An Ciro Daga: Bakura, A.R., & Sani, A-U. (2026). Zogale a ƙasar Hausa: Magani, abinci, tattalin arziki. SAS Publishers. ISBN: 978-978-63958-1-4. https://doi.org/10.5281/zenodo.22682300
Ciwon
Sanyi
Kalmar sanyi Bahaushiyar kalma ce da take cikin jerin kalmomi jinsin sunaye na
maza. Tana ɗauke da ma’anar wani nau’in ciwo da yake wanzar da sagewar gaɓa ko gaɓoɓin jiki sakamakon wata cuta
da sanyin yakan haifar.
Mai fama
da matsalar sanyi, zai nemi ganyen zogale, ya dafa tare da jar kanwa ‘yar kaɗan. Za a tace sannan mai
ciwon ya rinƙa shan ruwan moɗa (kofi) ɗaya, sau biyu (2) a rana ga babban mutum. Yaro
kuwa ya sha rabin moɗa sau biyu a yini (Jinju, 1990 sh. 66). A nan, ruwan da
aka dafa zogalen shi
ne maganin. Yayin da shi kuma dafaffen zogale yakan zama abinci, ya kuma yi
rigakafin wata cuta ta daban da ba ta bayyana ba.
Haka kuma
ana tafasa furen zogale tare da albasa, a rinƙa sha
kamar shayi, don magance ciwon sanyi (Hayin Gulbi, 2015).
Idan
ciwon sanyi ya yi yawa, yakan shafi hanyar mafitsara, sakamakon da yakan haifar da wahala ainun kafin fitsari ya fito. Wani lokaci ma
fitsarin yakan faskara fita. Zai zaman maras lafiya yana jin fitsari amma ko ya
je ya duƙa (tsugunna) domin yin fitsarin sai abin ya gagara. A irin wannan
yanayi, sai a nemi saiwoyin zogale, a wanke su sosai domin a tsabtace su. A kuma sami
ruwan tsami da aka tsiyayo daga ƙullun gero, sai a jiƙa sayyun a ciki, idan sun jiƙa, sai maras lafiyan ya sha
moɗa ɗaya (1). Da izinin Allah
cikin ɗan ƙanƙanin lokaci fitsarin zai fito (Junju, 1990 sh. 66) da (Hayin
Gulbi, 2015).
Kasancewar ƙwayoyin cutar suna rayuwa
ne a cikin jikin mutun kaɗai, mace ko namiji ba mai
kamuwa da cutar sai ya yi jima’i da mai ita. Ana kuma iya kamuwa da ciwon yayin
da aka samu shafar ƙwayoyin cutar da suke hadda shi. Alamar cutar ya haɗa da:
a. Mutum ya rinƙa jin zafi idan zai yi fitsari.
b. Wani farin ruwa zai dinga fita daga al’aurar mai cutar.
Aibin cutar:
a. Idan ba a magance cutar da sauri ba, zafin zai ci gaba
da ƙaruwa.
b. Mutum zai yi ta jin fitsari, yayin da ya tafi yin sa ,
sai ya kasa yi sosai.
c. Yayin da kafar mafitsarar ta toshe yakan haifar da
salwantar rayuwa.
d. Takan haifar da rashin haihuwa.
e. Takan kawo amosani.
f. Takan wanzar da mummunan ciwon idon da kan haifar da
makanta.
Rigakafin cutar:
a. Ƙaurace wa aikata zina.
b. Yayin da za a yi aure, a tafi asibiti domin binciken
lafiyar ma’auratan, saboda maras lafiyar takan iya harba wa mai lafiya cutar ta
hanyar jima’i. Irin haka ne yake sa wasu ba sa haihuwa (East da Imam, 2007 sh.
371).
Idan namiji ya harbu da ƙwayar cutar, sai a nemo saiwoyin zogale wadda ba ta daɗe da tsira ba. Sayyun za a ɓare/kwanɗare ɓawonsu, sannan a dake su cikin turmi tare da jar kanwa. A yi kunun dawa, sai a ɗebo garin maganin a saka a cikin kunun. Maras lafiya zai riƙa shan kunun domin maganin wannan cutar ta sanyi (Hayin Gulbi, 2015).
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.