Ticker

6/recent/ticker-posts

Bida Da Tanadi a Bahaushiyar Al'ada (Neman Kudi Da Tattali a Gargajiyance)

An ciro daga littafin:

BIƊA DA TANADI A DUNIYAR INTANET
(Sana’o’i, Kasuwanci, Ƙwadago)

Na

Abu-Ubaida SANI
Abdulrahman ALIYU

Bida Da Tanadi a Duniyar Intanet (Sana’o’i, Kasuwanci, Kwadago)
Manazartar Littafi: Sani, A-U. & Aliyu, A. (2026). Biɗa Da Tanadi a Duniyar Intanet (Sana'o'i, Kasuwanci, Ƙwadago). Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-978-62480-1-1. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.21361768

Tuntuɓa Domin Samun Littafi: 
Dr. Abu-Ubaida Sani: Imel - abuubaidasani5@gmail.com | WhatsApp - 08133529736
Dr. Abdulrahman Aliyu: WhatsApp - 08036954354

1.2 Biɗa a Bahaushiyar Al’ada

Kalmar biɗa ba ararriya ba ce. Kalma ce ta asali wacce take ɗaukar ma’anar nema kamar yadda Nasiru (2018 sh. 100)[1] ya nuna. Karin harshen Yammacin ƙasar Hausa ne ya fi amfani da wannan kalmar ta biɗa. Takwararta a Hausar Gabas ita ce nema, kamar yadda Sule, (1986 sh. 1986) da Faruk, (2018 sh. 369) suka yi tarayya a kan wannan ra’ayi.[2] Wannan kalma tana da ma’ana ta gama-gari wadda ake iya samu a cikin ƙamus-ƙamus na Hausa. Haka kuma, tana ɗaukar ma’anoni na musamman a waɗansu bagirai na daban, kamar yadda ta fito a rubuce-rubucen masana da manazarta mabambanta.

Ƙamusun Bargery ya ba da ma’anar kalmar da: “... neman wani abu, misali neman ilimi ko neman abinci” Bargery, (1993 sh. 13). Wannan ma’ana ta yi kama da wacce aka bayar a Ƙamusun Jami’ar Bayero Kano. A cikin ƙamusun na Bayero, an bayyana ma’anarta a matsayin: “Binciken wani abu. Daidai da biɗiya ko nema” Sa’id et al., (2006 sh. 47). Idan aka lura, za a fahimci cewa duk ma’anonin ƙamusoshin biyu na gama-gari ne.

Lura da bayanan da aka kawo a sama, a ma’ana ta lugga, biɗa na nufin neman wani abu da yake kusa ko nesa, wanda za a iya samu cikin ƙanƙanin lokaci ko kuma wanda a al’adar rayuwa sai an ɗauki tsawon lokaci kafin a same shi, mai sauƙin samu ko mai wahala.. Binciken Nasiru ya jero waɗansu abubuwa da Hausawa suke fita biɗa da suka haɗa da “fatauci, ci-rani, almajiranci/scholarship, noma, biɗar magani ko mata ko mafaka, asali da kasuwanci” (Nasiru, 2018 sh. 98).

Al’ada da adabin Hausawa cike suke da lamarin biɗa.[3] Fitattun nau’o’in biɗa da suka shahara tsakanin Hausawa sun haɗa da:

a. Biɗar arziki

b. Biɗar aure

c. Biɗar buwaya

d. Biɗar dabarun zaman duniya

e. Biɗar ɗaukaka

f. Biɗar ilimi

g. Biɗar magani

h. Biɗar raba gardama

i. Biɗar sa’a

j. Biɗar sarauta/matsayi (Faruk, 2016 sh. 148); (Faruk, 2017 sh. 69-77); (Nasiru, 2018 sh. 101-102)

Wannan littafin ya mayar da hankali ne a kan na farko a cikin waɗannan nau’o’in biɗa, wato biɗar arziki. Idan aka ce biɗar arziki kuwa, ana nufin duk waɗansu hanyoyi da matakai da dabarun da ake bi domin neman kuɗi ko wani abu da yake da daraja kwatankwacin tasa .

