An Ciro Daga: Bakura, A.R., & Sani, A-U. (2026). Zogale a ƙasar Hausa: Magani, abinci, tattalin arziki. SAS Publishers. ISBN: 978-978-63958-1-4. https://doi.org/10.5281/zenodo.22682300
Sanyin
Ƙashi Da Kumburi
Mai fama da lalurar sanyin ƙashi ko kumburin jiki, sai ya nemo
‘ya’yan zogale a soya, sannan a daka har su zama gari. Za a haɗa
garin da man kwakwa a rinƙa
shafawa a wurin da lalurar take (Maikano Bakura 2015). Haka kuma binciken
Godine (2015) ya tabbatar da shan garin zogale yana yaƙar kumburi. Masanin
bai ayyana kimanin yawan da za a sha ba.
Sanyin
Ƙashi
A wannan nau’in kuwa, za a
sami saiwar zogale da tafarnuwa a kirɓe su.
Daga nan sai a dinga haɗawa da man tega ana shafawa
a ƙafa sau uku (3) a rana, har tsawon kwana
bakwai. Za a sami sauƙi da
ikon Allah (Maikano Bakura, 2015).
Ana kuma kwaɓa
garin zogale tare da manja, a riƙa
shafawa a wurin da ake jin raɗaɗi (Hayin
Gulbi, 2015).
Gyambon
Ciki (Olsa)
A dafa ganyen zogale da zuma
a sha kamar shayi, sau uku a rana, don maganin gyambon ciki. Haka kuma ana cin
‘ya’yan zogale. An jaraba shi, kuma cikin ikon Allah an samu cikakkiyar lafiya
(Ibrahim Maru, 2015). A yayin da Axe (2016) yake bayanin amfanin da zogale take yi, ya nuna cewa tana magance matsalar ciwon olsa da ke addabar
al’umma.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.