An Ciro Daga: Bakura, A.R., & Sani, A-U. (2026). Zogale a ƙasar Hausa: Magani, abinci, tattalin arziki. SAS Publishers. ISBN: 978-978-63958-1-4. https://doi.org/10.5281/zenodo.22682300
Harbin
Kunama
Kalmar harbi, Bahaushiyar kalma ce da take cikin jerin
kalmomin aikatau. Takan ɗauki wasullan /e/, /i/, /o/,
/u/. Kalmar
tana ƙunshe da ma’anoni kamar haka:
(i). Jefe mutum ko dabba ta hanyar
amfani da bindiga ko kibiya
(ii). Sa wa wani mutun cuta
ta hanyar saduwa (jima’i)
(iii). Duka da ƙafa
(iv). Suka da ƙari (BUK, 2006 sh. 196).
A wannan bagiren abin nufi
da harbi shi ne cizon da kunama takan yi wa mutun a wani sashen jikinsa da ƙarinta tare da sakar masa ruwan dafi.
Idan kunama ta harbi mutum (Allah ya tsare), sai a nemo ganyen zogale, a murmurza
tare da turare, sai a saka a daidai wurin da ta yi harbi. In Allah ya so za ta
faɗi ba
tare da jinkiri ba (Hayin Gulbi, 2015).
Tsayar
Da Zubar Jini
Ta fuskar dakatar da jini
daga zuba kuwa, nan ma zogale
a ba a baya take ba. Domin in mutum ya yi
rauni ta hanyar yanka ko sara ko tuntuɓe
wanda har ya haifar da kwararar jini, sai a sami ganyen zogale ɗanye,
a muttsika shi, a shafa ruwan a
wurin raunin. In Allah ya so jinin zai daina zuba (Hayin Gulbi, 2015).
Shi kuma Godinez (2015) ya bayyana shan garin yana dakatar da zubar jini.
Rauni
Ko Gyambo
A nan an kawo kalmomi guda biyu masu ɗauke da ma’ana
kusan ɗaya ko ma a ce guda . Za a kawo ma’anonin kalmomin, ɗaya bayan ɗaya domin mai
karatu ya yi saurin fahimtar inda aka dosa. Yayin da aka dubi kalmar rauni
za a tarar tana cikin jerin kalmomin Hausa jinsin sunaye maza, jam’i kuwa raunuka.
Tana ƙunshe da ma’anar jin ciwo
musamman ta fashewar fata da zubar jini.
Gyambo kuwa, Bahaushiyar
kalma ce da take cikin jerin sunaye jinsin maza, jam’i kuwa gyambuna. Tana
ɗauke da ma’anar
ciwo mai fitar da mugunya, musamman a ƙafar mutum, wanda
ya daɗe bai warke ba. Ita
kuwa kalmar mugunya, ta kasance cikin jerin kalmomin Hausa jinsin mata. Tana
ƙunshe da ma’anar ruwan ƙurji mai launin fari.
Wanda ya ji ciwo har fatar jikinsa ta fashe tare da zubar jini, ko kuma
yana da wani miki (ciwo) a ƙafa da ya daɗe bai warke ba, lamarin
ya kai yana fitar da mugunya (ruwan ƙurji mai launin
fari) - sai a nemi garin zogale a zuba a kan raunin ko gyambon. Insha
Allahu zai yi saurin warkewa (Hayin Gulbi, 2015) da (Maikano Bakura, 2015).
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.