Wani muhimmin abin lura a nan shi ne, za a iya kallon biɗar arziki ta fuskoki guda biyu. Da farko dai akwai biɗar arzikin shi kansa. Wannan kuwa ya shafi duk wata sana’a ko wani kasuwanci ko fatauci da mutum zai runguma domin inganta tattalin arzikinsa. Yana kuma iya kasancewa taron jama’a ne suka haɗa kai ko kuma ma ƙasa gaba ɗaya, suka duƙufa kan sana’a ko kasuwanci ko fatauci, duk dai domin inganta tattalin arziki. A taƙaice, duk wani yunƙuri na neman kuɗi da sauran al’amuran da suka shafi wadata da walwalar rayuwa, to ana iya kiran su da biɗar arziki. A bisa wannan, idan aka ambaci biɗa, hankali zai koma kan waɗannan:

i.Sana’ar da za a yi domin biɗar kuɗi

ii.Kasuwanci da za a yi domin biɗar riba

iii.Fatauci da za a yi domin biɗar riba

A ɓangare guda kuwa, ana iya samun biɗa a cikin su kansu hanyoyin biɗar arziki (sana’o’i da kasuwanci da fatauci) Misali:

1. Sana’a

a. Biɗar ilimin gudanar da sana’a

b. Biɗar kayan gudanar da sana’a

c. Biɗar wurin gudanar da sana’a

d. Biɗar masu sayen abubuwan da aka samar (masu ciniki)

e. Biɗar hanyoyi da matakan yin fice da buwaya kan sana’a

2. Kasuwanci

a. Biɗar ilimin gudanar da kasuwanci

b. Biɗar jarin gudanar da kasuwanci

c. Biɗar wuri ko wuraren gudanar da kasuwanci

d. Biɗar abokan gudanar da kasuwanci (masu sayen kaya)

e. Biɗar matakan inganta kasuwanci

3. Fatauci

a. Biɗar ilimin gudanar da fatauci

b. Biɗar abokan fatauci

c. Biɗar jarin yin fatauci

d. Biɗar abubuwan da ake buƙata yayin fatauci (dangin tafiye-tafiye da kare kai da sauransu)

La’akari da waɗannan, za a iya kallon biɗa a matsayin babban ginshiƙin da yake tallafe da tattalin ariƙin al’umma. Ga al’ummar Hausawa, biɗa ce ta kasance ƙashin bayan tattalin arzikinsu tun inda aka fito har zuwa yau. Daga cikin dalilan da suke tabbatar da hakan akwai:

a. Ta hanyar biɗa ne Hausawa suka samu kasuwanci da sana’o’i da sauran hanyoyin dogaro da kai.

b. Ta hanyar biɗa ne Hausawa suka samu dabaru da magungunan buwaya domin bunƙasa tattalin arzikinsu.[4]

1.3 Tanadi a Kadadar Al’adun Hausawa

Kalmar tanadi ba baƙuwa ba ce ga kunnuwa da bakunan Hausawa. Ta samo asali ne daga tanada. Ita kuwa kalmar tanada kamar yadda Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero, Kano ya kawo ma’anarta a luggance, tana nufin: “(i) Shirya ko adana (ii) Ajiye wani abu saboda ɓacin rana, daidai da tattala” (Sa’id et al., 2006 sh. 425).[5] A farfajiyar wannan bincike kuwa, tanadi na nufin duk waɗansu matakai da dabarun neman kuɗi ko abinci ko kayan amfanin yau da kullum ko wani abu mai daraja ko amfani ga ɗan’adam, tare da adana shi domin cin moriyarsa a lokacin buƙata ko lokacin da darajarsa ta ƙaru. Shi ma tanadi za a iya kallon sa ta manyan fuskoki guda biyu kamar haka:

