Ticker

6/recent/ticker-posts

Maganin Ciwon Ido Da Kunne Da Ciwon Kai Ta Amfani Da Zogale

An Ciro Daga: Bakura, A.R., & Sani, A-U. (2026). Zogale a ƙasar Hausa: Magani, abinci, tattalin arziki. SAS Publishers. ISBN: 978-978-63958-1-4. https://doi.org/10.5281/zenodo.22682300

 Na

Adamu Rabi’u Bakura

Da

Abu-Ubaida Sani

Zogale a Kasar Hausa: Magani, Abinci, Tattalin Arziki

Ciwon Ido da Kunne

Kafin a ce wani abu, zai fi dacewa a bayyana abin da ake nufi da kalmar ciwo, yin haka zai ba mai karatu damar saurin fahimtar inda aka dosa. Ciwo kalma ce Bahaushiya da take cikin jerin kalmomin Hausa jinsin namiji., Jam’inta kuwa shi ne ciwace-ciwace ko cuce-cuce ko kuma ciwuwwuka. Kalmar tana ɗauke da ma’anar rashin lafiya ko rauni ko ɓacin rai, haka kuma kalmar tana nufin wata nau’in mujiya. Garba, (1990 sh. 29) ya bayyana ma’anar kalmar da zafi, a matsayin ƙari bisa ga bayanin da ya gabata.

Ta la’akari da abin da masana suka bayyana, tare da dubi wannan fagen bincike, za a iya bayyana ma’anar kalmar a matsayin wadda take nufin rashin samun sukunin jin daɗin jiki da yake wanzar da zafi da raɗaɗi a wani ɓangaren jiki ko jikin baki ɗaya.

Yayin da mutum yake fama da lalurar ciwo ido ko kunne, sai ya ɗebo ɗanyen ganyen zogale. Ya murza, ya matse ruwan ya dinga ɗigawa a ido ko a kunne, insha Allah za a samu lafiya kamar yadda (Jinju, 1990 sh. 19) da (Tulawa Hayin Gulbi, 2015) suka nuna. Binciken Samuel (2013) ya tabbatar da cewa zogale yana ƙara lafiyar idanu.

Ciwon Kai

Ga mai fama da lalurar ciwon kai, sai ya nemi ɗanyen ganyen zogale, ya murtsuka shi ya shafa a goshinsa. Da izinin Allah zai sami waraka, kamar yadda Tulawa Hayin Gulbi (2015) ya nuna. Axe (2016) ya tabbatar da zogale yana maganin matsanancin ciwon kai. 

Post a Comment

0 Comments