Ticker

6/recent/ticker-posts

Kalmomin Fannu a Littafin Bida Da Tanadi a Duniyar Intanet (Sana’o’i, Kasuwanci, Kwadago)

An ciro daga littafin:

BIƊA DA TANADI A DUNIYAR INTANET
(Sana’o’i, Kasuwanci, Ƙwadago)

Na

Abu-Ubaida SANI
Abdulrahman ALIYU

Bida Da Tanadi a Duniyar Intanet (Sana’o’i, Kasuwanci, Kwadago)
Manazartar Littafi: Sani, A-U. & Aliyu, A. (2026). Biɗa Da Tanadi a Duniyar Intanet (Sana'o'i, Kasuwanci, Ƙwadago). Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-978-62480-1-1. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.21361768

Tuntuɓa Domin Samun Littafi: 
Dr. Abu-Ubaida Sani: Imel - abuubaidasani5@gmail.com | WhatsApp - 08133529736
Dr. Abdulrahman Aliyu: WhatsApp - 08036954354

KALMOMIN FANNU

Kalmomin harshen Hausa da dama suna da yalwar ma’anoni. Akan samu kalma guda ta zo da ma’anoni mabambanta musamman yayin da aka yi amfani da ita a wani bagire na musamman. Wannan ɓangare na littafin yana ɗauke da waɗansu muhimman kalmomin fannu da suka shafi ƙunshiyarsa. An kawo ma’anoninsu domin jagoranci ga mai karatu. A cikin wannan littafi, kai tsaye kalmomin suna ɗaukar ma’anonin da aka alaƙanta su da su a matsayin bayanan kalmomin fannu, ko da kuwa suna da waɗansu ma’anonin na daban a wani bagire koma-bayan wanda aka kawo cikin littafin.

Biɗa: Biɗa na nufin duk waɗansu hanyoyi da matakai da dabarun da ake bi domin neman kuɗi ko wani abu da yake da daraja kwatankwacin ta kuɗi.

Duniyar Intanet: Duniyar intanet na nufin farfajiya ko bagiren intanet.

Intanet: Intanet fasaha ce ta zamani wadda ta ƙunshi haɗakar tsauraran al’amura da suka haɗa da harsuna da na’urori da sabis waɗanda haɗuwarsu take samar da al’amari ko bagire da yake tattare da hadahada da fannoni tamkar waɗanda suke duniyar yau-da-kullum, ciki har da abubuwan da suka shafi sadarwa da makarantu da bankuna da kasuwanni da shaguna tare da sauran halittu kamar mutane da dabbobi da waninsu.

Kasuwanci: Kasuwanci fasaha ce ta saye da sayarwa ko musanyen abubuwa masu daraja domin samun riba, ta hanyar bin matakai da dabarun da suka haɗa da gano wurin ɗauko kaya cikin sauƙin farashi da amfani da dabarun talla da jan hankali da tarairayar abokan hulɗa da fikirar daɗin baki a zantukan cinikayya.

Sana’a: Sana’a na nufin hanyar amfani da fasaha da hikima da kayan aiki domin sarrafa wani abu, musamman dangin albarkatu saboda samar da wani abin amfani da za a iya sayarwa ko musanyawa da wani abu mai daraja, ko kuma gyara wani abin da ake mora da ya lalace ko tsaftace muhalli ko jiki, ko gudanar da ayyukan samar da warakar jiki da gamsuwar zuciya domin samun kuɗi ko wani abu mai dajara kwatankwacin na kuɗi.

Tanadi: Tanadi na nufin duk waɗansu matakai da dabarun neman kuɗi ko abinci ko kayan amfanin yau da kullum ko wani abu mai daraja ko amfani ga ɗan’adam, tare da adana shi domin cin moriyarsa a lokacin buƙata ko lokacin da darajarsa ta ƙaru.

Fassarori

Wannan littafin yana ƙunshe da waɗansu kalmomin fannu da ba su da fassarori na gama-gari. Ma’ana, ba a riga da an yi musu takamaiman fassarori da suka sanu a tsakanin ɗalibai da manazarta da masana Hausa ba. A bisa wannan dalili, littafin ya zayyano ire-iren waɗannan kalmomi ko batutuwa tare da bayyana fassarar da aka ba wa kowanne. An yi hakan domin mai karatu ko nazari ya fahimci abin da ake nufi da kowace kalma ko batu.

a. Artificial Intelligence (AI): Ƙirƙirarriyar Basira

b. Availability Check - Tambayar Damar Karɓar Aiki

c. Facebook: Fesbuk

d. Followers - Mabiya (a kafar TikTok)

e. Graph: Giraf

f. Natural: Al’adar Rayuwa

g. Network: Netwok

h. Service: Sabis

i. Subscribers - Mabiya (a kafar YouTube)

j. Translation Tools - Injunan Fassara

k. Twitter: Tuwita

Fassarar Kalmomin Fannin Kuɗaɗe Da Kadarorin Intanet

Akwai kalmomin da suka kasance na fannu, waɗanda suka shafi ɓangaren kuɗaɗe da kadarorin kan intanet. An yi la’akari da siffa da bagire da yanayi wajen samar da fassarar da za ta iya dacewa da kowace kalma.

a. Air Drop - Ruwan Kuɗi

b. Arbitrage Trading - Kasuwancin Bin Kasuwanni

c. Crypto – Kirifto

d. Cryptocurrency – Kuɗin Intanet

e. Day Trading - Kasuwancin Rana

f. Farming - Noman Kuɗi

g. Futures Trading – Kasuwancin Bashi Mai Takunkumi

h. Margin Trading – Kasuwancin Bashi Mai ‘Yanci

i. Mining - Haƙo

j. NFT Trading - Kasuwancin Dauwamammiyar Kadarar Intanet

k. Position Trading – Kasuwancin Doguwar Ajiya

l. Proof of Stake (PoS) - Shaidar Bayar Da Gudummawa

m. Proof of Work (PoW) – Shaidar Aiki

n. Scalping – Kasuwancin Fakafaka

o. Security Deposit - Kafin Alƙalami

p. Spot Trading - Kasuwancin Kuɗi-Hanu

q. Staking - Kulle Kuɗi

r. Swing Trading - Kasuwancin Bin Hawa Da Sauƙar Farashi

s. Trading – Kasuwanci

Taƙaitattun Kalmomi

Littafin yana ƙunshe da waɗansu taƙaitattun kalmomi. Sun haɗa da abajadan sunayen hukumomi (alphabetism) da kuma taƙaita sunayen hukumomi da batutuwa (abbreviation). An kawo ma’anonin ire-irensu a wannan ɓangare na littafin domin yin jagoranci ga mai karatu.

a. BBC: British Braodcasting Corporation

b. DW: Deutsche Welle

c. ND/nd: No date (Ba shekara)

d. P.: Page (Shafi)

e. para.: Sakin layi (paragraph)

f. RFI: Radio France Internationale

g. Sh.: Shafi

h. SL.: Sakin layi

i. VOA: Voice of America

Post a Comment

0 Comments