1. Tanadin Kayan Biɗa: Kamar yadda aka yi bayanin biɗa a baya (a ƙarƙashin 1.2), akwai tanade-tanade da ake gudanarwa yayin fara biɗa. A wannan ɓangare, biɗa da tanadi suna faruwa lokaci guda. Ma’ana a nan ita ce, yayin da za a tanadi kayan da ake buƙata domin aiwatar da sana’a, to biɗo kayan ake yi. Haka ma idan aka ce za a biɗo kayan gudanar da sana’o’i, to maƙasudin bai wuce tanadin su domin gudanar da sana’o’in ba. A taƙaice za a iya lura da cewa, tanadin kayan biɗa ya shafi:

a. Tanada kayayyakin da ake buƙata yayin aiwatar da sana’a: Mai gudanar da sana’a yana buƙatar tanadar waɗansu kayayyakin aiki. Misali a nan shi ne, maƙeri zai nemi awartaki da uwar maƙera da gawayi da guduma da sauransu, domin gudanar da sana’ar ƙira.

b. Tanadin kayayyakin da ake buƙata yayin gudanar da kasuwanci: Kasuwanci da dama na buƙatar a yi musu tanadin kayayyaki ko abubuwan da za su taimaka wajen gudanuwarsu. Misalin wannan shi ne yadda mai kasa goro ya sayar yake neman faifayi da algarara da hitta da sauransu.

c. Tanadi domin fatauci: Za a iya ganin misalin wannan cikin yadda fatake suke tanadar dabbobin hawa ko na ɗaukar kaya. Sun haɗa da jakai da dawaki da raƙuma da kuma alfadarai.

2. Tanadin Arziki: Arziki a nan ya shafi kuɗi da dukiya da kadara. A taƙaice, ya haɗa da duk wani abu mai darajar da za a iya sanya wa farashi. Tanadin arziki a nan yana nufin tanadin kuɗi ko wani abu da za a iya sayarwa a samu kuɗi domin amfani da su a lokacin da buƙatar hakan ta taso. Tun inda aka fito, Bahaushe yana amfani da wasu hanyoyi da dabaru domin tanadar kuɗin da zai yi lalurori ko biyan buƙatu na musamman. Ire-iren buƙatun da Bahaushe yake yi wa tanadi sun haɗa da:

a. Aure

b. Bukukuwa

c. Doguwar tafiya (guzuri)

d. Haihuwa

e. Ƙaura

f. Samun jari

Yayin gudanar da ɗaya daga cikin waɗannan hidindimu (da ma wasu makamantansu), akwai buƙatar kuɗi. Hausawa sun ce: “Mai kwarmin ido da wuri yake fara kuka.” Bugu da ƙari: “Don tuwon gobe ake wanke tukunya.” Kamar haka ne Bahaushe yake fara tanadi tun da wuri yayin da yake fuskantar wani al’amari da yake da buƙatar kuɗaɗe masu kauri. Daga cikin fitattun hanyoyin da yake bi domin tanadi a gargajiyance akwai:

A. Adashe: Akan yi adashe domin gudanar da wani aiki mai muhimmanci yayin da aka kwashe shi .

B. Ajiya: Bahaushe ya gama magana inda ya ce: “Ajiya maganin wata rana.” Akan ajiye wata kadara ko dukiya domin yin amfani da ita yayin da wata buƙata ta musamman ta taso.[6]

C. Ajo: Ajo a nan na nufin gudummuwa da ake kaiwa yayin biki, musamman da nufin ko sa ido kan rama biki[7] yayin da hidimar wadda ta kai ajon ta taso. Wannan na nuna cewa, kai ajo tamkar ajiya ce M.M. Hamma (keɓantacciyar tattaunawa, 4 ga watan Janairu 2024).[8]

D. Asusu: Akan yi asusu domin wata hidima ta musamman. Yayin da hidimar ta zo sai a fasa asusu a biya buƙata. Ba don wannan tanadi ba ta hanyar asusu, to kuwa da wuya a samu adadin kuɗaɗen da ake buƙata kai tsaye a yi hidimar.

