayin da aka yi rashin sa’a al’umma ba ta da
wakilai a kan intanet, za a samu wasu mutane na daban waɗanda za su riƙa ɗora bayanai dangane da al’adunta. Ba dole ne su ɗora
ingantattun bayanai ba kasancewar ba su da ilimi na haƙiƙa game da al’adun. I.S.S.
Abdullahi, (keɓantacciyar tattaunawa, 1 ga watan Satumba 2017) ya yi tir da
bayanan da ya ci karo da su a wata kafar intanet mai suna Maguzawa, kasancewarsa
masani a wannan ɓangare.
[8] Prof. Aliya Adamu wadda a lokacin take
Shugabar Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya na Jami’ar Jihar Sakkwato, ta furta
wannan batu ga Prof. Umar Bunza. Shi ya kasance dakta (a lokacin) a ɓangaren
adabi a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.
[9] “... may impact positively on the development of the language... Thus, it will lead to greater participation in the media by the majority and facilitate access in mass mobilization for national and regional development.” (Garba, 2013 sh. 125)
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.