An Ciro Daga: Bakura, A.R., & Sani, A-U. (2026). Zogale a ƙasar Hausa: Magani, abinci, tattalin arziki. SAS Publishers. ISBN: 978-978-63958-1-4. https://doi.org/10.5281/zenodo.22682300
Ƙurajen Jiki
Kalmar ƙurji Bahaushiyar kalma ce da take cikin jerin
kalmomi jinsin sunayen maza. Jam’inta
kuwa
shi ne, ƙurarraji ko ƙuraje. Kalmar
tana ɗauke
da ma’anoni kamar haka:
(i). Ƙaramin kumburi da yakan fito a jikin
mutum ya ɗuri ruwa
(ii). Ciwo ko ƙaramin gyambo
(iii). Lahani a jikin abu
(BUK, 2006 sh. 286)
Shi kuwa Abubakar (2015 sh. 315)
ya bayyana kalmar
a matsayin: “ciwo a fatar jiki mai kamar ɓullar
wata ƙwayar tsakuwa ko ta hatsi.” A ma’anarsa
ta biyu kuwa cewa ya yi: “Ɗan
fasasshen ciwo a jiki.” La’akari da waɗannan ma’anonin, ana iya cewa ƙurji wani
kumburi ne da yakan ɓullo a sassan jiki ya ɗuri ruwa sakamakon
wata cuta.
Idan mutun yana fama da ƙuraje a jikinsa, sai ya nemi garin
zogale, ya haɗa da man zaitun ya kwaɓa.
Daga nan sai ya riƙa shafawa
a jiki. Zai sami waraka insha Allah (Hayin Gulbi, 2015). Axe (2016) ya bayyana
zogale yana magance matsalar ƙurajen
jiki.
Ciwon
Haƙora
Haƙori Bahaushiyar kalma ce da take cikin jerin
kalmomin Hausa jinsin sunaye na maza, jam’i kuwa haƙora. Haƙori kuwa yana nufin wani farin ƙashi mai ƙarfin
gaske da yake kafe a baki wanda ake tauna abinci da shi. A wani karin harshe kamar Sakkwatanci, akan kira shi haure.
Shi kuwa wanda yake fama da
matsalar ciwon haƙori,
sai ya nemo ƙaron (jirrai/jillan) zogale,
ya liƙa a inda yake ciwon (Jinju, 1990 sh. 23)
da (Hayin Gulbi, 2015). Wannan ba abin al’ajabi ba ne in aka yi la’akari da
irin sinadaren da suke ƙunshe
cikin zogale waɗanda
suka
ruɓanya
na cikin madara da ayaba da lemun zaƙi da
karas, alhali duk suna da fa’ida ga haƙori.
Ciwon
Ɗankakkare
Ɗankakkare
ciwo ne da yake shafar yatsun hannu ko na ƙafa.
Akan kuma kira shi da lafazin karkare. A irin wannan yanayi ne yatsa yakan kumbura, ya riƙa
ciwo da zogi (raɗaɗi)
mai tsananin gaske, har sai wurin ya ja ruwa, wanda yake bayar da damar yin sakiya.
Ana amfani da ganyen zogale
wajen maganin wannan cuta. Mai fama da wannan lalurar sai ya samo ganyen zogale,
ya muttsuka shi, sannan ya saka
kanwa, ya ƙunsa a yatsan da yake ciwo, kamar yadda ake ƙunsa (ɗaura)
lalle. Da izinin Allah, cikin ‘yan kwanaki kaɗan
kumburin zai sace ya kuma daina raɗaɗi
sai wurin ya ƙafe (bushe). A
binciken Godinez (2015) an tabbatar zogale yana yaƙar kumburi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.