E. Turka: Turka a nan na nufin kiwata wata dabba musamman domin sayarwa tare da yin amfani da kuɗin yayin biyan wata buƙata ta musamman. Ana kuma iya yin turka a matsayin tanadin abin yanka lokacin salla ko wasu bukukuwa da sauransu.

Lura da duka waɗannan bayanai, biɗa da tanadin Hausawa a wannan bagire ya shafi manyan kalmomin tattalin arziki ne guda uku (3). Kalmomin su ne:

a. Kasuwanci

b. Sana’a

c. Tanadi 

Rubuce-rubucen ilimi masu yawa a fannin nazarin al’adun Hausawa sun tattauna waɗannan batutuwa.[9] An samu saɓanin ra’ayi game da ma’anoni da siffofi da abubuwan da suka ƙunsa. A gaba a cikin wannan littafin, za a ga ire-iren rubuce-rubucen. Bugu da ƙari, littafin ya yi ƙoƙarin samar da wata fahimta daga haɗakar ra’ayoyinsu ta hanyar lura da alƙaluma daban-daban.




[1] Ya nuna cewa, daidai take da kalmar quest ko search a Ingilishi, ko kuma kalmar cherche a Faransanci.

[2] Duk sun tafi kan cewa, ana amfani da kalmar biɗa ne a Hausar yankunan yammacin Ƙasar Hausa kamar su Sakkwato da Zamfara da Kabi da Katsina da waɗansu sassan Jamhuriyar Nijar Sule, (1986 sh. 1986) da Faruk, (2018 sh. 369).

[3] Ko cikin karin maganganun Hausawa, ana iya kallon yadda lamarin biɗa ya ratsa. Karin maganganu game da biɗa da ake yawan ji a bakunan Hausawa sun haɗa da:

1. A rashin kira karen bebe ya ɓata

2. A rashin tayi akan bar araha

3. Bar ganin ka tara, ka kiyayi mai nema

4. Kowa ya ci zomo ya ci gudu

5. Sana’a goma maganin mai gasa

6. Tafiya mabuɗin ilimi

7. Zafin nema ba ya kawo samu

8. Zomo ba ya kamuwa daga zaune

[4] A duba Faruk (2017) da Nasiru (2018) domin samun ƙarin bayani game da biɗar magani.

[5] Tanadi abu ne mai muhimmanci ga Hausawa. Za a iya kallon hakan a cikin adabin Hausa. Misali, karin maganganun Hausa da dama na nuni ga muhimmancin tanadi a rayuwa. Daga ciki akwai:

a. Bawan damina, attajirin rani

b. Don gobe ake wankan dare

c. Don tuwon gobe ake wanke tukunya

[6] Yayin da ajiya ta shafi kuɗi, musamman waɗanda ake tarawa sannu a hankali, to ana iya kiran ta asusu.

[7] “Rama biki na nufin kai ajo ga wacce ta taɓa kawo miki.” M.M. Hamma (keɓantacciyar tattaunawa, 4 ga watan Janairu 2024). Ma’ana a nan ita ce, yayin da wata ta kai wa ‘yar uwarta gudummuwa yayin wata hidimarta ‘, to ta kai ajo. Yayin da ita ‘yar uwar ta kawo mata gudummuwa lokacin da hidimarta ta taso, to ta rama biki ke nan.

[8] A cewar M.M. Hamma (keɓantacciyar tattaunawa, 4 ga watan Janairu 2024), mata ne suka fi yin ajo. Ta bayyana cewa: “A lokacin bukukuwa, duk gudummuwar da aka kai wa mace, to za ta lura da waɗanda suka kawo da kuma abubuwan da suka kawo. Su ma idan hidimarsu ta taso, to za ta kai musu kwatankwacin wannan ko abin da ya haura shi.”

[9] Rubuce-rubucen da suka tattauna hanyoyin biɗa da tanadin Hausawa sun haɗa da Asiru, 2009; Sallau, 2009; Dalijam, 2012; Mika’il, 2017; Aliyu, 2018; Rambo, 2018; Nasir, 2021; Shehu, 2022.

Post a Comment

0 Comments